← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 198

Sashe 117

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun ya faru ne shekara d'aya da dawowar Ammar daga Canada, a lokacin ba'a gyara wurin hutawar dake bayan gidan ba, da sassafe ne tashinshi kenan ya zagaya da wayarshi a hannu, yana zuwa ya samu Hamna da Amna suna nishad'unsu bakin bishiya, kamar an koreshi daga sama saiko k'adangaren nan ya fad'o saman hannun Hamna, wanda yanzu haka akwai shatin yagin daya mata, k'wala k'ara tayi ta zabura ta mik'e tsaye ta fara rawar disko a wurin ido rufe tana ihu tana neman a taimaka mata, Amna da ita Allah bai saka mata tsoron wannan abubuwan ba rik'ota tayi jikinta ta buge k'adangaren da shima ya gigice yake neman hanyar barinta, tana bugeshi ya kama gabanshi shima, shiru tayi suna kallon k'adangaren daya bar wurin, daga bayansu Ammar dake ganin komai yace "Shegiyar kankana, ashe sakara ce ke, d'an waccen abun ne kike ma wannan zullon har kina neman cire da siket d'inki."

Juyowa sukayi suka kalleshi, turo baki tayi ta harareshi tace "Eh d'in, ina ruwanka?"

Dalla mata harara yayi yace "Ke ki kiyaye ni wallahi, ni ne maraininki kenan da zaki juya min d'an banzan baki kamar na tsaka."

Murgud'a baki tayi amma ba tace komai ba, juyawa yayi zai bar wurin Hamna ta bishi da harara tace "K'aton wofi, dube shi watak'ila shima tsoronsu yake."

Tsaf a kunnenshi, a hankali ya juyo ya fara takowa kansu yana saka wayarshi aljihu, haba ai sai tattare siket tana shirin zabgawa a guje, tako biyu yayi ya fizgota ta dawo baya, rik'e hannunta yayi sosai ya fara kallon bangon wurin yana fad'in "Yanzu zakiyi tsallen mai digri idan ya shiga rigarki ya sosa miki baya."

Ko da taji haka ta durk'ushe duk da yana rik'e da hannunta ta fara kuka tana bashi hak'uri, cire slipas d'inshi yayi ya wurga ma wani k'adangare da ya zo wucewa, tip ya fad'o k'asa a mace, janta yayi k'iiii saida ya kaita kusan k'adangaren ya sunkuya ya d'aukeshi da hannu, tana ganin ya d'auka ta k'ara zabga wata k'ara iya k'arfinta, yana nufowa dashi kusanta ta lumshe ido ta lamgab'e tana shirin fad'uwa k'asa, da sauri ya rik'ota yana kallonta, suma tayi da gaske, d'ago idon shi yayi ya kalli Amna dake gefe d'aya ta takure, cikin shan kunu yace "Kawo ruwa."

Da gudu ta juya dan kawo ruwan, yana ganin ta tafi ya saki Hamna ta fad'i k'asa da k'arfi, wayar shi ya fiddo ya ci gaba da latsawa, Amna na zuwa jikinta sai rawa yake kamar ita ce ya damk'a, mik'a mishi ruwan tayi ya juyo ya mata wani kallo, har zata bud'e ta zuba mata sai kuma yasa hannu ya karb'a, yana bud'e bakin robar ya shek'a mata su a fuska, a firgice ta mik'e tana sakin yar k'ara, yana ganin ta mik'e ya jefa mata robar ya nufi hanyar fita, Hamna da takaici ya gama kasheta sai cewa tayi "Allah ya isa sojan banza sojan wofi, k'wara da baka zama sojan ba nasan da duk ka harbe kowa, dan ba k'aramin marar imani za ayi ba."

Juyowa ya sake yi da sauri ya nufota yana sa wayarshi aljihu, Amna ce tayi saurin cewa "Dan Allah yah Ammar ka..." Bai bari ta fad'a ba ya mata wani jan kallo yace "Kina son kanki da rahama?"

