← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 198

Sashe 125

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wucewa yayi ya barshi nan, tare da yaron da ya zo suka tafi shi a motar lieutenant har suka isa. Yayi mamaki sosai da aka ce wai Ammar na son ganinshi, Ammar dai daya sani? A gaskiya ba dan Ammar d'aya ya sani ba a duniya idan ka cire *sahabi Ammar bin Yaseer wanda suka fara shahada a musulunci* da sai yace shine amma ba nashi ba, dan nashi in ya zo kai tsaye yake shiga ko da yana tare da bak'i ne, izinin shigowa yasa aka masa, saida ya ganshi ya dai tabbatar shi d'in ne, cikin nutsuwa ya zauna kan kujerar dake fuskantarshi ya bashi makullan yace "Abba gashi, nagode."

Shima cikin yanayin kulawa yace "Har ka dawo ne? To ya ake ciki?"

"Ba komai Abba." Ya fad'a babu walwala tare dashi, saida ya gyara zama ya kalli lieutenant yace "Abba, akwai wata masaniya da nake son baku kan wani mutum, bansan ko kana so ba?"

Kallonshi yayi da murmushi, ko ma wanene tashi ta k'are cewar lieutenant, amma sai yace "Zamu so mana idan ya shafi aikinmu."

Sai kuma kawai ya mik'e zai fita yace "Shikenan, zan nemo." K'ofa ya tunkara lieutenant ya bishi da kallo, me yake nufi kuma? Ganin zai fita yasa yace "Ammar."

Juyowa yayi da fad'in "Na'am." Saida ya kalli agogo yace "Da k'arfe hud'u na yamma ka same ni gidan gona ta dake kusa da *Olga oil*."

Da d'an murmusawa yace "To Abba."

Fita yayi da wayarshi a hannu yana neman wata lamba, saida ya shiga mota ya zauna sannan ya aika kiran, bayan an d'auka sun gaisa ya fara mishi wasu tambayoyi, sun d'an jima suna magana kafin daga bisani yace "Ka tabbatar motar kayanshi ce ake d'orawa?"

Daga d'aya b'angaren aka ce "Na tabbata yallab'ai."

"Ya yanayin lodin yake?" Ya tambaya, daga can tace mishi "Eh to, kwalayan (karton) indomie ne da lipton, sai atampopi daga sama da shadda, sai kuma buhunan shinkafa a sama."

Wani murmushin da shi kad'ai yasan ma'anarshi yayi yace"Nagode, zan sake kiranka."

Yana kashewa ya tayar da motar ya d'auki hanyar, wannan binciken k'wak'wafin shi ya wuni yana yi, daga nan zuwa can daga can zuwa nan, waya kuma har ya gaji da amsawa duk saboda son kawo k'arshenshi, sai misalin *12:30* ya d'auki hanyar komawa gida cike da gajiya, kai tsaye b'angarenshi ya nufa da makulli a hannu da waya, da wata zazzak'ar sallama ya shiga sai dai babu kowa bare bare a amsa mishi, falon yasha gyara sai k'amshin turaren wuta yake na jonawaa lantarki, ga kwanukan abinci da aka jera wurin ya k'ayatu, murmushi kawai yayi ya aje makullin da waya akan teburin tsakiyar falon ya shiga d'akinta. Tana tsaye gaban madubi tana d'aure k'ananan kitsonta, yana ganinta ya fad'ad'a murmushinshi da fad'in "Wow, duniyata."

Da sauri ta juyo ta kalleshi, murmushi tayi ita ma tare da takowa cike da kunyar kayan data saka, tana zuwa ta narke a jikinshi tana sauke numfashi a hankali, ni'imtaccen k'amshinshi turarenshi ne ke ratsa hancinta, shafata yake tare da mamatsa bayanta yana cika hannu da tsokar bayanta ido rufe, har tsakiyar kanshi yake jin duk wasu albarkatun jikinta na sake samun matsuguni a na shi jikin, turaren na kwantar mishi da hankali sosai, a hankali ta d'ago kai ta kalleshi, kallon tattausan fuskarsa wacce ke canza launi duk sanda ta so yasa ta lumshe ido, saida ta d'aga k'afafunta ta kai bakinta daidai na shi ta sumbata, babu wata k'ara ko sauti, saidai tasirin sumbar yasa ya lumshe ido, lokaci d'aya suka bud'e ido a tare suka kalli juna, murmushi ta sakar masa tace "Ka gaji ko yah Ammar?"

Girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace "A'a ba yah Ammar ba, ki saka min wani sunan na daban."

Saida ta jujjuya matsakaitan idonta tace "Umm! Kamar wane kenan kake so?"

Murmushi ya mata yace "A ganinki wane sunan na cancanta? Ni dai kinga na baki sunan duniyata, saboda kin zama dunuyata, ni kuma fa me na zama naki?"

Saida ta k'ara rik'e k'ugunshi da kyau da hannayenta tana kallon k'asumbarshi sannan tace "Nima ka zama duniyata, sabuwar rayuwata kuma farin cikina."

Raba jikinshi yayi da na ta ya d'an turata gefe ya k'ura mata ido, kallonta yake kamar zai had'iyeta, dogon wandon jeans bleue dark da riga bleue light mai hannaye iya damtse, dogayen takalmi bak'ak'e sai yar gajerar kwalliya da tayi, juyawa yayi yana zagayata dan ganinta da kyau, masha Allah duk da tana da gaba sosai, amma kuma sama suke can mak'ale da k'irji, bayan nan kam tubarkallah yau data saka wando ya zauna mata daram akansu sai abun ya bayar da citta. Kiran sallah a masallacin dake jikin gidan nan ne yasa yace "Bari na dawo daga masallaci, ina nan tare dake sai la'asar zan fita."

Ban d'akinta ya fad'a yayi alwala ya fito, gabanta ya tsaya ya danna mata wata mahaukaciyar sumba a goshi sannan yace"Saina dawo."

Tare suka fito daga d'akin shi ya fita ita kuma ta zauna zaman jiranshi.

Tunda Ummy ta shiga d'aki bata sake fitowa ba, har asibiti ake ta kiranta wasu k'ananan ma'aikatan na tambayarta kan wani abu idan ya shige musu duhu, har akayi sallah azahar aka gama bata fito ba, damuwa da halin da take ciki yasa Zeituna shiga d'akinta dan ta gani, da sallama ta shiga Ummy kuma naji bata amsa ba, dan haka bata shiga ba saita tsaya daga k'ofar tace "Ummy Ammar kina lafiya? Naga har anyi sallah kuma baki fito ba."

Tasowa tayi daga inda take ta zo ta bud'e k'ofa, kallon kallo sukayi sai yanayin damuwa tare da ita, cike da kulawa tace "Ummyn Ammar lafiya ko? Ko ba kya jin dad'i ne?"

Saida ta rufe d'akin ta fito ta fuskanceta sai kawai ta d'auketa da wani wawan mari, dafe kumci tayi lokaci d'aya ta saki k'ara, Zeinabu da fitowarta kenan daga sallah taji saukar marin, da sauri ta matso tana kallonsu da mamaki, Nana ma dake kan ajiye abinci a tebur ita ma k'ura musu ido tayi, Inna ma saukar marin taji ta tsaya, ba tare data bari ta d'ago ba Ummy ta nunata da yatsa tace "Wannan shine abinda ke faruwa, bana son munarfici da iyayin tsiya."

Tsaki tayi ta bita da harara ta fita harabar gidan, Zeituna data kasa had'a ido da ita saida taga fitarta ta tafi a guje d'akinta, Inna ce ta bi bayanta har d'akinta, tana zuwa ta sameta ta zauna kusanta tace "Amarya kiyi hak'uri, hakan zaman ya gada dama indai ance zo mu zauna to zo mu sab'a ne."

Saida ta share hawaye sosai ta kalli Inna tace "Ba komai Inna, ni ai ba bak'uwar zafi bace, kawai ki kwantar da hankalinki."

