← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 198

Sashe 11

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan b'ab'atun ne yasa Hajia Husseina fitowa daga d'akin ta, Soueba ce tace "Dan Allah Zeinabu kiyi hak'uri, da Ammar da Junaid ai duk d'aya ne a gurinki kamar 'ya'ya suke a wajenki, dan sun samu sab'ani bai kamata ace muna jin zafi haka ba, yan uwane su kuma mabiyi da mabiyi, dole dama ana samun haka saboda zaman tare, amma bai kamata ki dinga fad'in haka a kan shi ba."

Hajia Husseina ce tace "Lafiya ku kuma meke faruwa ne?"

Zeinabu ce tace "Hajia, Ammar ne ke fad'a da Amar, Junaid daga zai raba kawai ya samu shima ya bubbuge shi saboda fin k'arfi, shine yanzu nake magana Soueba take nuna min ba hakanan ba, to dan Allah yanzu su Ammar yara ne da za ace har yanzu suna fad'a? Sanda sukayi fad'an k'uruciyar wa ya tab'a cewa wani abu, ko da suna yara ma kullum shine ke saka mana yara kuka, kuma yanzu ace sun girma ma ba zasu huta daga kaidin shi ba saboda shi ya zama wani shaid'an."

Murmushi Husseina tayi tace "Ai gaskiya Soueba ta fad'a, ba kina kwaroronton sun samu sab'ani yanzu ba? To zuwa gobe ko jibi a falon nan zaki tarar da su kuma suna wasa tare kamar lokacin da suke yaran, kuma kema kin sani ko wasa suke sunfi tsokanar Ammar d'in, amma shi ko magana bai cika son yi ba, kenan meye abun wannan fad'an?"

Amar da yana shiga d'akin ya samu Ummy zaune kan kujerar coiffeuse (dressing miror) zunbur ta mik'e tana kallonshi ta nuna mishi k'ofar fita tana fad'in "Fitar min a d'aki Amar, fita."

Cikin muryarshi ta shan wahala ga dishi-dishin da yake gani yace "Ummy kiyi hak'uri na fad'a miki ab..."

Cikin tsawa tace "Ka fad'a min me Amar? Me zaka fad'a min? Shin Amar tun yaushe nake fad'a maka ka dinga hak'uri da halin d'an uwanka? Sau nawa ina fad'a maka kai da shi akwai banbanci na hallaya ka dinga kiyaye b'acin ranshi? Amar na fad'a maka kai ne d'an uwanshi wanda ko bayan ba ranmu zaka iya tsaya mishi duk da shine babba, me ya sa ba zaka dinga hak'uri ba da duk maganar da zata fito daga bakinshi? Tunda kafi kowa sanin halinshi magana indai har ta zo bakinshi ko ni uwarshi fad'a min yake bare kuma wani, amma ku tsaya kamar yara yan shekara biyar wai kuna fad'a, fad'a Amar da girmanku da komai? Amar so kuke duk gidan nan na zama mujiya ko kuma kamar wacce ta haifi annoba?"

Komawa tayi ta zauna cike da damuwa kamar zata fashe da kuka, cikin sanyin jiki da rashin jin dad'i ya durk'usa kusanta ya rik'e k'afar ta yace "Dan Allah Ummy kiyi hak'uri ki yafe mana, wallahi har cikin raina bana jin dad'i na ga kina damuwa akan halin Ammar, Ummy in kina damuwa da halinshi hakan zai iya janyo mishi fushin ubangiji, kiyi hak'uri dan Allah ki daina Ummy, nayi kuskure dana kula shi, amma na miki alk'awari hakan ba zata sake faruwa insha Allahu."

