← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 198

Sashe 171

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirin daya musu ya tabbatarwa da Hajia ba lafiya ba, dan haka tace "Ina? Tana ina Babba?"

Cikin sanyin murya yace "Hajia ta tafi, nima ban sani ba."

"Kamar ya baka sani? Babba zauna."

Zaune yayi ya aje jakarshi gefe ya kalleta, cikin rashin son wasa tace "Fad'a min ina taje da safiyar nan? Ni dai banga sanda ta fita ba."

Ba tare daya had'a ido da ita ba yace "Hajia ta tafi, akan abinda ya faru ne, ita ce mai laifi ma amma har ta tsaya gabana tana fad'in idan na gaji da ita ta tafiyarta."

"Sai ka ce mata me?" Cewar Hajia, saida ya waina kanshi yace "Shine ta tafiyarta, tace na aika mata da takardarta."

Da k'arfi Hajia tace "Babba, kana da hankali kuwa? Yanzu kai baka ji kunyar fad'ar maganar nan ba? Matar ta ka?"

Gambo dake kallonshi da mamaki ne yace "Wai me ya faru ne haka da zafi? d'an uwa a sani na daku baku tab'a samun sab'anin da yasa tayi ko da yaji ba, me yayi zafi haka da girmanku da komai kuna fad'an yara."

Kallon Hajia yayi ranshi a b'ace yace "Hajia ni zan tafi."

Mik'ewa yayi zai fita Hajia tace "Ban gama magana da kai ba zaka mik'e min a kai Hassan, zauna min kaji malam."

Muryar da tayi magana da ita ta waccen Hajiar ce, dole ya dawo ya zauna yana sunkuyar da kai, Hadiza kam mik'ewa tayi ta kalli Hajia tace "Hajia zan jira a waje, akwai buk'atar ku tattauna."

Cikin mutumtawa Hajia tace "Zauna Hadiza, ai ke ma har yanzu iyalin gidan nan ce."

Murmushi tayi tace "Ban k'i ta taki ba Hajia, amma duk da haka akwai buk'atar kuyi magana tsakaninku."

"Hadiza karki manta fa yara biyu ne dake wanda kika samu a gidan nan, sannan abinda ke faruwa yanzun yana da alak'a da d'aya daga cikin ya'yan naki, ki zauna dan Allah sai muyi magana."

Komawa tayi ta zauna gabanta na fad'uwa kan abinda Hajiar tace, kallon lieutenant tayi tace "Kira min Sa'ada ka ce inji ni duk inda take yanzu ta zo ina nemanta."

Wallahi wannan Hajiarsu ce ta baya mai magana d'ayan nan, in yayi wasa zai sha ashar yanzu dan haka da sauri yace "To."

Wayar shi ya fiddo ya shiga neman lambarta, Gambo ta kalla tace "Ka kira min Ammar ka ce ya zo."

"To." Ya fad'a yana ciro wayarshi a aljijun balaluwarshi, yana gama magana dashi a lokacin har ya fita da yaran, sake umartarshi tayi daya kira Hamna sannan ta kalli Hadiza tace "Husseina na ciki, ki ce ta fito zamuyi magana."

"To Hajia." Ita ma ta fad'a ta nufi d'akin jikinta har rawa rawa yake na tunanin abinda ya faru tsakanin Ammar da Hamna daya har yasa Ummy suke k'ok'arin rabuwa da lieutenant.

Hamna ma ko da kiranshi ya shigo wayarta tana k'ofar gidan, saida hancin motar ta ya shigo sannan ta d'auki wayar, shi kuma yana hangenta ma saiya kashe kawai.

_Kuyi hak'uri da wannan, yau ne sai a slow._

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:38 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_66_

Husseina ta fito ta samu wuri ta zauna, tunda sauran matan suka fahimci zaman ba dasu bane kowace tayi d'akinta, sai lieutenant dake kiran Ummy, k'in d'aukar kiranshi tayi tunaninta hak'uri zai bata, Hajia ya kalla yace "Hajia ta k'i d'auka fa."

