← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 198

Sashe 145

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare da ita suka tafi asibiti kuma suka dawo tare, tana rik'e da macen jaririyar (ni dai bansan sunan da zan kira yaran nan na Ammar ba dan ya birkita min lissafi) suka shiga ciki, aje yarinyar tayi ta d'auko katifa ta mata shinfid'a a falo, inda Soueiba kuma ta d'ora mata ruwan wanka sai Zeituna data shiga kawo mata abinci mai lafiya da gina jiki, bayan ruwan sun tafasa ta shiga wanka su ma yaran aka fara musu ana canza musu kaya, ya shigo gidan da k'atuwar leda da kayan bebys ciki, Amna dake shan tsumagiyar kaba a hannun Husseina tana mata wanka ce ta dasa wata k'ara tana fad'in "Zafi, zafi Hajia ba zan iya ba, bana so wallahi ya isa haka."

Kallon Zeituna yayi dake shafawa yarinyar kwalli yace "Uwa me take ma kuka ita kam?"

Dariya tayi tace "Wanka ne ake mata."

Zaro ido yayi yace "Da tafasashen ruwa halan?"

Kai ta d'aga masa hakan yasa shi zabura ya nufi ban d'akin dake cikin falon yana fad'in "Na rantse da Allah babu mai toya min mata kamar yar wuta, ta gama azabar nak'uda kuma ta koma shan ruwan zafi, anya kuna da imani kuwa?"

Soueiba ce tace "Ammar mu ne marasa imanin da muke taimakawa matarka? Kasan dai inba wankan nan aka mata ba da kanka wata rana zaka ce a mata shi."

Juyowa yayi yace "Haba tanti, ni d'in banza da zan kiraku da marasa imani."

Ban d'akin ya shiga saida Husseina taji tsoro, ita kanta Amna kunya ce taji ta kamata, kallon Husseina yayi da tace masa "Lafiya Ammar? Wani abu kake so?"

Cikin taushin murya yace "Hajia bari na k'arasa mata wankan nan, naji sai ihu take mana daga wankan da bai taka kara ya karya ba."

Tsaye ta mik'e rik'e da kabar hannunta ta kalleshi sai ta rasa me zata ce mishi ma, Amna na jin haka tace "Hajia ci gaba dan Allah, yah Ammar ka fita zan tsaya yanzu."

Ummy na shigowa aka ce mata ya shiga kawai tabi bayanshi, tana zuwa ta tsaya bayanshi tace "Bawan Allah ko zaka iya basu wuri suyi abinda ya dace?"

Juyowa yayi yace "Me zai hana kuwa Ummy."

Kallon Husseina yayi yace "Ayi wanka lafiya."

Juyawa yayi kamar zai fita saiya sunkuya cikin kunnen Amna yace "Karki bari ta k'ara k'ona min ke wallahi, inba haka ba ita ma saina mata wankan jegon nan, haka kawai ba za'a barki ki huta ba."

Mik'ewa yayi ya fita Husseina ta bishi da kallo baki bud'e, kallon Amna tayi da mamaki tace "Anya kuwa Amna mijin nan naki zai bari a miki abinda ya kamace ki?"

Ita dai k'ala ba tace mata ba kawai tana jiran taji saukar ruwan zafin, ko da ta gama shiryawa ma tuni gidan ya fara gaurayewa da yan barka.

*Da dare* Jumare ta zo tare da Jumma suka ga yara suma, suna fita lokacin Hamna ta raka k'awarta Amie data zo ita ma, kusan a tare suka fita sai Ammar daya zo zai shigo, yana ganin Amie yace "Lah budurwata ce? Kina lafiya?"

Kallonshi tayi ita dai har ga Allah matashin ingarman saurayin na birgeta, ko yanzu idan zai fito da niyyar aurenta saita aure shi, amma matsalar d'aya ta fahimci mutum ne da kanshi ke rawa, murmushi ta masa tace "Angon jego kasha k'arni, barka to Allah ya raya."

