← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 198

Sashe 75

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin kururuwar Amna yasa mutanen gidan fitowa suka kawo mata d'auki, ganin abinda ke faruwa yasa Ummy tahowa da gudu ta durk'usa ta rumgumo Amna, babu namiji ko d'aya a gidan sai yaran hakan yasa Ummy kallonshi cikin b'acin rai tace "...

*Addu'arku yan uwa.* 👏
22/06/2020 à 17:26 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕

_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_12_

Ma'aruf ne yace "Wai ke yaushe ne zaki fito da kud'in nan a raba kowa ya kama gabansa?"

Ba tare data kalleshi ba tace " Kana gaggawa ne da son samun naka kason?"

A d'an hassale yace "Ban gane? To idan ba'a raba ba uban kud'in zasuyi a account d'in? Kinga ki fito dasu kawai kowa ya d'auki nashi ya san inda dare ya masa."

Aje wayar tayi ta zaburo tace "To idan fa na k'i? Ai dai kasan kud'in a account d'ina aka saka ko? Kuma sai ni ce ke da damar cirewa? Dan haka ka bini a hankali har lokacin da naga dama sannan na fito dasu mu raba."

Shima tasowa yayi yace "Wallahi baki isa ba, ni zaki d'auka d'an iska, wato kinga kud'i kenan shine zaki nemi ki raina min hankali? To baki isa ba wallahi, kinsan ko k'arfi ne zansa na karb'a."

Da k'arfi tace "K'arfi? K'arfi fa kace? Wai kai ka ma san wahalar da nasha kafin a samu kud'in, kana nan zaune nasa kaina a had'ari wanda da sun gano ni me kake tunanin zai faru da ni? Haka na kwashe kwanaki a gidan ina tunanin abunyi har na cimma nasara, kasan ta yanda akayi na shawo kansa ne? Da k'yar ya kwanta dani shima bayan na ci maruka daga gareshi, haka ya shigeni babu imani ya sussuke ni, duk kai kana nan zaune kuma shine yanzu zaka wani bud'e min ido, to bari kaji da kyau tunda abun na ka ya zama iskanci, wallahi kud'in nan ko sisin kwabo ba zan baka a ciki ba, sai dai na maka alk'awarin zan karb'o maka ko million biyar ne ko goma a wurinshi, dan na fahimci baisan zafin neman kud'i ba."

Sai lokacin maganganun Meena suka fara dawo masa da tace ko ita Ma'arufa ta samu yanda zatayi ta cinye kud'in ita kad'ai to zatayi ne, dan haka shi ya mik'e ya karb'i kud'in inba haka ba zai zama d'an kallo, wani iska ya furzar daga bakinshi ya jinjina kai yace "Shikenan, ki samo min million goman, ke saiki rik'e waccen d'in."

A wulak'ance ta kalleshi tace "Ai na d'auka zakayi gardama ne?"

Murmushin mugunta yayi yace "Gardama tame kuma? Abinda ba kai ka tara ba."

Mik'ewa yayi zai fita yace "Yaushe kenan zan saka rai?"

A yamutse tace "Zuwa gobe zan masa magana, yanzun ma dan dare yayi ne."

Baice komai ba ya fita ya barta, daga nan kuma hotel d'in da Meena take ya zarce, tsaf ya fad'a mata komai, tab'e baki tayi tace "Ai dama na fad'a maka, yanzu kawai lambar account d'in nata zaka samo mana, ni inada mutanen arzik'i sosai a garin nan, zamu san yanda za'ayi a maka transfert d'in kud'in zuwa naka account d'in."

Kallonta yayi yace "Amma yaya zamuyi haka alhalin tana raye?"

Zaune tayi kan cinyarshi ta sagala hannunta ta bayan wuyanshi tace "Kalamanka suna so su nuna kamar ka d'au saiti? Ni kuma in hakane ina da maganin matsalarka."

Juyawa tayi bayanta ta d'auko jakarta ta bud'a ta d'auko wani k'wayar magani mai kamar ampicillin ta bashi tace "Kawai ya gyauraya a abun shan ta."

Karb'a yayi ba tare da tunanin komai ba kafin ya had'e bakinshi da na ta, suna lulawa nima na lulo nayi waje .

Abbas da kanshi ya samu magabatan Abdul ya sanar dasu za'a d'aura auren gobe bisa wani dalili mai k'arfi, su kuma cikin farin ciki suka amsa mishi da ba komai ai Abdul d'an shi ne, shi kanshi Abdul d'in farin ciki yayi saboda zai mallaki abar son shi, yayin da zazzab'i kuma ya rufe Raihan baiwar Allah, har likita ya zo ya dubata ya bata magani, tana kwance d'akin Sameera tana bacci, ita kuma Sameera shiryawa tayi cikin kayan baccinta taje bed d'in shi, tana shirin yin kwance yace "Idan ba damuwa ki koma d'akin ki mana?"

Da mamaki ta kalleshi tace "D'aki na kuma? Kana gari me zaisa mu raba shinfid'a?"

A k'ufule yace "Haka nake buk'ata, ina buk'atar kad'aici."

Matsawa tayi kan kujerar da yake zaune ta sunkuya ta kama hannunshi cikin magiya tace "Sir, dan Allah ka fad'a min meke damunka mana? Ni fa matarka ce, Sameera, ko ka manta ne? Idan ni nayi maka laifi dan Allah ka fad'a min saina baka hak'uri, idan kuma kana hushi dani ne kan maganar haihuwar da kake so, na amince ka bar hushin dani, muje sai ka min cikin mana na shirya d'auka, amma bana son hushinka wallahi."

