Sashe 57
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sam baiyi dariya ba saboda baya so ta samu damar sauke mishi tijara, amma yasan yau kam mai rabasu sai Allah, ko bata zage shi ba saita dake shi, har zuciyarshi yasan tana buk'atar taimako, amma danya d'an fara bata tsoro idan yace tayi sau d'aya ba sai ya maimaita ba yasa ya k'are mata kallo ya fita a d'akin, tana ganin haka ta tattara k'arfinta ta mik'e zaune da k'yar, kallon kanta tayi ta madubin dake gefenta tace "Ni zai yi wa haka? Lallai ma mutumin nan."
Misalin *09:00* na dare suna zaune dukansu kan dinning table, sanye take da doguwar rigar material mai kyau da tsada bleue light da d'an kwalinta, babu komai a fuskarta data shafa idan ka cire mai da lips a bakinta, tana hango Ammie zaune ta sake sangarta tafiyarta cikin shagwab'a ta k'arasa ta rumgumeta ta baya ta fashe da kukan sangarta, da sauri Ammie ta fara tambayarta "Auta ta lafiya? Waya tab'a min ke?"
Abbas da tunda ta fito yake kallonta, maganar gaskiya kallo d'aya ya mata ya ga har tayi wata ramar k'arfi da yaji, hatta tafiyarta ma ta kasa daidaituwa da kyau duk jikinta ya saki, wani haushi ne ya tokare masa mak'oshi yaji kamar ya mareta, shin bata lura da bak'uwar dake wurin bane? Idan ma bata ganta ba ai tasan Abdul na wurin yaron dake shirin zama sirikinta, kasa amsawa tayi yayin da yaran duk suka k'ura mata ido har da Ma'arufa dake mamakin karuwanci Sameera, Ammie ce ta gyara zamanta kan kujerar da nufin zaunar da Sameera kan k'afafun ta, amma suna had'a ido da Abba taga kallon da yake ma Sameera tasan duk yanda za ayi zai iya d'aukar wuk'a yace zai gagara mata, dan haka ta mik'e tsaye tace "Auta zo muje d'aki na ki fad'a min meya sameki, naga duk kin canza kamar ba ke ba."
Hannunta Ammie ta kama zasu fice sai idonta ya sauka kan bak'uwar su, yanzun ma kamar ganin ta da ita na farko sai taji gabanta ya fad'i tare da jin haushin yarinyar, wani tunani ne ya d'arsu a zuciyarta take a wurin, shin idan fa k'addara tasa yarinyar ta aurar mata miji? Kanta ta bawa amsa ta hanyar fad'in "Ai kuwa babu abinda zai hanaki k'ona gidan nan kamar yanda kike fad'a masa."
Da haka suka tafi part d'in su Ammie suka zauna falo, cikin rarrashi Ammie tace "Auta fad'a min meya miki?"
Turo baki tayi gaba ta kwantar da kanta saman k'afafun Ammie tayi shiru, cire mata d'an kwalin tayi ta fara shafar kanta data ji shi a jik'e, take ta fahimci komai, dama ba kunya ce tsakaninsu ba dan haka Ammie tace "Auta halan hukuntaki yayi saboda baki taho tare da mu ba?"
D'agowa tayi ido taf da hawaye kamar zata fashe da kuka tace "Ammie hukuncin ma mai tsanani, wallahi bai tab'a min irin shi ba sai yau, bansan a ina ya koyi wannan muguntar ba, ni gaskiya Ammie daga yanzu d'akin ki zan kwana har saiya bani hak'uri."
Kwantar da kanta tayi tana daddab'ata b'angare d'aya tana toshe baki tana dariya, labari ta fara bawa Ammie yanda sukayi da matar waziri, dariya kawai Ammie take tana godewa Allah da abun ya tsaya iya mari kawai, suna haka sai ga Abbas ya shigo tak'im tak'im kamar wanda aka bawa sarauta, Ammie na ganinshi ta had'e rai tace "Kai kuma malam lafiya? Meya kawoka wajenta?"
