← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 198

Sashe 97

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsawa tayi kusanshi amma bata zauna ba tayi murmushi cike da dattako tace "Yallab'ai nasan meya kawoka, dan haka ba sai ka wahalar da kanka ba, Zeituna k'anwata ce kuma abokiyar zama na, insha Allahu zamu zauna lafiya ta yanda zakayi alfahari damu, mun riga da mun fahimci junanmu, tunda ba yau muka san juna da ita ba, nasan wacece Zeituna, duk da ana cewa d'an adam ya kan sauya, amma ina da yak'ini akan Zeituna cewar ba zata canza ba, yarinyar kirki ce ita d'in, tana girmamani da ganin darajata, zanyi k'ok'ari naga na rik'e wannan girman sannan nima na bata matsayinta, insha Allahu na maka alk'awarin ba zaka tab'a samun mu da wata matsala ba, kawai kuje ku kwanta."

Cike da jin dad'i da kuma k'aunarta ya sakar mata murmushi yace "Allah ya miki albarka uwarsu Ammar, nagode miki sosai, hak'ik'a samun mace irinki a zamanin nan sai an tona, Allah ya bar min ke."

Murmushi tayi kanta k'asa tace "Nagode."

Kallon Zeituna yayi dake tsaye kanta k'asa har yanzu yace " Ke me zaki iya cewa to? Kin dai ji abinda yer uwarki ta fad'a."

Rau rau ta fara yi da ido ko d'agowa ba tayi ba bare tayi magana, murmushi Ummy tayi tace "Yallab'ai kai bai ma kasan ai ba zatayi magana, kunya take ji har yanzu, amma ka bata d'an lokaci k'ank'ane."

Mik'ewa yayi yana fad'in "Shikenan to, saida safe ko."

Zeituna na jin haka ta juya da sauri dan barin d'akin, shi kuma ko a jikinshi saida ya jawo kan Ummy ya manna mata sumba a goshi tare da shafar gefen fuskarta kafin ya sake ce mata "Saida safe masoyiyata, ki kular min da kanki."

Murmushi kawai ta masa har ya fita, yana fita ta fad'a kan gado ruf da ciki tayi shiru, tabbas ta so tayi kuka, amma kuma cikin ikon Allah saita fi k'arfin zuciyarta har bacci ya d'auke ta. A wajen lieutenant kam shima yasha gwagwarmaya da zuciyarshi, dan so da dama zuciyarshi ce ke tunasar dashi wannan auren fa na mahaifina ne, duk rashin kulawar da zan nuna mata kamar na wofantar da maganar mahaifina ne, da hakane fa har suka kwanta bacci yayi dubarar mayar da ita matarshi ta sunna.

*07:05* duk da yau asabar ce amma kowa na gidan ya gama shiryawa, yara sunyi shirin islamiyya manya kuma zasu fita, Hajia na zaune a inda ta saba zama, Zeinabu da Soueiba da Ummy na ci gaba da gyaran gidan tare da Iya, sai su Nana dake ta k'ok'arin kammala abin karin kumallo, colonel ma cikin shirin tafiya ya fito ya gaishe da Hajia, kamar kullum ta amsa babu wani sakin fuska bare sa albarkarta, bai jira komai ba ya d'auki hanya tare da masu tsaron lafiyarsa dake biye da shi. Tun a falonsu suka had'e kowa ya fito daga d'akin shi, hannu Amar ya bashi yana fad'in "Malam Ammar ka tashi lafiya?"

Hannu ya mik'a mishi a cikin mak'oshi ya amsa da "Um." Murmushi kawai yayi yace "Tun jiya ina ta nemanka ban ganka ba, ina ka shiga ne haka?"

Ba tare daya kalleshi ba yace "Yaushe ka fara aikin jarida?"

Wani murmushin ya sake yi yace "Daga tambayar k'waya d'aya? To Allah ya baka hak'uri."

Fuska a had'e yace mishi "Idan ya bani kabi dare ka k'wace mana."

