← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 198

Sashe 61

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayawa yayi ya kalleta, wannan idon nata har yanzu dai basu sauyawa ba cewar Jibril, kai tsaye ya mayar da kallonshi ga Huda yace "Ba damuwa ai ba jimawa zanyi ba, wani abu na tuna da shi yanzun nan."

Murmushi ya ma Huda yace "Nurul Huda ko? Zan dawo yanzu sai muyi hira dake."

Cike da gatsali Maryama tace "Huda, zanyi magana da tonton d'in ki mijin da zan aura, ki tafi tare da waccen *Abban nanki* kafin mu gama kinji ko."

Huda da har cikin zuciyarta taji dad'i da yau har mahaifiyarta ta iya nuna mata wani namiji ta kuma kirashi da abbanta, da farin ciki ta zagaya kusan Jibril daya kafe yarinyar da ido, *Abbanta*, ta tabbata dai kenan? Na shiga uku ni Jibril, yanzu wannan 'yata ce? To ya zanyi da ita? Haka kawai saina nunata a gida gida a matsayin 'yar wacce nayi wa fyad'e ko me? Junaid ma mamaki Maryama a bashi sosai jin yau tana alak'anta Huda da d'an uwanshi, to me hakan ke nufi? Gamon jini ne ko me? Da k'yar Jibril yayi murmushi ya shiga motar ya zauna, zuro hannayenshi yayi ya d'auki Huda ya ajeta mazaunin mai zaman banza sannan ya rufe, suna kallonsu har sukayi nisa kafin Junaid ya kalleta yace "Abun mamaki."

Kallonshi tayi da fara'a tace "Me fa?"

Ba tare daya daina kallonta ba yace "Wace irin sa'a Jibril ya zo da ita haka da har kika yarje masa ya tafi da Huda haka? Wace irin sa'a ce haka ke tattare da shi da har kika iya kiranshi da Abban Huda kuma a gabanta? Maryama ko dai da wani abu ne?"

Jin yana neman harbo jirginsu ita kuma ba haka take so ba yasa tace "Ba sa'ar shi bace, taka ce, domin nayi niyyar saurarenka, sannan na shirya fad'a maka abinda ke raina a game da kai, ko da baka zo ba yau ni zan neme ka, ina so ne na fad'a maka na amince zan aure ka, shiyasa ma na so sai Huda tayi nisa da ni sannan na fad'a."

Tunda ta fara magana yake kallonta cike da jin dad'in abinda take fad'a, da farin ciki yace "Mari, kina nufin kin amince zaki aure ni?"

Gyad'a mishi kyai tayi alamar eh, tafukan hannayenshi yasa ya rufe fuska da su, saida yayi godiya ga Allah kafin ya bud'e ya kalleta yace "Nima maganar dake tafe dani mai girma ce, domin kuwa jiya warhaka muna cikin filin gidanku tare da kakarki muna cin abinci muna hira da ita."

Waro ido tayi tace "Kakata? A ina kuka ganta? Gidanmu kuma?"

Murmushi ya mata kafin ya kwashe komai ya fad'a mata tun daga labarin da Iklima ta bashi har zuwansu garinsu da kuma abinda ya faru gidansu, kuka ta dinga yi tana ji a ranta lallai son ta yake sosai, sai dai kuma ita har k'asan zuciyarta babu wani son aurenshi a ranta, son da take masa ma ba wani so bane na azo a gani, yanzun haka ta amince ni zata aure shi saboda uban yarta data gani, ko ba komai zata gasa masa aya a hannu, saita rama zalincin daya mata, saita d'and'ana mishi irin *uk'ubar* daya sata ciki shima, abun mamaki saiga Junaid sunyi hira ta fahimtar juna da Maryama, kuma duk abinda yace saita amince ta nuna ta yarda, harda cewa yau zai had'ata da dreban da zai mayar dasu gida ita da Huda, gobe kuma za aje nema mishi aurenta, bata mishi musu ba sai cewa da tayi bari taje tayi sauri su had'a kayansu.

Tunda Jibril ya d'auki hanya ya rasa meke masa dad'i, shi fa daya shigo motar ya so ya samu damar da zaiyi k'wararan ihu ne da zaisa yaji sakayau , amma kuma an had'a shi da Huda, tsayawa kawai yayi bakin titi yana kallonta tana ta waige waige a cikin motar da tab'a abubuwa alamar dai kamar shigarta ta farko kenan, a zuciyarshi yake ayyana data hanyar data dace aka sameki da wannan motar zata iya zama taki wacce dreba ma na musamman gareki da zai dinga tuk'a ki, ganin kallon da yake mata yasa ta zauna tsaf ta daina tab'a komai tsoro ya bayyana tare da ita, fuskarshi ba yabo ba fallasa yace "Kina karatu?"

A hankali ta kalleshi tace "Eh Abba ina yi."

Wani kallon ban gane *Abba* ba? Ya mata kafin yace "Maryama mamanki ce?"

"Eh Abba." Ta sake fad'a d'orawa yayi da "Ina Abbanki yake? Mamanki ta tab'a nuna miki shi?"

Cikin sanyi jiki Huda ta girgiza kai tace "A'a, nima ban sani ba, amma dai yaran unguwarmu suna ce min shegiya ce ni 'yar karuwa, kuma Mamana kullum sai tayi fad'a da mutanen gidanmu idan suka ce min shegiya ce ni ko ragon suna ba'a yanka min ba, kuma idan na tambayi Mamana waye Abbana saita dinga hushi tana min tsawa da fad'a tace na tashi na bata wuri."

