← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 198

Sashe 5

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata tattausan murya ce daga bayansu aka ce "Yallab'ai ga shayin."

Hassan ne ya juyo ya sauke idonshi akan kyakyawar matarshi, hannu yasa ya karb'a yace "Nagode uwarsu Ammar."

Murmushi ta sakar masa mai tsadar gaske tare da kallon Gambo tace "Sannu da zuwa gwamna, ya hanya?"

Da fara'a ya amsa mata da "Alhamdulillah madame, ya muka same ku?"

"Lafiya lau muke? Ya mutan can d'in?"

"Lafiya lau, ya 'yan rigamarki (su Hamna ba)?"

Murmushi tayi tace "Yara na ai sun girma yanzu sun daina rigima."

"To zan gani dai, dan banga alama ba sai dai ko Amna."

Hassan ne ya mik'a mata kofin shayin tare da karb'ar hularshi kalar shud'i ya d'ora akai ya daidaita mata zama yanda a dace, (ikon Allah, idan dai na fahimci wani abu wato duk gidan nan boko ce ta yanke musu cibiya, lallai wasu kayan sai amale), *lieutenant Hassan Suley Hassan Gaga* babban douane na garin Maradi, murmushi ya sakar mata yace "Mu zamu fita kuma sai Allah ya mana dawowa."

Murmushi ita ma tayi tace "To muje na raka ka ko, ko ba kya son addu'ar tawa yau?"

Murmushi yayi daya bayyanar da hak'oran shi yace "Zan iya hak'ura da tenue (kaki) na amma ba dai addu'ar ki ba."

Wucewa sukayi ya dafa kafad'ar Gambo yana fad'in "D'an lukuti saina dawo."

Murmushi kawai yayi yace "A dawo lafiya, madame ke ba zaki tafi wajen aikin ba yau?"

Juyowa Hassan yayi yace "Ai saita fara iza k'eyata gaba take tafiya."

Dariya sukayi suka fice shi kuma ya nufi d'akin Hajia dan ya fara kai mata gaisuwa, Hamna ce ta sake fitowa ta d'oro hijab akan kayan baccinta sai Amna a bayanta, kallonsu yayi da sauri Amna tace "Bonjour (ina kwana) Abba."

"Bonjour." Ya fad'a yana tafiya ya d'ora da "Attend moi ici (ku jira ni anan), je salut mes parents (zan gaida iyayena)."

Amna ce dai ta amsa da "Ok Abba."

Yana isa a lokacin kuma Hussein ya fito, sallama ya mishi ya fito da zuwan saiya dawo, ganin su Hamna zaune a falon yasa ya kallesu yace "Yarana ya dai?"

Gaishe shi suka fara yi, kafin suce wani abu kuma Ammar ya shigo ba sallama, hasalima fuskarshi had'e take saboda yaga kankana a wurin, amma yana ganin kawunshi sai kawai ya k'ame wuri d'aya tare da sara masa wai shi a dole soja ne, shi ma colonel d'in sara masa yayi tare da dafa kafad'ar shi yace "Bien réveillé (ka tashi lafiya)?"

Cikin k'amewa irin ta sojoji ya amsa da "Oui chef."

Kamar wanda suka had'u a filin daga haka shima colonel d'in yace "Da kyau, yanzu kaje ka fara da motsa jiki, kar ka ci abu mai nauyi sosai, sai ka wuce wajen aiki, compris (ka fahimta)?"

Da k'arfi ya amsa da "Tout de suite (yanzu kuwa) chef."

Sai lokacin ya saki jikinshi tare da d'an fad'awa jikin kawun nashi suka yi gaisuwa cikin nutsuwa, sai lokacin yace "Tonton (kawu) na d'auka hutu ka zo mana ai, ya kuma zaka fita yanzu?"

Ba tare daya saki hannunshi da sukayi musabaha ba yace "Ba jimawa zanyi ba, wani taro ne zanje anan *gazawa*."

Ba karsashi yace masa "Saika dawo tonton."

