← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 198

Sashe 134

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Soueiba ce tace "Jamila dan Allah kiyi shiru ki k'yaleshi, d'inki aka miki fa karki tada shi da d'aga muryar nan da kike, ko tari ba so ake kiyi ba bare wannan fad'an haka."

Kallonta tayi cikin zubo da hawaye tace "Amma duk abinda ya faru ai shi ya ja, ni yau bak'in ciki na yana ta hidima da yarinyar nan amma saiya nuna min kawai yana yi ne dan ya ma yah Junaid kara, sannan gabanshi babu irin iskancin..."

Jibril ne yace "Naji na d'auka Jamila kiyi min duk abinda zakiyi, amma dan Allah yanzu kiyi shiru ko dan halin da kike ciki."

Tank'washe k'afafunta tayi ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka, da sauri Soueiba da Zeinabu suka tashi suna bata hak'uri Zeinabu na k'ok'arin d'agata tana fad'in "Ki gyara zamanki mana karki ji wa kanki ciwo a banza."

Tasowa yayi ya tsaya gabanta ya sunkuya ya ja k'afafunta ya mik'ar mata dasu, hannayenta ya b'amb'are ya tallabo fuskarta yana kallon idonta yace "Dan girman Allah Jamila karki cutar da kanki akan banza irina, ki kwantar da hankalinki ki nutsu, ki kula da kanki da yaronki kinji, ba dan ni ba kiyi dan iyayenmu."

Fizge fuskarta tayi ta kawar da kai gefe, ganin ta daina kukan yasa shi zagayawa ya kalli abokanshi dake rik'e da bebyn, fita sukayi inda Zeinabu da Soueiba sukayi ta bata baki kan karta yarda damuwar ta kusa illata ta.

*Safiya* na yi ta gama shiryawa dan zuwa ganin Jamila, dama tare suka shirya tafiya dan haka suka fito duk a tare, Hamna na tare da Ummy wacce yau zata fara zuwa aiki, tayi fes da ita kamar tayi bik'i fa haka ma Shureim yasha shiri tsaf da shi, saida Ummy ta bud'a mota ta zauna cikin mota suka k'araso wurin, da girmamawa dukansu suka ce "Ina kwana Ummy."

Kallon Amna tayi tace "Lafiya lau, antashi lafiya?"

"Lafiya lau." Amna ta amsa, matsowa Ammar yayi kusan Hamna dake rik'e da Shureim ya tara hannayenshi zai karb'eshi, kallonshi tayi da fararen idonta haka kawai ta tsinci kanta cikin jin dad'i yanayi, mahaifin d'anta zai karb'eshi a hannunta, murmushi tayi da ita kanta bata san ya zo mata ba, zata bashi shi cikin had'e fuska Ummy tace "Kawoshi na kusa makara."

Take murmushin fuskarta ya b'ace ta sake kallonshi, wallahi bata san wane irin yanayi ne take ji ba a game dashi, amma dai har k'asan zuciyarta tausayi taji ya bata da Ummy ta k'i yarda ya amshe shi, mik'a mata shi tayi suna kallo ta rufe motar ta tayar ta bar gidan. Amna ya kalla ya kama hannunta yace "Muje."

Suna gaba Hamna na bayansu har suka shiga gaba ita baya, saida suka daidaita ya juyo ya kalleta yace "Dan ubanki ni kike jira na fara gaishe ki kome? Wai ke me yasa baki da wayo ne?"

Saida ta rumgume hannaye ba tare data kalleshi ba tace "Bana da wayon ne, kuma idan kai ka fara gaishe ni miye a ciki indai har kasan darajar mutum."

Da k'arfi ya juyo cikin nasara ya finciko wuyanta had'e da hijabinta ya matse sosai yace "Ni kike fad'awa duk abinda ya zo bakinki, sa'anki ne ni? Tambayarki nake?"

