← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 198

Sashe 172

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gambo ne yace "Amma Hajia ko ma menene dalilinta ai bata k'i d'an uwanta ba, ko dan marayunshi ai zata amince."

A hankali Hajia ta kalli lieutenant ta kuma kalli Husseina, kallon Gambo da Hadiza tayi tace "Magana ta gaskiya bai kamata mu ci gaba da b'oye muku ba, ku kuka haifi abarku ya kamata kusan komai dake faruwa kan 'yarku."

Gaban Hadiza ne ya sake fad'uwa dan ita tun farko tayi tsammanin jin wani mummunan abu, kallonta suke sosai kafin ta gyara zama tana fuskantarsu da kyau tace "Kuyi hak'uri dan Allah ku yafe mana dukanmu, sannan zan so ku nutsuwa kuyi duba na tsanake akan lamarin, karku yanke hukunci cikin hushi, hakan zai iya janwo mana dana sani."

Shiru tayo sai Hadiza da tace "Hajia ko me ya faru bai kamata ace kina neman afuwarmu ba, mu 'ya'yanki ne baki buk'atar wannan."

Gambo ne yace "Hakane, koma menene Hajia ai ba sai kin rok'e mu ba."

Numfasawa tayi cike da muryar rarrashi da nuna nadama tace "Shekara biyar da rabi kenan da wata mummunar k'addara ta fad'a kan Hamna, idan kaji ance tsautsayi to akwai ganganci a ciki, shi yasa na ce muku k'addara dan ku fahimta da kyau, k'addarar data tashi fad'a mata ma sai ta fito daga ruhin d'an uwanta Ammar, bayan abinda ya faru ya faru ciki ya shiga jikinta, hakan kuma ya tabbatar mana da lallai wannan abun daya faru rabon wannan yaron ne, dan da wani yayi k'ok'arin shiga tsakanin faruwar wannan al'amari, ko shakka babu wannan rabon zai iya ajalinshi, *Shureim*, shine yaron wanda Sa'ada a matsayinta na uwar yarinyar da kuma yaron tayi k'ok'arin b'oye wannan laifin dan kar mutumcin yaranta ya zube a idon duniya, bata so 'yarta ta rasa kimarta ta 'ya mace, ta d'auki zunubin da hannu bibbiyu ta d'ora akanta, tayi mana k'arya duk dan ta kare mutuncinsu, ta yaudari mijinta dan ta tseratar dasu a matsayinta na uwa, ta nuna mana zata iya yin komai akan 'ya'yanta, tabbas laifi ta aikata amma fa a dalilin soyayyar da take wa yaranta, muyi k'ok'ari mu fahimceta dan Allah, uwa takan iya yin komai ta kan iya tarar kowane bala'i saboda yaranta."

Ajiyar zuciya tayi tace "Da wannan nake nema mata alfarma a wajenku dan Allah ku yafe mata, kuma iyayen yaran nan ne, ku kamalta da idan kune abun ya faru a idonku me zakuyi? Nasan ko baki abinda tayi ba zakuyi makamancin shi."

Tirk'ashi! Yanzu abinda ya faru kenan da 'yarsu da kuma d'an su? Tambayar da suka ma kansu kenan? Sai dai Hajia ta gama sage musu gwiwa, ta gama dasu tunda tace k'addara, babu wanda ke kauce mata inda ta tashi fad'a masa, sannan ta k'ara d'auresu da tace tana nema mata alfarmarsu, uwa ce ita gare su sannan Ummy ta rik'e yaran kamar ita ta haifesu a cikinta, sun gamsu ba tayi haka bane dan ba ita ta haifeta ba, sai dai su ce kawai k'addarar da kuma sharrin shaid'an, bugu da k'ari ma abun ba yanzu ne ya faru ba, shekaru har biyar to wane fad'a zasuyi kuma da dama ya wuce suyi hak'urin? Cikin jinjina al'amarin Gambo ya kalli Hadiza ya kuma kalli lieutenant yace "Abinda ya shiga tsakaninku kenan har kuka samu sab'ani da matar da baku tab'a sab'awa ba?"

