← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 198

Sashe 114

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amna ce ta kalli Ummy ranta a matuk'ar b'ace na marin data wa mijinta, d'an k'aramin iska ta furzar irin na rashin jin dad'in nan kafin ta matsa kusa da Ammar da har yanzu ya k'asa d'agowa, a hankali ta kama hannunshi tana kallonshi, ganin bai kulata ba yasa ta kalli Hajia tace "Hajia dan Allah kiyi hak'uri ki barta anan, wallahi bata san tafiya ita ma."

Wani kallo ta mata tace "Ita ta fad'a miki bata so? Ko kin ari bakinta ne kin ci mata albassa?"

Kallon Hamna tayi tace "Na sani bata so, kuma gata nan ku tambayeta."

Mahaifinsu ne yace "To ko bata so ba dole ta hak'ura ta so ba tunda Hajia tace a tafi da ita."

Hajia ce ta kalli Hamna tace "Ke kika fad'a mata ba kya son tafiyar?"

Kallon Hajia tayi ta kalli Amna da ita ma ta kafeta da ido, kallon kiyi hak'uri ta mata sannan ta kalli Ummy dake kusa da ita, a k'wayar idon Ummy ta hangi abinda ta kasa fahimta, shin tana son tafiyarta ne ko kuma a'a, rashin sanin amsa yasa ta kalli Hajia ta sunkuyar da kai tace "Ni ban fad'a mata ba, ina so na tafi tare da Abba."

Kallon mamaki da takaici Amna ta mata, me yasa za tayi haka? Cikin jin haushi tace "Amma ai ni nasan ba kya son tafiyar, kuma idan kin manta na tuna miki, kina shirye shiryen tafiyarki koyon kwalliya ne."

Idan har ba bak'ar magana ta fad'a mata ba tasan ba zata rabu da ita cikin sauk'i ba, dan haka tace "Ni bana son koyon wata kwalliya, wajen mahaifina zan koma da zama."

Murmushin rainin hankali Hajia ta bisu da shi tace "To kinji abinda ta fad'a da bakinta, dan haka ki barta ta tafi can, idan da rabo ma ta samu miji acan aure zan mata, sai dai kawai kije bikinta idan da hali."

Da k'arfi ya kalleta, *miji*? kuma *aure*? acan d'in? Hummm! Juyawa yayi da sauri ya nufi hanyar barin d'akin, da sauri Amna ba tabi bayanshi dan bata ga abinda zata zauna tayi ba, kai tsaye b'angarensu suka koma.

Kallonta Hajia tayi tace "Ki d'auko kayanki ki zo ku wuce."

Juyawa tayi ta koma sama, ba b'ata lokaci ta d'auko ta sauko k'asa, tana zuwa Gombo ya mik'e yana wa mutanen wajen sallama, tafiya sula fara yi suna barin falon, anan Ummy ta samu damar fad'awa Hamna cewa "Karki damu Hamna, ki tafi dasu yanzu, tunda Hajia ta yanke hukuncin nan babu mai hanawa, amma ina so duk abinda kike ji a jikinki karki bari kowa ya sani, ki kira ki fad'a min zansan abun yi, kafin lokaci mai tsayi kuma nasan ta hak'ura tasa a dawo dake."

Jinjina kai kawai tayi suka fita, a farfajiya daidai k'ofar fita suka samu an saita hancin motocin, anan suka samu Aissata tsaye tana amsa waya da harshen zarma, saida ta gama wayar kafin ta kallesu cike da izza da d'aga kai sama tace "Sai anjima."

Zeituna da Zeinabu ne suka amsa da "Sai anjima, Allah ya kiyaye hanya."

Mai aikin data taho da ita ce ta bud'e mata k'ofa zata shiga, tsayawa tayi ganin Hamna na shirin shiga motar gabansu ansa jakarta a but d'in motar, da mamaki tace "A'a! Me wannan kuma take yi ne haka? Ina zata je ne?"