Yanda ya k'arashe da d'aga murya yasa ta rintse ido tace "Kayi hak'uri to, ina kwana."

Turata yayi da k'arfi kanta ya kaiwa kujerar karo, hararanshi tayi shi kuma ya tayar da mota yana baya baya yana fad'in "Shashanci, ita ta raba kanta dani, k'anan nawa ma rabani zatayi dashi, zanyi k'ok'ari na dakatar dashi daga nan, ba zan bari ya ci gaba da faruwa ba, ba zan bari soyayyarshi ta ci gaba da wanzuwa a cikin zuciyata ba, Allah kaine shaida ina ganinshi naji nafi son shi fiye da sauran 'yan uwana, miye laifina a ci? Wane irin virus ne a jikina da har zata nemi nesanta ni dashi? Matsala."

Daga Hamna har Amna sun fahimci abinda ke zuciyarshi ne ya fito, Amna kuma dake kallonshi tuni ta ga idonshi sun fara rikid'a alamar kad'an ya rage ya zubo da hawaye, Hamna ma tasan dalilin Ummy kenan tana so ta nesanta shi da d'anshi ne, sai dai kash gashi daga abinda ya fad'a yanzu ta gane soyayyar yaron ta riga data shiga zuciyarshi, haka suka d'auki hanya tana danna wayarta har suka isa. Tare suka shiga wajen Jamila suka dubata, taji dad'in ganinta ita ma dan haka ta saki jiki suka fara hira, ganinsu ne yasa Zeituna da Soueiba suka ce su zauna anan suje gida su dawo, ita Soueiba tana son yin wanka a tsanake saita dawo, Amna ma shiga tayi wajen awo abinka ga masu abun tuni aka gama mata ta dawo, jiransu sukayi dan dama basu zo da niyyar tafiya da wuri ba.

*Samun* labarin rashin kunyar da tayi a gidan yasa malam Rabi'u tahowa da ita har gidan, yace dole ta basu hak'uri kuma ba zai ba mijinta hak'uri danya maidata ba, duk da babu yara kuma ita kanta Zeinabu likita take kwana wajen Jamila, amma anyi katarin ta zo saboda zuwan colonel da zai kwana d'aya ya wuce *Mali*, gaban Hajia ya zaunar da ita tace "Dan Allah kuyi hak'uri da rashin kunyar dana muku."

Jin wani murmushi da Hajia tayi yasa Maryama d'agowa cikin jin haushi, murmushi ta mata tace "Haba."

Cike da iyayi Hajia tace "Ke ni fa abinda kikayi ko a jikina wallahi, kin tona mana asirin da bamu sani bane, dan haka ni banga abun damuwa ba, ban sani ba dai ko ga ita wacce abun ya shafa."

Ta fad'a tana kallon Husseina, murmushi Maryama tayi ta kalli Hajia tace "Hajia ke babba ce a gidan nan, babu kyau fariya ga d'an adam bare ke musulma, bai kamata ki dinga tsarkake kanki da ahalinki ba, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, ko matan baki isa kiyi shaida akansu ba bare mazan, to wai ma akan me kike cika baki? Tare dasu kike fita? Ko kuma kina bibiyar duk abinda sukeyi ne a wajen? ko kuma a cikin gidan kina saka ido akan lamuransu? Ko d'aya fa ba kyayi Hajia, kuma a hakane kike ganin ya zama wajibi akansu su kare kawunansu? To ubangijin daya hallicemu ma ai muna sab'a masa bare kuma ke 'yar adam."

Mik'ewa Maryama tayi sai malam Rabi'u cikin barbarci da yace "Mari rashin kunyar ce har a gabana? Lallai kin rik'a."

Nuna Hajia tayi tace "Malam ba rashin kunya bane, ita tana ganin kamar iyalinta sunfi k'arfin aikata laifi laifin ma kuma na zina, alhalin bata san tana tare dasu ba kuma suna kewaye da ita."

