← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 198

Sashe 65

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin zubo da hawaye tace "Iya na kamu da so, son wanda bai kamata ace na kamu da son shi ba, son mutumin da ba zai tab'a kallon ko da fuskata ba bare ya ji wani abu mai kama da so a zuciyarsa a game da ni, son mutumin da ko da ace 'ya ce ni mai gata yafi k'arfi na saboda wasu dalilai, Iya bansan ya zanyi ba dan Allah ki bani shawara?"

Cike da kulawa ta kalleta tace "Zeituna har yanzu a duhu kike saka ni, ki fito ki fad'a min matsalarki, kin manta na fad'a miki ke kamar 'ya ce a gurina?"

Gyad'a kai tayi alamar eh kafin Iya tace "Dan haka Zeituna karki sare, ke fa 'ya mace ce, kina da damar da zaki so kowa kuma kowa ma ya so ki, karki k'ask'antar da kanki har ki dinga ganin baki dace da samun soyayyar wani d'a namiji ba, ke nifa na yarda da yata wallahi, tsaye da kyau haka zaune da kyau, har waye zai ce ma baya sonki? Ai ki k'addara koma waye to shi yayi babban dace da har samu nasarar samun soyayyar ki, dan haka fad'a min naji waye shi?"

Cikin murmushin jin dad'i na yabon da Iya tayi mata ta kalleta sororo tace "Iya Abban Ammar ne, mijin aunty Sa'ada, lieutenant Hassan Gaga."

Har gaban Iya saida ya fad'i a wurin, zaro ido tayi lokaci d'aya kuma dan karta sanyaya mata gwiwa taji ba dad'i sai kuma ta wayance tace "Haba dai? Dama ai na fad'a miki koma wanene shi yayi dace ba ke ba, ke baki ga banbancin dake tsakaninku da shi bane?"

Da mamaki Zeituna ta kalleta tace "Wane irin banbanci Iya? Lieutenant fa nace miki na gidan nan, mahaifinsu Ammar."

Da yar harara ta bita irin ta yo shi d'in fa kafin tace "To sai me? Tabbas yana da kud'i da kuma ilimi, amma duk da haka akwai abinda ke ma kika fishi."

"Me kenan Iya? Cewar Zeituna da har yanzu take mamaki.

Murmushi Iya tayi tace "Kin fishi k'urucuya, Zeituna ke yarinya ce shi kuma tsoho, hakan zaisa ba zai iya juyawa soyayyarki baya ba."

Rufe ido Zeituna tayi irin wai kunyar nan tana fad'in "Kai Iya, Allah ba tsoho bane."

Waro ido Iya tayi tace "Iyeeh! Kaji min yarinyar zamani ko, to zan gani idan ba tsohon bane."

Had'e murmushin kan fuskarta tayi tace "Iya zan bar garin nan."

"Me? Barin gari? Meyayi zafi? Ke duk zafin soyayyar ne? Zeituna karki halaka kanki mana, ki bi komai a sannu kina kai kukanki wajen ubangiji, nima zan tayaki da addu'a." Duk iya tayi maganar ne tana kallonta.

Girgiza kai tayi tace "Iya ba wannan bane matsalar, matsalar kawu Mamu ce."

Nan ta kwashe komai ta fad'awa Iya wanda taji suna tattaunawa, kuka take sosai Iya na rarrashinta da cewa tayi hak'uri kar tayi saurin barin gari tunda babu inda zata je, sun jima nan zaune suna tattaunawa har Alhaji ya bar wurin cikin matuk'ar sanyin jiki, d'akin baccinshi ya shiga ya zauna kan kujerar da bata da maraba da gado yana tunani, hak'ik'a *so* wani abu da babu wanda ya bari, babu ruwanshi saiya shiga zuciyar babba komai girmansa ya kuma gaura shi a k'asa, haka kuma ya shiga zuciyar matashi komai k'uruciyarshi yayi maganin wautarshi da rashin hankalinshi, tunanin Zeituna da halin da take ciki ne ya tsaya masa a rai, kawun ta? Amma baya tsoron mahallicinsa? 'Yar d'an uwanka zaka nemi ka jefa rayuwata a harkar karuwanci? Da wannan tunanin Alhaji ya jima zaune ya kasa yin komai har saida ya samu tsayayya kuma gamsashiyar shawara sannan ya mik'e ya shiga wasu harkokin.

