← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 198

Sashe 22

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shafa bayanta ta fara yi tana fad'in "Ya kamata fa kisan girma kikeyi takwarata, shiyasa kullum mijinki ke k'orafin ni na lalataki kika raina shi."

Sake gyara kwanciya tayi tace "To Ammie idan banyi ba wa zan ma, shekaru na d'auka babu soyayyar uwa a tare dani saita uba, shiyasa ma ban damu da Abba ba kamar yanda na damu dake, Ammie nayi rayuwar kad'aici da maraici wanda har yanzu idan na tuno na kanji ba dad'i, soyayyar uba goma d'aya take data mahaifiya k'waya d'aya tak."

Hannu Ammie tasa ta juyo da fuskarta tuni hawaye sun fara mata zuba, goge mata yake tana fad'in "Nasan da haka takwarata, shiyasa ma har yanzu bana kallonki a matsayin wata babba, nasan kinyi kewar mahaifiya a kusa dake, kin rayu cikin mutanen da baki da wata alak'a ta jini dasu, amma yanzu ba gashi komai ya wuce ba kina tare da ni."

Rumgume Ammie tayi sosai kamar tana bata nono, tana jin soyayyarta na sake shiga zuciyarta, sai dai har yanzu tana ji ina ma zata ga mahaifiyarta ido da ido ko na awa d'aya, da zata k'arar da lokacin wajen nuna mata irin yanda take son rayuwa da ita.

Sallamar su Raihan ce tasa ta tashi zaije tana kallonsu cikin kayan makarantarsu, Ameer ne ya taho da gudu ya fad'a da jikinta yana kuka wai shi ba zai je makaranta, kallonshi tayi tace "Haba dai Babana, da girmanka da komai ka ce ba zaka je makaranta ba, dubi fa kowa ya shirya kuma tafiya zasuyi , kamata yayi ace kaine ma shugaban tafiyar nan, ko ba kaso ka zama kamar Abba ne?"

Cikin kukan ya amsa da "Ina so." Murmushi ta masa tace "Good man kenan, dan haka ka wuce gaba ka rigasu shiga gaban mota, kaji ko."

Aida gudu ya juya ya bar d'akin, sai lokacin ta kalli Abdul da suke gaisawa da Ammie, suna had'a ido yayi k'asa tana gaisheta, amsawa tayi tare da cewa "Har kun gama shirin kenan?"

Da alkunya ya amsa da "Mun gama Ammie, amma kuma bamu ga Dady ba."

Murmushi tayi tace "Sai dai kuyi hak'uri kam, amma yanzu haka dadynku na sararin samaniya akan hanyarshi ta zuwa Belgium."

Raihan ce tace "Ammie Belgium fa, amma shine ko ya mana sallama."

Raudat ce tace "Ai zai dawo gidan ya samemu, Allah ba zan mishi magana ba."

Sameera ce tace "To sarauniyar masu wayon duk duniya, kuna bacci ya tafi, amma bai fita daga gidan ba saida yace na tabbatar na sumbaci dukanku a madadin shi."

Khalifa sarkin surutu da sauri ya fad'o jikinta yace "Ni ne farkon da za'a farawa, dama ko a haihuwa nine farin cikinshi na farko."

Tab'e baki Raihan tayi tace "Dallah malam matsa min daga nan, taya zaka zama farin cikinshi na farko bayan an haifeni kafin kai."

Matsowa tayi kusan Sameera ta sunkuya tace "Ammie ni ce farko."

Hararansu Sameera tayi tace "Ga Abdul babban amma saiku da kuka fi kowa son girma."

Hannun Abdul ta kamo ta matso dashi kusanta, kunya ce ta rufe shi dan shi yanzu kallon suruka yake mata ba uwa kad'ai ba, haka ko ta dafe kumatunshi ta sumbata tare da shafa kanshi tace "Allah ya albarkace ku yarana."

Cike da jin dad'in addu'ar ta yace "Ameen Ammie, mun gode da addu'ar ki gare mu."