Ajiyar zuciya lieutenant ya sauke yace "Gaskiya raina ya b'ace sosai, matata uwar yarana ta ha'ince ni har haka? Mtsss."

Hadiza ma data gama sawa zuciyarta ruwan sanyi ta yanke hukunci taushe komai ta had'iye ya zama sakayyar da zata musu na kula da yaranta da sukayi ta kalle shi tace "Abban Ammar, dan Allah muna nema mata alfarma kayi hak'uri ka dawo da ita, tayi hakane saboda 'ya'yanka, idan zaka nutsu kayi tunani zaka fahimci da a lokacin kowa yasan abinda ya faru, kayi tunanin irin abinda zai faru marar kyau, sannan kayi duba da shekarun da kuka d'auka ba tare da kun samu sab'ani irin haka ba, kayi hak'uri dan Allah, mu ma wallahi mun yafe babu komai, Allah ya yafe mana baki d'aya."

Gambo ne ya kalle shi yace "Ku daina bashi hak'uri ma dan Allah, yanzu zai tura dreba ya d'aukota ya dawo da ita."

Wani kallon ban son iskanci lieutenant ya mishi, shi ma hararanshi yayi yace "Allah sai kayi ko baka so, ba dan ma raini ba matar taka ta shekaru zaka yarda ta bar gidanta a wannan lokacin, to ina kake so taje? Ko kunya abun ba zai baka ba ace ta tafi gidansu, da yaranku da jikoki ku tsaya kuna abu kamar yara."

Had'e fuska yayi yace "Gambo, kayi shiru da bakinka kafin ranka ya b'ace."

Shi ma ba alamar wasa yace "Ya b'ace d'in mana, an fad'a maka ina jin tsoro ne."

Tasowa lieutenant yana fad'in "Zan tosheka kuwa yaro."

Da sauri Gambo ya tashi yayi baya yana dariya yana cewa "Ni ne yaron? Ni kake kalla ka kira ni yaro? Haba."

Hajia ce tace "Karka tab'a min auta wallahi, inba haka ba ranka zai b'ace."

Dawowa Lieutenant yayi ya zauna yana murmushi, Hadiza kam banda k'yalk'yata dariya ba abinda take, komawa yayi shi ma ya zauna yana dariya, Hajia ce tace "Dole zaka tura a d'aukota, kuma ba dreba kad'ai nake so ba, har da kai ma zaka tafi."

Kallonta yayi yace "Haj..." Bata barshi ya k'arasa ba tace "Bana son jin wata magana, abinda ka mata zaisa taji kamar ba a bakin komai take a wurinka ba, ba zan lamunci haka ba gaskiya, matar data k'arar da shekarun rayuwarta a tare damu, ta maka biyayya ni kuma ta min bauta, haka kawai yau ka wulak'anta ta."

Cikin marairaicewa yace "Shikenan Hajia zan tafi, amma ki min uzuri dan Allah har zuwa gobe, wallahi yau ina da muhimmin aiki a gaba sosai."

Fuska a d'aure tace "Shikenan, kaje Allah ya bada sa'a."

Da farin ciki ya amsa da "Ameen nagode."

Tashi yayi ya kallesu yace "Sai anjima."

Husseina ve tace "Allah ya tsare."

Sada ya fita Gambo ma yace zai fita ya dawo kafin Hadiza ta shiga d'aki ta samu Hamna, kwance ta same ta gefenta farantin kankana amma da alama bata sha ba, zaune tayi tana kallonta tace "Tashi zaune zamuyi magana."

Cikin muryar kuka tace "Dan Allah Mama in akan maganar nan ne kawai ki barta, ba zan iya ba wallahi."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Tashi Hamna, c'est très important."

Tashi tayi ta zauna tana ci gaba da share hawaye kuma wasu na bin wasu, kallon basira ta mata kallon fahimta tace "Hamna, me yasa kika ce ba zaki iya auren Ammar ba?"

