← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 198

Sashe 141

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa tayi ta fita suka bita da kallo, murmushi kawai yayi ya mayar da hankalinsa kan Amna dake d'an ciccije leb'e, cikin kulawa yace "Lafiya dai?"

Cikin yamutsa fuska tace "Ciwo nake ji yah Ammar, bayana ke wani irin abu ba dad'i."

Cikin son gano abinda ke faruwa yace "Tashi ki d'anyi tafiya to ko haihuwa ce zata zo da sauk'i insha Allah."

Had'e labb'enta tayi ta yunk'ura ta tashi, rik'e take da bayanta tana ta safa da marwa a tsakiyar d'akin, ikon Allah da yake haihuwar na kusa bata jima da fara wannan sassarfa ba taji ciwo na tasowa sama, kallonta yake duk inda tayi yana lura da halin da take ciki da kuma yanayinta, da fari duk sanda wuyan k'aramar rigarta ya fad'i saita jashi sama ta mayar, amma yanzu yaga bata kula ba har rabin k'irjinta duk a fili, ga kuma wata uwar zufa dake ta tsatsafo mata a goshi da wuya, sannan idan ciwon ya turnuk'ota saita rabka sallalami da dafe duk abinda ke kusa da ita ko ta durk'ushe k'asa, yanzun ma durk'ushe tayi amma kuma tashin ya gagara, hannunta ta d'ora kan k'aramin teburin dake wurin ta rintse ido sosai take fad'in "La'ilaha ilallah, ya hayyu ya k'ayyum bi-rahmatika astagisu, la'ilaha..."

Da k'arfi ta kalleshi tace "Dan Allah ka kaini asibiti karna mutu, yah Ammar ka taimaka min mutuwa zanyi."

Da sauri ya taso yana taka k'afarshi da k'yar ya durk'usa kusanta shima yace "Kalleni Amna, kalli fuskata kinji."

Kai ta dinga girgizawa cikin rad'ad'i tana fad'in "Ba zan iya ba, ka kaini asibiti dan Allah, ka kira min Ummy, bayana ciwo yake kamar zai tsage."

Mik'ewa yayi tsaye ya dawo kan kujerar da yake ya d'auki makullin mota da wayarshi, dawowa yayi kusanta ya tallabota da nufin su fita, tana mik'ewa sai kuwa ta cakumo rigarshi tamau ta fasa ihun data shiga dodon kunnenshi, yanda yaga tana neman sulalewa k'asa yasa shi azamar tarota, ya fara takawa da ita sai yaji tayi wani irin nishi kamar dai wani abu ya tunkaro zai fito, tsayawa yayi ya kalleta da kyau sai yaga daga inda take durk'ushe har inda suke yanzu duk wasu ruwa ne suka b'ata wurin, dafe goshinshi yayi yace "Oh mon Dieu."

Da sauri ya fara latsa wayarshi ya danna kiran wayar Ummy, tunda taga kiranshi a wannan lokacin tasa a ranta cewa Amna ce ba lafiya, dan haka ma saida ta mik'e da sauri ta rarumi gyalenta kafin ta tashi lieutenant, tana d'aukar wayar yace "Ummy Amna ba lafiya, kiyi sauri ki zo."

"To gani nan." Ta fad'a ita ma da sauri, tare da lieutenant suka fito yana rik'e da Shureim, fita tayi shi kuma ya je d'akin Hajia ya sanar da ita, tare suka k'arasa a lokacin Ummy na shiga Ammar yace "Ummy haihuwarta kusa take, ki dubata in zaiyi mu kaita asibiti."

Kamata tayi ta kalleshi tace "Taimaka min da safa."

