Sashe 152
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan tunanin data tafi yasa bata san har sun tashi daga zaman ba, Zeituna ce kawai ta rage a wurin tana kallonta, suna had'a ido suka sakarwa juna murmushi, cikin ladabi Zeituna tace "Gaskiya Hajia ta fad'a Ummyn Ammar, yana d'aukaka lamarinki fiye da komai, duk da rashin kulawar da kike nuna masa baisa ya tab'a yin hushi dake ba, duk yanda yake ganin darajata idan ya kirani kafin mu gaisa saiya fara tambayata ya Ummy take, saina tabbatar masa da kina lafiya kad'ai zai iya gaishe ni, aunty na fad'a miki a baya kuma yanzu ma zan maimaita miki, Ammar so da kulawarki kad'ai yake buk'ata, duk abinda yake yi wanda ba kya so kuna zama dashi cikin sauk'i zai daina."
Ita ma barin wurin tayi suka barta, ta jima nan zaune tana tunanin abunyi kafin ta koma d'akinta. Hajia ma na d'aki Hamna ta sallamo, amsa mata tayi ta bata izinin shigowa, cikin sanyin jiki ta k'araso cikin ladabi tace "Hajia dama na zo neman alfarmarki ne?"
Kallonta tayi ta aje wayarta gefe tace "Wace irin alfarma Hamna?"
Cikin nutsuwa tace "Hajia dama su aunty *Hana* ne (k'anwar mamansu) zasu tafi Niamey bikin *Abdu*, shine nace zan tambayeki idan kin amince ina so mu tafi tare dasu?"
Murmushi ta mata tace "Ba komai Hamna, kuje Allah ya tsare, a kula sosai kinji."
Saida ta sunkuya tace "Nagode Hajia, insha Allahu."
Da kallo ta bita har ta fita, har zuciyarta yanzu kam ta fara tausaya mata, sam babu maganar aure a sabgarta, samari da masu mata suna gosulo a k'ofar gidan akan ta, amma kowa sai tace bai mata ko ta kushe shi dole a rabu da ita, ita kuma bata so ta fitar mata da miji a yanda yanzu ta k'ara mallakar hankalinta take rik'akk'un shekaru ga kuma wayewa da karatu ba lallai ta yarda ba, sai dai kawai su ci gaba da addu'a Allah ya fito mata da miji ita ma tunda gashi har k'annan baya suna aure suna barinta. D'akin Ummy ta wuce ta fad'a mata zata tafi amma fa zata jima gaskiya, Allah ya tsare ita ma ta mata kafin ta fito, tsaf ta shirya kayanta wayewar gari kawai take jira.
Tsakanin mata da miji ance sai Allah, Amar da ake tunanin d'aukar mataki akan Umaimah shi kuma ko da yaga jinin da take zubarwa sai kawai tausayinta ya lullub'eshi, (😂 auren kenan) sai ga Amar ya rarrasheta kan tayi hak'uri dukan da tonton ya mata, ko nasiha bai mata ba na abinda tayi, saida ya gama ita ma amarya Farisa ya lallab'ata yace tayi hak'uri. Da safe saida aka had'asu aka ja kunnensu sosai tare da tsorata ta hanyar fad'a mishi inta sake yayi duk abinda ya dace.
*Bayan wata takwas*
Ko da ya kira gida cikin farin ciki ya sanar dasu Amna fa ta haihu, abun farin cikin kuma shine ta sake haihuwar 'yan biyu duka maza, duk da basu gari amma gidan haka aka dinga murna da farin ciki, dan dama ana cikin hidimar haihuwar Zeinab ne Farisa kuma har tana da sati biyu da haihuwa. Ranar suna ko da ya kira yace an yi wa Alhaji da Alhaji takwara, ma'ana *Suleiman* da kuma *Yunus*, wannan abu ya ma kowa dad'i na wannan iyali, babu wanda ya tab'a tunanin a familyn Hajia kuma Ammar zai iya saka sunan Alhaji Inussa, dangi daga masu kiransu da Alhaji sai mai kiransu Baba, amma shi ya musu alkunya da *Abba* da kuma *Imam*, daga Niamey Hamna ta kirasu ita ma tayi musu barka, wqcce ita ma har yanzu tana can bata dawo ba tayi zamanta, musamman data tafi da kayan aikinta hakan yasa acan ma bata zauna ba, babu inda bata zuwa yin kwalliyarta, dan shiga gidan yana wuya saboda tsaro.