Girgiza kai kawai Amar yayi yace "Kasan banji dad'in rashin ganinka ko d'aya daga cikin sabgar Abba ba, Ammar meyasa kake haka? Ba kyau fa."

A daidai farfajiyar gidan yayi tsaye ya juyo ya kalleshi yace " Dan Allah Amar samu madaki ka bibbige ni, shine kad'ai zaisa nasan baka ji dad'i ba, yau ni naga jaraba, dole ne saina je d'aurin auren? Yanzu da banje ba meya faru? An fasa ne? Ina ce amaryar a gidan nan ta kwana kuma tare dashi."

Juyawa yayi a fusace ya tunkari falon Hajia yana fad'in "Kawai mutum ka addabeni ka addabi rayuwata, kuma ni na fad'a maka banje ba? Ina ce ni na rakashi ma d'akin amaryar, haka kawai ka dameni da surutu."

Amar na jin abinda ya fad'a ya matso da sauri yace "Me kace? Ka raka shi fa naji ka ce?"

Sake tsayawa yayi ya juyo a hassale yace "Eh haka nace, ni na raka shi, da matsala?"

Girgiza kai yayi dan ya fahimci yau ya tashi da yan sababin, shine ya fara shiga falon ba sallama kamar kullum inda Amar ke biye dashi da sallama, kujerar dake gefen Hajia ya zauna ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana fad'in "Ina jin dad'in zaman kujerar, bansan meyasa ba bana gajiya da zamanta."

Kallon Hajia yayi wacce ita ma ta kafe shi da ido tana kallonshi, murmushin nan dai daya saba mata na iskanci ya mata yace "Au na manta fa, ashe ni d'in jinin Hajia ne, jika na farko ga hajajju mutan makka, dole ne kujerar nan ta dinga burgeni, ashe gado nayi, dan naga kema ke da kujerar nan kamar kujerar mulki ce, duk wanda zai bud'e idonshi a gidan nan to zai wayi gari ne ya ganki a samanta, haka kuma duk wanda zai kwana to zai rufe idonshi ne bayan ya miki gani na k'arshe a kanta."

Had'e rai tayi tace "Kai ka kiyaye ni, meya kawoka nan d'akin?"

Dariya ya mata yace "Karki damu Hajiata, insha Allahu ko a lahira saikin zauna kan kujerar nan a matsayin shugabar tsofaffi ta gidan aljanna."

Hannu ta kai cikin zafin nama zata mareshi, da azama cikin isa da k'asaita ya cabko hannunta ya rik'e sosai, kallon baki da hankali ya mata yasa d'aya hannu yana shafar hannunta yana kallon k'wayar idonta, tana kallonshi ya kai hannun a bakinshi ya sumbaci bayan hannun nata kafin ya kalli hannun yace "Ni kam Hajia in tambayeki mana?"

Jin tayi shiru tana kallon sarautar Allah yasa yace "Nasan dai zamanin kina budurwa hannayenki abun sha'awa ne? To amma ya akayi yanzu naga sun zama haka? Duk sunyi tamoji sun jeme sai aukin jijiyoyi kamar..."

Fizge hannunta da tayi yasa yayi shiru ya kalleta, hararenshi tayi tace "Allah ya wadaranka Ammar, wallahi ba dan kayi kama da shalele ba da sai nace kai ba jini na bane, amma ba laifinka ban nawa ne."

Gyara zama yayi irin ya sa mata bak'in ciki yana fad'in "Da gaske? To amma me yasa kika ce haka? Kina nufin duk ahalin nan naki ni kad'ai ne d'an baiwar da yayi nasarar ya gadoki ta ko wani fanni?"

Sakin baki tayi da alamar mamaki a fuskarta, za tayi magana ya sake cewa "Kuma da kika ce muna kama da shalele, shin shine yayi kama dani ko nine nayi kama dashi? Ko kuma dai ke ce mukayi kama dake?"