Saida ya harari Sameera yace " Ni ba wurinta na zo ba."
Zaune yayi kan kujerar dake fuskantarsu ya kalli Sameera dake wurga masa harara yace "Ke tashi ki bamu wuri zamuyi magana da uwa ta."
Sake mak'alk'ale Ammie tayi tace "Ba zan je ko ina ba, ka fad'i duk abinda zaka fad'a ina gaban uwata."
Murtuke fuska ya sake yi, matsalarshi da ita daman kai tsaye zai bata umarni tace ita ba haka ba, kafeta yayi da ido kawai hakan yasa Ammie kallonta tace "Yarinyata, shiga d'aki na ki kwanta abinki gani nan zuwa yanzu, idan kin shiga ki duba a drower akwai kayan dad'i ki d'auka kinji."
Mik'ewa tayi a kasalance ta wuce ko d'an kwalin nata bata d'auka ba, da kallo ya bita kafin ya kalli Ammie wacce tace "To ina jinka, lafiya da zaka wani katsewa yata jin dad'in ta?"
Mik'ewa yayi yace "Ba komai, dama zan d'an fita."
Kafin tayi magana taga ya sa kai ya nufi d'akin nata kuma, girgiza kai tayi tace "Kaji da munafurcinka, da nace wurinta ka zo ai cewa kayi a'a."
Sameera na sunkuye zata d'auki chocolat taji saukar mari a mazaunanta, da sauri ta d'ago ta dafe kayanta tana fad'in "Washhhh."
Tana ganin yanayin shi sai kuma tayi shiru, cikin muryar shagwab'a tace "Dan Allah Abban Ameer ka daina wahalar dani haka, ya kamata fa ace yanzu na wuce ajin shan wahalarka, wacce na sha ma a baya lokacin da nake maka bauta ta isa haka."
Yana kallon k'aramin bakin har saida ta dasa aya sai kawai ya had'ata da bango ya had'e bakinsu, wani bala'in kiss ne yake mata mai matuk'ar zafi kamar zai cire mata labb'a, tuni idonta suka kawo ruwa ta rufe ido wasu hawaye masu zafi sirara suka shiga fitowa suna bin kumcinta, a gefen fuskarshi ne ya ji alamar lema hakan yasa ya tsaya yana kallonta, cikin wata irin murya ba tare daya matsa daga cikin jikinta ba tace "Sam ki dinga jin magana ta mana, bana so muna irin haka dake dan mun girma yanzu, ki ce zaki dinga ji duk abinda na fad'a miki, ni kuma ba zan sake bari ki zubar da hawaye ta dalili na ba."
Bud'a ido tayi cikin shashek'a tace "Zan dinga jin maganarka indai kayi alk'awarin ba zaka sake min irin muguntar nan ba ta yau?"
Yanda tayi maganar saiya k'ayatarda shi, bud'e mata hannayenshi yayi alamar ta taho, sake fashewa tayi da kukan da bata san dalilinshi ba ta fad'a cikin lafiyayyen k'irjin shi, matseta yayi sosai yace "Na miki alk'awarin ba zan sake ba indai nima zaki dinga jin duk abinda zan fad'a miki."
Cikin shashek'ar kuka tace "I promise u, please forgive me."
Cikin shafar tattausan bayanta yace "I forgive u my Meerata, i really love u."
Sake k'amk'ame shi tayi a haka suka fito falon tare, Ammie na ganinsu rumgume da juna sai ita taji kunya, dama kuma ba sabon abu bane a wurinta, kullum suka samu matsala saita tsaya bayan Sameera ko tasan ita ce bata da gaskiya, ba jimawa kuma sai ka gansu a had'e a jone.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Abbakar ne ya samu Saleem a d'akin shi yana waya da Fadila kamar sun jima da fahimtar junansu, yana ganin shigowarshi ya datse kiran yana fad'in "Yah Abbakar, kaine yanzu?"