Mai aikin ce ta girgiza tace alamar bata sani ba ita ma, Gambo ne ya tsaya daga shirin shiga motar yana kallonta yace "Tare zamu tafi da ita."

Yamutsa fuska tayi tace "Ban gane tare zamu tafi ba? Tare muka zo da ita ne?"

"Umarnin Hajia ne, dole haka za ayi madame." Cewar Zeinabu, rai a b'ace ta juya ta kalli Gambo, kallon kiyi hak'uri mana har muje gidan ya mata, saida ta matse baki alamar akwai magana kafin ta shiga motar, tasan kawai dan Hajia ta muzguna mata ne ta had'a su tafiya da Hamna, amma inba haka ba meye na sawa a tafi da ita, yaran da ko da k'uruciya basu tafi ba bare yanzu da girmansu, suna kallo suka ja motoci suka fita daga gidan anata jiniya, basu zame ko ina ba sai filin jirgi, daga nan kuma suka d'aga zuwa Niamey.

D'akinshi ya shiga ya rufe zauna kan gado, tunanin abinda ya faru yake yi, yaji zafi sosai, ba wai marin data masa bane ya b'ata masa rai, marinshi da tayi a gaban wacce zai iya kira da matarshi, ta d'aga hannu ta dalla mishi mari, jin bugun zuciyarshi ya fara canzawa yasa shi mik'ewa da sauri ya fito daga d'akin yana fad'in "Ina! Ba zan tab'a bari damuwarku ta sa min ciwon zuciya ba, idan na mutu ma ba ciwo zakuji ba."

Falon ya dawo ya nufi wajen fridge ya bud'a ya d'auki ruwa, saida yasha sosai sannan ya dawo ya zauna kan kujera, tv ya kunna yana kallo sai kuma ya tuna da Amna, tunda ya nufi d'akinshi ita ma tabi bayanshi, amma kallon daya mata yasa ta shiga d'akin ta ita ma. Mik'ewa yayi ya shig d'akin, kwance take kan gado tayi ruf da ciki, k'arasawa yayi ya zauna kusa da ita yana ci gaba da kallonta, sai dai yafi mayar da hankalinshi kan hannunta na hagu wanda ta mik'ar dashi, ta kifa hannun ta mik'e yatsunta wanda ke rufe da jan lalle, amma yatsanta manuniya sai bubbugashi take akan katifar da sauri sauri kamar tana bubbugashi akan tebur, shafa hannun nata yayi hakan yasa ta tashi zaune tana kallonshi, sunkuyar da kanta tayi sanda taji wasu hawaye sun taho mata, da alamar damuwa ya kalleta yace "Kuka ne kike? To me akayi kuma yanzu? Amna bana son kuka fa ko da na yaro ne."

Abinda ya fad'a ne yasa ta rushewa da kuka ta d'ora kanta akan kafad'arshi, cikin kuka take fad'in "Yah Ammar bana jin dad'i, zuciyata kamar zata fashe, yer uwata yau tayi nesa dani, sannan Ummy ta mare mijina a gabana, banji dad'i ba ko kad'an, kawai dan babu yanda zanyi ne."

Murmushi yayi duk da bata kallon fuskarshi, cikin wata k'asaitacciyar murya yace "Hakan na nufin zaki iya tsayawa sosai akan kare min mutumci na?"

D'agowa tayi ta kalli k'wayar idonshi abinda ta jima ba tayi ba tace "Yah Ammar kai fa mijina ne, zan iya yin komai akan kare mutumcinka."

Wani murmushin ya kuma yi tare da jawota ya rumgume, shafa yake yi a hankali yana fad'in "Dama na fad'a miki Amna, ina so ki zama farin ciki na da kwanciyar hankali na."

Da sauri ta sake d'agowa tace "Zan zama, zan zama yah Ammar, ka kwantar da hankalinka."

Sake dawo da ita yayi jikinshi ya sauke k'akk'arfar ajiyar zuciya har iskan bakinshi ya sauka kanta kafin yace "Allah na gode maka, ka bani uwa ta gari da fari yanzu kuma ka ban mata wacce zata kula dani."

