← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 198

Sashe 15

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya k'alau." Ta fad'a da murmushi sosai, maida kallonta tayi ga *Wassila* dake shirya kayan abinci a dinning duk da ba lokacin cin abinci bane, mik'ewa tayi ta kallesu tace "Bismillah Harira, ku zo ku ci abinci."

Daga ita har Adamu babu wanda yace a'a saboda dama basuyi karin kumallo ba suka fito, k'arasawa sukayi suka zauna akan kujerun suna jinsu kamar akan wuta, suna kallo Wassila ta gama shirya komai ta zubawa kowa ta aje masa gabanshi kafin tace "Aci lafiya."

Tana tafiya suka fara tsakurar abinci cikin kunya, Sameera kuma da dama ba ci za ta yi ba saboda ta ci abinci lemu kawai take sha, ganin suna kallon farantin dake gabanta yasa ta d'an fara kaiwa bakinta ita ma, ganin sun kasa sakewa yasa ta mik'e tace "Ina zuwa ko, ku ci dan Allah sosai, ku saki jikinku kamar gida kuke."

Kicthen ta nufa inda suka bud'e sosai suka dinga cin abinci suna had'awa da naman ciki da lemu, saida sukaji cikinsu yayi k'at alamar ya cika kafin suka sarara suna kallon shi kanshi wajen cin abinci, sai lokacin Sameera ta fito tace su dawo falo, nan suka samu wuri suka zauna kafin Sameera tace "Harira, kince kun zo gani na ne, Allah yasa dai lafiya?"

Saida Harira ta nisa sosai kafin tace "...

*Kuna son ci gaban labarin ne ko kuwa???*

*Barkanmu da sallah, Allah ya maimaita mana ya karb'i ibadunmu.*
27/05/2020 à 14:46 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💕 _*MASOYA NA*_💞

_Bismillahir rahamanir rahim_

_2_

"Sameera mun zo neman taimakonki ne, dan Allah ki taimaka mana kamar yanda Allah ya taimake ki, ki wa yallab'ai Abbas magana akan iyayenmu da ya sa baki a fito da su, wallahi muna cikin wani hali saboda rashinsu a kusa da mu."

Shiru tayi tana goge hawaye kafin ta ci gaba da cewa "Sameera a dalilin abinda iyayenmu suka aikata yasa duk k'auyenmu an tsanemu, k'annan mu basa iya shiga cikin yara suyi karatu ko wasa ba tare da an tsagwamesu ba, haka muma dake manya a cikin hantararmu ake, ana fad'a mana an gadar mana bak'in hali, son kud'in iyayenmu yasa suke d'aure, Sameera in tak'aice miki wallahi aurena ya mutu saboda maganar iyayenmu nan, shi ya sa muka ce bara mu zo mu rok'i alfarma ko zaku iya taimaka su fito, izuwa yanzu nasan sunyi nadama tare da tuba akan zunubinsu."

Cike da tausayi Sameera tace "Allah sarki, a gaskiya Harira na tausaya miki, amma meya shafi matsalar iyayenki da aurenki kuma?"

Kallonta tayi tace "Sameera kinfi kowa sanin halin mutanen k'auye, abu k'ank'ane suke mayar dashi babba, da k'yar akayi aurena saboda kafewa da dangin mijina sukayi wai ba zai aureni ba, da k'yar akayi auren amma da nasan abinda zai faru a gidan aurena kenan da banyi auren ba ma, tun bayan aurenmu nake fuskantar matsi da takura a wajen iyayen mijina, ina hak'uri sosai wajen zama dasu tare da hak'urin da mijina ke bani, ko shekara bamuyi suka saka shi dole ya k'ara aure saboda cewa ban haihu ba, matsala ta sake rub'anya ne daga lokacin da amaryarshi ta zo, ita ma matarshi d'orawa tayi daga inda yan uwanshi suke min rashin mutunci, kullum habaici da k'ananan maganganu da zagin iyayena suke, a shekara d'aya ta haihu ni kuma shiru har lokacin, a haka na d'auki tsawon shekara hud'u ina wannan rayuwar har ranar da Allah ya kawo k'arshen zamana a gidan, kuma hakan ta faru ne sakamakon fad'an da mukayi da amaryarshi saboda ta zagi iyayena, nan ya goyi bayanta ya fad'a min magana sannan ya sake ni, kinji abinda ya faru Sameera, yanzu haka muna zaune tare da k'anwar mahaifiyarmu ce wacce mijinta ya rasu da kuma 'ya'yanta, wallahi ba zamu tab'a cewa muna jin dad'in zama da ita ba, saboda babu abinda take taimaka mana da shi duk da cewar tana sana'a."

Kuka sosai take saida Sameera ta koma kan kujerar da take ta dinga rarrashinta, kallon Adamu tayi tace "Adamu kuyi hak'uri dan Allah, naji uzurinku kuma na tausaya muku sosai, amma ku sani ko Dadyn mamana (Abbas) bana jin yana da hurumin da zai iya fito da iyayenku, dalili kuwa shine an kamasu da laifin dumu-dumu kuma su da kansu sun amsa, hukunci ne aka yanke musu wanda dole sai su gama wa'adinsu, kunga kenan bana jin akwai taimakon da zamu iya yi muku akan maganar nan, yanzu hukuma ce ke da wannan hakk'in amma bamu ba, amma dan Allah kuyi hak'uri, amma a shirye nake da na muku wani taimakon idan kuna buk'ata."

Adamu ne yace "Yanzu kenan babu abinda zaku iya yi mana?"

Jinjina kai ta d'anyi tace "I think so." Kallon idonta yayi duk da haibar matar na mishi kwarjini amma haka ya daure yace "Amma idan kuka janye k'arar tare da yafe musu laifinsu ai ina ganin za'a sake su."

