← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 198

Sashe 159

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fad'a ya wuce ciki shi ma ya barta, bin bayansu tayi suka shiga ciki, anata shagali ba kama hannun yaro, kowa na farin ciki da dariya amma banda shi, kujera ya samu ya zauna ya buga tagumi yana kallonta, rawa suke tare da k'awayen inda angayen ke musu lik'i suna jin dad'in kallonsu, jikinta ya bata yana kallonta shiyasa ma bata yarda sun had'a ido ba, shi kuma yana mamakin yanda take son zama, ke da za ayi aurenki amma gida suka bari ta fito, wannan wace irin rayuwa ce akayi a gidan nan? Tab'e baki yayi alamar ba ruwanshi matsalarsu ce.

Mutum mugun icce (ina yawan fad'in haka), duk abin alkairi sai wani ya kawo cikas, daren yau dai ko da Hamna ta dawo gida ta riski tashin hankalin da bata tab'a tsammaninshi ba, jin kunya tozarci k'ask'anci duka taji a wannan rana, sati uku ya rage aurenta amma yau an turo manya daga gidansu Habib wai an fasa, abun takaici shine wai mahaifinshi yace "...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_60_

Wai babanshi yace "Sai dai in bayan ranshi zai aureta, amma da ranshi dai har abada kam."

Habib fa abun bai masa dad'i ba, amma danginshi da matarshi su abun ya musu dad'i, a ranar haka aka kwana ana jajanta wannan magana kowa na fad'in albarkacin bakinshi, kowa yana son gano bakin zaren dan yaji dad'in fad'a, Amna kwana tayi tana kukan fasa auren yar uwarta, amma ita Hamna ko a jikinta dan sai taji wani sanyi ma.

*Da safe* bayan ya dawo daga d'aurin aure ya shigo falon dan gaishe da Ummy, Soueiba Zeinabu da Hassana ya samu suna hirar abinda ya faru, abun mamakin kuma kowace hasashenta take fad'i wanda ya janyo fasuwar auren nan, shigowa kawai yayi bai kulasu ba, saida ya gaisheta ya fito ya gaishe su ya fita, zai nufi b'angarenshi ya kira wayar Amar, yana d'auka yace mishi "Har yanzu kana cikin grp d'in ahalin gaga?"

"Eh." Amar ya fad'a a tak'aice, d'orawa yayi da "Ka fad'a musu akwai taro gobe a gidan margayi Alhaji Suley, idan mutum ba zai samu damar zuwa ba ya turo wanda zai iya wakiltarshi."

Da sauri Amar yace "Taro kuma? Na me?"

"Kayi abinda nace." Yana gama fad'a ya kashe wayar, kamar yanda ya fad'a haka Amar yayi, ya kira taron da babbar murya inda kowa ya amsa da zai zo, kowa tunaninshi da hasashenshi bai tab'a hasaso mishi abinda Ammar d'in ke shirin yi ba.

*K'wansu da k'wark'watarsu* haka suka taru amma banda yara, d'akin ya kaure da hira kowa na jiran yaji abinda zai masa dad'i, yasan kowa zai zo shiyasa ma yake kwance yana shan baccinshi hankali kwance, cikin abokan wasansu ne wata ta kalli Amna tace "Wai ke ina wannan d'an rainin hankalin ne? Ko kuma gadinshi zamuyi ne?"

Cikin murmushi Amna tace "To miye a ciki ma idan kunyi gadin na shi? Ai ya isa har ya batse."

Cikin uwaye ne wata tace "Ki dai taimaka ki nemo mana shi tunda ance yana ciki bai fita ba, muna da abunyi nan da kike ganinmu."

Mik'ewa tayi tace "To bari naga idan zan iya." Fita tayi tana tunanin kalar mutanen da zata samu sun hau kanshi yau idan ta tashe shi, sun dai kwanta lafiya lau, amma yanzu zata iya tashinshi ya burma mata ashar yace waya aiketa? Wani iska ta furzar data tuna ai gata zai mata idan ita kad'ai ma ya kunyatar d'in, ko da ta shiga har d'akin na shi ta wuce, yanda ta barshi haka ta same shi, a hankali ta k'arasa ta kwanta bayanshi tana shafa bayanshi, ta jima haka kafin tasa harshenta cikin kunnenta tana karkad'ashi, a hankali ya fara motsa kanshi tare da mimmik'e k'afafunshi, juyowa yayi idonshi rufe ya k'ara matseta jikinshi, ganin abinda take mishi yana ratsa shi sosai yasa ta cire harshenta ta kalli fuskarshi tana murmushi tace "Barka da safiya."

Kallonta yayi ya k'ara matsota kusa dashi ya fara sinsinar wuyanta yana shafa bayanta har ya zura hannunshi cikin rigarta, a hankali taji ya fara b'alle bras yana son kaiwa wani wurin, rik'e hannunshi tayi ta kalleshi tace "Duniyata bak'inka fa sun iso tun tuni kai kad'ai suke jira."

Lumshe ido yayi ya jawo kanta ya rad'a mata a kunne cewa "Je envie de toi chérie."

Kallonshi tayi tana dariya tace "Daga tashinka daga bacci?"

Turo baki yayi yace "Ce toi qui ma attaqué."

Murmushi tayi tace "Ok, yanzu ka tashi ka shirya sai mu tafi."

Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi zaune, sauka yayi daga kan gadon ya d'auki doguwar rigarshi fara tas ta saka, turare ya fesa kafin yaja hannunta suka fita, cikin takon isa da mulki da izza dake nuna wannan yaron na Hajia ne ya shigo😂, murmushi yayi ganin cikin k'ank'anin lokaci wai suka taru haka, bai gaishe da kowa ba ya tsallaka ya zauna kujerar da Hajia ke zama kasancewar bata fito ba saboda hayaniyar mutanen, kamar tasan da zuwanshi kam sai gata ta fito, kanshi tayi gadan gadan dan son zama kan kujerarta, gyara zama yayi ya shige cikin kujerar sosai ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana shafar gemunshi da hannu, ko da Hajia taga haka kawai tayi shataletale ta zauna kusa da su Hassana da Husseina, dan tasan in tace ya tashi zai fad'i wani abu ne da zaisa a mata dariya, kowa kallonshi yake cikin rashin mutumci da jin haushi, saida ya gama kallon kowa ya d'ago daga jinginar da yayi yana kallon kowa.

Cikin taushin murya da girmamawa yace "Barkanku da safiya iyayena kakanni na da yayuna da k'annaina na kaina."

Wasu tab'e baki sukayi suna tunanin abinda ya tarasu ya fad'a musu kenan ko me? D'orawa yayi da "A yanda nasan danginmu da gulma da jin dad'in yad'a labari nasan izuwa yanzu kowa yasan abinda ya faru jiya na fasa auren yarinyar nan, to akan shi ne dama zamuyi magana."

Kallon kallo suka wa junansu tare da k'ananan maganganu na abinda ya fad'a wai gulma, ba tare da damuwa ya d'ora da "Naji da kunnuwa na na gani da idona a cikin gidan nan masu cewa wai an fasa aurenta saboda hanyar data d'aukarwa kanta marar b'illewa, da jimawa a cikin gari naji da kunnuwana masu zaginta da aibatata, kuma maganar ta samu matashiya ne daga cikin gidan nan, da ku ahalinta ake zaginta a cikin gari saboda shigarta, mu'amularta da k'awayenta, amma abun tambayar anan su waye silar lalacewarta? Su waye sanadiyar rugujewar aurenta?"

Tsit kowa yayi sai zuba masa ido da akayi, Hamna kuma dake zaune kan kujera tare da Amna da Umaimah ne ta kalleshi tace "Malam, duk yawan mutanen wurin nan sai akai na ne kawai zakayi maudi'inka."

Ko kallonta baiyi ba kamar baisan da hallitarta ba ya ci gaba da cewa "Kune silar komai wallahi."

Alhaji *Mani* ne yace "Ya zaka ce mune sila kuma? Yarinyar da take ganin ta waye tana da ilimi da kud'i."

Cikin jin haushi Hamna ta mik'e ta kalleshi tace "Na zauna ne saboda yan uwana dana gani amma ba dan jin shirmenka ba."

Juyawa tayi zata fita ya kalli kowa na wuri yana murmushi yace "Kun gani, babu wanda yayi yunk'urin yi mata magana kan abinda tayi yanzun, kai tsaye ta nuna ni mashirmanci ne kuma zaman nan baida anfani, bata duba kasancewata babba a gareta ba, hakan bai isa a gareku da zai zama dalilin da zaku tsawatar mata ba."

Mik'ewa yayi tsaye yace "To ku saurara, dalilin had'uwar nan ba wai saboda ita bane, wani babban kuskuren mu ne na ke so na tunatar daku shi dan ku gyara, idan kuma baku gyara ba ni dai Allah ya gani kuma ya sani na tunatar daku, tunda a cikin nan akwai wad'anda zan iya musu fad'a, akwai wanda na isa na d'auki bulala na zane su, haka kuma akwai wad'anda ko kallon da bai dace ba zan iya musu ba."

Cikin misaltawa da hannu yace "Naji zafi sosai har zuciyata sanda nake tsintar k'ananan maganganu a cikin gari cewa Hamna wai tana abinda take so, daga cikin gidan nan ban tab'a gani ko jin ance anga wanda ya tsawatar mata ba, ban tab'a ganin wanda yace mata ta canza shiga ko kayan jikinta ba, a cikin gidan nan ma babu wanda ya damu da ita bare kuma daga waje, kuma abinda na lura ya jawo hakan ba zai wuce wariyar launin fatar da ake nunawa ba, wai yau lalacewar ahalin nan ya kai matsayin da kowa nashi kawai ya sani, babu wanda zai iya kallon d'an dan uwanshi ya mishi magana ko fad'a kan abinda yayi bai dace ba, kowa yafi son ya tsaya daga nesa yana nuna d'an uwanshi da baki, wannan wace irin rayuwa ce?"

Husseina ya kalla da Hassana da Hajia yace "Kune manyan da suka rage mana a ahalin nan, kuna da dama da iko a hannunku yanda zaku iya tank'wasa duk wani k'aramin tsagera, saboda kuwa ku kuka haifi iyayenmu, amma me kukeyi dan gyara iyalin nan?"

Matse bakinshi yayi yace "Kowa nashi yaja ya killaceshi a jikinshi yake bashi kulawa, d'aya ba zata iya iya tattaunawa akan matsalar data shafi d'aya ba, ko da na tashi a gidan nan cikin sauk'i na fahimci wacece kakata wacce ta haifi mahaifina, wanda ba haka ya kamata abun ya zama ba, yanda gidan nan ke da girma da mutane ya ci ace yaro zai sha matuk'ar wahala kafin ya gane mahaifiyarshi ma bare kuma kaka."
Chapter 159 · 0% Book details