Sashe 6
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Tsaka mai wuya Ammar (ka sunkuya Hajia ta mareka, ka k'i sunkuyawa Ummi tace bata yafe ba).*
_Ku bashi shawara_😂
18/05/2020 à 13:48 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*BADAK'ALA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
👨👩👧👦 _*AHALI NA*_👨👩👧👦
_Bismillahir rahamanir rahim_
_3_
Alhaji ne yace "Kai Ammaru, wuce dan Allah ku tafi wajen aikinku kaji, sai kun dawo."
Da sauri Hajia ta kalleshi wato ita zai rainawa wayo, Ammar na jin haka ya juya cikin takon k'arfi ya fice daga falon, cikin sanyin jiki Ummi tace "Umma sai mun dawo, Abba mun tafi."
Amma sai dalla mata harara da tayi Alhaji kad'ai ya amsa da "A dawo lafiya Sa'ada."
Wucewa tayi tasa gyalenta tana share yar k'wallar data tarar mata a ido, Amar ma bayanta ya bi ya dafa kafad'ar ta yana rarrashin uwatai, sai Junaid da shima ya musu sallama ya wuce, Jibril ma cewa yayi ya tafi sai Alhaji ne yace "To *B A* (sunan projet da yake aiki kenan, kasancewarshi d'aya daga cikin jigajigen ma'aikatar duk da k'arancin shekarunshi yasa Alhaji dama wasu daga mutanen gari ke kiranshi da haka) yau kuma wani garin zaku kaiwa girgiza?"
Dariya yayi yace "Alhajin Allah kenan, yau tafiyar ba mai nisa bace, wani k'auye ne nan kusa nake so na shiga da kaina tare da sabbin ma'aikatan da muka d'auka, kasan sai ana nuna musu yanda aikin yake kafin su zama yan gari, amma komai dare zan dawo insha Allahu."
"To Allah ya bada sa'a, Allah ya tsare." Cewar Alhaji, da murmushi ya amsa da "Ameen."
Hajia ya kalla yace "Hajia ni na tafi saina dawo."
Dayake shi ba daga tsatsonta yake ba sai kawai ta d'auke kai kamar bata ganshi ba, shi kuma ko a jikinshi dan in da sabo ya saba, wajen kakarshi ya nufa Husseina yace "Yar tsohuwa na tafi saina dawo."
Da murmushi ta amsa da "A dawo lafiya d'an tsoho, Allah ya kiyaye."
Umaima kyakyawar budurwa yar boko mai wayewa wacce ke koyon aiki (stage) a bankin da Amar ke aiki wanda shi dama *DG* (directeur général) ne a ma'aikatar, kasancewar gidan duk boko ne yasa ta samu hanya cikin sauk'i a ma'aikatar dan da kanta ta zab'i inda take so, kuma dama mata su kam Hajia tana basu damar yin abinda suke so, maza dai ne take son suyi wanda take so saboda tana son cimma wani burinta a game da hakan, ita ke biwa Junaid sai Jamila dake bi mata, duk da shekarunta har yanzu babu maganar aure a tsarinta, kuma dayake shi aure lokaci ne sai Hajia bata damu da lamarinta ba bare tace zata had'a ta da wani ko a cikin mazan gidan, doguwar rigar ce jikinta data kamata kuma ta fito da jikinta sosai, sai gyalen data d'ora da jaka a hannu kalar takalminta, ita ma gaishesu tayi ta kalli Amar dake rarrashin Ummi tace "Yah Amar ka jira ni mu tafi tare, mota ta na wajen gyara har yanzu."
Juyowa yayi da kai ya mata alamar ta taho, da irin haka gidan yayi shiru ya rage sai iyayen, yara dama ana had'a musu abin kari ne su tafi dashi, in kaga sun zauna cin abincin kari to su suka zab'i abinda za'a dafa musu da safe, manya kuma dama babu wanda ya damu da abincin gidan, ba wai na safe ba har na dare ba wani sai yayi sati bai jefa abincin gidan cikin bakinshi ba, kuma hakan baya rasa nasaba da yawon gidan da kuma kowa na da 'yan canji a aljihunshi.
Yanzu haka masu aiki ne su biyu gogaggu a fannin girki da kuma kula da tsabta wanda Hajia ta yarda dasu rik'a girka mata abinda zata ci ke ta kai kawo a madafa, d'aya budurwa ce sai babbar wacce bazawara ce, kafin ma ta yarda su fara aikin saida sukayi aiki a gidan na sati guda ta gamsu da abincinsu da kuma tsabtarsu kad'ai, sai guda biyu suma d'aya budurwa yar shekara *goma sha tara* da kuma dattijuwa su kuma aikinsu shara da goge goge, yanzu haka ma sune ke goge wajen cin abincin, sai Soueba da Zeinabou da su basu aiki ke jera kwanukan abincin, duk da ba su ke girkin ba amma suna taimakawa masu aikin, wani lokaci kuma suna girkawa da kansu, abin karyawa ana dafawa ne kawai, amma na rana dana dare sai wanda Hajia tace tana so, saida suka gama shiryawa Soueba ta zo cikin fargaba tace "Hajia an gama shirya wajen cin abincin."
Wani kallo ta mata kamar kashi kafin tace "Ina zuwa to."
Dukansu ne suka mik'e suka nufi wajen cin abincin, sai *Alhaji Labaran* mahaifin Jibril dayake shi d'an kasuwa ne yasa bai da k'ayadadden lokacin fita, gyara rigarshi yayi ya kalli Alhaji yace "Ni zan fita Alhaji, sai mun dawo kuma."
