Sashe 62
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana zuwa cikin takon rashin mutumci ya shiga hotel d'in, zuwanshi yayi daidai da Hamna na sakawa wani saurayi a cikin abokan ango lambarta a wayarshi, k'are mata kallo yayi, har zuciyarshi fa shi ya zo ne da niyyar ci mata uwar raina musu hankalin da tayi a gida, amma yana ganinta cikin ankon shagalin duka yan matan riga da siket ne jikinsu na less, amma yanda suka fitowa da da Hamna komai na jikinta saida yaji zuciyarshi ta buga, abinka ga mai yar k'iba k'irjin nan an fito dashi ya tsaya tsam-tsam, ga faffad'an k'ugun nan ya fito da kyau, d'aurin d'an kwalin dake kanta iya rabin kan kawai ya tsaya, inda manyan kitsonta na gashin doki (atach) ya kwanta a bayanta har yana kusan kaiwa a k'ugun, wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi, gani yake kaf mazan wurin surarta kawai suke kallo suna yabawa, jinjina kai yayi irin yana nufin zaki ci ubankin nan kafin yace " Wato ni zata rainawa wayo?"
Daidai Hamna ta mik'awa saurayin wayarshi cike da jan aji zai karb'a idonta ya sauka kan boss, fad'uwar da gabanta yayi da d'aukar rawar da jikinta shima yayi yasa ta mantawa harta saki wayar bada gangan ba, saida taji fad'uwar wayar kuma tayi sauri ta kalli wayar ta rufe baki da hannu, zata sunkuya ta d'auka kuma Ammar na daf da kawowa, d'an girgiza kanta tayi a ranta tace "Wallahi wannan kallon rashin mutumci ne yake min, ba zan zauna ya kunyata ni ba cikin mutane."
Ai saita mik'e ta kalli saurayin tace "Kayi hak'uri dan Allah."
Fittt, ta kutsa cikin taron tana neman mafaka duk da saurayin na fad'in "Ba komai."
Tsaye yayi gaban saurayin daya sunkuya ya d'auki wayarshi, kasancewar sun san juna yasa ya figzi wayar ta shi, ganin lambarta rau akan écran d'in daya fara tsagewa yasa shi goge lambar ya cilla mishi wayar, rashin sanin zai cillo mishi yasa bai rik'e ba wayar ta sake fad'uwa k'asa, rai b'ace saurayin yace "Ammar meye haka? Ya zaka fasa min waya?"
Gwa da gwa ya kalleshi yace " Ita data saki ta fashe murmushi ka mata ka ce ba komai da yake mace ce ita, amma tunda ni gardi ne shine zaka nuna min karuwanci ko, to na fasa *Abdu* ci min uwa."
D'aga hannu Abdu yayi yace "Allah ya baka hak'uri, wuce." Ya fad'a dan yasan shi fa k'aramin aikin shine a wurin su zubar da kwadon rashin kirki, gashi dai mutum mai ilimi da aji amma wani lokaci kamar jahili.
Wucewar ko yayi ya ratsa mutanen suma, duk k'ok'arion shi na son ganota ya gagara, dan haka ya dafe k'ugu yana tunanin abinyi, duk da akwai maza wurin amma mata da iyaye sunfi yawa sai tarin yara, murmushi yayi ya nufi wajen mc dake sako baitoci, yana zuwa ya d'an mishi magana a kunne kamar abun arzik'i, hakan yasa mc d'in mik'a mishi amsakuwar (micro) d'in hannunshi ya tsayar da wak'ar dake tashi a wurin, Ammar kuma wayarshi ya ciro ya d'anyi danne danne kafin ya saita wajen sautin wayar ya jona a micro d'in, yana danna play sai ji kake
*Tatatatatatatatatatatata!!!* 😂😂😂k'arar bindiga, ba mata ba da suka fashe da k'ara da ihu har maza wanda ke tsaye zaune yayi, wanda ke zaune kuma ya fad'o daga kan kujerar, yara ma ihu suka saka inda wasu kuma yaran ke ganin kawai nishad'i ne sai kuwa suke da tafi, lokacin da wasu suka rage tsayi ta hanyar durk'ushewa da yin kwance lokacin ne ya hango kankana da ita kuma tsoronta na ganinta da boss zaiyi, kallon mc yayi ya mik'a mishi micro ya kashe satin wayar tashi ya wuce wajenta, ta juya dan son ganin ina yake sai kuwa sukayi tozali.