A hankali ya k'araso cikin jan k'afar shi ya tsaya kusa da shi yana kallonshi yace "Saleem baka kwanta ba har yanzu?"
Murmushi yayi yace "Ban kwanta ba yah, amma kai ma ya akayi baka kwanta ba har yanzu?"
Shima murmushi yayi yace "Ina ta tunaninka ne Saleem."
Da mamaki yace "Tunani na kuma yah? Akan me? Ko dai tunanin Zeenat?"
Girgiza kai yayi yace "Tunaninka nake Saleem, tsoro kake bani, ina gudun kar kaje kayi abinda zai saka mu cikin matsala, shiyasa na gagara bacci har na zo na sameka, kwanan nan kana wayon fita kuma baka zama sosai a shago, sannan kashe kud'in ka ya k'aruda kaso goma, me kake yi da kud'i Saleem? Ina kake zuwa idan ka bar shago?"
Cike da nuna alamun rashin gaskiya ya fara shafar kai yana fad'in "Yah ba komai fa, ka yarda dani mana, ni fa yanzu ba k'aramin yaro bane, nasan abindake daidai da wanda ba daidai ba, so calm down bros."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Saleem kai ba yaro bane, amma dai kasan ina gaba da kai ko? Please Saleem ka fad'a min idan akwai wani abinda ke damunka, na maka alk'awari insha Allah zan taimaka wajen solven matsalarka, amma bana so kaje kayi abinda ya sab'awa shari'a da ma al'ada da mutuntaka ta d'an adam."
Shiru Saleem yayi baice komai ba, jin ba zaiyi magana ba yasa Abbakar cewa "Saleem idan kana da matsalar sha'awa ne ka fad'a min sai mu maka aure, amma karka jefa kanka a harkar neman mata, mummunan zane ne da zaka yiwa kanka na har abada."
Cike da k'aguwa ya kalleshi yace "Yah ba komai fa, dan Allah kaje ka kwanta, ba zan tab'a neman mata ba kai ka sani."
Cikin sanyin jiki ya juya ya bar d'akin inda Saleem yace "Har na fara jin k'amshin yanda zan kuntatawa rayuwarsu zaka zo min da wata magana, yanzu kana komawa d'akin ka hoton matsiyaciyar yarinyar nan zaka d'auka ka fara kallo har gari ya waye maka."
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Gari na wayewa yau yan matan suka shirya driver ya kaisu school dubo result d'in, suna zuwa kuma basu sha wahala ba suka samu sakamokonsu mai kyau suka juyo cike da murna, kai tsaye gida suka sake dawowa, suna zuwa da farin ciki kowace ta nuna nata, gaskiya ne Raihan tafi k'ok'ari sai Fadila sai kuma Ma'awa, hakan yasa Bashir da Naseer suka dinga yabawa Raihan har kowane yayi alk'awarin kawo mata kyauta, Abbas kuma su Fadila ya dinga yabawa wanda yasa Fadila jin kawai yana yaba musu ne saboda iyayensu basu yaba musu ba, shima cewa yayi zai bawa kowace kyauta, suna tsaka da raharsu Harira ta fito cikin kwalliyarta kamar yanda ta saba yanzu ta kawowa Ameer takalminshi, saida ta durk'usa har k'asa ta saka mishi takalmin kafin ta mik'e ta juya tana jijjiga, duk da Sameera ta ga hakan amma saita barshi a matsayin zawarci tana neman mijin aure ne, kuma tasan babu abinda mijinta zaiyi da Harira, dan haka bata damu ba, nan Abbas yace yaran su shirya sai su fara tafiya basraba, nan da sati biyu idan aka gama bikin Husna sai a tafi tare da su kan amarya daga nan zasu iya yin hutun su a can, sunyi farin ciki sosai saboda zasu fita wata k'asar da ba tasu ba.