← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 198

Sashe 33

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'asa tayi da ta ta muryar tace "Duk da ba tursasani kayi ba ai ba kana nemana na amince maka ba, sannan bani na ce ka kirani inda kake ba, da kuma na zo kaga zan tayar maka da hankali me ya sa ba kayi gaggawar korata daga wajenka ba?"

D'orawa tayi da "Duk kai ka ja mana wallahi, ba dan kasa tsoron Hajia a ranka ba da yanzu muna rayuwa cikin salama, amma tsoron wanda baida wutar da zai samu ya saka mu sai aikata laifi muke akan wani laifin."

Rintse ido tayi saboda jin k'arar ya bugi wani abu da yake nuna mata da ita ce a kusa da ita ya kaiwa wannan haura, datse hak'oran shi yayi ya rasa bakin magana, ina ma zai ji an kawo masa hari ta baya ko ya samu damar huce wannan haushin, jin baiyi magana yasa tace "Ni duk ba wannan ba, kayi azamar turawa Inna kud'in ta kamar yanda kukayi da ita, dan ni dai ba zan so asiri na dana yarona ya tonu ba a wannan lokacin, gaskiyar magana kenan."

"Kutumar bala'i." Inji colonel a cikin zuciyarshi dan har yanzu ya kasa sakin hak'oran shi, "Wannan ma ai raini ne, Zeinabu umarni ne take bani ko me? Ni? Ni? Ina!" Buga wayar yayi a bango ta baje tare da kai wa bangon naushi, Zeinabu dai ta fad'i abinda ke ranta ta kashe waya ta dawo falo.

Jibril ne a d'akin kakarshi bayan ya gama cin abinci suna hira, kallonta yayi da fara'a a fuskarshi yace "Yar tsohuwa, insha Allahu idan aure na da Amna ya tashi da kaina zan tuk'aki ki kaini wajen dangi Baba, dan wallahi ina so na gansu sosai."

Tunda yayi maganar nan ta had'e fuska tayi shiru, jin shirun yasa yace "Hajia, wai a wane gari dangin mahaifin Baba suke? Na gaji da tambayar Umma akan wannan."

Ba alamar wasa ta kalleshi tace "Kenan ni ce yanzu zaka dama? Malam tashi ka fitar min daga d'aki."

Da mamaki ya kalleta yace "Hajia, kema damuwar ce kamar yanda Umma ke damuwa a duk sanda na mata magana makamanciyar wannan?"

Cikin d'aga murya tace "Ban sani ba Jibril, kuma in har baka son gayyato fushina to kayi gaggawar janye wannan k'udirin naka na son ganin dangin mahaifin mahaifinka."

Mik'ewa yayi da tsantsar mamaki yace "Saboda me? Meyasa Hajia baku so ana..."

"Na ce ka fita." Ta fad'a da k'arfin gaske, juyawa yayi jiki a sanyaye ya fita yana tunanin meke faruwa, fitowa yayi k'ofar gidan da tunanin shiga motarshi daya bari anan, Junaid ya had'u da shi zai shigo hakan yasa ya tsaya ya fito suka gaisa, Jibril ne yace "Na ga yau sai wani farin ciki kake mutumina, ko dai Maryama ta amince ne?"

Wani murmushin ya sake yi yace "Bata amince ba, amma dai na gano hanyar da zanbi nasa ta amince."

"Wace hanya kenan?" Ya tambaya da zumud'i, da murmushin gefen labb'a yace " *Zan je garinsu, sannan na shirya tsakaninta da mahaifiyarta da sauran danginta."*

Da fara'a Jibril yace "Eh to kuma fa ka zo da dubara, kana shirya tsakaninsu zaka ga ta amince kosu su amince da kai."

Kallonshi yayi yace "Amma dai zaku rakani ko?"

Zaro ido yayi yace " Ni da wa?"

Hararanshi yayi yace "Kai da zaratan 'yan uwa na mana."

"Har da Ammar?" Cewar Jibril, ba wasa yace "Har da shi mana, ai watak'ila ma ya mana anfani fiye da kai, dan in mukayi sa'a muka had'u da wani tsagera a cikin dangin mai taurin kai shi zai mana maganinshi."

Juyawa Jibril yayi zai nufi motarshi yana fad'in "Shikenan to sai kuje babu ni."

Da sauri ya rik'o shi yana dariya yace "Kai haba daga wasa, kai fa zaka nuna mana hanyar ma tunda ai kasan hanyar *Gouré*."

Cak ya tsaya ya juyo yana kallon Junaid, Goure, wannan yarinyar? Tana nan har yanzu? A ina take? Ina zanje na sameta? Rik'e hannun Junaid yayi yace "Da gaske kake? Yaushe zamu tafi?"

"Eh to, ni ko gobe ma zan iya tafiya, amma ka bari mu fara jin ta bakin su Ammar da Amar."

Hannunshi ya kama zuwa cikin gidan yana fad'in "Muje ciki muyi magana da Ammar yana nan, Amar idan ya shigo zamu fad'a mishi kuma kasan ba matsala zai bamu ba."

Wucewa sukayi ciki Junaid na fad'in "Wai duk wannan saurin na miye haka? Kamar wanda zaije ganin tashi budurwar."

Wani murmushi Jibril yayi, dan haka kawai ya ji kamar ana fizgarshi da yaje garin, yana so ya Allah ya sake had'a shi da yarinyar nan, suna zuwa suka saka Ammar tsakiyarsu Junaid ne yace "Babban yayanmu, dama wata alfarma muka zo nema, dama yarinyar nan da nake so ce ta fad'a min garinsu, to akwai yar matsala tsakaninta da iyayenta, shine nayi shirin tafiya neman aurenta wajensu tare da shirya tsakaninsu, to bana so ne naje ni kad'ai gaskiya, nafi so muje tare da ku dan su san ni d'an dangi ne."

