Sashe 86
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya tayi tace "Da kaina zan d'aura maka, tunda saika d'aura shine zaka fito a buzun."
Mik'ewa tayi tace "Saida safenku, ku kwanta da wuri kunsan gobe ne fa auren ubanku."
Sai lokacin Ammar ya kalleta ta wutsiyar ido ya kuma d'auke kan shi, fita tayi inda Ammar ya mik'e zai shiga d'aki, Amar ne yace "Ka tabbatar ka tashi da wuri fa, dan Abba yace ni da kai ne zamu take masa baya muna karb'ar bak'i."
Juyowa yayi ya kalleshi k'ala baice ba ya shige ciki ya barsu, Jibril ne ya gyara zama yace "Yau fa mutanen sun motsa."
Murmushi Amar yayi yace "Allah dai ya kyauta."
"Ameen." Cewar Junaid.
A nesa da k'ofar gidan ya paka mota ya tsaya inda kawu Mamu ya shiga dan kiran Zeituna, ba laifi gidan ya kaure da cacaniya alamar dai biki za ayi gobe, tuni dama ansa Zeituna ta shirya cikin wani kalar d'inki na atamfa wanda ba dan ta sanya hijab ba sai a mata dariya, dan kaf dangin babu mai wayewa ta zamani haka ita ma, dan ba k'awaye gareta ba bare tasan abu mai kyau ko marar kyau, lalle da kitso ma tayi sa'a a unguwar aka samu wanda suka iya suka mata, wata doguwar jagira aka ja mata tare da shafa mata jan jan-baki, fitowa tayi tana hard'e k'afafu saboda tsoron abinda zata tarar, tana isa ta inda yake ta tsaya kanta k'asa, tunda ta taho lieutenant ke hangenta yana raya abubuwa da dama, tana tsayawa ya sauke gilashin murya a d'an kausashe yace "Sai ki shigo ko, kinga ni ba yaro bane bare na fito na tsaya kowa na kallo na."
Gabanta ne ya tsananta fad'uwa ta zagaya ta kama k'ofar ta shiga, da k'yar ta janyo k'ofar ta rufe ta sake mayar da kanta k'asa tana wasa da yatsunta daga cikin hijabi, kamar yace ke ta zuba a guje take ji, wai yau gata a mota da Abban Ammar ana shirin d'aura musu aure gobe, jin shirun ne yasa ta tsargu ba tare data d'ago ba tace "Ina wuni."
Ajiyar zuciya ya sauke dan dama yana jiran tayi magana ne, kallonta yayi yace "Lafiya lau, ya hidima?"
Shiru tayi kamar ba taji ba, kallonta yayi kamar ya shareta sai kuma yace "Tun yaushe kike so na? Kuma kina ganin hukuncin da Alhaji ya yanke bai tauyeki ba? Har zuciyarki zaki iya zama da ni?"
Zeituna dake jin tambayoyinshi kamar saukar guduma a kanta tasan ba zata iya amsawa ba, sai kawai ta fashe da kuka tasa hannu ta toshe baki, sororo yayi yana kallonta da mamakin kukan na meye? Wani abu ya fad'a daya b'ata mata rai? Ko kuma sangarta ce tana so ya fara rawar k'afa yana rarrashinta? Ai ko abinda ba zai yiwu ba kenan, fuska ba annuri yace "Meye na kuka kuma? Na fad'i wani abu ne? Ko kuma dai takuraki akayi?"
Girgiza kai tayi hakan yasa yace "Shin akwai wani abu da kike buk'ata ne?"
Nan ma girgiza kai tayi hakan yasa ya kawar da kansa yace "To ni zan tafi, saida safe ko?"
Ji tayi wani kukan ya taho mata wanda yasa tayi saurin bud'e k'ofar ta fito, rufewa tayi ta taka da hanzari ta tunkarin gidan, saida ya ga shigarta kad'ai ya ja d'an k'aramin tsaki ya tayar da motar ya bar unguwar.
*11: 49* na dare Ammar ya mik'e zaune tsakiyar gadonshi, tsaki yayi tare da kama hantsar wandonshi yace "Shikenan mutum idan baida aure baya da nutsuwa har abada."
