← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 198

Sashe 138

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da k'yar ya iya b'oye tashin hankalinshi da tsoron al'amarinta, shi bai ma san ta zubar da ciki ba sai yanzu, lallai abun azimun ne, shirun da yayi yana kallonta yasa ta kalleshi tace "Ammar yanzu ne na fahimta banda masoyi a duniyar nan sama da kakanka, ashe duk yasan da abun nan kuma bai tab'a nuna min ko ya fad'a min ba, duk irin rashin mutumci da wulak'anci dana masa..."

Kuka ne ya k'wace mata ta sunkuyar da kai tana kuka, saida ta nutsu ta d'ago tace "Da wane ido ne zan dinga kallonshi yanzu, Ammar babu irin k'ask'ancin da ban mishi ba a rayuwa, a rayuwar aurenmu nasan akwai lokacin da yayi farin ciki, amma bak'in cikin da yayi ya ninka farin cikin sau ninkin ba-ninkin, duk da yasan lagona yasan makullin ruguza duk wani gidan rashin mutumcina amma bai bud'e ba, Allah sarki bawan Allah, wannan dalilin ne yasa nake k'ara son shi kullum, *hak'uri*, yana da matuk'ar hak'uri."

Murmushi yayi yace "Hakane Hajia, amma ki gode Allah da yasan kika fahimci haka tun dukanku kuna raye, kinga kenan akwai damar neman yafiya da gyara kuren gaba."

Kallonshi tayi tace "Hakane Ammar zanyi, amma dan Allah ka fad'a min idan kasan akwai wani abu daya kamata na sanshi?"

Shafa gemunshi yayi yana nazari, sake matsowa yayi kusanta ya rik'o hannunta yana kallon idonta cikin bin kowace kalma daki-daki yace "Hajia, bansan komai a game da kowa ba sai wanda ke fitowa yanzu, kaina kawai na sani."

Bakinshi ta k'urawa ido tana kallo kamar mai son fahimtar yarenshi tace "Ka aikata wani abu ne kai ma daya kamata na sani?"

A hankali ya jinjina mata kai alamar eh ba tare daya rusuna idonshi daga kan fuskarta ba, cikin zak'uwa tace "Meye? Me ka aikata Ammar? Kenan pentina ya shafeka?"

Kai ya fara jinjina mata tare da cewa "Eh, Hajia nawa yafi na kowa muni, kowa abun bai faru dashi da wani na shi ba, amma ni da yer uwata haka ya faru, wacce muka tashi tare uwa d'aya ta rainemu, da ita d'in ma hakan ya faru ne a d'akin uwata mahaifiya."

Yanda suke kallon juna kai kace basa gane yaren junansu, cikin mamakin dake son kasheta tace "Wa kenen? Ka fad'a min kaina ya kulla na gaza tuna komai."

Marairaicewa yayi yace "Wallahi Hajia tsautsayi ne da kuma k'addara, ban shirya yin hakan ba, banyi niyyar yin hakan ba kawai aikatawa nayi."

Fahimta da tayi yasa ta kafeshi da ido tace "Hamna ko Amna?"

Saida yayi k'asa da idonshi yace *"Hamna."*

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallahu wa ni'imal wakil."

Wani irin kallo ta masa taja baya sosai tace "Wallahi Ammar ba dan kana d'aya d'aga cikin wanda suka min sanin shanu ba da yau saika raina kanka."

Sunkuyar da kai yayi baice komai ba, d'auke kanta tayi daga gareshi tace "Jikana da jikanyata? A cikin gidana suka aikata zina? La'ilaha illallah."

Jujjuya kai ta dinga yi tana ta fafutakar saita nutsuwarta, kallonshi tayi ta mik'e tsaye da duka sauran k'arfin daya rage mata ta gaura masa mari a kumatun dama tace "Kasan kayi wannan ta'asar akan me ka yarda aka aura maka yer uwarta? Kai wane irin shaid'ani ne Ammar, kayi tarayya da babba kuma kayi da gaba d'aya tazarar lokacin dake tsakaninsu bata wuce minti biyu zuwa uku ba."

