← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 198

Sashe 103

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_32_

*Jan layi biyu* shine abinda ya nuna, tana rintse ido taji hawaye sun kwaranyo mata, bud'e baki tayi tana so tayi salati kuma ta kasa, shiru d'akin ya d'auka inda Hamna ta k'ura mata ido tana karantar yanayinta, ganin sai zufa take yasa ta taka kusa da k'ofa ta kunna mata ac ta juyo ta dawo tace "Ummy lafiya? Me yake faruwa?"

Girgiza kai Ummy tayi ta bud'e idonta da k'yar wanda suka mata nauyi, gaba d'aya d'akin ne taga yana juya mata kamar zai kifata k'asa, hakan yasa tayi saurin matsawa jikin gado ta zauna tana dafe kai, ita ma zaunawa tayi ta dafata murya a raunane tace "Ummy dan Allah ki fad'a min meke faruwa?"

Saida ta sake lumshe ido tace "Hamna, ciki ne dake, ciki Hamna, cikin Ammar jikinki, Hamna na shiga uku na lalace, ban san ina zansa kaina ba, Hamna ki tayani rok'on mutuwa kafin lokacin da kowa zai san abinda ke faruwa..."

Kukan daya ci k'arfin ta yasa dole tayi shiru ta fara rizgar kuka, Hamna data daskare a wurin kamar an zuba mata ruwan sanyi, ta nema hawaye a idonta ta rasa, zuciyarta ta cunkushe ta yanda taji ta kasa maganar zuci ko tunanin abunyi, ta rasa fahimtar yanayin da take ciki, farin ciki? Ko bak'in ciki? a lokacin sai taji tafi tausayin Ummy ma fiye da ita kanta, dawowa tayi hayyacinta ta fara rarrashin Ummy tana fad'in "Ummy ki daina kuka, wannan *ita ce k'addarar mu*, mu rumgumeta hannu bibbiyu Ummy, mu mayar da al'amarin mu ga Allah shi zai mana mafita."

Kallonta Ummy tayi tace "Hamna na daina kuka fa kike cewa? To me zanyi inba kuka ba? Ciki fa nake fad'a miki kina da, ko dai ba kya fahimta ne? Cikin d'an mutum ne jikinki cikin haihuwa, wanda kika samu sanadiyar kwanciyar da Ammar yayi da ke, ki fahimci tashin hankalin da muke ciki mana."

Kawar da kai tayi tace "Tashin hankalinmu na yanzu ba shi zai hana mu shiga na gaba ba, zaifi kawai mu tanada kukanmu a tashin hankali na gaba."

Tsayawa tayi da kukanta ta kalleta, tabbas abinda ta fad'a hakane, to kenan ya zasuyi? Hajia kullum son ganin laifinta take ta yanda zata tozarta ta, a girman laifin data aikata ma a yanzun zata iya sakawa lieutenant ya saketa, dan haka ta mik'e tsaye tace "Zan samo mana mafita Hamna, wannan abun ba zamu bari ya fito ba, ke dai ki ci gaba da b'oyewa kar kowa ya sani, zuwa gobe zamu san abunyi, yanzu mu fita kar a d'auka wani abun muke."

Mik'ewa tayi tana kallonta tace "Ummy me zakiyi? Dan Allah ka da ki saka kanki a had'ari saboda ni, kawai ki bari kowa ma yaji, k'addara ce wacce babu wanda ya isa ya kauce mata."

Hannunta ta kama tace "Ke dai mu tafi, ai ba kowa zai fahimci haka ba, hakk'i na ne Hamna na kula da ku, amanarku aka bani."

Fita sukayi aka ci gaba da hidimar dasu, sai dai ko kad'an babu walwala a tare dasu, Hamna kuma dake tare da k'awayen ta wanda ta gayyata lokaci bayan lokaci saita shafa cikinta, a hankali take furta kalmar "Ciki." Da haka aka gama shagalin yau sai kuma na gobe idan da rai.