Nuna shi tayi da yatsa tace "Dan ubanka in kana k'aunar uwarka ka tashi ka bar d'akin, wallahi ban son ganinka."

Tsaf ya mik'e ya kalleta yace "Idan kika ce ba kya son gani na a cikin gidan nan ma zan iya daina zuwa, amma fa saboda soyayyar uwata, dan ba zai yiwu na bar gidan nan ba bayan kuma nine babban magajin gidan."

Wani kallo ta mishi a shek'e tace "Wai kai a ganinka kaine babban magajin gidan nan?"

Dariyar rainin hankali ya mata yace "Ba'a ganina bane, a ganin kowa ma hakane, shiyasa fa hausawa suka ce *ko ba'a sonka a haifeka da fari*, gashi dai ni d'in ba sona kuke ba amma kuma ni na fara bultsowa duniyar, kai wallahi ni d'in mai sa'a ne."

Hannu ya bawa Hajia da nufin su kashe yana fad'in "Ban biyar Hajia ta, Allah ina mugun sonki."

A daidai lokacin da Ummy ta fito daga madafa kenan, yayi daidai da fitowar lieutenant da Zeituna a bayanshi Hajia tace " *Ni kuma na tsaneka Ammar, kaji da kyau, wallahi bana sonka har zuciya ta, bana son mu'amula da kai saboda kamar mahaukaci kake, Ammar ba dan ina asibitin ba a lokacin da uwarka ta haifeka da sai nace kai ba jini bane, wallahi sai nace wani d'an Allah bani ne kai, sakarai kawai.*"

Wata marainiyar dariya ya mata tare da k'ok'arin mayar da hawayen da suka cika idonshi taf, gyara tsayuwa yayi ya shirya dan ya fad'a mata abinda har ta mutu bata mantawa, sai dai kuma kafin ya fad'a Hajia ta juyo ta kalli Ummy tace "Sa'ada kina jin rashin mutumcin da d'an ki ke shuka min ko? Wallahi idan bai kiyayeni ya kusa barin gidan nan."

Daga inda take tsaye ta wurgo masa da harara kafin ta kalli Hajia tace "Kiyi hak'uri Hajia, ni kaina al'amarin shi ya fara bani tsoro, hakan yasa ma nake ganin da k'yar in aljanu basu shafe shi ba, dan a yanzun ni kaina barinshi gidan nan ne kad'ai kwanciyar hankali na."

Wani shak'iyin murmushi Hajia tayi ta kalleshi tace "Kaji ko? Uwarka ma data haifeka tana so kayi nesa da ita, bare kuma ni da ban haifeka ba, dan haka ka kiyaye."

Tunda Ummy ta fara magana Zeituna dake nesa da ita ta k'ura mata ido, jin furucinta akan Ammar ba sabon abu bane a wurinta, amma ta rasa dalilin da yasa yau taji babu dad'i, a zuciyarta take fad'an "Akan me Ummy zata fad'i haka akan d'an data haifa? Meye ga Ammar d'in da har ya dace da wannan furucin?" Ita kam bata gani ba sai ma zunzurutun soyayyarta da yake d'awainiya da ita, soyayyar da har ta isa ta sashi ya ma mahaifinshi kashedi akan ta, amma ace ita tana fad'in haka akan shi, gaskiya har ranta ba taji dad'i ba. Lieutenant kam kallonta yayi kawai ya tako ya zo gaban Hajia ya gaisheta, duk lokacin Ammar na tsaye da Amar a bayanshi, kawar da kanshi gefe yayi ya d'anyi murmushi mai nuna k'unar zuciya da takaici, lokaci d'aya kuma ya kalli Ummy yana wannan murmushin yace "Ina da shafar aljanu kam, na tuna muku idan kun manta, mufa duk aljanunmu na gado ne, sai dai bansan daga ina ne muka gadosu ba, daga b'angaren uwa ne ko kuma uba, ni kuma aljanin daya shafeni sunanshi *ifritu*, shiyasa muke kama da shi a halayya."
Chapter 97 · 0% Book details