Jabeer ta kamo shima ta masa kafin Raihan da Khalifa da kuma sauran yaran, bye bye suka musu suka tafi har Khalifa na juyowa ya kalli Ammie yace "Yar tsohuwa naga sai kallona kikr yau ban kulaki ba ko, to zan siyo miki goro idan zan dawo."

Tab'e baki tayi tace "Ka ci k'aniyarka ko da kai da goron."

🤴🏻 *Masautar Basraba*🤴🏻

Sarki Imran Musayyib ne zaune akan sofa wacce tasha kwalliya mai d'aukar ido da birgewa, sanye yake cikin kaya na alfarma kuma na sarauta, sai dai babu nad'i a kanshi sai hula kawai, hatta takalmin k'afar shi irin na sarauta ne masu kwalliya daga sama kuma rufaffe, sai gefenshi liman ne tare waziri suna kallonshi da girmamawa yace " Liman kunce zakuyi magana dani mai mahimmanci, shiyasa ma na ce mu zo nan ciki saimu tattauna."

Duk da yana sarkinsu amma suna jin dad'in yanda yake girmamasu saboda shekarunsu da kuma dad'ewarsu a fada, dan tun mahaifin Sameera na kan mulki suke tare da su har mahaifinshi ya karb'a kuma shi yanzu gashi a kai, liman ne ya kalli waziri yace "Waziri sai kayi bayani ko."

Kallonshi waziri yayi ya kuma kalli sarki yace "Ranka shi dad'e Allah yaja zamaninka, dama magana ce data shafeka ta kuma shafi cikin gida, to mun jima muna sonyin maganar amma duba da yanda zaka d'auki maganar yasa mukayi shiru, yanzun ma mu fara jin jita-jita ne a gari da kuma labari daya zo mana daga wasu masarautun na magaganu da ake ta yad'awa akan ka, shiyasa muka ga hakk'inmu ne mu sanar da kai abinda ke faruwa."

Wata lallausar ajiyar zuciya yayi ya kallesu a tsanake cikin fitar da kowace kalma a bakinshi yace "Liman, waziri, kar kuji komai ku fad'i abinda ke ranku, ina kallonku ne kamar iyaye na, kuna da damar sakani nayi abu ko bana so."

Cike da jin dad'i waziri yayi murmushin gefen labb'a ya k'ara gyara zama yace "Mai martaba dama magana ce akan aure, kamar yanda kasan dokar garin basraba ta bawa mace damar yin mulki in har tana da aure, to haka ma dokar basraba ta bawa sarki damar auren mace biyu, uku, hud'u, amma mata d'aya bata dace da sarkin wannan gari mai tarin albarka ba, yanzu haka tsegumin da al'uma keyi kenan da ma wasu masarautun ana cewa sarki ya karya doka ta hanyar zama da mace d'aya har na tsewon shekara goma sha biyar, shine muka ga ba zamuyi shiru ba al'umar gari su ci gaba da tsegumi akan masarautar nan ba tare da munyi yunk'urin dak'ile matsalar ba."

Shiru yayi kansa k'asa yana tunani akan abinda suka fad'a, tabbas gaskiya ne shi kanshi yana tunanin k'ara aure ko da zuciyarshi na son *Ameera* ne kad'ai, amma kuma ganin matsalar mata da ba'a rabasu da kishi musamman yanda suke k'azanta shi idan ance sun had'u gidan sarauta ko wani babban gida, shi shaida ne akan irin kishin da matan mahaifinshi keyi da mahaifiyarsu, duk da sun gamsu shine magajin sarki amma kuma suna bak'in ciki da hakan, kawunansu shi da yan uwanshi ba a had'e yake ba saboda yan ubanci, to wannan ne yake mishi shamaki da tunanin k'ara aure sai yaji yafi so yayi ta zama da Ameerarsa kuma sarauniyarsa, yana cikin tunanin abun fad'a musu liman yace "Ranka shi dad'e ba abu bane na ujila da muke buk'atar jin amsa daga bakinka yanzu yanzu, zamu koma mu, lokacin daka yanke shawara ma ji."

