← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 198

Sashe 187

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tab'e baki tayi ta rab'ashi zata wuce ya sake tare ta yace "Sai fa kin biya ni yarinya."

A hassale tace "Kai kasan ni ba matsiyaciya bace, amma ba zan biyaka ba dan kaji dad'in kiran wasu yan iska kana hira dasu."

Da wani mamaki a fuskarshi yace "Iyeee Hamna, ni ne d'an iskan ko yan matan?"

Sama da k'asa ta harare shi ta juyo ta tsaya gaban gadon Ummy, bayanta ya tsaya yace "Allah sai kin biya ni kud'in wayata, na yafe miki sauran ma ki ban d'ari biyu, sauran babanki zai cika min."

Juyowa tayi tace "Saboda shine ya fasa wayar? To ko ni dana fasa ba zan biya ba."

Gashinta dake jik'e da ruwa ya fizgo da k'arfi ya matso da ita kusanshi, k'ara ta saki sanda ya rik'e gashin nata, rik'e hannunshi tayi tana kallon fuskarshi da ido jawur tana shirin yin kuka tace "Sake ni Ammar."

Jinjiga kan yayi yace "Waye Ammar d'in?"

Da k'arfinta tace "Kai, kai ne Ammar, Ammar Ammar Ammar! Na fad'a sunanka ne ai."

Sakin gashinta yayi ya jawo k'ugunta ya had'e da na shi yana mata wani kallo mai ma'anoni yace "Naji zan yafe miki kud'in, amma sai munje b'angarenmu."

Hannu biyu tasa ta ture shi tace "Da wa? Ni? Har abada Ammar, wallahi sai ka..."

Leb'enta na k'asa yayi saurin cab'owa da yatsunshi biyu cikin tsananin tashin hankali yace "Karki yarda bakinki ya sake fad'in ba zaki koma gida na ba, tawa ce ke har abada, kin gane?"

Idonshi ta kalla tana sako da hawaye masu zafi tana fad'in "In dai har kana kula irinsu Amie, to ba gidanka ba kad'ai har da tsanarka saina koyawa kaina, zan tsaneka Ammar tsana ta har abada."

Da sauri ya saketa yana sunkuyar da kanshi, hannu d'aya yasa yana murza fuskarshi yana sauke huci mai zafin gaske, kallonta yayi kallo na basira yace "Babu komai tsakani na da ita Hamna, yau na had'u da ita kuma a yau na bata lambata, amma sam ba abinda kike tunani bane."

Da k'arfi ta tureshi baya tana fad'in "To miye inba haka ba? Akan me zaka bata lambarka? Me take da shi a jiki dani bana da shi?"

Da sauri ya rik'e hannayenta yace "Babu Hamna, bata da komai da yake birge ni ma, ke kad'ai ce ke birge ni a yanzu, bayan ke wallahi babu kowa a gabana."

"Amm.." Da sauri Ummy dake tsaye ta zuba tagumi tana kallonsu, kanta har ya fara ciwo saboda cacar bakin nan (ni ma yanzu haka nawa kan ciwo yake Ummy, tunanin yaranki kad'ai nasa gabana ya fad'i), mamakin yanda suka manta da ita a d'akin suke ta maganarsu ma take, wani na fad'a wani ke d'auka shi ma ya fad'a, ita sun hanata damar fad'an wani abu ma, nuna musu k'asan gadon tayi tace "Ku zauna."

Kallon Hamna yayi saida ta zauna k'asan tana rufe kafad'unta da k'aramin towel d'in kafin shi ma ya zauna yana ta kallon fuskarta, kan gadon Ummy ta zauna ta kalle shi a nutse tace "Me ya had'aka da k'awarta har ka bata lambarka?"

Zunbur ya sake gyara zama kamar mai zaman tahiya yana fad'in "Ummy yarinyar nan bata da hankali karki saurare ta, na kai uwa Zeituna wajen bikin Jumare, na dawo shine na ganta na tsaya muka gaisa..."