*Shekara d'aya*
Rasuwar Alhaji Inussa ma bata dawo dashi ba, Zeituna ta haihu Jamila Umaimah duk sun sake haihuwa, lieutenant ma ya saka masa ido ya dawo ko ya zauna can duk d'aya, amma Hajia ta damu sosai da rashin dawowar har ta fara fad'a tana cewa akwai abinda aka masa, kullum ya kirata sai dai ya mata shirmenshi ya mata kalaman soyayya yace mata zai zo idan lokaci yayi, ana haka Alhaji ya wayi gari babu lafiya, mutumin da bai tab'a ciwo ba, hakan yasa yanzu ko da ya kwanta sai abun ya masa kwaf yayi yawa, dan farko ma da aka d'aukeshi aka kaishi asibiti baisan halin da yake ciki ba, a ranar hankalin kowa ba kwance ba, asibiti kuma sun ce ayi gaggawar kaishi Niamey, Gambo ne ya turo jirgi musamman tare da lieutenant da Hajia suka tafi dashi, sai colonel da suka samu acan garin, saida aka kwana biyu Ammar yasan abinda ke faruwa, a ranar shima ya shirya ya taho hankali a tashe.
Asibiti ya wuce kai tsaye a taxi, colonel kad'ai ya iya kallonsa yace "Ammar kai ne? Yanzu ka shigo garin?"
Idonshi akan Alhaji dake kwance ido rufe duk jikinshi na'ura ce yace "Eh kawu, ya jikinshi? Me ya same shi ne?"
Kafin yayi magana Hajia ta fad'a kan kafad'arshi tana kuka, hannunshi ya d'ora bayanta yana shafata yana fad'in "Ya isa Hajia ta, ban sanki da raguwar zuciya ba fa, ko kin manta ke ce kakata?"
D'agowa tayi tana share hawaye da gyalenta tace "Tsoro nake ji Ammar, mutuwa karta rabani da Alhaji na, har yanzu ban nemi gafararsa ba."
Kallon lieutenant yayi da colonel sai kawai suka mishi alamar ya fita da ita, a hankali yana rumgume da ita ya jata suka bar d'akin, a k'ofar d'akin suka zauna kan kujera ta k'arfe mai sulb'i kamar zaiba, rik'e yake da hannayenta yace "Hajiata, kiyi shiru ki daina kukan to, babu abinda zai same shi zai tashi, taya ma zai tafi ya barki bayan shekarun da kuka d'auka, ai ke dashi mutu ka raba ne."
Kallonshi tayi cikin wani kukan tace "Kana cewa ba zai barni ba kuma gashi kace sai mutuwa ce zata raba mu, to idan fa lokacinta ne yayi?"
Saida ya k'ara matse hannunta sosai yana kallon k'wayar idonta yace "Hajia, ke da Alhaji kun ci nasarar rayuwa, kun zo duniya kun rayu tare da iyayenku, kun girma kuka rayu da 'ya'yanku cikin gata da kulawa, sannan yanzu kuna tare da jikoki da yaran jikokinku, kun ci ribar rayuwa sosai, ku godewa Allah daya baku arzik'i na gidan duniya, wasu sun rayu da kud'i babu 'ya'ya, wasu sun rayu da yara babu kud'i sanadiyar talauci yasa yaran fad'awa mummunan rayuwa, wasu kuma ya basu komai kamar ku, Hajiata, a familynki babu irin mai matsayin da babu, colonel na soja, kina da lieutenant na douanes, kina da babban k'usa a cikin siyasa, kina da babban professeur da da likita, kina da ma'aikacin ga wanda yake karantar shari'a, ga k'anwarmu dake son zama yar sanda, ga mai kwalliya ga yar kassuwa ga wacce ke son fitowa a alk'ali, sannan ga k'aramin k'ananmu wanda tun yanzu ya zama ustaz kuma yake burin zama babban malami da dai sauransu Hajia, kuma duk k'ok'arinku ne ya janyo hakan, ni kam Hajia me zaisa kuyi bak'in ciki ne a sanda zaku bar duniyar nan wacce ko ba dad'e ko ba jima dai sai an barta."
