← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 198

Sashe 155

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarshi ya fiddo ya d'an daddana kafin ya nuna masa yace "Idan ba matata bace to ta uban wacece?"

K'uri mutumin yayi yana kallon hoton Amna da Ammar suna tare da Ameer Ameera, amma da yake a zaune take kuma ga kama sosai da kwalliya a fuskarta sai kawai ya d'auka tabbas Hamna ce, kallonta yayi yace "Hamna, taya..."

Ammar ne ya katseshi da fizge wayarshi yace "Malam saida izini na zakayi magana da ita."

Kallon Ammar yayi yace "Kayi hak'uri bawan Allah, ka tabbatar matarka ce ko kuma dai tsohuwar matarka?"

Wani kallo ya mishi yace "A ganinka haukana zai iya sa na mallaki wannan kayan kuma na rabu da ita? Kai ba kayan bane ka biyo?"

Matse baki kawai yayi yace "In kuwa har matarka ce yanzu to akwai buk'atar ka sake saka ido akanta, kayi hak'uri."

Kallonta yayi yace "To kai baka ganta bane? Mahaukaciya ce fa ta sakawa a gidan gaba, yanzu haka magani take d'auka."

Girgiza kai kawai mutumin yayi ya wuce abinshi, kallonshi tayi sai kawai ta fashe da kuka ta juyawa da sauri zata koma ciki, da k'arfi yasa hannu ya jawo gashinta yayo baya da ita, sam bata tsammanin haka ba sai kawai ta fad'o a jikinshi gaba d'aya, cit wurin yayi kafin ta fara k'ok'arin tashi da k'afarta, sakinta yayi ta mik'e daga jikinshi inda suka sake kallon juna, cikin masifa da neman sababi tace "Wallahi Ammar ka fita a hanyata, ya zaka korar min saurayi na wanda nake tunanin shi zan aura? Kana da matsala dani ne?"

Sunkuyar da kansa yayi ya d'ago idonshi kamar wani zaki yana kallonta, tambaya yake wa kansa me yasa bata nesanta kanta da wasu ne? Ya jima yana kallonta haka ita ma tana kallonshi kafin ya gyara tsayuwa yace "...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_58_

"Hamna ame kika d'aukeni?"

Sauda ta d'aga masa gira sama ta kalleshi tsaf sannan tace "A babban mah...mana."

Wani kallo ya mata jin rainin hankalin data masa, mahaukaci take so tace amma shine bata k'arasa ba, kenan mahaukaci take kallonshi? Ai kuwa zai nuna mata a aikace, matsawa yayi kusanta zaiyi magana sai ta k'ara ja baya tace "Malam tsaya daga can mana."

Jiniyar motocin da suka ji ne yasa su juyawa duka suka kalli k'ofar, mahaifinta ne ya dawo cikin rakiyar masu bashi tsaro kamar kullum, suna kallo akayi pakin motocin aka bud'e mishi ya fito, sauran motocin duk wajen ajiyesu aka nufa dasu inda wasu jami'ai biyu ke biye a bayanshi, kallonshi tayi ta harareshi sama da k'asa ta juya baki tare da jan dogon tsaki tace "Malam ka shirya saina sa ka bawa saurayi na hak'uri, sannan da kanka zaka bashi aure na a matsayinka na babban yayana."

Shigewa tayi a lokacin kuma mahaifinta ya k'araso, saida ya d'an rumguma Ammar a jikinshi suka gaisa, tare suka shiga babban falon, suna shiga Aissata ta tarbe shi sai ma'aikata da suke ci gaba da gyara wajen cin abinci, Ammar kuma kallon kawun nashi yayi yace "Ina zuwa tonton."

Bayan Hamna ya bi data haye sama d'akinta, ko zaune ba tayi ba taga ya fad'o mata d'aki yana cire mata cazar waya a jikin bango data saka, da mamaki tace "Malam lafiya? Me ya shigo da kai d'akina?"

Rintse ido yayi ya sake bud'esu akan ta tarau, da k'arfi ya d'aga cazar ya zuba mata a baya, wata uwar ihu ta sake tare da juyawa ta fara taka rawar da babu shiri tana matse k'afafunta da taji fitsari na barazanar danno mata kai, kuka take da iya k'arfinta ta rasa me ke mata dad'i, bata gama jin azabar ba taji ya shak'o wuyan gashinta a daidai infa ta d'aureshi da ribom ya jawota, hannu tasa ta rik'e hannun nashi d'aya kuma ta rik'e rigarshi daidai mab'allan rigarshi tana sakin wani kukan tana fad'in "Kayi hak'uri yah Ammar, kayi hak'uri dan Allah ba zan sake ba, karka dake ni dan Allah na tuba."

Tunda suka ji ihunta suka d'aga kai sama suna kallo, suna ganinsu ya sauko da ita k'asa har gabansu ya gurfanar da ita, tonton ya kalla fuskarshi babu alamar ya tab'a dariya a rayuuwarshi yace "Ku zama shaidata, wallahi saina karya yarinyar nan idan ta sake tara mana yan iska a gida, sannan..."

Ya fad'a yana sake kallonta yace "Ki tattara kayanki gobe zaki koma gida, nan dan kinga babu mai saka miki ido yasa kike abinda kika ga dama, to zaki koma can gaban Hajia da Ummy."

Cazar hannunshi ya jefa mata a jiki ya sunkuya ya nuna ta kamar zai tsone mata ido yace "Ki tuna da cewa indai akwai rai da rabo, sannan akwai lokaci to wata rana zanyi iko akan ki."