Ya juya da niyyar shiga d'aki Amna ta sake wani nishi mai k'arfin gaske tana rirrik'e da hannun Ummy, haba mantawa yayi da ciwon k'afarsa ya juyo da gudu, yana zuwa makullanshi ya cillawa Ummy yace "Ummy bud'e min d'akin magani na." Da sauri ta mik'e ta shiga gaba shi kuma kamar wata yar beby haka ya lailayeta da iya k'arfinshi ya bi bayan Ummy, suna shiga da ita d'akin ya kwantar da ita kan gadon dake wurin musamman na haihuwa, Ummy kuma safa ta sanya da sauri ta tunkarota zata duba ta, kafin ta ida k'arasawa kusanta ta sake d'an d'agowa ta danno wani nishin kamar dai wanda take yi, haba ai wani abu taji ya zubo kamar kayan cikinta tare da wani irin gumi, kukan yaron da suka ji ne yasa Ammar saurin dawowa inda yaji kukan yaron ya sake bud'e k'afafun ta, bai tsaya saka safa ko wani abu ba kawai ya d'auki yaron da cibiya ta laulayeshi, cikin nutsuwa ya fara warware mishi da wani faffad'an murmushi a fuskarshi ganin yaronshi a hannunshi, Ummy ce ta matso tasa almakashi ta yanke cinbiyar, zata kai hannunta da niyar janyo uwa sai kawai Amna ta damk'i hannunta ta sake dank'aro wani nishin, fit sai ga wata santaleliyar budurwa ta fad'o ita ma sai wutsilniya take da kuka a hankali, kallon fuskar Amna yayi yace "Ke duniyata, ya kike neman kashe ni da farin ciki, daga farawa saiki fara min da bibbiyu."

Kallon Ummy yayi baki bud'e yace "Ummy biyu ne, wallahi yan biyu ne, wayyo Allahna dad'i, Amna nagode nagode kinji, Allah ya saka miki da alkairi."

Lumshe ido Amna tayi ta kwanta luf, Ummy ce ta kalleshi tace "Ka d'auko mana kayan haihuwarta."

"To Ummy." Ya fad'a yana nufa k'ofa rik'e da jinjirin, kallonshi Ummy tayi tace "Ina kuma zaka je dashi a haka?"

"Oh." Ya fad'a yana dawowa ya mik'a mata shi, aje shi tayi gefen Amna ta yanke cibiya ta fito mata da uwa, hannu tasa ta fito mata da gudan jini, kallonta tayi tace "Amna ci gaba da tausa ciki kina murzawa saboda jini ya fito."

Ido rufe tasa hannu tana murza ciki tana danna mararta tana ji jini na zubo mata. Yana fitowa ya ga duk iyayen tsaye Zeinabu ce kawai babu, cike da shak'iyanci ya fara taka rawa yana tafa hannaye yana juyawa, takon rawar a hankali mai birgewa, a haka kuma wak'a ya dinga rerawa ta godiya ga Allah wacce shi ya k'irk'ireta yanzun nan, lieutenant ko da yaga haka yasan ta haihu sai shima ya fara tapi yana biyar wak'ar yana gyad'a kai alamar yanayi da wak'ar sun masa dad'i, Hajia ce tace "Kai ta haihu ne?"

Girgiza kafad'u ya shiga yi yana kallon fuskarta ya kwaso shoki daga k'ololuwar k'asa yayi sama da ita ya wurgata fuskar Hajia yana fad'in "Hajia 'yan biyu ta haifa min, aradu mace da namiji ne Hajia, kai nima fa ashe jarumi ne."

Murmushi ta masa tace "Hakane, amma duk jarumtarka mijina dai ya fika, shi uku yake haifa."

Alhaji dake tsaye rik'e da carbi kunya yaji ta kamasa, su lieutenant da Labaran kuma dariya sukayi cike da jin kunya, shafa kumatunta yayi yace "Bari na dawo Hajia Allah yau sai kin taka rawar jin dad'i."

Da gudu kamar yaro ya nufi hanyar b'angarensu, da sauri ya d'auko kayan ya kawowa Ummy, Ummy da kanta ta gyara yaran ta bashi ya kawo musu, yana dawowa ya samu tana dannawa Amna mararta da jini ke ta fitowa, tana kallonshi tace "Zare nake so zan mata d'inki."

Kallon Amna yayi ya matsa kusa da ita yace "Wayyo duniyata yarana sun k'ara ki ko, sannu kinji, insha Allahu ladar ta tabbata gareki."

Rufe idonta tayi a ranta tace "Kai da kan ka ma ka k'ara ni bare su, ai kamar uba kamar 'ya'yansa ne."