Duk abinda ya faru ya fad'awa Ummy kafin ya kalli Hamna yace "Shine dan ubanta ta fasa min wayata sabuwa, Allah sai kin biyani ko kuma na siyar da motarki."

Nuna shi tayi da yatsa tace "Kar sake zagar min uba malam, ya isheka haka fa."

Dafe k'irji yayi da hannu ya zaro ido yace "Lah na shiga uku, Hamna ni kike nunawa da yatsa? Mijinki ne ni fa."

Hararanshi tayi tace "Ka sake zagina ma sai kaji tafi a fuskarka Allah."

Ummy ya kalla yace "Shikenan Ummy 'yarki wuta zata shiga."

Cikin juya baki tace "Sai ka kaini ai tunda kai ke da wutar."

Kallonshi Ummy tayi, wai fa so yake ta koma a hakan har ya fara jigata shi, amma dai nuna tsananin damuwar da kuma lallab'ata shine baisan ya zaiyi ba, har da zagi yake had'awa, to a hakan zata koma ko me yake nufi? Had'e fuska tayi ita ma tace "Taje ta fasa wayar, to bari kaji ba ita ba ko ni naga ubanka na waya da wata Allah bayan na fasa wayar ma saina fasa mishi kai, ai kai ta maka mai sauk'i ma, malam fitar min a d'aki."

Galala ya kalli Ummy, me take nufi? Ganin baiyi niyar mik'ewa ba yasa Ummy kallon Hamna tace "Yar albarka tashi canza kayanki, zanje da kaina na d'auko miki kayanki adadin da kike buk'ata."

Wata dariya ya shek'e da ita yana mik'ewa tsaye yace "Eh lallai Ummy ba zaki iya zama alk'aliya ba, kuma da nasan wariyar da zaki min kenan da ban kai uwata wajen bikin nan ba har sai an gama wannan yak'in."

Mik'ewa tayi ita ma ta ja rigarshi tana fad'in "Muje waje a barta ta huta, saina bata maganin ciwon kai tasha saboda damuwar nan daka saka mata."

Juyowa yayi ya kalleta yace "Ke yanzu zaki iya zama babu ni a kusa dake? Kinfa san abinda nake baki kina ci cikin dare."

Ita kanta Hamna saida ta dara tace "Bana so, ka ci kayanka kai kad'ai."

Tsaye yayi ya rik'e k'ugu yace "Ummy kin kassara min zuciyata wallahi, zan fita yanzu amma ba zan sake dawowa nemanta ba, amma Ummy ki tabbatar kin ware mata gadonta, dan zan dinga kawo mata ziyara."

Kallonshi tayi tace "To bismillah kaga yanda zanyi da kai."

Saida ya kai k'ofa ya juyo ya kalleta yace "An dake ni kuma an hanani kuma, ke dai baki da imani wallahi ko kad'an."

Ummy ce tace "Zama da kai ne yasa ta rasa nata ita ma."

Ko da ya shigo da dare da sabuwar waya ya saka layikan nashi a ciki, yana zaune yana duba sak'onnin dake shigo mishi ta WhatsApp yaga bak'uwar lamba ta turo mishi hotuna, shiga yayi dan ganin wanene, tashin hankali sanda ya bud'a hotunan, Amie ta turo mishi hotunan ta tsirara, wanda ke da kayan ma kamar ba'a saka ba na d'aukar hankali ne, da sauri ya lik'e idonshi yana fad'in "Ya salam."

Bud'ewa yayi ya shiga ya goge su duka tare da bloquén d'in lambar, kiran lambar yayi ko da ta gani ta d'auka jiki na rawa, na yan Maradi ya mata ta hanyar cewa "Ke dan mai... me kike nufi da ni? Na miki kama da d'an iska irinki? To saurare ni da kyau kiji."