*Washe gari*

Tunda asuba Ummy ta samu Hamna suka keb'ea farfajiyar gidan, saida ta gyara hijabinta da tayi sallah dashi tace "Ummy lafiya kika kirani yanzu?"

Kallonta tayi sosai tace "Hamna bacci kikayi wai?"

D'an turo baki tayi gaba ba tace komai ba, murya k'asa k'asa tace "Hamna, na samo mana mafita, amma kiyi alk'awari zakiyi duk yanda na ce?"

Cike da sangarta tace "Ummy ina ji, bacci fa nake ji har yanzu."

Da tsantsar mamaki Ummy ta kalleta tace "Hamna anya kuwa kinsan abinda kike yi, gaba d'aya fa kina nuna kamar abun bai dameki ba."

Take fara'arta ta d'auke ta kalli Ummy tace "Ummy raba dare nayi ban iya rintsa ido na ba, tunani na yafi karkata kan yanda yer uwata zata d'auki al'amarin idan taji."

Cike da damuwa Ummy tace "Hamna dole ne ki tuna yer uwarki a wannan halin, amma ni nafi tunanin wani abun daban, kinsan me nafi tunani?"

Girgiza kai tayi alamar a'a, ci gaba tayi da cewa "Hamna Hajia, kinfi kowa sanin yanda ta tsani d'an da bai fito ta hanyar aure ba, domin kuwa saboda hakane ma kika ga tana nunawa kawunku Labaran k'iyayya har da ma yayanshi, kiyi tunanin hukunci ko matakin da zata d'auka, ga kuma kawunku wanda jin hakan ba zai masa dad'i ba, sannan Ammar, Hamna a tak'aice bansan wane kallo zai yiwa al'amarin ba, ina tsoron abinda zai iya faruwa."

"To Ummy yanzu meye abunyi?" Saida ta kalli k'wayar idonta sannan tace "Hamna zan karb'i cikin nan naki, ma'ana ni ya kamata kowa yasan inada ciki, bayan kin haihu saina karb'i abinda kika haifa kamar ni na haifeshi, in kuma ba haka ba Hamna sai dai a zubar da cikin nan tun kowa baisan da maganarshi ba."

Wani irin tsamm taji jikinta yayi, sai yanzu ne ta gane girman al'amarin daya tunkarota, maimakon tace wani abu saita fashe da kuka ta rumgume Ummy, ita kanta Ummy kuka ta sanya, sun fara rera kukan kenan kuma sai Ummy ta dakata ta d'ago Hamna tace "Hamna ya kike so ayi? Wallahi bana son kowa yaji labarin nan, bayan b'acin rai da zan gani har da kunya, Hamna zanji kunya sosai ta iyayenki, ki amince da d'aya daga cikin zab'in nan Hamna."

Cikin share hawaye tace "Ummy ina jin tsoro sosai wajen zubar dashi, idan wani abu ya faru sai kin fi ganin b'acin rai."

"To kenan kin amince na zama uwar jikana?" Ummy ta fad'a tana mai kafeta da ido dan jiran amsarta, kallonta ita ma tayi tace "Amma taya haka zata faru Ummy?"

Murmushi ta mata tace "Kin manta ni likita ce? Hamna inhar kin amince wannan ba matsala bane, zamanki gidan nan ne kawai zai bamu matsala."

"Kamar yaya?" Ta sake fad'a kanta a matuk'ar d'aure, saida suka gyara tsayuwarsu da kyau sannan tace "Zan fad'awa kawunku ina da ciki, akwai tablet d'in da zan fara sha wanda zai sauya min yanayi na, daga yanzu har zuwa lokacin da cikinki zai shiga wata hud'u zaki zauna a gidan nan, amma fa sama da wannan lokacin ba k'aramar barazana bace garemu ki ci gaba da zama anan."