Sakin wandon yayi ya sauko daga kan gadon, ban d'aki ya shiga ba wani jimawa ya fito, rigar wandon baccinshi ya d'auka fara ya saka ya fito, duk wani kwanon abinci daya gani a falon nasu saida ya duba amma babu abinci, fridge ya duba nan ma sai lemu kawai da ruwa, wani tsakin ya kuma ja tare da nufa k'ofar fita, acan bayan gida yake jin hayaniyar matan suna aiki, kai tsaye falon Hajia ya shiga wanda ke bud'e har yanzu saboda matan basu shiga ba bare a rufe, madafa ya wuce da niyyar shiga sai yaji k'ofar a rufe, baiyi mamaki ba dan dama idan dare yayi ana rufe k'ofofin ko ina, dawowa yayi da niyyar fita kawai dan ba zai iya jura jin bak'ar magana daga bakin kowa ba, ta kusurwar d'akin Alhaji yabi zai wuce sai yaji motsi, d'an murmushi yayi ya matso ya kama k'ofar zai bud'e sai yaji muryar Alhaji na magana da alama addu'a yake yana fad'in " *Allah kaine Allah, Allah kai kace mu rok'eka zaka amsa mana, gashi ina rok'onka kaina k'asa, Allah ka kare min zuri'ata da ahalina, Allah ka karesu daga aikata alfasha, Allah ka kare min 'ya'ya da jikokina daga sharrin zina, Allah ka kub'utar dasu da ikonka, Allah kai shaidane ban tab'a aikata zina ba, ban tab'a k'etara iyakar wani ba ta hanyar cin zarafin iyalinshi, amma ya zama dole na rok'awa iyalina kariya saboda sharrin zamani, sannan iyali suna kimtsuwa ne idan ka zab'ar musu uwa ta gari, nayi kuskure tun farko dana amince da auren Zeeya'atu, duk da a waccen lokacin ina da k'arancin ilimin addini ban kuma farga ba saida muka hayayyafa, Allah ina rok'onka ka kare min zuri'ata kada zunubin zina da mahaifiya ko kakarsu ta aikata a lokacin k'uruciyarta ya shafesu, Allah ka nesanta su da laifin zubar da cikin da mahaifiya kuma kakarsu tayi kar ma ya shafesu daidai da k'wayar zarra, Allah ka sani baiwar nan taka har yanzu bata neman shiriya daga waccen laifin, kullum tsanar mazinata take k'arawa a zuciyarta saboda tasan muninta, Allah ka shiryeta dan tsarkin mulkinka, Allah ka farkar da ita ta gane kurenta na baya ta buba gareshi, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah ya Allah.*"
Jin wannan addua'r yasa Ammar sakin k'ofar yayi jim, Hajia? Hajia dai, wannan shine dalilinta na tsaurara sa idonta akan zuri'ar ta kenan? Wannan shine dalilin da yasa take k'in yayan da aka haifa bata hanyar aure ba? Ashe ita ma tayi rayuwarta a baya ta holewa? Kukan da cikinshi yayi ne na yunwa ya farkar da shi daga tunaninshi, dafe cikin yayi ya juya ya kalli d'akin Ummy, murtuke fuska yayi kafin ya tukari d'akin da niyyar tambayarta makullin madafa, dan ba zai tambayeta abinci ba yasan zata fad'i bak'a ne, yana isa ya zura hannu zai bud'a sai yaga k'ofar ba rufe take ruf ba, turawa yayi ya ga ta bud'e sai kawai ya shiga cikin takon isa da k'asaita.
Mahaukacin turarenshi ne ( *Respond*)ya ganar da ita shine, da sauri ta d'ago ta sauke ido a kanshi saida gabanta ya fad'i, mamaki take meya shigo dashi a wannan lokacin d'akin Ummy? Dare fa yayi, shi kanshi mamaki yake ganinta a tsakiyar gadon Ummy zaune da littafinta na makaranta da kuma farantin kankana a gabanta, cikin kallon tuhuma ya tsaya gaban gadon fuska a had'e yace "Me kike anan d'akin?"
