Sashe 26
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin fara'a yace "Wai kina nufin 'yan biyu na?"
Kai kawai ta d'aga mishi alamar eh, dukansu farin ciki ne ya bayyana a tare da su, suna tsaka da tattaunawa ita kuma harta juya zata tafi ta ji murya Zeituna tace "Aunty babu wani abu da za ayi? Gida nake son tafiya."
Dukansu da mamaki suka kalleta banda colonel da ko kallonta baiyi ba, Soueba mamaki ne ya hanata magana, dan duk ma'aikatan gidan babu mai kwana anan sai *Nana* dake budurwa, ita ma kuma saboda ba 'yar garin nan bace, sannan wani lokacin Hajia na neman abun ci kuma tafi son na ta, amma banda ita duk sauran suna tafiya ne bayan sallah isha'i, amma ga Zeituna har goman dare kuma bata san tana nan ba sai yanzu, a cikin kallon da take mata ne na tuhuma ta fahimci hankali da idon Zeituna suna kan lieutenant, abun al'ajabin shine kallon da take masa yasa ta kasa fahimtar yanayin dake fuskarta, shin tsantsar *so* ne take hangowa ko kuma *k'auna* ce, wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ta sauke ta saci kallon lieutenant d'in, amma shi sam baisan ma tanayi ba sai hirarsu suke, sake kallonta tayi tace "Ba komai Zeituna, zaki iya tafiya gida, amma ki kula dan Allah dan kinga dare yayi, kuma ke gashi unguwarku da duhu akan hanyar."
Saida Zeituna ta k'ara kallon lieutenant sannan tace "To aunty, saida safe."
Juyawa tayi zata wuce ta sake kafeshi da ido ta sunkuya tace "Abban Ammar saida safenku."
Take ya kalleta shi da Labaran suka amsa da "Saida safe."
Fita tayi daga gidan bayan ta sauke ajiyar zuciya, murmushi tayi sosai kamar mahaukaciya kuma saita dinga tsalle tsalle tana dariya harda juyi akan hanya tana farin ciki kawai saboda ta ga lieutenant kuma lafiyarshi k'alau, dan ita bata san tafiyarsu ba saida ta ankare daya wuce lokacin dawowarshi ne hankalinta ya fara tashi, shiyasa ta kasa tafiya gida tace ko zata kwana sai taga ya shigo dan ta tabbatar da lafiyarshi lau, tana cikin haka wani mai moto daya karyo kwana suka kusa had'ewa da ita, odar daya danna mata ce tasa ya dawo hankalinta, cak ta tsaya dan ta d'auke ma ya bige ta ne, masha Allah mai moton shi kuma da manyan idonshi kamar zasu fito waje ya k'ura mata ido, a ranshi yake ayyana kaga wani irin gamdakatar, yarinyar da nake nema gata na samu a cikin dare, duk da dai ya k'are mata kallo amma a wajenshi mai neman biyan buk'ata ba komai bane, tana samun kulawa zata wanke tayi fess, ita kuma sai lokacin ta dawo hankalinta ta tuna inda zataje, waro ido tayi ta dafe k'irji tace "Na shiga uku ni Zeituna, yau ya zanyi da kawu *Mamu*?"
Haba ai saita wuce da sauri har da gudu gudu take hannu d'aya a kai tana fad'in "Nasan ma kashe ni zaiyi wallahi, oh ni Zeituna, soyayyar wanda baisan ina yi ba na neman haukata ni."
Haba wannan mutumin da shima yake ganin ya samu abinda yake nema ai sai ya juya kan moton ya fara bin bayanta, dan in yace ya tsayar da ita ya tabbatar ba zata saurare shi ba dan alamu sun nuna sauri take, dan haka ya dinga binta har saida ta shiga wani layi dake da babban kwalbati gaban kwalbatin kuma katangu ne kawai wanda kake iya hango bukkokin ciki, d'aya daga cikin gidajen ta shiga wanda ke d'auke da bukka uku a ciki, yana ganin haka ya juya da moton shi da tunanin dawowa gobe da safe.