Da safe bayan sun karya Hajia tace lieutenant ya kira colonel ya sanar da shi gobe zasu je Goure neman auren Maryama, haka kuma ya kira gwamna ya sanar dashi an tsayar da auren 'yarsa Amna, yanda tace haka yayi hakan yasa colonel daya samu sararin aikin kiran da aka mishi ya d'auko mota ya kamo hanya tare da masu tsaronsa a biye da shi.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Tunda suka je asibiti ko aiki ya had'a su Ummy ta k'i yarda ko ido su had'a, ya fahimci hushi take dashi abinda ya tsana kenan a duniya, yawan sakawa Ummy na fushi dashi yasa yake k'ara jin haushin Hajia shima, har lokacin tashin shi yayi ya shirya ya fito, har zai wuce ta gaban d'akin inda ake kwantar majinyata saiya hangeta tana cirewa tsohuwar da yasa a kwantar da ita saboda tana neman agajin gaggawa, turo k'ofar yayi ya shiga babu sallama, juyowa Ummy tayi tana ganinshi ta d'auke kai, amma saboda dokar aiki da kuma ba kowa yasan d'a da uwa bane yasa cikin dakakkiyar murya a harshen fransanci tace "Docteur har ka fito? Na ga lokaci ya d'an ja kuwa."

Saida ya kalli robar ruwan ya kalli tsohuwar ya zauna bakin gadon kusa da tsohuwar yana kallon fuskarta yace "Kaka ya jikin naki?"

Kallonshi Ummy tayi, wato ba zai kulata ba dan ma ya samu ta mishi magana? K'wafa tayi a cikin zuciyarta ta juya da wani d'an kwano kwano kuma shi ba faranti ba a hannunta wanda ake zuba 'yan magunguna da allurai zata fita, ji tayi yace "Madame jira."

Tsayawa tayi ta had'e wani abu a mak'oshinta kafin ta juyo da fara'a a fuskarta, a lokacin kuma tsohuwar ta amsa mishi da "Jiki da sauk'i likita."

Fuskar dai a yabo ba fallasa yace "Ina fatan dai baki manta duk abubuwan dana fad'a miki ki kiyaye ba ko?"

Cikin murmushi tace "Ban mance ba likita."

Mik'ewa yayi ya dauk'i abun sauraron bugun numfashi ya dinga d'ora mata a k'irji, ajewa yayi akan farantin dake hannun Ummy ya d'auki abun awon hawan jini ya zura mata a hannu ya d'aure mata ya danna wani madanni, nan ma saida ya samu sakamakon da yake buk'ata kafin ya d'an duba idonta, katinta dake aje kusan kanta ya d'auka ya duba tare da wasu yan rubuce rubuce, takardar maganin daya bata tun farko ya sake nuna mata yace "Kaka ki tabbatar an siyo wannan magungunan fa."

Gyad'a mishi kai tayi tace "Yaron nawa ma yana zuwa yanzu zan bashi ya siyo."

Murmushi ya mata wanda ya ba Ummy mamaki, tana tsaye tana kallon shi ya d'an dafa kafad'ar ta yace " Da kyau kaka, Allah ya sawak'e ya kara afuwa."

Kallon Ummy yayi yace "Madame idan yaron nata ya zo ku tabbatar kun bashi ya siyo maganin, idan ya kawo ku nuna mishi yanda zatayi aiki da shi babu jinkiri, daga bisani sai ku sallame ta, amma zata dawo nan da sati biyu."

Ummy ita tasan kawai bura uba ce yake mata, amma haka ta daure tayi murmushi tace "Ok docteur, za ayi yanda ka ce."

Wani d'aure fuska yayi yace "Haka nake so."

Cikin takon k'arfi ya fita ya shiga motarshi, da kallo tsohuwar ta bishi tayi murmushi tace "Allah sarki likitan babu ruwanshi, Allah ya mishi albarka."