Ummy na shiga d'akinta Zeituna tabi bayanta, tana shiga ta same ta tsaye tana kai da kawowa da alama hankalinta ba kwance ba, k'arasawa tayi da girmamawa tace "Ummyn Ammar dan Allah zamu iya yin magana idan ba damuwa?"

Babu alamar sakin fuska a tare da ita ta tsaya wuri d'aya ta kalleta tace "Ina jinki."

Saida ta numfasa ta d'an kalleta tace "Aunty akan abinda ya faru ne yanzun dama, sai nake ganin kamar kinyi saurin marin yah Ammar, shi fa yanzu ba yaro bane, ya mallaki hankalin kanshi sannan yana da iyali, ko kamar Kamal yanzu a wannan zamanin duka baya gyara shi bare kuma kamar yah Ammar, ina ganin zaifi kyau idan kika jawo shi jikinshi, idan kikayi haka zaku fahimce shi da kyau kusan matsalarshi, dan na fahimci daga ke har Alhaji babu wanda yake nuna damuwarsa akan shi, wallahi wani lokacin sai kuyi kamar ba iyayenshi ba."

Tunda ta fara maganar Ummy ta rumgume hannaye tana mata wani kallo, saida ta dasa aya cikin mamakin k'arfin halinta tace "Zeituna wacece ke? Meye ruwanki da sabgar data shafi ni da d'ana? Me kike ji dashi da har zaki tare ni da maganar nan? In haifi d'an a ciki na ki nemi ki koya min yanda zan tafiyar da al'amarin daya shafi tsakani na da shi? Akan wane dalili?"

Kallonta Zeituna tayi a wannan karan babu wani girmamawa tace "Kawai dai ina so na ankarar dake ne da wuri kafin lokacin nadama ya zo muku, dan n..."

Tsawa Ummy ta mata ta hanyar fad'in "Shiru."

Shirun tayi tana kallon babu alamar jin tsoro ko makamancin haka, d'orawa tayi da "Bari kiji Zeituna, wannan ba abinda ya shafeki bane, ki fita a harkata tsakanina da yaro na, idan kuma ba haka ba zaki ga wata Sa'ada wacce baki tab'a tunanin zaki santa ba."

Girgiza kai tayi tace "Allah ya baki hak'uri, Allah yasa ku gane gaskiya." Tana fad'a ta juya ta bar d'akin, da harara ta bi ta dan dama ranta a b'ace yake, zaune tayi bakin gado ta soma tunanin abunyi na gaba tunda Hajia ta wargaza musu shirinsu.

*Zuwa* magrib duk wani bak'o daya zo bikin nan ya koma garinsu, ana sallah magriba lieutenant ya d'auki Zeituna suka tafi ganin kawu Mamu, a k'ofar gidan ya tsaya ita ta shiga ciki da sallama, babu wanda ya amsa sallamarta sai Jumma dake cikin garken awaki da tace "Wake sallama?"

Saida ta zagaya inda taji muryarta tace "Inna Jumare nice."

Duk da ta d'auki muryarta saida tace "Ke ce wa?"

"Zeituna." Ta bata amsa, da sauri ta saki k'afar akuyar da zata d'aure ta taho da sauri tana gyara d'aurin k'irjinta tana fad'in "Yawwa sannu da zuwa, naji dad'in zuwanki, kamar kinsan ina nemanki dama."

Tsaye tayi tana kallonta inda ita kuma ta fara masifa cikin fulatanci tana fad'in "Zeituna wane rashin mutumci ne wannan? Daga an aiki yarinya gidanki sai yaron gida ya mareta, me ta mishi to? Kuma ke a gabanki amma babu abinda kikayi, dama had'a baki kukayi dan a ci mutumcinta ko, ke tunda muke dake a gidan nan kin tab'a ganin ni ko ubanta wani ya d'aga hannu ya daketa? Sai wani d'an k'ato kawai kamar ya samu jaka ya marar min yarinya."
Chapter 114 · 0% Book details