Hawaye ne suka taho mata ta d'ora kanshi a saman cinyarta ta kasa cewa komai, ita yanzu babban tashin hankalinta idan Hajia ta zo ta ga Amar da wannan ciwon a fuska, tashin hankalin zai fara ne idan aka ce Ammar ne ya dake shi, _kowane d'an adam da wanda Allah yake jarabtarshi da son shi, Hajia ita ta ta jarabta Amar ce, duk cikin 'ya'ya da jikoki babu wanda Hajia ke nunawa k'auna kamar Amar, babu wanda take nuna damuwarta a kanshi kamar Amar, takai ta kawo Amar na iya mata magana kan wani hukunci data yanke kuma ta janye shi, tun yana yaro yake samun kulawarta da soyayyarta, hatta yayesu da za ayi ita ta amshi Amar hannunta, kuma sun fara samun rashin jituwa ne da Ammar saboda kullum shi ke nasara akan Amar in dai ana fad'a, da kaji Amar na kuka to Ammar ne ba makawa, ita kuma saita dinga wa Ammar fad'a tana nuna mishi tsana a fili, hakan yasa shima baya wani k'aunar ta bare al'amuranta,_ to wannan ne yanzu damuwarta dan tasan sai rai ya b'ace fiye da yau, tana cikin wannan tunanin suka ji muryar Zeinabu na wannan fad'a, cikin sanyin murya tace wa Amar "Ka ji ko, na tabbata suna magana ne akan abinda ya faru."

Mik'ewa Amar yayi yace "Ummy ni fa bana jin dad'i na ji ana fad'an maganganun marasa dad'i akan d'an uwa na, zanje na fad'a musu kar wanda ya damu da abinda ya faru yanzu, tsakaninmu ne wannan kuma zuwa anjima zamu shirya."

Rik'e hannunshi tayi tace "Bara na duba maka ciwonka tukuna."

Zage hannunshi yayi yace "A'a Ummy zan dawo yanzu, kinsan tanti (Zeinabu)da ji-nini."

Mik'ewa tayi ita ma ta bi bayanshi, suna tsaye lokacin Husseina ke tambayar lafiya? Duk abinda ta fad'a akan kunnensu, Amar zai tafi wajenta Ummy ta rik'e shi, tana cikin wannan fad'an kuma sai ga Ammar ya shigo falon da takonshi na k'arfi kamar zai tashi k'asa.

Tunda ya koma b'angaren su tunanin Ummy ya dameshi yasan yanzu tana can tana kuka, shiyasa ya tashi yayi wanka ya canza kayan jikinshi zuwa wata shadda ruwan k'asa ya fito, tunda ya doso falon ya ji wannan hayaniyar ya sake tamke fuska kar ma aga damarshi, Zeinabu na fad'in "Ai dan ya ga wuri ne shiyasa yake mana iskancin son ranshi, suma ba dan suna wasu sakarkaru ragwaye ba har yaushe mutum kamarku wanda duk cikinsu babu wanda ya bawa wata biyu da haihuwa amma ku tsaya yana lallasaku son ranshi."

Husseina dai murmushi ne nata tace "Zeinabu ai abun a jini yake, tun daga yanayin tafiyarsu zaki duba, zaki fahimci ko a tafiya shi da k'arfi yake tashi sab'anin su."

Tsaki tayi tace "Ala wadaran naka ya lalace, to badan basu da wayo ba ai ko taron dangi ne su mishi wata rana su jijjiga shi shima ya ji jikinshi, wallahi sai kiga an zaunnnn..."

Gimtse bakinta tayi dan har ga Allah ta tsorata kuma gabanta ya fad'i lokacin data d'ora idonta akan Ammar daya had'e fuska yake kallonta ido jawur kamar kullum, Ummy da suke k'ofar d'aki tsaye tasan sai yayi magana, dan haka daga can tace "Ka wuce ka tafi inda za ka."

Amma ko kallon Ummy baiyi ba kuma har yanzu bai daina kallon Zeinabu ba yace "Idan kina ganin zasu iya ki basu shawara mana tunda kun shirya rasa 'ya'yanku."