Kallon idonshi tayi sai kayi ta saki murmushi, ita ma rik'e hannunshi tayi sosai tace "In fad'a maka gaskiya Ammar?"
Kai ya d'aga mata alamar eh, cikin rad'a tace "A gaskiya da bana son mutuwa ko kad'an, amma yanzu daka tunasar dani yawan zuri'ata da kuma matakai na rayuwa da suka taka a rayuwarsu sai naji ko yanzu na mutu banda damuwa, saboda nasan ko ba dukanku ba dole zan samu tsirarun da zasu bini da addu'a ta alkairi."
Murmushi yayi sosai tare da sakin hannayenta yace "Bari na duba jikin Alhajin."
Jinjina kai tayi ya shiga ciki, Alhamdulillah kam jikin a lokacin yayi dama, sai dai dukansu babu mai tunanin su bar wurin nan da Alhaji, dan kuwa su manya ne sun san komai shi kuma Ammar likita ne yasan yanayin, yanda suka ga Alhaji yayi yasa duk suka sare da al'amarin, tubarkallah wani kyau ne aka zubo mishi yayi jawur dashi, ga kumburi da k'afafunsa sukayi, haka dai daya farka suka sha hira shi da Ammar har da dariya sukeyi, da dare iyayen sun fita sai Ammar da Hajia zaune, da hannunshi ya bashi abinci yana idawa ya aje plate d'in, har zai kwantar dashi sai kuma yace "Alhaji zauna ka ci gaba da kallon Hajiarka, na yau dai kawai na danne kishina."
Dukansu murmushi sukayi sai Alhaji daya kamo hannunshi yana sauke numfashi, saida ya saisaita nutsuwarsa da numfashinshi kafin yace "Ammar, dan Allah ku kula da kanku sannan ku rik'e zumunci, kai ne babba a yaran nan ka zama mai tsayawa kan lamuransu, Ammar ka rage zuciya da saurin hushi, sannan ka ci gaba da biyayya wa iyayenka, sannan ka..."
Sai kuma yayi shiru, dukansu ido suka sakar masa hakan yasa yayi dariya ya kalli Hajia yace "Ka kula min da Hajia Zeeya'atu na, kakar nan taka babu wanda ya iyata sama dani, ni ne mijinta anan kuma ni zan zama mijinta a lahira ma, ta dace dani, nima kuma na dace da kayata."
Cike da tabbatarwa yace "Insha Allah zanyi Alhaji."
Yanda ya k'arashe yana dariya yasa Hajia fashewa da kuka, d'ora kanta tayi kan k'afafunshi dake mik'e, dafa kanta yayi yace "Bana son ganin kukanki Zeeya'atu, ki daina kinji karki sani kuka nima."
Ba tare data d'ago ba cikin kuka tace "Tun bayan rasuwar iyayena a bakinka kad'ai nake jin sunan Zeeya'atu, Alhaji bana so na daina jin sautin nan, ka ci gaba da kirana haka dan Allah, hakan zaisa naji a raina akwai mutum d'aya daya isa dani kuma yake da iko a kaina."
Kallon Ammar yayi sukayi murmushi, k'ara shafa kanta yayi yana fad'in "Zeeya'atu na, Zeeya'atu na ki daina kuka kinji, bana son ganin hawayenki Zeeya'atu."
D'agowa tayi ta kalli tace "Zan iya yanzu Ammar?"
Fahimtar inda maganarta ta dosa yasa shi d'aga mata kai yace "Yanzu ne lokacin daya dace Hajia."