Fita yayi daga falon ya wuce inda zashi, Ammar kuma juyowa yayi inda su Hamna suke zaune, ai yana kallonsu sai kuwaHama ta bushe da dariya, Amna baiwar Allah tana so ta dara amma ba dama, k'ara tsumimiye fuska yayi yana kallonta baice komai ba, ita ko dariya take shek'awa kamar zararra harda tashi daga kan kujerar ta koma bayan Amna tana fad'in "Oui chef, hhhhhhhhhh, tout de suite chef, wayyo cikina harya k'ulle, yer uwa."

Ta fad'a tana tab'o Amna ta ci gaba da fad'in "Allah dai wani ya zare a gidan nan saboda bai samu abinda yake so ba, kullum shine fad'in, oui chef, a vos ordres chef, caca-caca, kai haba ina."

Kwabar dake gefenshi ya kallasai kuwa yayi sa'ar samun faranti na tangaren, d'auka yayi ya saita daidai kan Hamna zai jefa sai kawai kawunshi Gambo ya fito tare da Hajia da kuma Alhaji, sauya akalar farantin yayi cikin dubara ya aje shi mazauninshi, Hamna na ganin haka ta mishi gwalo tare da kwaso wata shegiyar shoki ta watso mishi a fuska tana fad'in "Eh, eh-eh-eh shokiii."

K'wafa yayi a zuciyarshi kawai ya juya ya bar d'akin, lokacin kuma Hajia Husseina da Soueba suka fito tare suma, da haka har falon ya sake cika da iyalin Gaga yara da manya, saidai kowa yana haramar tafiya sabgar gabanshi ne, yara da matasan école (school) suka nufa, sai samarin dake fitowa cikin nasu shirin tafiya ma'aikatunsu.

Hamna da suka saka mahaifinsu tsakiya sai shagwab'a suke masa, Ammar da Amar ne suka shigo tare, k'are musu kallo Hamna keyi tana son banbance boss da kuma Amar a ciki, dan dukansu riga ce chemise a jikinsu kuma fara k'al, kuma dukansu basu b'alla botira biyu ba na sama, haka ma wandon jikinsu mai duhu ne sai dai ba kala d'aya ba, zaka fahimci hakane idan sun matso kusa da kai, sannan takalmin k'afar su iri d'aya ne da kuma gilashin idonsu fari mai kyau, a ciki ba zata iya cewa ga boss ba dan bata gama fahimtar Ammar ne ya saki fuskarshi ko kuma Amar ne ya had'e rai kamar boss, cikin takonsu na zataran maza majiya k'arfi suka k'araso kusan kawunsu, mik'ewa yayi tsaye suka rumgume juna da su cikin farin ciki da k'aunar juna, saida suka raba jikinsu Gambo ya kallesu da kyau yace "Yaran nan raina min hankali zakuyi ko? To a ciki ina Ammar?"

Wani ikon Allah sai kawai Amar ya d'an saci kallon Hamna lokaci d'aya kuma ya d'auke kanshi, ai kuwa Hamna sai cewa tayi "Abba ga boss nan." Ta fad'a har da nuna shi da yatsa.

Tare suka kalleta amma tana had'a ido da Ammar d'in sai taji gabanta ya fad'i da k'arfi, Gambo ne yace "Waya saka dake?"

Turo baki tayi shi kuma ya sake kallonsu sai Ammar daya matso kusanshi yace "Tonton."

Murmushi yayi yace "D'an soja ya aikin na ka?"

Cikin gimtse hak'ora ya amsa da "Pa mal (ba wuya) tonton."

Kafin yace wani abu ya sake cewa "Tonton je dois mon aller (ina so zan tafi), j'ai une visite dan quelque minute ( ina da wanda zan gani nan da 'yan mintuna)."

Kafad'ar shi ya dafa a lokacin Amar yace "Amma dai tonton zamu sameka gida ko?"

Kallonshi yayi yace "Pourquoi tu demande ça (me ya sa ka tambaya)?"

Kallonshi shima yayi yace "Parce que hier j'ai reçu une carte d'invitation en fecebook dans mon counte (saboda jiya na samu wani katin gayyata a fecebook a ma'ajiyata), ce pour cela je demande (shiyasa na tambaya)."