Saida ya gyara zama yace "In kika k'ara kula ni ma ko a hanya wallahi daga ubanki har kakanki na ashirin sai sun zubar da hawaye, in kika k'ara tuna ko sunan matata ma sai yan uwanki sunyi nadamar kasancewarsu yan uwanki, In kuma kika sake aiko min hoton rub'abb'ar fuskar nan taki mai kama da gurb'ataccen tumatir Allah saina watsa miki asid kin k'arasa dahuwa, shegiya b'abb'akar banza ke ba kyau ba ba kyan jiki ba har ki tsaya kina bariki, to ki kiyaye ni kafin ki fara nadamar sani na da kikayi, yanzu ma wallahi na raga miki ne dan ni dan ni fad'a da mace ba aikina bane, amma da namiji ce ke da tuni na nemi inda kike na cire miki k'ashin baya, 'yar banza mai kama da agwaluma."

*Kuyi hak'uri da jaruminku, bakin ya saba da...*

Amie da tunda ya fara magana tayi shiru take saurarenshi, saida taji ya kashe wayar ta bi wayar da kallo, ya ci mutumcinta sosai fa ta yanda ba zata iya mantawa ba, amma ya zatayi daya wuce tayi wuri ta aje shi, dan tasha jin labarinshi wurin Hamna tun kafin su b'ata, tasan in tace ma tayi dashi ita ce a kasa da cizon yatsa.

Ko da ya gama fad'a shima ya aje wayar ya mik'e ya shiga wanka, daya fito shiryawa yayi cikin kayan bacci ya fesa turare ya fice wajen matarshi. Da sallama ya shiga ya same su duk zaune a falon, kusan Hajia ya zauna yana kallon Nazifa dake kusa da Hamna suna kallon waya yace "Ke tashi samo min abinci."

Mik'ewa tayi a ladabce ta shiga madafa, kallon Hajia yayi yace "Hajia jikar nan taki bata san meye miji ba, kiga fa babu ruwanta da na ci abinci ko ban ci ba, ita dai data samu ta cika tunbi shikenan ni na mutu dan yunwa."

Ko kallonshi ba bare ta tanka masa, haka ma Hajia bakinta taja tayi gum, jin babu wanda ya kula shi yasa yace "Hajia yau wace rana?"

Kallonshi tayi tace "Yau talata."

"To juma'a insha Allahu zamu koma sabon gidanmu."

Duk yayi maganar ne yana kallon Hamna, duk da bata kalleshi ba shiru tayi daga danna wayarta, sanda tayi k'ok'arin kallonshi kuma saita lura da wajenta yake kallo, dan haka bata yarda ta kalleshi ba, Ummy ma kallonshi tayi ba tace komai ba sai Hajia da tace "Ammar da gaske kake?"

A lokacin Nazifa ta fito ta sunkuya ta mik'o mishi abincin, saida ya karb'a ya fara ci yace"Allah kuwa Hajiata, tafiya zanyi daga nan mu barku ku sarara kuma."

Cike da rashin jin dad'i tace "Ammar bana so ku bar nan wallahi, in na bari kuka tafi kamar ban cika burin marigayi ba na son zama a waje d'aya, kuma kaga yanzu kana tashi daga nan sauran ma zasu ce zasu tashi."

Gyara zama yayi yana kallonta yace "Hajia kiyi hak'uri dan Allah ku ba kowa dama ya d'an matsa, ni na miki alk'awari zumuncinmu ba zai lalace ba sanadiyar tashinmu, na kuma miki alk'awarin ko da na tashi daga nan kullum zan dinga zuwa kowace safiya ina gaishe ki, haka ma kafin na kwanta saina tabbatar da na zo kin ganni na ganki sannan."

D'an lab'e baki tayi tace "Shikenan, Allah yasa alkairi."

Su Ameer ya kalla dake kewaye da Husseina tana musu tatsuniya ya kalla yace "Heyy, duk wani wanda yasan mallaki na ne shi ya had'a kwomantsanshi, dan babu wanda zan bari."
Chapter 187 · 0% Book details