Waziri da sam maganar liman bata masa dad'i bane ya kalleshi, tsaki yayi a cikin zuciyarshi saboda takaici, shi fa burinshi yanzu bai wuce ace 'yarsa ta shigo gidan sarauta ba a matsayin matar sarki, kuma yayi sa'a *uwar d'aki* (mahaifiyar Imran) har yanzu bata son Ameera saboda ganin basu dace ba, shiyasa ma ta k'arfafa masa gwiwa kan su tuntub'e shi da maganar k'ara aure, ita ko ta mishi magana zai shawarci *takawa* (har yanzu suna kiran tsohon sarki da wannan sunan), kuma takawa zai bashi zab'i ne yayi idan yana so idan baya so ya bari, uwa uba kuma 'yar uwarshi Sameera kuma mai bashi shawara akan harkokin mulki dama na cikin gida, ita kanta zata zame musu matsala, dan hakane ya taho da liman dan su mishi magana saboda yana matuk'ar ganin girman liman saboda mutum ne da babu wanda yake shakka in banda ubangijinshi, zuwansu tare ne zaisa ya yarda da duk abinda suka fad'a ya kuma gamsu, muryar sarki ce ta dawo dashi daga duniyar tunani yana fad'in "Liman na yarda da bayaninku, amma duk da haka zanyi shawara, duk abinda na yanke zaku ji."

Da girmamawa liman ya amsa da "Allah ya shige mana gaba, Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana."

Mik'ewa yayi yana fad'in "Mun barka lafiya ranka shi dad'e."

Mik'ewa waziri yayi yana bin bayan liman da harara, shi da ya so ayi komai a k'are yau d'in nan, amma gashi ya mishi shamaki da matsayin dake tunkaro shi, suna fita ya mik'e ya d'auki babbar alkyabarshi ya saka ba tare daya d'ora hular ta ba, cikin tako d'aid'ai ya tunkari k'ofar fita, yana isa k'ofar fadawa biyu ne tsaye suka sunkuya suna masa kirari, wucewa yayi suka take masa baya, duk da dare ya fara yi amma har yanzu ana kai da kawowa gidan, iya hangenka iya girman gidan, a haka ya isa b'angaren tsohon sarki wanda yanzu baya komai sai zaman gida da bawa mutanen gidan karatu, dan har yanzu jikinshi babu kyau tun rashin lafiyar daya kwanta sakamakon rashin sanin inda d'an uwanshi da yarshi suke, kamar yanda baya buk'atar k'yale k'yalen duniya hakan yasa ko mai gadin shiga k'ofar shi babu, Imran kuma dama kai tsaye yake shiga wajen mahaifin nashi, dan haka yanzu ma suna kawowa ya dakatar da fadawa shi kuma ya k'wank'wasa k'ofa, yaye labulen yayi dan tunda yaga k'ofar bud'e yasan zai iya shiga kai tsaye, zaune ya hango Musayyib ya tank'washe k'afafun shi da wani babban littafi a gabanshi yana karatu, yana ganinshi ya rufe littafin yana sakin murmushi da fad'in "Imaran kai ne yanzu? Zo zauna nan." Har Imran ya zauna shima yana murmushin, saida ya gama daidaita zama kamar yanda mahaifinshi yake kafin ya kalleshi yace "Ni ne Abba, Abba na karatu ake?"

Da murmushi ya amsa da "Kamar dai kullum."

"Allah ya k'ara maka lafiya Abba na, Allah ya k'ara maka nisan kwana."

Murmushi yayi sosai yace "Imaran, ko yanzu na mutu Alhamdulillah, na rabu da iyayena lafiya, nayi mulkin jama'a kuma na tabbatar ban bar hawaye a idon talakana ba sai wanda ubangiji bai bani ikon saninshi ba, ina zaune da ku lafiya, to ni kuwa me zan nema a wata doguwar rayuwar?"

Ba tare da murmushi ya bar fuskar Imran ba yace "Hakane Abba, ina fatan Allah yasa na kamalta mulki irin naka."
Chapter 22 · 0% Book details