Komawa tayi ta zauna kan gadon ta kalleshi cike da jin haushi tace "Fitar min a d'aki."

Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Kuyi hakuri Hajia, wannan shine dalilin da yasa duk wanda yayi katob'ararsa yake rufe abarsa, kowa yafi so kiji daga baya yanda zuciyarki zata buga ki mutu kowa ma ya huta."

Da kallo ta bishi, shima hushi ne yayi shiyasa ya fad'i haka, gajeran tunani tayi sai gata babu buk'atar yin zafi a wannan lokacin, kuma abinda ya fad'a gaskiya ne kawai, cikin taushin murya tace "Dawo nan Ammar."

Tsayawa yayi daga shirin bud'a d'akin ya dawo ya zauna inda ta nuna masa. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi ta rik'e hab'a tace "Duk laifina ne da bana iya fahimtar komai, kamata yayi ace na gane yarinyar dake gabana, amma ban gane hakan ba."

Kallonshi tayi tace "Amma me yasa baka fad'a min har ka bari ka auri yer uwarta kuma? Ai da sai ka auri ita Hamna."

Kallonta yayi shima yace "Ummy ce matsalar, bata so kowa ya sani sannan ta daina kulani."

Cikin raha tace "Rabu da ita kawai, yanzu ma karka fad'a mata na sani nasan dai duk nice take jin tsoron kar na sani."

Rik'o hannayenta yayi yace "Dan Allah Hajia ku gafarce ni ku yafe min, Allah nima ina jin kunyar kaina dan nasan ban aikata daidai ba, ku yanke min duk hukuncin daya dace dani zan d'auka, ba zan ji kunya ko tsoro ba, kuma zan nemi kowa yafiya daga iyayenmu dana zubarwa da mutumci har ita Hamna da kuma Amna."

Da sauri ta girgiza masa kai tace "A'a Ammar, muyi shiru d'in shi yafi, ka sani a rayuwa akwai abubuwan da ba'a buk'atar su fito fili, yin shirun shine maslaha a yanzu duk da dai nasan akwai ranar da zasu fito, domin kuwa daga yanda yanzu naji sirrin k'uruciyata a wajenka ya tabbatar min babu wani abu fa da za'a b'oye bai fito fili ba, sai dai kafin mu fitar dashi mu fara duba maslahar dake cikin rashin fad'an da kuma fad'an."

Cikin nutsuwa tace masa "Misali yanzu idan Hazida taji me kake tunanin zatayi?"

Saida ya d'an rarraba ido yace "Ba zata ji dad'i ba Hajia."

Da hannu ta masa alamar tace "Ba iya rashin jin dad'i kawai ba, hatta zumuncin dake tsakaninta da mahaifiyarku zai lalace, 'yarta ce fa data haifa kuma su kad'ai gareta, sannan ni kaina zata min alawadai da salon rainon nawa tace shiyasa ban barta da yaranta ba, shin zakaji dad'i idan haka ta faru?"

Girgiza kai yayi a hankali yana d'an shigar da leb'enshi na k'asa cikin baki, d'orawa tayi da " Sannan ka duba al'amarin ta b'angaren yer uwarta da kake aure, Ammar ya zakayi ka fahimtar da ita sanda taji? Wane irin gamsashen bayani zaka mata?"

Shiru yayi yana d'an girgiza kai, shi fa bai tab'a tunanin yanda Amna zatayi ba idan taji, kawai a yanda ya tsara ko da abin ya fito kowa yaji zai murje ido ne ya tsula tsiyarshi dole kowa ya shafa mishi lafiya, Amna kuma daya bubburma mata ashar tare da mahaukacin mari dole ko mafarkin yi mishi iskanci tayi sai tayi addu'ar tsari ta juya kwancinta, kamar Hajia tasan me yake tunani sai kuwa tace "Kasan adadin kishin matarka? Ammar kasan suffar da mace ke zama yayin data rikid'e sakamakon kishi? To ko da wasa ne ka jaraba ka gani, wannan mai tsoron na ka kamar mutuwarta zata kalleka ido cikin ido, rawar muryar da take sanda take magana da kai zata rera maka b'acin ranta kamar tana rera k'ira'a, shiru da takeyi sanda ka daketa to ba fa lallai ta iya yin shirun ba, Ammar, a wannan fannin ba lallai ka samu girmamawa daga wajen Amna ba, dan haka shirun nan shi yafi kamar yanda mahaifiyarka tayi."

