← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 198

Sashe 58

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da dare kam su Bashir sun cika alk'awari ta hanyar kawo musu kyaututtukansu, sai dai Abbas ne ya gwangwajesu da manyan wayoyi yan zamani duk iri d'aya, sunyi godiya sosai tare da binshi da addu'a kafin daga bisani kowa ya nemi gado ya kwanta, Sameera da Abbas ma har sun kwanta ya tuna sam rabon da yaga bak'uwar nan tunda rana, dan duk hayaniyar nan da aka dinga yi tana d'akin ta, dan haka ya fito dan dubata, yau ma k'wank'wasa k'ofar yayi ta bud'e, sai dai yau doguwar riga ce a jikinta ta bacci, tambayarta kawai yayi ya k'afar ta ta amsa da sauk'i ya mata saida safe ya koma, Sameera kuma yana zuwa ta fara mishi mita akan yarinyar nan ita fa bata son ganinta, ya fad'a mata yana so ta samu sauk'i ne saita fad'a musu gidansu ya kaita, amma tace me zai hana ya tambayeta tun yanzu saiya kaita can tayi jinyar? Da dai yaga yana tarota tana zillewa sai kawai yace ina alk'awarin data d'aukar masa jiya jiya? Hak'uri ta bashi tace to yayi hak'uri ta daina kuma zata zuba mishi ido har lokacin daya sallameta.

*Bayan kwana biyu*...
12/06/2020 à 15:19 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_15_

Kai tsaye dama yake shiga d'akin Hajia, sallama kawai yayi ya tura k'ofar ya shiga, zaune ya same ta kan gado cikin doguwar yellown riga ta bacci, saida ya ja kujera ta gaban madubinta ya zauna ya kalleta, ita ma shi take kallo tana murmushi kafin tace "Shalele na ka ci abincin?"

A dak'ile ya amsa da "Na ci."

Cike da kulawa tace "Ina fatan dai baka tare da gajiya ko?"

Saida ya sake b'ata rai yace "A'a."

Murmushi tayi saboda yanda ya turo baki saita tuna lokacin yana k'arami, mik'a mishi hannunta tayi alamar ya taso, bata hannun yayi ya taso ya zauna kusa da ita ta fara shafar sumar kanshi, a ranta tana ayyana ai dole ma ta so shi, dan kaf cikin yaran babu wanda suka d'auko kalarta kamar shi da d'an uwanshi, hatta gashin kansu ya murd'e yake, dogayen hanci har baka da k'aramin baki jawur da shi, kurmin ido kuma manyan ido masha Allah, sannan gasu zabga zabga wajen tsayi wanda nan kuma kakansu ne sukayi Suley, tana kallonshi tace "Shalele ina fatan dai zab'in dana maka yayi maka ko?"

Kallonta yayi da mamaki, wato ta kira shi ne dan taji idan zab'in ya birgeshi, idan har yace bai mishi ba yasan dole zata canza mishi kuma cikin dubara, ganin kallon da yake mata yasa tayi murmushi tace "Kasan wani abu shalele? Ina matuk'ar k'aunar ka a zuciyata, kaine jin dad'i na da rayuwata, na zab'ar maka Umaima ne saboda kaga tafi sauran yan matan wayewa da ilimi, bata da kwaramniya da shiga abinda bai shafeta ba, sannan kaga tana koyon aiki a inda kaima kake aiki, shiyasa na maka wannan zab'in."

Shi dama baida matsala da zab'in data mishi, matsalar shi kawai yan uwanshi dake cikin damuwa saboda zab'in nata, dan haka yace "Hajia, ni banda matsala da zab'in da kika min, kin sani nima ina sonki kuma ina son farin cikinki, saidai Hajia 'yan uwa na ba duka ne suka gamsu da zab'in nan ba, idan zai yiwu dan Allah ki bar kowa ya zab'i wacce yake so."

Wata hamshak'iyar dariya tayi tace "To meya shafeka da su? Ai ka barsu kawai babu abinda zai faru, duk wanda aka kaiwa macen d'akin shi ba zai fasa kulata ba."

Cikin butsuwa yace "Hajiata, aure fa rayuwa ta din-din-din, ya kuke tunanin zasuyi farin ciki idan basa son junansu? Wallahi dukansu zasuji basu da maraba da marasa 'yanci, Hajia dubeki mana ke da Alhaji, a shekarun nan da kuka d'auka tare kina ganin da babu soyayyar junanku a zuk'atanku da zaku iya zama da juna ne? Ko da kun zauna Hajia dole d'aya daga ciki yana jin an takura shi, wannan rayuwar ce bana so yan uwana suyi, Hajia Junaid yana da wacce yake so, wacce yasa mukayi doguwar tafiya dominta, haka ita ma Hamna tana da burin da take so ta cimma, lokacin auren da kika saka yayi daidai da lokacin daya kamata ta fara zuwa koyon darasin zanen ta, yanzu haka kuka na barota tanayi saboda tana ganin kamar an ruguza mata burinta ne, shi kanshi Junaid d'in yana can kukan ne kawai baiyi ba saboda shi namiji ne ya fita dauriya da juriya, dan Allah Hajia ki taimaka ki musu wannan alfarma."