D'auke idonta tayi daga kanshi ta harareshi ta wutsiyar ido a zuciyarta tace "Kai baka ga abinda nake bane?"
A zahiri kuma cewa tayi "Karatu nake."
Cike da kallon raini yace "Yawon biki ya hanaki d'aukar darasinki ko? Da alama kuma jarabawa zakuyi gobe, to Allah yasa ki fad'i watak'ila ki shiga hankalinki."
Baki bud'e ta kalleshi da mamaki irin wace irin magana ce wannan? Fahimtar kallon yasa shi cewa "Eh naje na fad'a, ko zaki ci min uwa ne?"
Wani murmushin baka da hankali ta masa tace "Ah haba dai ranka shi dad'e, ni na isa, Allah dai ya k'ara girma."
"Zaki iya mana, ba kece sarauniyar ce min Allah ya isa ba."
Yanda yayi maganar yasa ta zabura ta durka daga kan gadon da nufin shigewa ban d'aki, da sauri yasha gabanta ya tsaya k'ik'am, sai lokacin ya k'are mata kallo ya fahimci ashe wando ne iya gwiwa a jikinta da rigarshi saidai basu kamata ba, sai wata hula data saka bak'a mai duwatsu masu k'yali a gabanta, kasancewar yafi ta tsayi sosai yasa yayi k'asa da kanshi yana kallon k'irjin ta wanda da gani kasan rigarce kawai babu bras, kawar da kanshi yayi ya d'an cije leb'e, ba tare daya kalleta ba yace "Koma ki zauna, ai idan na tashi hukuntaki duk inda zaki shiga zan biki."
Turo baki tayi gaba ta kalleshi kamar zatayi kuka, yana kallonta yayi saurin d'auke kanshi ya furta "Ya Allah." Lumshe ido yayi ya d'aga kai sama, wannan yanayin da tayi ba k'aramin tashin hankalinshi tayi ba, "Meyasa take birgeshi wani lokacin?"
Kafin ya samu amsa ya sake kallonta rai a b'ace saboda halin da take k'ok'arin jefashi yace "Ki koma ki zauna na ce."
Kamar sakara haka ta saki baki da tunanin to meyasa kai ba zaka tafiyarka ba? Juyawar da tayi ita tafi sa shi yin nadama, gaskiya Allah ya musu hallita ta wannan fanni kam sai godiyar Allah, juyawa yayi ya zagaya inda ya fara tsayawa ita ma ta koma ta zauna, kankanar da take sha ya d'auki yanka d'aya yasa a baki ya guntsira, wani matashin murmushi yayi yace "Kankana."
Kallonshi tayi sai kuma ta mayar da kallonta ga littafinta, sauran daya rage hannunshi ya mik'o mata da fad'in "Sha."
Wani yamutsa fuska tayi alamar k'yama k'arara, sake zuro mata yayi kamar zai saka mata a baki hakan yasa tayi saurin kawar da kanta, cikin tsawa yace "Karb'i nace."
Juyowa tayi tasa hannu ta karb'a zata aje yace "Cewa nayi kisha."
Kallon fuskarshi tayi tana d'an nuna mishi da hannu cike da k'yama tace "To ai yah Ammar ni...wallahi bana son wannan..abun ne."
Kafeta yayi da ido yace "Meye ba kya so?"
Saida ta matsa baya kafin tace "Ka gane yah Ammar, gaskiya ba zan iya sha ba saboda wannan dogon gashin na fuskarka."
Na farko daya kalleta da mamaki, wai dogon gashin fuskarshi, tana nufin gemunshi fa? Gashin da man da yake shafa mishi ma wata rana saiya zagaye garin nan bai samu ba sai yasa abokanshi da sukayi karatu a France sun aiko mishi, shine za tace wai tana k'yama, shi kam ya zaiyi da kankana ne? Kama gemun yayi yana shafawa tare da kallonta, can ya saki wani murmushi na mugunta, ba tare daya daina murmushin ba yace "Wato kina k'yamarshi ko?"