Tsoron daya gani a idonta a lokacin ya sani da zai auna jininta zaiga ya hau, matsawa yayi daga gabanta fuska ba annuri yace "Wuce muje gida."
Ita kam da a gida ne tasan zata samu masu ceto, amma anan? Kuma yace su tafi gida? Tab'idjam! Hayaniya ce ta kaure a wurin na son sanin abinda ya faru, ganin babu mai kulasu hakan ne ya bata damar saka kuka tace "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri ka bari har muje gida, a kan motona na zo fa."
Wani murmushin mugunta ya sakar mata tare da jerawa kusa da ita ya kama hannunta, a tare suka ji wani shocking ya baibaiye su, sororo take kallonshi tana zubo da hawaye tana ci gaba da bashi hak'uri, hankalin mutane ma baya kansu Hamna kuma har juyowa take taga ko da wanda zai iya rabata dashi, amma wak'ar da aka saka yasa hankalin kowa ya koma kan yaran dake rawar, suna fitowa ta kan matantakalar dake k'ofar shiga da ba tafi uku zuwa hud'u ba, yana saukowa daga na d'aya dana biyu ita kuma ta cije ta k'i gusawa, juyawa yayi ya kalleta, haushi ne ya sake kama shi wai akan me zata dinga fita haka tana tallar kanta a waje, k'wafa yayi tare da zagaya hannunshi ta bayanta kan cinyoyinta, d'aya hannunshi kuma ya kamo nata hannun ya wurgashi kan wuyanshi, cak ya d'auke ta ya d'ora kan wuyanshi ya nufi mota da ita, ihu take tana wutsil wutsil da k'afafu tana so ya sauke ta, boot taga ya bud'e ya nufi nan da ita, ai kuwa yana zuwa ciki ya watsata kamar buhun shinkafa, k'ara ta saki tare zunbura ta taso zaune zata mishi magana d'if ya rufe ta ya koma mazauninshi ya tayar, bubbuga k'ofar ta fara yi tana k'walla kiran yayi hak'uri dan Allah amma ina, dan ita tunaninta wani wurin zai kaita, shi kuma takaicin yanda ya sameta a wurin har tana bawa wani lambarta ne yake k'ara tunzura shi.
Bai kula da tsiyarta ba har suka iso gida ya paka motar, fitowa yayi ya bud'e mata yana hararanta, tayi sharkaf da zufa ga hawaye ga majina, da k'yar ta durko ta fito takalmi d'aya a hannu da wayarta dan ky d'in moto dama yana hannun Nafi, rufe boot d'in yayi yana kallonta sai wani tank'warewa take kamar tsohuwar data gaji da duniya yace "Maza yarinya tattare min wannan shegen siket d'in zakiyi ki min tsallon kwad'i a wurin nan."
Zaro ido tayi tace "Kwa me?"
Dak'uwa ya mata yace "Kwad'i." Belt d'in shi ya k'ok'arin zarewa yana fad'in "Ko ba zakiyi ba?"
Da sauri tace "A'a ni na isa? Zanyi wallahi."
Cire takalmanta tayi d'aya ta aje gefe ta fara tattare siket d'in da k'yar saboda ya kamata, cikin jin haushi yace "Yanzu wannan da zaki saka shi uban wa ya kama miki? Duk kibi ki d'aure jikinki haka ki hana komai numfasawa, mtsssss."