Kallonta Ummy tayi a ranta tace "Bala'i, tsohuwa dan baki san shi bane shiyasa kika ce haka."

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Ana idar da sallah la'asar Hamna ta shirya cikin kayan makaranta da kuwa jakarta, saida ta sake jadaddawa Amna tsarinsu tunda ita ba zata tafi ba, a tsorace dai Amna tace "Dan Allah karki jima kiyi sauri ki dawo, kinsan fa in suka gane zan sha masifa a gurin Hajia."

"To naji dan Allah." Ta fad'a alamar matsuwa, fitowa sukayi falon Hajia na zaune, ganin kayan makaranta a jikinta yasa Hajia ta bita da kallo kawai bata hanata fita ba, Amna dake nesa da Hajia zaune tana kallo ne ta kalla tace "Ke kuma ba zaki je makarantar ba ne kome?"

Murya a tausashe tace "Hajia yau zamuyi hadda ne na alk'ur'ani, ni kuma kwana biyu kenan bana tab'a Alk'ur'ani shiyasa ba zan je ba."

Shiru tayi mata Hamna kuma na jinsu amma ta fice abinta, a motonta ta tafi ba jimawa ta isa gidansu k'awarta *Nafi*, tana zuwa ta cire kayan makarantar nan ta shiga tsarawa kanta kwalliya, sun d'auki lokaci suna shiryawa kafin suka gama suka d'auki hotuna, yamma lik'is suka hau moton dan zuwa wajen kamun k'awarsu da akeyi yau wanda gobe ne d'aurin auren, a cikin *hotel jangwarzo* ne dan haka basu wani jima ba suka iso.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Sai bayan sallah azahar ya dawo gidan bayan ya ci abincinshi a waje, dan rabon da yace ya ci abincin gidan nan harya manta, yana zuwa kayan jikinshi ya cire ya watsa ruwa ya kwanta, ba jimawa kuma bacci mai dad'i ya d'auke shi, kiran sallah ne ya farkar dashi dayake akwai babban masallaci wanda ya kasance na gidan ne dake kallon juna da gidan, a kasalance ya tashi yayi alwala ya tafi masallacin ya dawo, yana zuwa ya samu kira a wayarshi rutu-rutu, baiyi tunanin mayarwa ba ya nufi ban d'aki dan yin wanka, wani kiran ne ya sake shigowa wayarshi ya dawo ya d'auka yana tsaki, daga can b'angaren aka ce "Anyi walk'iya mun ganku, yanzu Ammar mu zakawa rashin mutumci?"

Saida ya zauna bakin gadon cikin muryar bacci yace "Idan kana son gani na ni ko ba ayi walk'iya ba zaka iya haskani da fitila, rashin mutumci kuma yanzu na fara darza muku shi, kafin nan fad'a min dalilin kiran nawa?"

*KB* da yasan halin kayanshi ne yace "D'an iska kana nan da halinka, indai za'a fad'a to sai ka fad'a kai ma."

Kamar bashi da lakka yace "Ai ni na wuce ka kirani d'an iska, sai dai d'an rai-rai (sahara), malam muryarka na damuna fad'a min meya faru."

Kb ne yace "Domin Allah Ammar tun yaushe muka fad'a maka da bikin *Abdullahi* ya taso? Tun shekaran jiya aka fara k'unshi amma bamu ga k'eyar ka ba, yanzu ma muna shirin tafiya wajen kamu ne nace bara na kiraka dan naga iskancin naka ba mai k'arewa bane."

Yana d'an tattausa wuyanshi ya lumshe ido yace "Ni ne zaku gayyata wani wai k'unshi? Kawai muyita yawo a rana wai zamu je d'aukar abinci kamar 'ya'yan da aka haifa lokacin hamada (yunwa), sannan yanzu kamun me zanje? Idan naje uban wa zan kama? Amaryar ko ango? Kaga malam nifa bana cikin wannan salon 'yan banzancin, ranar d'aurin aure naje na shafa fatiha dani."
Chapter 65 · 0% Book details