Shiru gidan da alama sunyi bacci sai wani dattijo dake kan tabarmar kaba kusa da wata bukka da redio yana saurare, kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki haka ta k'arasa gabanshi ta durk'usa cikin harshen fulatanci tace "Kawu walijam? noi chomrii (ya gajiya)?"
D'agowa yayi daga kwanciyar da yake ya sauke idonshi a kanta, kafin yayi magana ya d'auki k'aton takalmanshi na fata mai shegen nauyi ya mazga mata a fuska, Allah yasa bai sameta a kunci ba sai a goshi, taji zafi sosai dan haka ta dafe wuri ta fashe da kuka, cikin harshen fulatancin da yafi k'warewa akai ya fara zazzaga mata bala'i na daren da tayi, wannan surutun na shi yasa matarshi *Jumma* fitowa, maimakon bashi hak'uri sai ita ma ta dinga fad'in a harshensu "Ai dama na fad'a maka yarinyar nan karuwanci take zuwa, wani irin aiki ne zai tsayar da ita har wannan lokaci, ni fa tuni nayi nisa a bacci ace sai yanzu zata shigo gida, da k'ofa gare mu kenan saita bubbuga ta nunawa mak'wabtan mu ta dawo a zo a bud'e mata k'ofa, saida suka gama zageta ta uwa ta uba babu tunanin marainiya ce suke rik'o sannan 'yar d'an uwanshi sannan yace ta b'ace mishi da gani, ta tashi zata shiga bukkarsu wacce suke su uku a ciki ita da yaransu Jumma tace "Abincinki fa? Ko da yake ma ai nasan kin gama k'oshi a wajen yawon."
Cikin kuka tace "Mihari (na k'oshi)."
Kawu Mamu ne ya fara magana da hausa saidai a yanayin daya iya yace "Wane abinshi jaki bata? Ke ki shaurare ni ma da kyau kiji, wannan ishkanshin nata ya kusha karewa domin kuwa aure jan mata, janje kauyen *gwadojji* na shamo mata miji kafin ta ja min abun kunya, shannan na tsawon kwana uku ban lamunshe ki bata abincin gidan nan ba, ja ta shi ashan wajen yawon ishkanshin na ta."
Dad'i Jumma taji hakan yasa ta juya zata koma bukkarta tace mishi " Jamwala (saida safe)."
Tana shiga bukkar ba tare da damuwa ba ta cire hijabinta ta shinfid'a k'asa ko tabarma babu ta kwanta tana kallon yaran dake kan katifa duk da dai ba wata ta kirki bace, amma a wajenta da take kwana k'asa wannan d'in kamar gado ce na alfarma, tunanin iyayenta ta shiga yi wanda suka nuna mata gata da soyayya lokacin da suke raye, amma mutuwa ta d'auke su a lokaci d'aya sakamakon had'arin daya ritsa da su na mota, wani sabon kuka ta dasa ta ci ta k'oshi hata gode Allah kafin bacci yayi gaba da ita.
*Gaga's falimy*😂
*10:30* na dare Amar dake zaune a falo suna kallo shi da duka 'yan uwan wayarshi tayi k'ara, yana dubawa ya d'auka yana fad'in "Ummy baki kwanta ba har yanzu?"
Ammar dake zaune nesa da shi kamar zaiyi kwance yana latsa wayarshi ne ya kalleshi ta gefen ido, daga wajen Ummy ta amsa mishi da "Banyi bacci ba Amar, ka ci abinci ne?"
Amsawa yayi da "Ban ci ba Ummy, bana jin yunwa ne."
"A'a ban yarda ba, maza ka shigo ka samu wani abu ko marar nauyi ne ka ci, kai baka tausayin kanka ne da halin da kake ciki? To ka zo yanzu ina jiranka."