Cikin tsoro tace "Ina so yah Ammar, haka kuma ina so wa yar uwata ma, dan Allah ka k'yaleta ba zata k'ara ba."

"To ina zuwa." Ya fad'a yana yin kan Hamna data mik'e tsaye tana kakkab'ar kayanta, kamar guguwa, guguwar wacce ta taso a tsakiyar sahara, haka taji ya sunkuceta yayi sama da ita baki d'aya, saida yaje bakin bishiyar daya same su zaune ya tsaya, kamar a tsarin film sai kuwa ya sab'ata a kafad'a ya rik'e bishiyar ya fara takawa yana hawa da ita, zullo take tana k'ara tana kiran sunan Ummy duk da tasan tana asibiti. Amna ma da gudu ta tafi tana fad'in "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri ka sauko da ita."

Ita a tunaninta idan ya hau zai sakota ne ta b'are baya kamar yanda yake wayan cewa wata rana saiya b'are mata baya, saida yaji ya hau inda ya mishi sannan ya tsaya ya tallabota ya mata d'aukar jarirai ya azata kan bishiyar, zaunar da ita yayi sannan ya dirko daga kan bishiyar da k'arfi, d'aga kai yayi ya kalleta yace "Dan ubanki kice tak ki gani idan ban sa aka kawo min zaki ba na d'ora shi anan shima, kedai kinsan me zai faru ai."

Juyawa yayi zai fita cikin matsanancin kuka harda shashek'a tace "Dan Allah kayi hak'uri boss, wallahi Allah ba zan sake ba na tuba."

Hannuwa yasa aljihu ya d'aga kafad'a yace "Kin tab'a ganin boss yayi niyyar shek'e mutum kuma ya hak'ura ya barshi a raye?"

Tafiya yayi ya barsu nan sai Amna data fara k'ok'arin taimaka mata ta sauko, amma ita tayi nisa ba zata iya kama hannunta ba bare ta sauko, kallonta tayi tace "Bari na duba a waje na samo wani ya taimaka miki."

Fita tayi inda Hamna ta gumtse baki a zuciyarta tana fad'in "Azzalumi mai bak'ar zuciya mugu."

Jim kad'an sai ga Amna tare da Jibril da Iya sun shigo, tunda ya ganta saman bishiya ya kece da dariya, saida ya ci mai isarsa kafin yace "Ke kuma me kika mishi haka daya d'oraki kan bishiya?"

Shiru ta masa sai kumbura take kafin ya taka da k'yar ya kamo hannunta, saida ya sauko sannan ya k'ara kamata ta k'arasa dirowa, duk gidan babu wanda bai ji abinda ya faru ba, wasu sunyi dariya sosai inda su Ummy kuma suka yi ta masifa da fad'a.

*Ci gaba*

Zuwa *09:30* na dare ya kammala da majinyatanshi, ban d'akin dake cikin ofishin ya shiga ya fito, wata coffre ya bud'a ya fito da wasu kaya, wandon jikinshi ya fara cirewa ya sauya da wannan sannan ya zauna ya d'aura wannan guma'gumen takalman bak'ak'e, cire riga yayi ya saka wannan ya b'alla botiran ya d'an rage ma hayyanen tsayi ta hanyar nad'esu sannan ya soka rigar cikin wandon, d'amara ya d'aura sosai ya zarge kafin ya d'auki bindiga a cikin gidanta ya mak'alata a wandon, saida ya b'alle buton ya fito da ita ya kalla yayi murmushi ya mayar ya rufe, turare ya d'auka ya fesa sannan ya fito ya rufe ofishin ya d'auko hanyar gida, bai zame ko ina ba sai kwatancen da Zeituna ta masa na gidansu, fitowa yayi a cikin mota ya samu wani ya tambaye shi gidan aka nuna mishi, sallama yayi kawu ya amsa ya fito, yana zuwa ko da suka had'a ido ya d'an dafe cikinshi sakamakon juyawa da yayi, *soja?* Soja a gabanshi? Me yayi zafi haka? Idonshi take suka raina fata jikinshi ya fara rawa, cikin rawar murya yace "Aaaa...bbbb...barka rank...a shi dad'e."