D'an murmushin gefen labb'a tayi tace "Adamu kenan, magana ake fa akan wad'anda aka yankewa hukuncin."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kuma fa hakane, to yanzu meye abunyi dan Allah? Muna neman taimakonki Hajia, nasan idan kila saka baki zai iya yin wani abu akai."

Dafa kafad'ar Harira ta kumayi tana kallonta tace "Harira ku nemi wani taimakon, amma maganar gaskiya Dadyn mamana ko maganar da zata tuno mishi da baya baya so anayi."

Kallon kallo sukayi tsakaninsu kafin Harira tace "To in wannan ba zai samu ba Sameera ki taimaka min da ko shara ce ko wanke-wanken a gidan nan, ko na samu abinda zan dinga samarwa k'annan mu abinci."

Adamu ne yace "A'a Harira, bake ke da wannan hakk'in ba, nine ya kamata na nemi aiki dan na ciyar da ku."

Murmushi Sameera tayi tace "To ai ko dukanku kuka samu abinyi farin cikinku ne, dan haka wannan ba matsala bace Harira, in dai aikine kin samu a gidan nan ko da babu abinda zakiyi."

Da farin ciki ta kalleta tace "Da gaske zaki d'auke ni aiki Sameera?"

Ita ma dariya tayi tace "Me kuwa zai hana Harira, insha Allahu zaki fara aiki duk ranar da kika shirya."

"To wane irin aiki zanyi? Dan naga akwai ma'aikata a gidan."

Saida ta tashi daga kujerarta ta koma inda take ta kalleta tace "Um, gaskiya kam babu abinda babu wanda baya yinshi, amma idan zaki iya saiki zauna a b'angare na kina taimakawa ko da yara wajen shirin makarantar da kuma abinda ba za'a rasa ba."

"Shikenan wai abinda zanyi?" Cewar Harira, murmushi kawai ta mata mai tsadar gaske, Adamu ne yace "Wannan ma da kika mana mun gode sosai Hajia, Allah ya saka da alkairi."

"Ba komai." Ta fad'a a tak'aice, Harira ce tace "Yanzu yaushe zan fara aikin?"

"Duk ranar da kike so Harira." Cewar Sameera, da azama tace "Ko gobe ma zan iya dawowa?"

Dariya Sameera tayi tace "To da wannan me zai hana ki bari har jibi, lokacin munyi magana da Dadyn yara."

"To shikenan, hakan ma yayi, Allah ya nuna mana jibi, mu zamu koma Hajia, mun gode sosai Allah ya saka da alkairi." Harira ta fad'a suna mik'ewa, itama mik'ewa tayi tace "Ina zuwa ko."

D'akinta ta shiga kusan mintuna ta d'auka kafin daga bisani ta fito rik'e da leda babba a hannunta, tana zuwa ta mik'awa Harira tare da kud'i har dubu biyar tace su shiga mota, sai kuma Adamu data bawa kud'i shima har dubu arba'in tace "Ga wannan ka fara juyawa ko kafin muga yanda abubuwa zasu tafi."

Har k'asa ya duk'a yana mata godiya ita kam kunya ce ma ta isheta saboda ya na gaba dasu, da haka suka juyo suka taho suna godiya sosai, tun a hanyarsu ta komawa Harira ta fara sak'awa zuciyarta wasu abubuwa na daban, tabbas ganin Sameera a wannan halin yasa ta ji tana hassadarta, abun takaici wai har su nemi alfarmarta ta kasa yi musu, wannan shine dalilinta na neman aiki gidan, saboda tana so ta cimma wani buri da yau ne ta kitsashi a zuciyarta, inda Adamu kuma yake ganin taimakon data musu ma yafi wanda sukaje nema mahimmanci, koba komai iyayensu sune masu laifi, laifinsu ya shafesu ta yanda shi kanshi harya rasa aikin lebarancin da yake ciyar da iyalinshi dashi, amma yanzu gashi ta bashi jarin da zai iya tsayawa da k'afar sa k'am, da wannan tunanin suka isa k'auyen su, tun a hanya suka rabu inda shi ya nufi gidanshi ita ma ta nufi gida.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Bayan tafiyar su da kamar minti ashiri *Bilkisu* ta shigo gidan tare da *Imranatu* dake d'auke da yaronta, kamar dai yanda suka saba kullum yanzu ma da sallama suka shigo Sameera ta amsa musu, kai tsaye Bilkisu kitchen ta nufa tana fad'in "Matar Abbas nasan dai ba kya rasa abin dad'i a gidanki, dan haka bara na samo abin tab'awa."

Imranatu ce dake shirin zama ta aje yaronta tace "Ke dai wallahi anyi acici, ke ba kya da aiki sai ki kai bakinki."

Tana kusa da shiga ta juyo tace "Lafiya ce ta kawo haka, da babu lafiya sai kun dinga lallab'a ta akan na ci."

Dariya Sameera tayi tace "Gaskiya ta fad'a kuma, amma kuma abin mamakin bata tashi ciye-ciyenta sai ta zo nan gidan, bansan me ya sa ba?"

Imranatu ce tace "Baki ji tace ba kya rasa kayan dad'i ba, ai da wannan ne kika rabamu da mazajenmu ta yanda basa iya cin abinci idan ba nan ba."

Cike da murmushi tace "Kuma na samu kan mijina ba, kuma ai idan kuka so zaku iya rik'e su gidanku du dinga cin abinci."

Hannu ta mik'awa yaron daya fara zagaya tsakiyar falon da rarrafe tace "Oya *Muhsin*, come on beby."
Chapter 15 · 0% Book details