Rintse ido Jibril yayi saboda jin hawaye sun cika idonshi har suna neman zubo mishi, *ragon suna*? Shine abinda yafi tsaya mishi, 'yar dana haifa a cikina ko bata hanyar aure bane ace ba'a yanka mata rago ba, ya ilahi, shine abinda ya fad'a k'asa k'asa, d'an bud'a idonshi yayi ya juya inda Huda take, sai gani yayi tana ta goge hawaye da bayan hannayenta wasu na biyar wasu kam, gyara zamanshi yayi ya kamo hannunta ta mik'e tsaye ya d'auke ta ya zaunar da ita kan cinyoyinshi ya fara share mata hawayen yana fad'in "Yi hak'uri kinji 'yata, ba dai yana suna tsokanarki ba? To daga yau ba zasu sake ba saboda Abbanki ya dawo, kuma maganar rago ma ki fad'a min me kike so a yanka miki, kama daga rak'umi, saniya, da kuma raguna, ke da ana yanka zaki da su gwiwa ma ni zan yanka miki."

Kallonshi tayi tana dariyar jin dad'i tace "Ka zama *Abbana* daga yau?"

Gyad'a mata kai yayi yana murmushi, d'orawa tayi da "Kuma duk kana da kud'in siyan wannan abubuwan?"

Cike da tabbatarwa yace mata "Sosai ma, kuma ko da bana da saboda kiyi farin ciki ki wuce gori a idon jama'a ai ko bashi ne zan ci dan na siya miki."

Cike da yarinta tace "Abba saniya nake so babba, kuma nafi son kalar ja tafi kyau mai manyan k'aho."

Cikin dariya yace "Angama gimbiyar Abbanta."

Wani dad'i ne ya kashe Huda daya sata fad'awa k'irjin shi ta kwanta luf tana k'ara goge hawaye, wata ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi, a hankali ya lumshe idonshi ya fata shafa kanta wanda yasha sabon kitso ya fito tsaf da shi sai walk'iyar mai yake, hakan daya faru kuma saiya zama kamar antsaga zuciyarshi an dasa mishi soyayyar yarinyar, take yaji k'aunarta na gauraya da jinin jikinshi, ba tare daya bud'a ido ba ya sumbaci kanta, cikin tausashiyar murya taji yace "Huda ki yafe min, nayi gaggawa a waccen ranar, duk laifi na na komai daya faru, mahaifiyarki ba da laifi ko d'aya."

Ita dai da yau take jinta a k'irjin Abbanta yana shafata bacci ne ma ke sonyi gaba da ita, hakan ne yasa bata damu da me ya fad'a ba kawai ta sake yin shiru, ci gaba yayi da shafar kanta har yaji shirunta yayi yawa, yana lek'a fuskarta yaga ashe bacci harya d'auke ta, hak'ik'a mahaifiyarta ce tayi, daga kallon fuskarta kuma abubuwa dayawa ne suka ziyarci tunaninshi, ya zakayi da *Junaid, iyayenka ma, da ita kanta Maryama, sannan iyayenta ma da suka ganka*? Amma kallon fuskar Huda da yake sai yaji ya bashi k'arfin gwiwar tunkarar kowane irin bala'i da masifa, 'yace dai gata ta zo zo duniya, tasha wahala kafin bayyanarshi ya kuma dan da ita, amma daga yanzu daya sani har zuwa lokacin da kowa zai fahimce shi ba zai bari tayi kuka ba, shafa kanta yayi ya sake sumbatarta yace "Wannan *alk'awari* na ne gareki."

Ba tare daya d'auke ta daga kan cinyarshi ba ya tayar da motar a haka ya tuk'a suka isa wata alimentation, tsayawa yayi ba tare daya fito ba kawai ya sauke gilashin motar yace babbar leda yake so a had'a mishi ta kayan da suka san zasu birge yaro, saida ya siyo suka juyo dawowa inda suka bar Junaid, shi kad'ai ya samu zaune bakin dakali Maryama ta shiga dan kimtsawa, Junaid ne ya kirata a waya ta sake fitowa, fitowa Jibril yayi da Huda a hannu ya matsa daf da Maryama zai bata ita, murya k'asa k'asa tace "Baccin farin ciki ne take na ganin mahaifinta? Ko kuma baccin wahala ne?"

Da sauri ya sauke idonshi cikin nata idon da alamar tambayar me take nufi? A lokacin da zata amsheta ne tace "To ai naga kai idan har aka shiga mota d'aya da kai sai kayi b'arin ingantacciyar madarar da tana shiga mahaifa dole a tashi mutum da ita."

Kallon wannan wace irin magana ce haka? Ya mata kafin shima yace "Huda, 'Yata ce?"

Murmushi ta masa tace " 'Yar ka ce mana, a waccen ranar aka sameta, dalilin haka kuma na shiga karuwanci."

K'asa ya kalla tare da saisaita murya yace "Ya fad'a min kuna shirin tafiya, amma dan Allah kafin ku tafi ki jira naje na dawo."

Cikin makirci ta amsa mishi da "Karka damu zan jiraka, domin kuwa akwai matsalolin daya kamata mu warwaresu."

Gabanshi ne ya fad'i ita kuma ta kalli Junaid dake waya da wanda yake so ya had'a shi da dreba tace "Zan shiga ciki na k'arasa shiryawa."

Da kai kawai ya mata alama ta wuce ciki suma suka shiga mota suka d'auki hanya, gida Jibril yace ya aje shi, yana sauke shi kam d'akin shi ya shiga ya fito ya shiga motarshi shima, bai zame ko ina ba sai *Soura* mayanka.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Chapter 61 · 0% Book details