Murmushi ya mata yana sunkuyar da kai yace "Har kin sani jin kunya wallahi, to ameen dai tunda addu'a kika min."

Murmushi tayi ita ma ta mik'a masa hannunta tace "Ina tayaka murna sosai."

Hannunshi ya mik'a mata shima suka gaisa yana fad'in "Nagode sosai, yanzu ya labarin soyayyarmu?"

Sosai tayi murmushi tace "Labarin soyayyarmu kai zan tambaya."

Saida ya kalli Hamna wacce ko da taga hannunshi da nata sun had'u taji bak'in ciki da wani mak'ok'on abu ya taso mata ta fara hararensu, Jumma da Jumare dake gefensu ne Jumare tace "Inna ashe d'an iska ne, kiga fa gaisawa yake da ita."

Cikin sassauta murya Jumma tace "Rufa mana asiri Jumare karki sa ya jefa mu kurkuku."

Kafin ya bawa Amie amsa ya kula dasu Jumare suna kallonsu, Jumma ce tayi saurin cewa "Ina wuni yallab'ai, dama Zeituna ce ta fad'a mana an samu k'aruwa shine muka zo barka, Allah ya rayasu akan sunna, saida safe."

Daga yanda take magana ya nuna masa har yanzu a tsorace take dashi, cikin sakin fuska da fara'a ya amsa mata da "Lafiya lau, mun ko gode Allah ya saka da alkairi, ina baban namu?"

Jumma ce tace "Malam yana gida yace dai a gaisheku."

"Muna amsawa." Saida suka fara tafiya yace "Budurwata ya kike?"

Tsayawa Jumare tayi wanda hakan yasa Hamna da Amie kallonta da kyau, tab'e baki Hamna tayi taja hannun Amie tace "Muke kinji, wannan duk yan matan garin nan ina ga fa nashi ne."

Ita dai wuk'il ta masa da ido kawai sai shi daya matsa kusanta yana mata shak'iyanci wai saita fad'a asa tana son sa, Jumma ma dai matsawa tayi nesa dasu ta basu waje, saida Amie ta samu adaidaita sannan Hamna ta dawo, nan ta same su tsaye saida ta harareshi sannan ta nufi cikin gidan, yana ganin haka yace "Ke zo nan."

Abinda ta tsana a duniya yace mata ke, kuma a gaban yarinyar nan yar k'auye zai ce mata ke zo nan, da k'arfi ta juyo cikin b'acin rai ta tsaya gabanshi tace "Gani lafiya?"

Murmushi ya mata dan yana son cikata yace "Daga ina kike?"

Saida ta sake had'e fuska tace "Daga inda ka aikini mana."

Kallon Jumare yayi yace "Kinji gani ko? Da ita ce zan aura to matsalar k'walwa gareta, shiyasa nake so na aureki Jumyta dan naga uwata Zeituna tana da hankali nasan ke ma kamar ita ce."

Bud'a baki tayi zatayi magana sai kuma ta kasa ta kalleshi da tsananin mamaki ta kalli Jumare data kalleta, sake d'aga labb'enta tayi sai taji sun mata nauyi, amma fa ya wulak'antata mutumin nan, kallon Jumare tayi rai a b'ace cikin d'aga murya tace "Ke bar nan wajen kafin na miki dukan tsiya."

Baki Jumare ta saki kawai saita yarda da abinda ya fad'a, ganin ko niyyar barin wurin ba tayi ba yasa ta sake d'aga murya tace "Zaki b'ace ne ko saina karyaki a wurin nan."

Da sauri Jumare ta wuce sai kuma ya bita da dariya, yana cikin k'yalk'yala dariya ya kalleta sai kuma yayi tsitt kamar ba shi ba, saida ta harareshi sama da k'asa tace "Idan ni mahaukaciya ce kai kuma fa? Mai kula dani?"