Kallonshi kawai gwamna yayi dan ba zai iya cewa ba haka bane, sai Ammar daya kalli Imminsu wacce ke cikin shirinta yace "Ummi yau ba zaki fita asibitin bane?"

A tak'aice ta amsa da "Ina bayanka."

Kallon gwamna yayi yace "Tonton sai mun dawo."

"Ok yarana, Dieux vous bénisse (Allah ya muku albarka)."

Saida suka sunkuya suka gaishe da Alhaji da Hajia wacce ta hakimce kai kace wata matar gwamna ce, ta tsufa amma bata jin ta tsufa saboda ta tilasta yara suna yin aikin da take so, kowa ya ji k'ara (alerte) a counte d'in shi ita ma sai taji, ko sutura da take sawa kawai ya ishi gidan wasu cefanai na tsawon wata d'aya, saboda k'arfin hali waya ma cewa tayi sai babba take so wanda ake shafawa da hannu, shiyasa in ka kalleta kallon garaje ba zaka fahimci tsufanta ba, yanda Ammar ya gaisheta ne yasa ta yamutsa fuska ta kalleshi tace "Da ka rik'e gaisuwar taka ai, idan baka sunkuya ka gaisheni ba to ubanka har k'asa zan sashi ya duk'a ya gaishe ni, kuma bai zama lalle na amsa ba, imbécile kawai."

😂 *(Romo kenan)*

Ammar kuma da dama shi dai yake jin haushin hana shi abinda yake so da tayi shiyasa basa shiri, juyawa yayi zai wuce ya kalli Ummi data mik'e ita ma, daf da ita ya matso zai wuce ya fita murya k'asa k'asa tace "Ban yafe maka ba in har baka gasheta da kyau ba."

Cak ya tsaya tare da cije leb'e da k'arfi, shi dai ya rasa wace irin rayuwa ce wannan, komai k'ank'antar abu sai Ummi tace ban yafe ba, k'wafa yayi cikin zuciyarshi ya sake juyowa yaje gabanta, zai sunkuya ta d'aga mi shi hannu tace "Wallahi ka durk'usa saina tsinkeka da mari a wurin nan, ni zaka rainawa hankali, in tsuguna in haifi ubanka amma kana jin haushin gaisuwar fatar bakin da zaka min wai har sai uwarka ta saka ka, kenan albarkacinta na ci? To bana so ka rik'e tsiyarka, amma ka tambayi ita kanta uwar taka, ta shigo gidan nan ne saboda ni na zab'i ta shigo, sannan tana zaune a gidan nan ne har yanzu saboda ina so, kuran waya d'aya tak ya isa ya jefa uwarka a layin zawarci."

Ammar dake tsaye zuciyarshi sai bugawa take, hannunshi na dama sai rawa yake yana ji kamar ya kai mata haura guda, k'ara damtse leb'en shi yayi sosai ya kalleta da jajayen idonshi, a hankali ya d'auke idonshi ya kalli gefenta sai kawai Ummi, k'wayar idonta ya kalla ya ga sun cika taf da hawaye, da ido ta mishi alamar "Hankalinka ya kwanta yanzu?"

D'auke idonshi yayi yana ji kamar ya k'urma ihu, tafin hannunshi yasa ya dafe goshinshi yana d'an murza idonshi da yatsunshi ta k'asan gilashin shi, saida ya sauke ajiyar zuciya har sau uku kafin ya sake kallon Hajia, zai kuma durk'usawa dan bata hak'uri cikin tsiwa tace "Na fad'a maka wallahi saina mareka idan ka durk'usa gabana."

D'ago kai yayi daga shirin sunkuyawar ya sauke a kanta, a ranshi yace "Wai ni ya zanyi da tsohuwar nan ne?"

Ummi ya kalla danya nuna mata shifa ba zai zauna anan ya b'ata lokacin shi ba, sai yaga har yanzu wannan kallon ne take masa, ya kuma sani ita ma yanzu in suka je asibiti abinda zata mishi kenan, wani k'aramin tsaki yaja wanda bai ma san ya fito fili ba, muryar Alhaji ta dawo dashi yana fad'in "...
Chapter 5 · 0% Book details