Da sauri tace "Mama je ne peut pas, ba zan iya auren mijin yer uwata ba, kuma ni bana son shi ko kad'an."

Saida ta karanci yanayinta kafin tace "Corrections, mijin yer uwarki data rasu zaki ce, sannan Hamna zaki iya aurenshi ko da baki son shi, kinsan me yasa?"

Da ido ta kalleta hakan yasa tace "Saboda shine uban d'anki Shureim."

Da fari zaro ido tayi tana kallonta a firgice, sai kuma ta fad'a kan k'afafunta tana kuka tace "Mama kiyi hak'uri ki yafe min dan Allah, wallahi ba laifi na bane shine ya tirsasa ni, Mama bana manta tunatarwarki a kanmu kullum, dan Allah kiyi hak'uri."

D'agota tana share mata hawaye tana ji kamar tayi kukan ita ma tace "Karki sani kuka Hamna, na riga dana yafe miki har da shi ma, bana so ki karyar min da zuciya kuma."

Sassautan kukan tayi sai ita data d'ora da cewa "Hamna a gani na ki amince da auren shi, sai nake gani kamar ba zaki samu wanda zai dace dake ba kamar shi, sannan Hamna duk wanda zai fito neman aurenki yanzu ya zama dole a sanar dashi kina da yaro, kina ganin zai amince ya aureki duk yanda yake son ki? Ba lallai bane gaskiya a wannan yanayin da ake ciki, amma kinga shi ba zai k'yamace ki ba, zai rik'e ki kuma ya rik'e d'anku hankali kwance."

Girgiza kai tayi tace "Mama zan samu amma ba dai Ammar ba, mutumin daya rabani da mutumci ne yaushe zan iya rayuwar aure dashi? Kuma shi ma fa kinji abinda yace yana da wacce yake so, to me zaisa na tusa kaina gare shi."

Murmushi Mama tayi tace "Wallahi baya da wata wacce yake so Hamna, kawai ya fad'a ne saboda kinsan shi ba rainin wayo yake so ba, nasan yanzu yana can yana bala'i kin kalle shi kince baki son shi."

Kallonta Hamna tayi tace "Mama kawai ko bar maganarshi, ni idan ma ban samu mijin aure ba zan zauna na ci gaba da kulawa da yara na."

Da sauri tace "To ba gashi ba, Hamna kina son yaran nan sosai kuma kin k'i yarda kowa ya kama miki kula dasu, indai kina son ki ci gaba da rayuwa da su dole ki auri mahaifinsu, amma ba zan takura miki ba ki zauna kiyi tunani sosai, duk abinda kika yanke ki kira ni ki fad'a min."

Tashi tayi zata fita tace "Mama ina zaki je."

Juyowa tayi tace "Zan je gida na dawo na d'auki Ahmad."

Fkta tayi inda Hamna ta shiga d'aukar kankanarta da d'aya d'aya tana sha tana kuma tunanin abinda Mama ta fad'a, lallai indai zata rayu da yaran da ko kukansu bata so dole ta bi shawarar Mama, amma kuma Ammar? Kai! Tana cikin wannan tunani wayarta ta shiga k'ara, d'auka tayi ta ga ko suna babu a lambar, d'auka tayi suka gaisa kafin ta tambaya wake magana, nan ya fad'a mata sunanshi tace bata gane ba, dan haka yace ta bashi izini ya zo zai ta ganshi ido da ido, burinta na son samun wanda ya dace yasa ta amince da ya zo anjima.

*Tsautsayi*

Bayan sallah isha'i ta gama shirinta cikin doguwar rigar shadda, duk da ba tayi kwalliya ba amma tayi kyau, wayarta ya kira ya shida mata ya zo, ko da ta aje wayar Imam ya shigo yana kuka wai Shureim ya dake shi, jawo shi tayi tana lallab'a shi ta bashi wayarta tace "Ka je kayi kallon abinda ka fi so karka bawa kowa, kuma zan ga Shureim d'in saiya gane kurensa."
Chapter 172 · 0% Book details