Rintse ido yayi yana jin kamar ya k'ona kanshi yace "Bana jin zan sake haihuwa da ke."

Dam! Taji gabanta ya fad'i yayin da ta kafeshi da ido da alamar tambaya, da tsantsar mamaki tace "Baka son sake haihuwa da ni? Akan me? Me nayi maka da zafi haka? Abban mama na yaran da muka haifa fa? Yanzu har girman zunubin dana aikata ya kai ka fad'a min wai ba zaka sake haihuwa da ni ba?"

Cike da k'osawa yace "Dan Allah ki fitar min daga d'aki."

Had'e kukanta tayi tace "To zamu iya yin magana akan matsalar 'yarmu?"

A tak'aice yace "Ba zamu iya ba."

Kallon fuskarshi tayi tace " 'Yar mu ce fa? Girman laifin data aikata yasa har ka daki yarinyar da ko tsawa mai k'arfi baka tab'a mata ba, sannan ka ce zaka aurar da ita gobe, kana ganin hakan ya dace?"

A gajiye ya kalleta yace"Ya dace Meerah, please ki bar ni nasha iska mana."

Mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta kalleshi tace "Sorry."

Juyawa tayi inda ya rintse ido matuk'ar tausayinta ne yaji ya mamaye shi, saida yaji ta rufe k'ofar d'akin ya juya ya kalli k'ofar wasu hawaye suka taho mishi yace "Sameera ba zan yarda na sake had'a jikina da na ki ba, nasan zan cutar dake a hakan, amma k'azamin jikina ba zai sake tab'a tsarkaken jikinki ba, Sam ki yafe min, ba zan iya fad'a miki komai ba, domin kuwa nasan a ranar ko baki kashe ni ba zaki cutar da kanki, ba zan bari ki kashe ni ba dan bana son ki shiga wuta dalilin banza iri na, ba kuma zan yarda ki cutar da kanki ba."

Tana shiga d'aki ta samu wayarta na ta kururuwa sarki Imran ne, d'auka tayi ko gaisawa basuyi ba ya fad'a mata abinda ke faruwa a masarauta.

*Basraba*

Bayan tafiyar Sameera sai kuwa waziri ya taso uwar d'aki gaba akan dole fa ayi auren nan da gaggawa, ya gama tsorata da recoding d'in da yayi tare da mata barazanar zai ce ita ta saka shi ya kashe takawa, nan fa jikinta ya d'auki rawa ta fara neman mafita, amma a k'arshe dai mafitar bata wuce tayi abinda yake so ba, nan ita ma ta tasa Imran gaba sai anyi aure nan kawai nan da kwana biyu, wanda yanzu ya kasance gobe za'a d'aura, Imran ya kira Abban Sameera amma yana hushi akan abinda ya faru yasa ya k'i d'aga kiranshi , dan haka ya kira Sameera dan ta fad'awa Abba akan ya zo ya dakatar da auren nan, shi bai ce ba zaiyi ba amma ba zaiyi aure ba kwana shida da rasuwar mahaifinshi, amma Sameera sai tace mishi kawai ya amince a d'aura dan a zauna lafiya, nan sukayi sallama kowa yaji da abinda ke damunshi.

*WASHE GARI*

Lafiya lau aka d'aura auren sarki Imran Musayyib Ali da matarshi ta farko *Safiyya Ahmad* da kuma mata ta biyu *Jawahir Ya'u* dukansu akan sadaki dubu hamsin hamsin, hankalin waziri ya kwanta kam dan yanzu ne burinshi zai cika, a wautar uwar d'aki ita ma tana ganin hankalinta ya kwanta tunda asirinta ya rufu yanzu, yayin da gimbiya Ameera tayi kuka sosai jin auren mijinta kamar a mafarki, tsawon lokaci ya d'auka yana rarrashinta da bata hak'uri da fad'a mata duk abinda ya faru, yayin da ake toya masa anan acan Abuja kuma ana toya wata masar ne.

*Abuja*

Kamar yanda Fadila ta samu labarin d'aurin auren Raihan a tsakiyar dare haka ita ma ta dokowa Abdul kira a dugun-dugun safiya, bayan ya d'auka ne ta fashe da kuka tana fad'a masa ita fa son shi take ya taimaka mata, cikin ruwan sanyi yake lallab'a ta yana bata hak'uri saboda akwai mutumci tsakaninsu, amma sai baud'ewa take tana fetsarewa, a k'arshe ma zuciya ce ta deb'eta tace "Yanzu kai ka d'auka zasu baka yarsu dan suna sonka ne? To ba gaskiya bane, soyayyar da suke nuna maka ta bogi ce yayin da a ransu babu hakan ko kad'an, sun d'auke ka kamar bawansu ne wanda suka siya da kud'i, Raihan ita ce rayuwarsu, hakan yasa suka tanadar mata kai dan rayuwar gidan aurenta ta mata dad'i kamar yanda suke so, a bayyane yake ai, inhar ka aureta ba zaka yarda ka muzguna mata ba ko ka mata ko da kallon banza, to wannan ne dalilinsu na son had'a ta da kai, amma a bad'ini suna maka kallon wanda ko mai aikin gidan yarsu baka kai."

Murmushi yayi mata yace "Idonki ne suka rufe har kike fad'in haka? To muje ma a hakanne, Fadila na amince zan auri Raihan, ai dama hallacin da iyayenta suka min bai kamata ace na harari ko da k'eyar Raihan ba bare gabanta."
Chapter 75 · 0% Book details