Da kanshi ya had'awa Ummy zaren ya bata kafin ta fito, namijin dake hannun lieutenant ya lek'a fuskarshi yana wasar masa baki yana fad'in "Kai wanene wannan? Kai yaron babanshi ne, d'an albarka ne, yaron Ammar ne wannan."

😂😂😂😂 *Allah ya kyauta.*

Soueiba ce ta kalleshi galala tace "Ammar yaron da ko ido bai bud'e ba kake ma wasa?"

Kallonta yayi yace "Ina so ya fara d'aukar sautin muryata ne kafin ta kowa."

Tab'e baki Hajia tayi tace "Duk tsiyarka kuma sai sun sun gane uwarsu kafin kai."

"Wannan ba matsala bane Hajia, ta cancanci haka ai, daga yanda naga ta canza d'in nan a yayin nak'udarsu na k'ara mik'o muku jinjinata."

Kalle kalle ya shiga yi kafin yace "Wai duk ina sauran mutanen gidan."

Husseina ce tace "Suna bacci mana, *12: 30* ce fa tayi na dare."

Zaro ido yayi yace "Wa? Bacci a lokacin da yan biyu na suka shigo duniya, ai Qur'ani basu isa ba, duk uban daya tsaya ma mutum ma saiya tashi, bari kuga yanda zan firgita nutsuwar kowa."

Labaran ne ya bishi da murmushi yace "Mun gode Allah da yasa ubannin gamu nan tsaye."

Dariya lieutenant yayi ya kalleshi yace "Kar ya baka wahala mana."

Suna kallonshi ya nufi wajen mai gadi kai tsaye ya fara bubbuga mishi k'ofa, yanda yaji buga k'ofar yasa shi fitowa da sauri da makullai a hannu yana tunanin fitar gaggawa ce, yana ganinshi ya tsaya yace "Alhaji k'arami wani ne ba lafiya? Bara a bud'e k'ofar."

"Kai tsaya dallah." Ya fad'a yana turashi baya, kallonshi yayi zuru da ido kafin yace " Ina bokitin nan naka da kake wanki?"

Saida ya had'e gira tsabar mamaki yace "Bokiti? Yana nan ciki?"

"D'auko min." Ya fad'a, shiga ciki yayi ya d'auko bokitin robar ya kawo mishi yana fad'in "Yallab'ai lafiya dai ko? Allah yasa ba laifi nayi ba."

Kallonshi yayi yace "Idan laifi kayi kuma shine sai a bokitinka zan huce saboda tsoronka nake ji."

Sunkuyar da kai yayi shi kuma ya juya zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yace "Baka da wani mabugi haka kamar sanda ko icce?"

Shi kam mai gadi baya da dan ko shayi ko girki idan buk'atar yi ta kamashi k'aramin gas gare shi, dan haka yace "Babu yallab'ai, amma bari a samo maka."

Takalminshi yasa da niyyar fita nema sai Ammar yaga tsumagiya aje, d'auka yayi yace "Bari wannan ma yayi."

Juyowa yayi ya kalleshi yace "Yallab'ai da ka bari na samo maka wanda yafi wannan, ita ma ina ajiya ne saboda yara wani lokacin."

Kallonshi yayi saida ya kawo bokitin nan gaf da kunnenshi ya tak'ark'are ya had'a tsumagiyar nan da bokiti ya shiga bubbugawa da k'arfi kamar zamanin da ake shela da baki, rintse ido yayi sosai saboda yanda k'arar ke shiga hudar kunnenshi, saida yaji yayi shiru sannan ya bud'e ido ya kalleshi, shima kallonshi yayi yace "Har gari ya waye babu mai kwana a gidan nan, baiwar Allah na can tasha fama ta haifo min yara har biyu, biyu fa." Ya fad'a yana nuna mishi biyu da yatsunshi ya ci gaba da cewa "A lokaci d'aya, kuma kuma ku kuna baccin iya shege."

Juyawa yayi cikin takon k'arfi kamar zai shiga filin daga ya shiga falon Hajia, saida ya tsaya tsakiyar falon ya fara bubbuga bokitin yana ihu yana fad'in "Kowa ya fito, kowa ya tashi."
Chapter 141 · 0% Book details