A hankali Hajia ta sauke k'afa d'aya kan d'aya tana kallonta tace "Ban gane ba? Kinsan me kike fad'a kuwa? K'arya kike wallahi."

Murmushi tayi tace "Babu maganar k'arya sai gaskiya, ya kamata ki farka daga baccin da kike Hajia ki tabbatar kin gano asalin kowane yaro daya fito daga tsatsonki, dan zai iya yiwuwa akwai yara dayawa wanda aka samu kafin aure kamar irinsu *Junaid*."

Zunbur ta mik'e tana kallonta ido a tsaitsaye, da sauri Zeinabu ta dafe bakinta da hannun dama ta daskare a wurin, Husseina Soueiba malam Rabi'u duka sororo sukayi, Junaid kam bai d'auki abin babba ba ganinshi kawai sharri ne, matsowa yayi kusanta yace "Kisan me zaki fad'a Maryama, dan na rabu dake bashi zaisa ki min wannan sharrin ba, ba k'aramin abu bane wannan fa."

Tab'e baki tayi tace "Dan ka rabu dani? To autan maza ne kai da zanyi bak'in cikin rabuwa da kai, kaga malam ka tambayi mahaifiyarka ta fad'a maka yanda komai ya faru, karka tsaya kana zare min ido."

Malam ta kalla tace "Malam mu tafi, zasuji da matsalarsu."

Tashi yayi yana waiwayen Husseina da shi dai yake son neman yafiyarta, suna fita colonel da lieutenant suka shigo tare da Alhaji cikin farin ciki, suna ganin yanayin mutanen wurin kowa yayi sororo ga Junaid yasa Zeinabu gaba yana magana k'asa k'asa yasa lieutenant k'arasawa da sauri wurin Hajia yace "Hajia lafiya? Meya faru duk na ganku haka?"

Colonel ma matsawa yayi kusanta yana karantar tsantsan tashin hankali daka fuskarta yace "Hajia lafiya?"

Dab'as ta zauna kan kujerar da kullum take jin dad'in zama kanta cikin isa da izza, duk yanda numfashinta ya fara barin gangar jikinta saida tayi k'arfin halin kallonshi cikin fitar da numfashi sama sama tace "Husseini..da gaske...ne.Ju...Junaid baaaa..."

Kasa k'arasawa tayi wanda hakan yasa colonel sunkuyar da kai, *wal'iyazu billah* shine abinda ya fad'a à ransa, kamar an jonata da kuran sai kawai ta tashi tsaye da k'arfinta, hannu ta d'aga sama da niyyar palla masa mari, sai kawai jikinta ya d'auki b'ari hannunta ya fara rawa da k'arfi kamar ta kama wayar lantarki, lieutenant da colonel d'in ne sukayi azamar rumgumata a jikinsu cikin tashin hankali lieutenant "Mu kaita mota."

Da gudu Zeituna ta k'araso tana k'ok'arin rik'eta tace "Ku saketa zamu kamata."

Soueiba ce ta taso da sauri suka kamata su kuma suka nufi mota, ana fita da ita sai asibiti wajen su Ammar, ganinsu ya d'aga musu hankali suma ba kad'an ba, Ammar da Ummy da kuma wata malamar asibiti ne suka rufa kan Hajia aka fara k'ok'arin ceto ranta.

*Awa biyu* suka d'auka kafin su fito fad'a musu halin da take ciki, Hajia kam dai...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_49_

Ammar ne yace "Cikin sarautar Allah komai ya daidaita, jininta ne ya hau sosai, amma yanzu mun samu mun shawo kan lamarin, ba wata bazarana a yanzu zaku iya komawa da ita gida, akwai magunan da za'a bata ta samu bacci."

Alhaji ne yace "Ammar kana ganin zamu iya tafiya da ita gida tun yanzu? Me zai hana ba zaku barta nan ba ta samu ta huta."
Chapter 134 · 0% Book details