Sake zaro mishi ido yayi bai amsa ba sai muzurai yake, k'ara tsorata yayi ya d'an sunkuya kamar zaiyi ruku'i yace "Ranka shi dad'e lafiya? Allah yasa dai ba lafiya nayi ba."

Mota ce ta zo wucewa ta haskasu hakan yasa ya ga fuskar Ammar d'in, amma a tunaninshi Amar ne dan shi kad'ai ya sani, ajiyar zuciya ya sauke ya saki jikinshi yace "Sannu ko, Alhaji kana lafiya? Kaine a gidan yau? Ai kuwa yanzu mahaifin naku ma suka bar nan."

Baice mishi komai ba sai kallonshi da yake dan haka yace " Ai ban samu damar zuwa d'aurin aurenku saboda bana jin dad'i lokacin, ya hidima kuma?"

Wani kallo ya masa yace "Ka sanni ne?"

Kallonshi yayi da mamaki, d'an murmusawa yayi yace "Alhaji ai..." Ji yayi kalmomin sun tsaya kuma ya tabbatar bashi ya tsayar dasu ba, hannun da Ammar ya d'ora akan bindigar dake k'ugunsui ce ya tsorata shi, cikin firgita yayi niyyar komawa cikin gidan yana fad'in "To sai anjima."

Zai koma ciki Ammar yace "Dakata, ba kaine mahaifin yarinyar nan ba? umm wa take ma? Juuuuu...k'arasa min mana."

"Jumare, Jumare, Jumare take, amma ni ban santa ba." Duk yayi maganar ne cikin razani, sake had'e fuska yayi yace "Mu shiga daga ciki mana baba, magana na zo muyi."

Ai da sauri ya shiga cikin gidan yace "Taho taho."

Saida ya k'ara bud'a k'irji cikin tafiya irinta sojawa masu ji da k'arfi ya bi bayanshi, kawu da jiki ke ta rawa ya tattara yara ya turasu d'aki, Jumma ya ma tsawa yace "Ke baki da wayon kawo tabarma idan kinga mutane?"

Tana d'ago kai ta kalli wanda ke bayanshi ta hasken fitilar dake wajen gida da sauri ta tashi ita ma, d'aki ta shiga d'aukar tabarmar amma gabanta da zuciyarta bugawa suke, haka ta d'auko ta shinfid'a musu ta koma d'aki, ba tare daya cire takalmin ba ya zauna a tank'washe k'afafu amma wajen takalmin a k'asa, saida ya d'aga kai ya kalli kowace kusurwa kafin ya kalli kawu dake gefenshi tsaye ya had'e hannaye yana kallon ikon Allah, a kaikaice yace "Fulani ne ku ko?"

"Eh Alhaji."

Kallonshi yayi ya saki fuska yace "Za'a samu nono?"

Kallonshi kawu Mamu yayi, nono kuma? Lallai yau farar rana ce a wurinshi, basu cika aiki da fura da nono ba sosai, amma yau saiya aiki Jumare ta siyo mishi fura da kuma nono mai yawa har da sukari (sugar), da sauri yace "Eh akwai, Alhaji ai ba'a rasa nono a wurin bafulatani."

Murmushi ya mishi yace "To a kawo min, sannan a sa sukari."

Da sauri ya shiga bukkar Jumma ya sameta, a k'warya yace ta zuba dan watak'ila bafulatani ne shima, dan duk da tsoro bai bari ya mishi kallon tsaf ba yaga sufarshi, yana zuwa ya kawo mishi ya juya zai koma ciki yace "...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

✪{T . N}✪📖🖊️

https://www.facebook.com/101305508365889/posts/101311008365339/?substory_index=0&app=fbl

_Bismillahir rahamanir rahim_

_41_

"Zauna mana Abba, ai wurinka na zo."
Chapter 117 · 0% Book details