Tsaki tayi ta shige cikin gidan inda ya sake bushewa da dariya yana cije leb'en kasa shima ya shiga, kai tsaye b'angarensu ya nufa, tun a k'ofa yake jin kukan Amna k'arama, yana shiga ya ganta hannun Amna sai nono take saka mata tak'i karb'a sai harshenta ke rawa tsabar kukan da take cancarawa, kakanni kam sai sharri ake mata suna kiranta da mai la'ana kamar uwarta, tak'im tak'im yaje gabanta yasa hannu ya amsheta ya fara jijjigata ya nufi d'aki da ita, bayanshi Amna tabi dan tana so ta fad'a mishi abinda take so, yana jin motsinta a bayanshi ya juyo yace "Wai me aka mata ne take wannan kukan?"

Kafin ta bashi amsa yaja hannunta ya zaunar da ita bakin gado ya d'ora mata ita a k'afa yace "Bata tasha."

A hankali ta fito da nonon dake mak'ale a k'irji ta d'aga kan jaririyar sosai tana so ta sa mata, amma daya shiga bakinta sai tak'i kamawa, cikin d'aga murya yace "Wai lafiyarta k'alau kuwa? Naga lafiya lau take yau."

Kallonshi tayi tace "Yah Ammar kawai fa dan an mata hujen kunne ne take wannan kukan?"

"Me?" Ya fad'a da k'arfi yana k'are mata kallo, cikin yanayin da yake nuna zai iya tabka rashin mutumci yace " Amna wannan yarinyar ce kika sa aka ma hujen kunne? Kuma shine har kike cewa wai dan an mata, wai ma ne kenan?"

Nufa yayi wajen coiffeuse (dressing miror) yana fad'in "Yau na tabbatar da ke baki da hankali har da ma wacce ta mata hujen, amma zan nuna muku ni na dameku na shanye wallahi, inba raina mutane ba yarinyar da aka haifa jiya, ke kikayi nak'udarta amma a gaban idonki ana juheta kina kallo, to ko de bake kila haifeta bane?"

Ya juyo yana kallonta, ita dai kallonshi take tana so kuma ta kama nonon, tana kallonshi ya fito da yan kunnanta na ziraniya da Hajia ta siya mata da kud'in daya bayar ya nufo kanta, ita dai bata san me zaiyi ba ta kuma kasa tuna girman abinda zai aikata, karb'ar yarinyar yayi ya aje gefe duk kukan da take kuwa, idonta ya kalla ya rik'e k'ugu yace "Ke mahaukaciyar ina ce Amna?"

Cikin fara tsorata da yanayinshi ta fara matso k'walla ta girgiza masa kai, nuna k'aramar Amna yayi yace "To uban wa yace ki yarda a mata huje tun yanzu? Waje zaki fara aikata ne tun yanzu da kike son ganin ta fita da kyau? Ko kuma idan ba'a mata yau ba shikenan zata mutu ne? Me zaisa ba za'a bari har ta k'ara wayo ba? Kawai tsabar rashin imani irin na ku Amna ku kama min 'ya ku huje mata kunnuwa, kuma ni abun bak'in cikin ma shine a gabanki, kuma wai har kike cewa wai dan an mata huje, kiji fa wai dan an mata."

Saida ya saita d'an kunnan hannunshi ya fizge hijabinta yana k'ok'arin rik'o kunnenta yana kallon yarinyar da har yanzu ke kuka yana fad'in "Ke yi shiru abinki yarinyata, da ubanki fa a raye waye zai takaki a garin nan? Ai ban ganshi ba na rantse da Allah, bari kiga yanda zan d'au maki fansar cin kacar da aka miki, yo mu rashin mutumci ai gidanshi ne aka zo har na siyarwa muna da."

Amna na ganin yana shirin burma mata kunne huje na uku kenan dan dama biyu garesu ita da Hamna, zabura tayi zata bar wurin ya kwantar da ita kuma tsaf yayi zaune kan ruwan cikinta, had'e hannayenta tayi wuri d'aya cikin fad'uwar gaba da kuka tace "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri, Allah wallahi ba zan sake ba na rantse maka."
Chapter 145 · 0% Book details