"To Allah ya tsare, Allah ya bada abinda aka je nema."
Amsawa yayi da "Ameen." Kallon Hajia yayi wacce tuni ta isa kan teburin Zeinabou da Soueba sun sakata tsaka suna zuba mata abinda ta zab'a, mahaifiyarshi ya juya yawa sallama haka ma Gambo da yake kallon agogon hannunshi saboda gudun wucewar lokaci, Soueba na ganin zai fita tayi saurin aje kwanon miyar zata nufi wajenshi, cikin akasi miyar ta d'an fallatso ga hannun Hajia, sai kuwa ta daka mata wata tsawa "Ke!"
Cikin tsoro ta tsaya tare da kallon Hajiar, d'orawa tayi da "Ke mahaukaciyar ina ce? Me kike kallo da zaki k'ona ni da miya? Ko jarabar ce ta motsa ta miji? Ina ce ai fita ne zaiyi ko, meye kuma na hanzarin biyarshi a baya?"
Cikin rawar murya tace "Yi hakuri Mama, ban..."
"Ba kiyi me ba? Dallah b'ace min da gani."
Labaran da yake jin duk abinda ke faruwa ko juyowa baiyi ba harya fita, Soueba kuma hanyar madafar ta nufa cikin sanyin jiki, tana daf da shiga taji tace "Ki turo min *Zeituna*."
Juyowa tayi da ladabi tace "To Mama."
Saida ta shige Alhaji ya kalleta kamar ya kifeta da mari, baya jin dad'in abinda take a gidan, yana son taka mata birki in tana irin wannan ikon nata, amma idan ya kalli yanda gidan suke girmamata da ganin darajarta mutumcinta ne zai zube yau da gobe idan yace duk sanda tayi ba daidai ba saiya tsawatar mata gaban mutane, dan wata rana iya shegen nata har gaban yara yi take, shiyasa yake bari sai sun keb'e wani lokacin yake mata magana, Husseina dai kallonta kawai take sai Gambo da shi dai yake fatan ma lokacin tafiyarshi ya kusa yayi abinda ya kawoshi ya bar garin kafin ta bijiro da wani abinda take so tace kuma dole yayi, suna haka Zeituna ta fito ta nufo wajen Hajiar, kallo d'aya zakawa budurwar kasan kyakyawa ce wacce Allah ya hore ma albarkatun jiki, amma talauci da rashin gyara yasa datti ya samu gurin zama a jikinta, tana kusa da k'arasowa Hajia ta d'aga mata hannu da fad'in "Dakata malama, koma kawai ma na fasa aiken na ki, jiki duk datti haka."
Juyawa Zeituna tayi zata koma taji tace "Wai ke yaushe rabonki da wanka ma?"
Pik'i-pik'i Zeituna tayi da ido tana kallonta hakan yasa tace "Anya ma kina wankan? Mtsss! Shiga ciki."
Shiga tayi baiwar Allah sai kawai ta fashe da kuka, sai abokiyar aikin nata wacce ita dattijuwa ce da suke kira da *Iya* ta bata hak'uri tace ya kamata ace ta saba da irin haka, Zeituna kuma ciwonta d'aya shine wata jarabawa da Allah ya jarabeta da ita, babar jarabawa ce gareta kam, dan ace ubangiji ya jarabeka da son wanda bai ma son kanayi ba babbar jarabawa ce, gashi ita ba kowa ba kuma ba 'yar kowa ba, sannan matar da zata iya sakata ta shigo gidan ta tsaneta, ita kam dole tayi kuka, gashi tun bata san meye so ba take jin mutumin na birgeta duk wani motsinshi, har ta girma ta fahimci ta kamu da son mutumin da a haife ya haifeta, halayyarshi daban take ko cikin su uku d'in, duk da shine babban amma yafi sauran raha da barkwanci, tun tana tunanin birgeta ne yake har ta yarda *so* ne kawai, *son* wanda ba ma iya kallonta idonta bare ya fahimci ciwonta, *son* wanda yake da mata goggiyar 'yar boko, *son* mutumin daya sha boko ya k'oshi kuma yake da ilimi har na addini ma, *son* mutumin da ko zaratan 'ya'yanshi sun fi k'arfin ta bare kuma shi da kanshi, Iya nata rarrashi ita kuma tana wani tunanin daban, d'aga kanta tayi sama tana zubar da wasu hawayen ta furta a zuciyarta "Allah kai ka jarabeni da wannan ciwon, Allah ka kawo min maganinshi idan har ba ciwon da zaiyi ajalina bane, idan kuma wannan jarabawar ita ce silar ajalina, to Allah na rok'e ka ko sau d'aya ne ka had'a ido na dana *Abbansu Amar* ya fahimci son da nake masa, idan haka ta faru burina ya cika, ko a lokacin wa'adi na ya cika banda takaici ban kuma mutu da buri ba."
Ba dan kar tayi sab'o ba da sai tace meyasa aka jarabceta da wannan k'addara, dan a ganinta bata cancanceta ba ko kad'an, amma kuma idan ta tuna da al'amarin ubangiji, yana da iko da k'arfin da zai juya daidai izuwa ba daidai ba, ya kuma juya ba daidai ba izuwa daidai, dan haka sai tayi shiru tana tunanin ko da Allah yasa soyayyarta batayi nasara ba, to tabbas ta koyi abu guda a wannan karatun, abun kuwa shine ta san ya *so* yake, ta kuma san zafin da ake ji da rad'ad'i lokacin da ka rasa wanda kake so, da wannan ta share hawayenta suka ci gaba da aiyukansu.
*So*
_(Mugun dafi)_