Saida Ummy ta lumshe ido, dan tasan dama sai anyi haka, shi fa in dai maganar zata zo to sai ya fad'a ko za'a yanka shi, babbar matsalar kuma shine bai damu da girman wanda zai fad'awa ba ko kuma d'acin maganar ko rashin dacewarta, zai fad'a ne in ya so kai kayi kuka dan bak'in ciki, ko kuma ka zage shi kayi tir da halinshi shi duk d'aya ne a gun shi, takawa yayi ya nufi wajen Ummy tana ganin haka ta shige d'aki ta rufe k'ofar da makulli tana wani sabon kukan, k'ofar d'akin ya tsaya yana kallon fuskar Amar da tayi jina-jina, wani irin buga k'ofa ne yayi d'aya biyu baiyi na uku ba sannan yace "Kiyi hak'uri fa ki daina kuka, kinsan zai iya ja miki ciwon kai, daga haka kuma ake kamuwa da hawan jini ko ciwon zuciya, kina so ne ace zan nuna k'warewata na zama likitan zuciya a kan ki?"

Yana fad'in haka ya juya zai bar d'akin, cak kuma ya tsaya saboda duk baya jin dad'in ganin Ummynshi na kuka saboda shi, d'an uwan shi kuma na fitar da jini a dalilinshi, juyowa yayi ya kalli Amar dake shirin bubbuga k'ofar d'akin, sake d'auke kai yayi kuma wata zuciyar na fad'a mishi ai sai ya d'auka ka damu da shi ne, a hankali ya lumshe ido ya sauke numfashi a zuciyarshi yace "Ka damu da shi mana Ammar, ku fa ko a cikin ciki tare kuka rayu, ka d'auka kai da shi kamar kuna rayuwa ne da rai d'aya."

Bud'a ido yayi ya sake kallon Amar wanda shi ma yake so ya ga sun shirya ko dan mahaifiyarsu ta ji dad'i, kamar baya son maganar haka ya motsa bakinshi yace "Muje na wanke maka ciwonka."

Da sauri ya k'araso kusanshi ya rumgumeshi dan sam bai d'auka Ammar zai fara mishi magana ba, sosai yake ta k'ara cakume shi saboda k'auna, amma me Ammar zaiyi sai kawai ya raba kanshi da shi ya had'e rai yace "Miye haka malam sai ka b'ata min kaya da jini, muje ni dallah."

Da k'arfi ya juya ya fita Amar ya bi bayan shi yana girgiza kai, lallai a duniyar nan in har shi ya kasa fahimtar d'an uwanshi to babu mahalukin da zai iya fahimtarshi bayan wanda ya halluce shi, Husseina da Soueba da dariya suka bisu har Husseina na fad'in "Kin gani ko Zeinabu, shiyasa shiga fad'an yara ke da kunya wallahi, dan Allah ki daina damuwa da rayuwarsu, mu yarda cewa haka Allah ya hallici Ammar."

Tab'e baki tayi tace "Hum! Ni bana so na ji kuna cewa wai yara, yaran nan fa ba dan dogon karatu da sukayi ba wallahi da yanzu sun aje mana jikoki bibbiyu ko sama da haka."

Dariya Zeinabu tayi tace "Gashi kema kin fad'a kince yara."

Shigowar Junaid cikin sabon shiri yasa suka kalleshi a tare, shima dai fuskar nan a had'e take dan ranshi ya b'ace sosai, Jamil ya kalla wanda ke zaune yana latsa wayarshi yace "Kai in za ka je ka taso mu tafi."

Mik'ewa ya yi yace "Mu tafi kawai."

"Ina kuma zaku je?" Cewar Husseina, a tak'aice Jamil yace "Gidan roumji."

Zeinabu ce tace "Inda ubanninsu suka tafi zasu je, amma babu wanda zai iya fad'a mana dalilin zuwa."
Chapter 11 · 0% Book details