Ita dai ta gefen ido take kallonshi harta tattare, d'an matsawa tayi daga kusanshi ta duk'a kamar gaske zata fara, tana d'aukar takalminta sai kuwa tayi wuf da iya gudunta, kallonta yake yanda take gudun abisa gaskiyarta mazaunanta su ma na neman tsira, abun mamaki wanda ni kaina banyi zatonshi ba shine dariyar da Ammar yayi, domin kuwa duk dariya ko murmushi da yake na iya shege da da iskanci, amma wannan dariyar ta abune ya baka dariya ainin, gyara belt d'in shi kawai yayi ya sake shiga mota ya bar gidan.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
An idar da sallahr isha'i kenan Alhaji ya fito daga d'akin shi zuwa falon cikin wata dakakkiyar farar shadda da taji kud'i, hula agogo da takalma duka farare ne, Hajia na zaune a kujerarta yara na ta yar hayaniyarsu amma cikin nutsuwa, inda matan kuma ke falon sama da yan mata, lieutenant ne ya shigo da alama yanzu ya dawo daga masallaci, kallonshi Alhaji yayi yace " *Babba* kaje ka shirya ka fito yanzu zamu je wani wuri."
Da ladabi lieutenant ya amsa da "To."
Ciki ya shiga Hajia kuma ta kalli Alhaji tace "Ina kuma zuwa da wannan shirin?"
Cikin sigar zolaya yace "Neman aure zan je, ki tayani da addu'a wannan karan na samu."
Wani murmushi ta saki tace "Allah na tuba ka yafe ni, macen da zata iya zama da kai a hakan nan ai sai ni."
Juyawa yayi dan bar mata falon yana fad'in "Dama kuma ke kika mayar da ni hakan."
Had'e fuska tayi a ranta tana fad'in "Wallahi duk da mun tsufa ko yanzu ka ce zakayi aure saina maka tijara, dan kuwa ina k'aunar ka kuma dan ni kad'ai aka halliceka."
Bai jima sosai ba ya fito cikin shirin dogayen kaya shadda kalar maroon da hula da takalmi, k'aninsu Ammar mai shekara sha hud'u wato *Kamal* lieutenant ya kalla yace "Ka fad'awa Ummynku na fita tare da Alhaji."
Shi fa yayi hakane tunda sun rabu da cewa zai tafi masallaci, tunda baisan ina zasu je ba da tsawon lokacin da zai d'auke su shiyasa yace a fad'a mata, amma Hajajju sai tayi mamakin abun da ganin kamar Sa'ada na son shiga hancinta da duk'unk'une ne, da kallo ta bishi har yace mata sun fita amma ko tanke, yana zuwa ya samu Alhaji na jiranshi jikin mota, shiga sukayi suka fita daga gidan sannan Alhaji yace "Gidansu yarinyar nan Zeituna zaka kaini."
Da mamaki ya kalleshi dan shi dai bai ma san gidan ba, Alhaji ne yace "Muje zan nuna maka, na tambayi Iya ta kwatanta min."
Ba tare daya daina mamaki ba yace "Alhaji me zamu je yi a gidansu? Wani abu ya faru ne?"
Murmushi ya masa yace "Alkairi ne zai kaimu, kuma ina fatan ba zaka watsa min k'asa a ido ba."
D'aurewar da kanshi yayi yasa bai iya cewa komai ba sai kwatancen da Alhaji ke mishi yake bi kawai, da haka suka iso dama kuma ba nesa bane da su, sunyi sa'ar samun kawu Mamu a k'ofar gidan zaune ya gama cin abinci, shi ya d'auka ma Jano ne ya dawo har ya mik'e dan gaishe shi cikin girmamawa, amma duk da haka ganin manyan mutane ne saida ya gaisa dasu cikin mutumci da basu girmansu, har zai shiga dan d'auko musu kujeru suka ce ya isa nan ma, zaune sukayi suka sake gaisawa kafin Alhaji yace "...
👏👏👏
16/06/2020 à 13:21 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*