A hankalce ta kalleshi tace "To yanzu shalele sun turoka ne ka samar musu abinda suke so?"

Murmushi yayi yace "Hajia ban isa su turo ni ba? Na d'auka yanzu kika gama fad'in nine rayuwarki, hakan da suka bai isa yasa su turo ni ba? Sannan ni babu wanda ya turo ni, na fahimci damuwar kowane ne kuma nake rok'a musu alfarma a wurinki, idan kuma ba zan samu ba saina hak'ura, amma dai abun zai tsaya min a zuciyata ace na kasa samun wannan yar alfarmar a gurin kakata da nake da yak'inin babu mafi soyuwa a zuciyarta sama da ni."

Shiru tayi ta zurfafa tunani akan buk'atar shalelen ta, ya zatayi Allah ya d'ora mata k'aunar shi, shi kuma jin shirun yasa ya mik'e yace "Saida safe Hajia."

Tana kallo yake tafiya harya kusa kaiwa bakin k'ofa, da sauri tace "Shalele na."

Cak ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, da murmushi a fuskarta tace "Na amince da buk'atar ka saboda jin dad'in ka, ka fad'awa Junaid zanyi magana da iyayenshi suje su nemo mishi auren yarinyar, amma karku d'auka zata samu karb'uwa a zuciya ta dan karuwa ce ita, sai kuma Hamna, ita ma ka fad'a mata zata iya tafiya duk inda take so indai ba zai kai ga fita k'asar waje ba, amma kuma ya zama dole ta zauna ta halarci bikin nan, dan yer uwarta ma na buk'atar ta a kusa da ita, idan sun amince da hakan to shikenan."

Dariya yayi sosai ta nuna tsantsar farin cikinshi, da sauri ya zo gabanta ya durk'usa ya kamo hannunta ya sumbata yace "Allah ya bar min ke Hajia ta, nagode sosai da wannan alfarmar."

Shafa kanshi tayi da hannu d'aya ta tallabo hab'arshi ta kalli farin cikin dake kan fuskarshi tace " *Amar*."

K'ura mata ido yayi dan bai cika jin sunanshi a bakinta ba, d'orawa tayi da "Ka ci gaba da farin ciki irin haka ko da bayan raina ne, wannan shine burina a kan ka, kuma ina fatan Umaima ta zamo macen da zata dinga saka ka farin ciki irin wannan, in tayi haka zata zama suruka ta farko data fara shiga zuciyata saboda kyautatawa, zan so ta, zan k'aunace, zan faranta mata rai, duniya zata mata dad'i, zan so duk abinda ya fito daga cikinta, suma 'ya'yanku zan so duk abinda zai fito daga garesu, kaji ko?"

Murmushi ya mata sosai hakan yasa ta kama dogon hancinshi taja tana fad'in "Ka tashi kaje ka kwanta dare yayi, saida safe."

Da haka ya baro mata d'akin, bai bi takan d'akin su Ummy ba dan yasan mahaifinsu na nan, a inda ya bar Hamna ya same ta tayi shiru, yana mata albishir taji dad'i, amma daya fad'a mata dole zata kasance a duk wata sabga sai kuma ta marairaice tace "Amma yah Amar ai kamar ba'a rabu da bukar bane aka haifi Abu."

Dariya yayi yace "To yanda zamuyi shine, bara na samu Hajia na fad'a mata kin amince da auren ma kawai."

Da gudu ta nufi falon tana fad'in "A'a yah Amar ba sai munyi haka da kai ba."

A gurin Junaid ma farin ciki ba'a magana, Jibril ya tayashi murna sosai inda Ammar yayi gum yana kallonsu, da wannan kawai suka samu suka kwanta da huta gajiya.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Ko da Zeituna ta shiga gidan yau ma babu wannan hantarar da kyara, abun mamaki ne shine wanka da Jumma tace tayi saita kwanta dan taji dad'i, haka ta shiga wanka amma bata jima ba ta fito, ta zo aje bokitin hannunta ne ta bukkar kawu Mamu taji suna hira a harshen fulatanci, kawu Mamu taji yace "Ki dinga matsa mata fa tana wanka akai akai, dan ni dai ba zan iya fitar da wasu kud'i ba dan gyaran jikinta, shi kuma Alhajin yace baya son k'azanta da tsami."

Jumma ce tace "To yanzu ma ba a gabanka ba nace taje tayi wankan ba? Ni wallahi gar yanzu ina d'an d'ard'ar da lamarin ne, bana son mu shiga bakin duniya, ina gudun azo mutumin nan kashe ta ma zaiyi."

Cikin fad'a kawu Mamu yace "Ke wai wace irin jahila ce? Na fad'a miki ba kasheta zaiyi ba, buk'atar shi kawai yace zai biya ta duburarta fa saboda akwai aikin da yake so ya cimma, kullum ina gaya miki amma kina wane baud'ewa kamar ke ce za ayi abin da ita."
Chapter 58 · 0% Book details