Ammar da hankalinshi ke kan waya saida yaji ya kai aya kamar mai ciwon haure yace "Ina da abinyi."

Yana fad'a kuma ya mik'e ya shiga d'akin shi, Junaid ma ya mik'e yana tab'e baki sai ga Amar ya shigo, nan suka fad'a mishi kuma kamar yanda suka sani dama ba zai basu matsala ba, shirya yanda tafiyar zata kasance sukayi kafin kowa ya nufi d'akin shi.

*Zanyi magana, amma ba yanzu ba.*
03/06/2020 à 23:33 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕

_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_6_

Ma'arufa ce da Ma'aruf a d'aki kowa da wayarshi yana dannawa, kwance take akan katifa mai tufun gaske shi kuma tashi katifar bata da maraba da bargo, kallonta yayi yace "Ke wai kin fara shirin tafiyar ne gobe ko kuma kina nan kina jan jikin?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Ba gobe zan tafi ba."

Ba tare daya daina kallonta ba yace "Saboda me?"

Kai tsaye tace "Saboda akwai wasu kud'i da Labo zai bani gobe idan ya zo, kuma ina so na shiga kasuwa na siyo sabbin yadin da za'a min sabbin riguna dogaye, tunda waccen gurguwar tace mutumin ba wai harkar matan banza yake ba."

Tsaki yayi yace "Ke dan Allah kiyi duk iskancin da zakiyi zuwa jibi ki bar garin nan, na k'osa kud'in nan si shigo wallahi harka ta bud'e, dubi shegiyar katifar da nake kwana akai."

Sai lokacin ta kalleshi tace "Wai kai yanzu ko kunya baka ji? Kana kwance gida ni ce zanje na nemo maka kud'in da zaka ji dad'in rayuwarka da su."

Ba tare da damuwa ba yace "To meye a ciki? Ke ma sau nawa ina miki anfani? Yanzu lokacinki ne yayi."

Tsaki taja ta mayar da kallonta kan wayarta tace "K'aton banza kawai."

Kallonta yayi amma bai biye mata ba saboda yana wata hira data d'auke mishi hankali, wata budurwarshi ce mai sunan *Meena* ke ikrarin daina harka dashi tunda baya sonta baya kashe mata kud'i, maida mata sak'on yayi da "Rabuwa dani a daidai wannan gab'ar na nufin ke asararriya ce."

Maido masa tayi da "Sai dai in kaine asararren, shege d'an iska wace tsiyar kake tsinana min?"

Shima mayar mata yayi da "Ke haba matsalata dake banza ce, kanki baya kawo wuta ko kad'an, ina nufin idan kika barni a wannan lokacin to zakiyi asarar wata opportunity da muka samu."

"Ban gane ba d'an rainin hankali, fahimtar dani?"

Nan ya fad'a mata wai sun samu wani Alhaji gara zasu wanke shi, kuma k'ashin bayan tafiyar abokiyarshi ce Ma'arufa, dan haka karta bari damar nan ta wuce ta, nan dai suka sulhunta komai ya wuce.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Yanda Abbas yayi tunanin aikin zai kaishi kwana uku sai ya zo da sauk'i, dan haka ya shirya ya taho ba tare daya fad'awa madame ba, su a lokacinsu dare ne dan har sun shiga bacci, saida ya fara shiga wajensu Ammie da suma har sun kwanta ya gaishe su, daga nan kuma part d'in shi ya wuce ya aje jakarshi yayi wanka, kayan bacci ya saka ya feshe jikinshi da turare mai sanyin gaske kafin ya d'auki makullin k'ofar da zata sada shi da falon Sameera ba sai ya fito ta farfajiyar gidan ba, yana shiga ya tabbatar sun jima da kwantawa, d'akin Raihan ya fara bud'a k'ofar a hankali ya lek'a, saida ya sauke ajiyar zuciya sabida ganin tana bacci hankali kwance, duk da har yanzu bai siya mata waya ba amma dai yana tsoron sharrin zamani da dubarar 'ya'yan yanzu, rufewa yayi ya lek'a d'akin Rauda, Khalifa da sauran yaran, amma yana ganin Abdul raheem shi kad'ai kwance a gadonshi babu Ameer ya tabbatar yana wurin mamanshi, a hankali ya shiga can cak ya tsaya, rarraba ido yakeyi tare da shafar kai, a hankali ya fara takowa har ya zo kusa da ita ya tsaya, jefar da makullayen yayi kan gado ya bud'e mata hannayenshi yace "Come on my angel, i miss u."

Sameera da tunda mota ta shigo gidan ta farka a hankali cikin turo baki ta bud'e hannayenta ta kwanta luf a k'irjin shi, lumshe ido yayi ya sauke wata ajiyar zuciya mai d'an k'arfi wacce iska da gumin bakinshi har suka sauka kan fuskarta, k'ara shiga jikinshi tayi tana sake matseshi sosai saboda k'aunar mijin nata, ido rufe take sauke ajiyar zuciya tana shak'ar turarenshi dake son mayar da ita bacci, cikin muryar shagwab'a tace "Me yasa baka fad'a min zaka zo ba?"

Saida ya fara yawo da hannayenshi a gadon bayanta yana latsawa saboda taushi da laushi ba tare daya bud'a ido ba yace "I'm sorry, nima bansan aikin zai sakeni yau ba, ina k'arasawa kuma naji ba zan iya kwana nesa da ke ba, shiyasa na garzayo na zo gareki."

K'ara daidaita zamanta tayi cikin k'irjinshi shi kuma yana sake matseta yana shafata, cikin wata murya mai kama data bacci yace "Meerata."
Chapter 33 · 0% Book details