Kamar zai taka ta haka ya wuce ko kallonsu tonton bai sake yi ba, da kallo ya bishi baki sake, shi fa ba mamakin abinda yayi bane yake bashi, kalamanshi na k'arshe da kuma yanda abun ya b'ata mishi rai, to duk me yayi zafi haka? Dawo da kallonshi yayi kanta yace "Koma ciki, sannan ki had'a kayanki gobe zaki koma, ba zan iya jarabar yaron nan ba."

Cikin kuka ta mik'e tace "Wallahi Abba babu inda zanje, haka kawai sai kace wani uba na."

Nunata yayi da yatsa yace "Ke ki bar bala'i yayi kwana, ina ce yanzu a gaban uban naki ya miki wannan k'wak'waran kashedin? To dan haka ki d'auka ma yafi ubanki."

Tumurmusa k'afafu ta shiga yi tana fad'in "Allah Abba ba zan koma ba, ni nafi son zama anan, kawai dan ya fad'a shikena ba zaka ce masa komai ba."

Matsawa yayi kusanta ya dafa kafad'arta cikin taushin murya yace "Yar albarka, kiyi hak'uri ki tafi kinji, shi da gobe ne zasu tafiyarsu, daya tafi saiki dawo idan haka kike so, pour les moment dai ki tafi kinji ko."

Jinjina kai tayi tace "Ok Abba, amma ka fad'a masa ya daina takura min ya fita a harkata, inba haka ba zan masa rashin mutumci."

Jinjina kai sha yayi ya shafa kanta yana kallo harta haye sama, kallon Aissata yayi wacce ita hausar ma bata gama ji da kyau ba yayi murmushi, ciki ya wuce da jinjina al'amarin yaron nashi mai kama da d'an uwanshi colonel a zafi.

Saida ta gama shiri tsaf yace ai tafiyarsu ba yau ba saiya koma gida, bata nuna bata ji dad'i ba saboda gudun tashin k'wank'wamanshi dan su rabu lafiya, da addu'a ta rakashi sam bata san tare da wa zai tafi ba, har d'akinta yaje ya tisota gaba suka fito, a motarshi daya bari suka d'auki hanya inda Hamna take addua'r sauka lafiya, gudu yake na ganganci da kauce k'a'ida, ita har ga Allah tasan a d'ane yake jaraba yake neman, a yanda yake tasan ko jami'an kan hanya yau saita Allah su rabu lafiya, ita kuma ba zata so ya ja mata kwana a magark'ama ba, a hankali ta kalleshi cikin rawar murya tace "Yah Ammar ka tafi a hankali dan Allah, kana taka doka fa."

Ashar d'in daya malmalawa masu dokar da wanda ma aka d'orata yana wajen yasa ta ja baki tayi shiru tana girgiza kai, shirun da tayi kuma wata masifar ce sai ya fara fad'a wai ta maida shi mahaukaci tayi banza dashi, cikin salon rashin kunya tace "To Allah ya huci zuciyarka, bana so nayi laifi ne."

Damtsen hannunta mai tarin tsoka ya mara yana fad'in "Ba dan kin raina mutane ba, wai ke har ki fito da wandon daya kamata ace mijinki ne kawai zai gani a gaban namiji, to me kile son nuna masa kenan? Ya gani yayi sha'awa ko me?"

Ta wutsiyar ido kawai tale kallonshi ba zata yarda tayi magana ba ya sata a boot ya rufe, cikin masifa ya sake cewa "Ke ko can na kaiki kika k'ara kula wani Hamna saina babbaka d'an iska sai dai uwarsa ta haifi wani."

Baki bud'e ta kalleshi tace "Saboda me? Akan wane dalili? Kar nayi aure kenan kake nufi?"

Shiru ya mata baice komai ba dan haka tace "So kake na zauna haka har k'arshen rayuwata?"

Ba tare daya kalleta ba yace "Zakiyi amma ba yanzu ba, zan samo miki wanda ya dace."

A ranta tace "Bigagge kamar ko?"

A zahiri kuma tab'e baki tayi ta kalli titi, suna cikin gudu sosai wata mota ta giftasu da gudu tana zabga oda ita ma ta wuce, zuro kai yayi tsabar neman fitina yace "Idan kunje ku d'auke hanyar kusa aljihu kar mu wuce."

Dawo da kanshi yayi yana fad'in "Yan iska kawai mashaya."

Ajiyar zuciya ta sauke ta rumgume hannaye, kallonta yayi ya taka birki da k'arfi yace "Meye? Na dameki? To koma baya."

Zage ceinture d'inta tayi ta bud'a zata fita dan tafi son haka ma sai kuma ya jawota da k'arfi ya zaunar da ita yace "Ba zaki koma d'in ba tunda ba drebanki bane ni, kenan ma da gaske na dameki ko? Ba komai Hamna Allah yana gani."

Gyara zamanta tayi ita dai ba tace komai ba har ya sake d'aukar hanya, kallonshi tayi kallo na nutsuwa da basira, yayi shiru abinshi, shigar yan gayu ce jikinshi bleue d'in jeans da bak'ar riga mai dogayen hannu amma ya lank'washe su har zuwa gwiwar hannunshi, takalminshi k'afa ciki bak'i masu kyau, gemun nan yayi luf dashi sai walk'iya yale idan suka gifta ta cikin rana, zara zaran gashin idonshi wanda ke rufe girman idonshi duk sanda ya rufe su, kakkaurar girar mai yalwargashi da tsayi, dogon hancinshi daya tafi daidai da tsayin fuskarsa abun gwanin sha'awa, amma kuma kyawun d'an maciji ne, nan idan yayi wani abun saika rantse a gidan mahaukata ne yake.
Chapter 155 · 0% Book details