Wayarta ta lalubo a bayanta tana fad'in "Ban ga laifinta ba mana."

Kallon Hajiar yayi da mamaki, wai duk abinda tayi bata ganin laifinta? Kiran Hajia kad'ai ta d'auka cikin ladabi tace "Hajia."

Kai tsaye tace "Kina ina Sa'ada? Maza ki zo gida ina son ganinki."

Cikin rarrabawa tace "Hajia..ina..kan hanyar...zuwa gida ne."

"Wane gida? Sa'ada kina da gidan daya wuce nan ne? Kina da hankali kuwa? Ke yanzu dan Allah idan kika je ki ce me? Yaji kikayi? Kiyi sauri ina jiranki yanzu."

Cikin ladabi tace "Wallahi Hajia da gaske na ke, ina cikin bus d'in da zata tafi *Arlit*, yanzu haka mun wuce *Tessaoua*."

Shiru Hajia tayi tana kallon lieutenant da shima yake kallonta yana sauraren abinda take fad'a, sunkuyar da kanshi yayi k'asa ita kuma ta harare shi, wata shawarar ta yanke kawai bari ta barta yaje har can ya dawo da ita, kashe wayar tayi cikin fad'a tace masa "Ka shirya tafiya yin bikonta gobe goben nan, babu ruwa na da iskanci kaji na fad'a maka, kai in ba'a hak'uri da ko haihuwarku nayi a gidan ubanku ma."

K'wafa tayi mai k'arfin gaske dake nuna ranta ya b'ace sosai, kafin wani yayi magana Hamna ta shigo tare da Ahmad, da mamakin ganin mahaifinta taje gabanshi ta zauna tana fad'in "Abba? Yaushe ka zo?"

Kallonta yayi yace "Banjour."

Lab'e baki tayi tace "Pardon Abba, bonjour."

Gaisawa sukayi sosai inda take kallon mahaifiyarta da mahaifinta tana jin kamar ace babu aure kan mamanta ta sake had'a aurensu, ba wai sai iyayenka sun mutu ba wani lokacin kake zama maraya, su kansu akwai abubuwa dayawa wanda sukayi musu manqué musamman daga mahaifi, lallai Ummy ta kai su kirata uwa dan ta musu abinda ta cancanci hakan, amma duk da haka uwa uwa ce, ko hakk'in rayuwa a cikinta kad'ai ya ishi d'awainiya dasu.

Sallamarshi tasa ta gyara zamanta ta tank'washe k'afafu ta matsa daf da k'afafun mahaifinta, yaran duk wurin Gambo suka nufa ya sumbaci kowane kafin yace suje sama suyi wasa zai zo ya ba kowa tsarabarsa, saida suka haye sannan Hajia ta kalli kowa tace "Abinda yasa na tara mu anan dama akan maganar yaran nan ne."

Yanda ta k'arashe maganar da nuna Ammar da Hamna da hannu yasa su k'ura mata ido, dukansu kallo ne suke mata suna tunanin hannun da zasu iya begeta dashi daga lokacin data tona musu asiri, ba tare data damu da kallon da suke mata ba tace "A gani na tunda Hamna har yanzu bata da wani tsayayye me zai hana mu had'asu aure da Ammar?"

Kallon kallo aka shiga yi sai dai wasu na su kallon farin ciki da al'ajabain maganar ne, Ammar Hamna kuma a d'an birkice suka fahimci abun, Gambo ne yace "Masha Allah, gaskiya Hajia wannan tunani ne mai kyau."

Hadiza ma murmushi tayi tace "Gaskiya ne, Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Lieutenant da fuskarsa ke had'e yana kallon Ammar ne yace "Amma Hajia ina ga da an ji ta bakinsu, tunda shi yayi rayuwar auren nan yasan komai dake cikinta, ita kuma bata tab'a ba dan haka da an tambaye su aji idan hakan ya musu."