Kashe wayar tayi shi kuma ya mik'e a gajiye yana fad'in "Ummy sai kace wani yaron goye, ni ba yunwa nake ji ba."
Junaid ne yace "To ina laifin Ummy, kulawa fa akace yabawa, ta damu da kai ne shiyasa."
Wani dogon tsaki Ammar yaja ya mik'e a hassale ya shige d'akin shi ya mayar da k'ofar ya rufe, da kallo suka bishi sai dai babu wanda ya damu bare yayi tunanin abinda yasa yayi hakan, fita Amar yayi a farfajiya ya had'u da Jibril ya dawo a matuk'ar gajiye, gaisawa sukayi kafin shi ya wuce babban falo shi kuma nasu falon.
Ammar na shiga cilli yayi da wayarshi kan gado ya fad'a ban d'aki, ba jimawa ya fito ya watsa ruwa ya kashe wutar d'akin ya kwanta daga shi sai gajeran wando, kifa kanshi yayi tsakiyar pilow yana k'ok'arin ya cire damuwar nan a ranshi, baya so abun ya dinga damunshi amma ya zaiyi mutum ne shi mai zuciya da jini, jin baccin na neman gagararshi yasa ya mik'e ya b'allo maganin bacci, a k'a'ida damuwarshi bata kai yasha guda d'aya ba, rabi ya kamata yasha, amma saboda haushi yasa yasha guda d'aya sannan ya kwanta, ai kuwa baifi minti sha biyar ba kwana ya d'auke shi marar dad'i sai dai mai k'arfi.
*Washe gari*
Kamar ibada yau ma hakane a wurin Zeituna, tana yin sallah asuba ta shiga d'ebo ruwa a panpo, layin data tarar yasa har gari yayi haske kafin ta samu ta turo kurar ruwan mai d'aukar jarka (bidon) takwas, da kanta ta dinga saukewa tana shigar da su tana juyewa a randa da tuluna da manyan bokitai, saida ta gama cas sannan tayi wanke wanke, data wanke ne ta samu ta d'ora d'umamen tuwon masara wanda miyar kukar taji daddawa, kafin yayi zafi ta gama sharar tsakar gidan, tana idawa ta zubawa duk wanda tasan tana zuba ma ta kai musu, tana dawowa babbar buta ta d'auka ta fara d'iban ruwa dan tayi wanka, amma Jumma na gani ta fito tace "Me ja kiyi da wannan ruwan?"
Cikin marairaicewa tace "Inna wanka nake so nayi , kinga fa yau kwana hud'u kenan baki barni nayi wanka ba, har Hajia ta fara min magana akan k'azantar jiki na."
Fizge butar tayi ta juye mata ruwan a jikinta tace "Ba ja kiyi ba, na ce ba zakiyi wankan ba marar mutunci kawai, ki wuce ki tafi hakanan in kuna son zuwa kafin nasa kawunki ya dakatar dake."
Cikin muryar kuka tace "Dan Allah Inna to ki bari na ci abinci saina tafi."
Da k'arfi tace "Abinci? Har abincinki ma kika fitar? To kiji da kyau jiya kawunki yace kar na sake baki abinci har na kwana uku, dan haka ki wuce ma karki wahalar da kanki."
Takawa ta fara yi cikin fitar da hawaye tana matse hijabinta wanda dattinshi yasa take sanyashi a birkice, yanzu gashi ruwan data zuba mata yasa duk wani tsohon datti da wari ya taso, ita kanta sai take jin k'yank'yamin kanta, tana zuwa ta ja kurar ruwan dake k'ofar gidan ta nufi wajen aikinta da ita, saboda tafiyar dake akwai dama yasa ta fad'awa mai kurar zata dinga kawo mishi in zata je wurin aiki, tana tafiya tana share k'walla harta isa ta aje kurar ta wuce.
*Babban gida*