Cikin marairaicewa yace "Hajia to dan Allah ki yafe min, idan kika yafe min nasan komai zai zo min da sauk'i insha Allahu."

Murmushi ta masa tace "Ba komai Ammar na yafe maka, nima ku yafe min kaji."

"Baki mana komai ba Hajiata." Ya fad'a da murmushi, kallon agogo yayi da sauri ya mik'e tsaye yace "Hajia zan tafi asibiti yanzu, saina dawo."

Kai ta jinjina alamar to, tana binshi da kallo har ya fita, yana rufe k'ofar d'akin ya sauke wata ajiyar zuciya mai k'arfin gaske yayin da yaji wani sanyi ya ratsa shi, ita kanta yana fita wani sakayau taji kamar ta rage nauyin wasu kaya data jima tana dakonsu a kanta.

A falon dai ya same su dukansu, saida yaje kusanta ya kalli fuskarta, murmushi kawai yayi yana mamakin taya wannan innocent face d'in zata tabka rashin mutumcin da Hajia ta zayyana masa idan idonta suka rufe akan kishi, yo shi kwarjininshi ma zai barta tayi? Ganin ya tsaya kanta yana murmushi yasa tace "Yah Ammar ya dai?"

Kallonta yayi sai kawai ya had'e girar sama da k'asa ya zama boss ya sunkuya yace "Kalli ido na."

Bud'a matsakaitan idonta tayi ta kalli k'wayar idonshi, Hamna ma dake gefe tana jin ya fad'i haka ta kalle shi duk da ba ita yake kallo ba, tab'e baki tayi ganin sun k'urawa juna ido. Tana kallon idon nashi tayi saurin sunkuyar da na ta tana dariya tace "Ba zan iya ba yah Ammar, mutuwa zanyi da tsoron abinda nake gani."

Wani shak'iyin murmushi ya mata ya shafa kumatunta yace "Ki ci gaba da kasancewa haka to ko da ranki ya b'ace a kaina."

Sumbatar bakinta yayi yace "Ina sonki aljannata."

"Nima haka." Ta fad'a tana mayar masa da martani, ta gefen ido ta harareshi ko da taji ya fad'i kalmar, tsaki tayi wanda yasa ya kalleta yace "Yarinya kiyi aure ki rage zafin zuciyar nan, kin ganni nan ba zan fasa abinda nayi niyyar yi ba da duniyata, wannan kayan halak d'ina ne kuma malak, naga wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama."

A hassale ta kalleshi tace "To ina ruwana, dama na fad'a maka zan hanaka wani abu ne? Su dake halak d'in naka dai kaji da su, wasu ai sun maka nisa."

Cike da rainin wayo yace "To ina ruwana dana wasu dama? Na ga dai duk abinda ke akwai can shine anan, to miye na k'aryar kuma?"

Ita ma murmushi tayi tace "Banyi musu ba cewa akwai hallitu dayawa da suke iri d'aya da na ta ba, amma bai zama lallai komai ya zama d'aya ba, kamar yanda tasirin ma ba d'aya bane."

Kallonta yayi da wata fassara a fuskarshi kafin ya kalli Amna yace "Duniyata na tambayeki mana? Yanzu dan Allah sai muka je shago tare muka siyo alawa iri d'aya a ledarta, yanzu zaki yarda na ce tawa tafi taki kyau da dad'i ko kuma ni na yarda idan kika fad'a min haka?"

A tare Hamna da Amna suka ce "Ya danganta."
Chapter 138 · 0% Book details