Yamutsa fuska tayi alamar mamaki tace "To Ummy ina zan koma? Kinsan Hajia bata barinmu fita haka kawai, bare na koma wani wuri da zama, makarantar dana shiga ma ta koyon kwalliya da yaya na samu ta barni Ummy?"

Dafa ta Ummy tayi tace "Yanzu dai mu fara da wannan, kafin tafiyar tayi nisa zamu san abunyi a gaba."

Cikin raunin murya tace "Ummy ina jin tsoro, kar wani abu ya faru kuma a d'ora miki laifin komai."

Murmushin yak'e ta mata tace "Karki damu, koma me zai faru zan d'auka, kuma in dai har zakiyi yanda nace miki to babu abinda zai faru da yardar Allah."

A hankali ta jinjina kai tace "Shikenan Ummy, zanyi duk abinda kika fad'a min."

Murmushi ta mata sosai tace "Yawwa yarinyata, yanzu da fari ki zama jaruma, duk abinda kika ji ki dinga k'ok'arin jurewa sannan kiyi gaggawar fad'a min, ko da baki jin dad'in jikinki ka da ki bari kowa ya sani idan ba ni ba, ni kuma yanzu zan bawa *Mamuda* (dreba) kud'i ya siyo min wani magani a pharmacie, idan kika karya kumallo sai ki sha."

Jinjina kai ta sakeyi sannan Ummy ta jata suka koma ciki, kamar yanda ta fad'a bayan anyi karin kumallo ta bata magani tasha sannan suka tafi wurin wuni na biyu. Da magrib lokacin da ake shirya amare dan halarta wata walimar a lokacin kuma aka shirya aka tafi wankan angaye, kasancewar wankan farko ne dangin uwa ne sukeyi yasa Jibril yana b'angaren nashi uwa, Junaid ma haka sai kuma Ammar da Amar wanda suke gidan *Zulai* wacce yaya ce ga Sa'ada sai dai ba uwa d'aya ba haka kuma ba uba d'aya ba, dan ita duk danginta da suke ciki d'aya suna Agadez, Amar ya riga Ammar isa gidan sosai, dan har saida yayi nashi wankan ya fito sula tafi da nashi abokan Ammar bai zo ba, hakan yasa dangi suka fara fad'a da tsegumi suna fad'in Ammar ya raina mutane, wasu har sunyi shirin tafiyarsu suka ji rubdugun motoci kamar zasu fasa unguwar, a k'alla mota ma tafi guda ashirin, moto kam ko tunanin k'idayasu ma bakayi, (infa baku manta ba abokanshi ma manyan mutane ne wanda na b'oye sunan wasu kuma anan gaba zan canza sunan wasu saboda tsaro), tabbas abokai sun mishi kara tun anan, kuma dama Ammar mutum ne ruwa biyu, yana kyautata alak'arshi a waje ga kuma mutanen kirki, akasin haka kuma zakaji ba dad'i, magana dai ce zai iya fad'awa koma wanene kai kuma babu ruwanshi.

Dangin sun fito waje dan ganewa idonsu amma abokan Ammar da yake akwai shak'iyai ciki kamar shi sai suka bud'awa Ammar hanya yana shiga cikin gidan suna mishi b'arin kud'i, kud'in ma sababbi kar dasu ko karyawa babu, (harkar fa ta manya ce), haka Ammar ya dinga ratsa kud'in nan wasu har takasu yake yana shiga cikin gidan, *gaba da gabanta*, sai gashi kama daga yara har uwayen suna bin bayan kud'in nan da suka ga in aka watsa ba'a komawa ta kansu suna wasoson d'auka, nan fa gidan ya hargitse da hayaniya ana ta ihu ana tsintsar kud'i, saida ya kai k'ofar ban d'akin da zai shiga wankan da taimakon jagorancin k'anwar Zulai sannan suka daina watsa kud'in, wani daga cikin abokan ne mai sunan *Pappa* ya kalli sauran yace "To mu jira shi ya fito sai mu d'ora ko."
Chapter 103 · 0% Book details