Murmushi tayi tace "Hakane amarya, Allah ya baki hak'uri da juriya, insha Allahu zaki zama fitilar gidan nan da zata haskaka kowa."

Murmushi ita ma tayi tace "Ameen Inna."

Tashi tayi tace "Ni zan koma wajen aiki."

Zata fita daf da k'ofa suka had'u da lieutenant zai shigo, gyara mata yayi ta wuce tana mishi sannu da zuwa, amsawa yayi da mutumtawa kafin ta fice shi ya shigo, da kulawa ya kafeta da ido ganin kamar tayi kuka yace "Lafiya amaryata? Meya sameki?"

Da murmushi tace masa "Sannu da zuwa, amma yana ganka a wannan lokacin?"

Matso da ita yayi gabanshi yana shafa fuskarta yace "Meya same ki Zeituna?"

"Ba komai fa." Ta fad'a tana neman zillewa, sake rik'ota yayi yace "Ni fa ba yaro bane, kinsan da haka?"

Kallonshi tayi cike da yamutsa fuska tace "Ciki na ne yake d'an min ciwo, amma kuma yanzu ya daina."

"Kin tabbata ya daina?" Cike da tabbatarwa tace "Ya daina."
Sakinta yayi ya nufi wajen wata drower dan d'aukar abinda ya kawoshi.

*Bayan* sallah la'asar ya gama shiryawa zaije gidan gonar, a falo ya sameta da wayarta a hannu, yana zuwa ya sunkuya ya sumbaci bakinta ya d'ago, kallonshi tayi tace "Sir har ka shirya?"

Saida ya shafi k'asumbarshi ya tsaya da kyau gabanta yace "To ya? Nayi kyau ne?"

Saida ta mishi da hannu👌tace "Ka had'u ba kad'an ba, sai fatan Allah ya kad'e idon mak'iya a kanka."

Murmushi ya mata ya juya yace "Saina dawo."

Mik'ewa tayi tabi bayanshi har bakin k'ofa, saida ya sake rumgume ta sannan ya juya zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo, kallonta yayi yace "Kin kira kankana ne tunda ta tafi?"

Saida ta d'an bud'a baki tace "A'a."

"Me yasa?" Ya tambaya yana kafeta da ido, saida ta turo baki tace "Yah Ammar k'aryata ni fa tayi gaban mutane, bayan kuma nasan bata son tafiya."

Saida ya wani tausasa murya yace "To sai me? Ki kirata kiji ya take, kinji ko?"

Yana fad'a ya fita ya barta, ciki ta dawo ta d'auki wayarta ta zauna ta kira yer uwarta, a lokacin bata tunanin ganin kiran Amna amma sai gashi ta gani, da farin ciki ta d'auka ta kara a kunne tace "Banyi tunanin zaki kira ni ba?"

Daga b'angaren Amna tace "Pourquoi?"

Daga kwance Hamna tace "Parce que je sais qui tu est."

Murmushi tayi ta gyara zama tana fad'in "Kamar yanda na sanki ba, fad'a min ya kike?"

Bata tsaya dogon tunani ba tace "Tante Aissata, elle est très méchante."

Dariya Amna tayi tace "Je sais, shiyasa ma na hanaki tafiya dan nasan babu yanda za ayi kiji dad'in zama da ita."

Hamna dake kwance a gado tace "Manta da ita kawai zanyi maganinta, fad'a min ya kike?"

Saida ta sauke numfashi tace "Lafiya ta lau."

Daga b'angarenta murmushi tayi tace "Est ta nouvelle vie?"

Cike da farin ciki tace "Bansan ya zan kwatanta miki irin farin cikin da nake ciki ba, ina cikin farin ciki sosai rabin jikina."

Da mamaki Hamna tace "Da gaske? Ammar fa Amna?"

Dariya tayi tace "K'warai kuwa shi, zakiyi mamaki idan kika ga yanda muke zaune dashi."

Zaune ta tashi tace "Amnaaa, anya kuwa? Kamar ya koya miki son shi ko?"

Cikin murmushin daya sub'uce mata tace "Si je le te dit la vérité je le te dit oui."
Chapter 125 · 0% Book details