Husseina ce tace "Hakane kuma, tunda babu yaro a cikinsu da za'a ma tilas."

Hajia ce ta kalli Hamna tace "Hamna kinji abinda aka ce, Me ye ra'ayinki? Ki fad'a mana abinda ke ranki dan ba za'a miki tilas ba."

Daram! Gabansu ya fad'i a tare, kallon juna sukayi kowa da abinda yake sak'awa a ranshi, Hamna a ganinta ba zata iya zama da tsohon mijin yer uwarta ba, taya ma zata iya auren yar uwarta saboda ta mutu? Mijin ma kuma Ammar wanda zata iya rantsewa da Allah ba zasu tab'a zama lafiya ba kamar yanda suka zauna da yer uwarta, gaskiya ba zata iya ba sai dai suyi hak'uri. Kallon da yake mata kallon son gane abinda ke ranta ne, bakinta yake kallo yana mai matuk'ar zak'uwa da son jin kalamanta, sanda kanta tayi k'asa tana wasa da yatsunta na hannu, Hadiza ce ta kalli fuskarta tace "Hamna kiyi magana mana, duka anan babu bak'onki."

Husseina ce tayi murmushi tace "Ai mace kunya ne da ita, shirun kuma shi ya bamu amsar tambayarmu."

Da sauri Hamna ta d'ago ta kalleta tace "A'a Hajia, gaskiya ni ina da saurayi, yanzu ma ni yake jira na bashi dama ya gabatar da kanshi."

Tana fad'a ta d'an kalle shi, da sauri ta d'auke idonta, ba zata iya yarda ta k'ara kallonshi ba, wannan kallon babu alamar arzik'i a ciki. Hajia da bata ji dad'in abinda ta fad'a bane tace "Amma Hamn..."

Ammar bai jira me zata ce ba yayi saurin cewa "Nima haka, ina da wacce nake so."

Ko da ya fad'a ya mik'e tsaye ya juya zai fita Gambo yace "Ammar dawo ka zauna."

Juyowa yayi cike da girmamawa yace "Dan Allah tonton, zan gabatar muku da ita nan da lokaci k'ank'ani."

Juyawa yayi ya fice ita ma a hankali ta mik'e zata shiga d'akinta, duk sai taji jikinta yayi sanyi da yace wai yana da wacce yake so, lallai ma mutumin nan! Kenan har ya manta da yer uwarta a wata shida kacal ya fara son wata? Tsaki tayi a zuciyarta tana fad'in "Allah ya tsine mata ma."

🤔 *Wacece?*

Gambo ne ya katse mata tunaninta da tafiyarta ta hanyar fad'in "Ke."

Juyowa tayi ta dawo ta durk'usa gabanshi, cikin kakkausar murya da gargad'i yace "Tunda kince baki son d'an uwanki to ki turo mana wanda kika ce d'in, yau d'in nan ba zan bar garin nan ba sai nayi magana dashi."

A mugun tsorace ta kalleshi, me kenan ta jawo ma kanta? Ita fa ta fad'a ne dan abar maganar shi, amma bata da wani tsayayye yanzu ita in banda 'yan abi yarima asha kid'a, yanda ta kakkafeshi da idonta babu ko k'yabtawa yasa shi daka mata tsawa cikin jin haushi yace "Tashi ki bani wuri, kina girma kina cin k'asa har yanzu kin kasa sanin ciwon kanki."

Saida ta juya zata tafi taji wasu hawaye sun taho mata, bata san abunyi ba a yanzun gaskiya, Hadiza ma da bata ji dad'in k'in amincewarta ba tashi tayi tana fad'in "Kuyi hak'uri dan Allah zanyi magana da ita."

"Dawo zauna Hadiza." Cewar Hajia, komawa tayi ta zauna tana kallon Hajiar da tace "Watak'ila tana da dalilinta na k'in amincewa, karku matsa mata dan Allah ku barta ta zab'arwa kanta abinda take so."
Chapter 171 · 0% Book details