← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 198

Sashe 189

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta k'ara jawo rigarshi tace "A'a d'auke ni, d'aukeni muje b'angarenmu kafin Ummy ta taho, ita ta koro ni fa daga can."

Murmushi yayi yace "Allah?"

"Eh." Ta fad'a da sauri tana d'aga mishi hannu saiya d'auketa, gyara tsayuwarshi yayi ya d'auketa gaba d'ayanta ya k'arasa sauka da ita, ba tare daya juyo ba yace "Ummy saida safe, yar yajinki ta koma."

Rufe fuska tayi cikin k'irjinshi har suka fice, har saida suka b'acewa ganinta sannan ta girgiza kai ta shiga saukowa a hankali tana fad'in "Allah kaine Allah, Allah ka shirya min yaran nan shirin addinin musulinci, Allah ka kawar da idon mak'iya da bakin mutane akan su."

*Ameen Ummy.*

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:39 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_75_

Ko da suka shiga ya sauketa kan gado, zaune yayi ya fuskanceta da kyau yace "Hamna, yanzu nan duk cutar nan da kika min shikenan kin cuci banza kenan?"

Saida tayi da gaske ta samu ta rik'e dariyarta tace "Rama to."

Zaro ido yayi yace "Ni! Ni d'in banza da zan rama, a'a na yafe."

Cikin bushewa da dariya tace "To bacci zanyi."

"Kwanta." Ya fad'a yana kallon idonta, zanin rufa taja ta rufa tana dariya k'asa k'asa, sai yanzu take hango sanda ta bankad'o shi yayo k'asan nan daram, sai kawai ta juyo tana k'ara barkewa da dariya, ganin tana dariyar ba tsayawa har da rik'e ciki yasa yace "In ban miki Allah ya isa ba ki ce ba sunana Ammar ba."

D'aga mishi hannu tayi alamar ta daina tare da rufe bakinta tana wata dariyar, shi dai har bacci ya d'aukeshi bai tanka mata ba tana dariya.

*Ko da* suka gama kari zai fita yace su tafi ya kaita, kallonshi tayi tace "Wai da gaske kake dama?"

Ba alamar wasa a tare dashi yace "Ina wasa dake ne?"

"A'a." Ta girgiza kai a hankali, d'orawa yayi da "Zaki tafi ko na tafiya ta?"

Cikin turo baki tace "Gaskiya ka tafi, Ummy tace zanga b'acin ranta."

Wani kallo ya mata na tsanake, shi fa akwai abinda yake nufi daya fad'i haka, in bata amince ba kuma akwai matsala, amma cikin ruwan sanyi zai bita sai kawai ya juya yana fita yace "Shikenan, saina dawo, amma kar kiyi mana abinci yau zamu fita waje." K'ala ba tace ba har ya fice.

*An shirya* dan fita kamar yanda yace, amma sanda ta fito cikin shirin riga da siket d'inta da mayafi saiya shiga zagayata, tsaye tayi tana binshi da kallon kafin ya tsaya gabanta yace "Yanzu Hamna dan zamu fita shine sai kin fad'a ma kowa cewa gaki nan kin fito."

Da mamaki tace "Kamar ya fa?"

Saida ya nuna kamar yana ganinshi yace "Shi wannan turaren da kika fesa fa?"

Yar ajiyar zuciya ta sauke tace "Ohh, yana da dad'i ko?"

Wata harara ya wurga mata yace "Dad'in banza dad'in wofi, ni ba dad'inshi nake tambaya ba."

Kamar wacce ta tuna da wani abu sai kuma tace "Au, sunanshi? Sunan shi *Oud zarkah*, ka gane."

Rik'e k'ugu yayi dan ya fahimci zata raina masa hankali ne yace "To je ki cire kayan nan ban son jin k'amshinshi jikinki."

A kasalance ta amsa da "Ba fa a kayana bane, a wuya da baya kunne kawai nasa."

Cike da raini yace "To je kiyi wanka."

A kasalance ta sake amsa shi da "Ko nayi ba zai fita ba, kamu ne dashi."

Da hannu ya mata alama yace "Can naga lalle iyakar kamu, je ki wanke min shi Hamna kafin ranki ya b'ace, ko da ruwan gidan nan da garin nan zasu k'are to zan d'ebo miki ruwan maliya dan ki wanke shi."

Galala ta kalleshi tace "To da wannan nayi zamana mana, fitar ta zama dole ne?"

Saida ya sake rik'e k'ugu gam yace "Qur'ani sai kin tafi."

Saida ta waina idonta alamar gajiya da zancen sannan ta juya ta koma ciki, canza kayan tayi ta sake wasu kafin ta fito suka fita.

Saida aka d'auki hanya yace ai fa an ma fasa cin abincin, kawai wasu almajirai zasu tsaya wani cin abinci a waje, ji tayi rainin hankalin ma ya wuce misali, k'ufula tayi ta had'e girar sama da k'asa ta rumgume hannaye, saida ya samu wurin da babu hayaniya ya caka birki ya tsaya, a hankali ya kamo hannunta yana kallon fuskarta yace "Baby, kalle ni nan."

Kallonshi tayi amma asali harara ce take masa, kashe murya yayi yace "In tambaye ki mana?"

Kafeshi tayi da ido alamar ina saurarenka, saida ya d'an muskuta zamanshi yace "Kina so na da gaske?"

Turo baki tayi tace "Me kuma ya kawo wannan maganar yanzu?"

"Ki bani amsa." Ya fad'a yana ci gaba da kallonta, juya kanta tayi tace "Eh."

Sakin hannunta yayi yana tayar da motar yace "Muje to na siya miki ice cream."

Kallonshi kawai tayi ita dai har suka fara tafiya, ta kusan salon d'inta suka bi wanda har ta kalli wajen ta ga a rufe alamar *Lina* har ta rufe, dama ba wata tsiya suke yi ba tunda ta bar zuwa sai jifa jifa, a hankali yake tuk'in zasu wuce ta wata majalisar samari, Hamna da idonta ke kallon hanya da sauri ta rik'o hannunshi da yake tuk'i tace "Lah! yah Ammar dubi mutumin nan da yasa aka daki yah Amar."

Saida ta gama fad'a sai kuma ta gane katob'arar da tayi, a hankali ta shiga sakin hannunshi tana jujjuya ido da matse bakinta, cak ya tsayar da motar yana kallonta yace "Yana ina?"

Ko kallonshi ba tayi tace "Wanene?"

Da k'arfi yace "Ban sani ba? Yana ina na ce?"

A tsorace ta kalleshi inda ta ga ranshi ya fara b'acewa zai iya cin ubanta ma, cikin i'ina tace "B..a komai fa, na d'auka shine."

Bayan wuyanta ya cakumo da k'arfi ya matso da fuskarta kusanshi cikin daka tsawa yace "Hamna karki b'ata min rai, ki nuna min shi ko na had'a duka wanda ke wurin na taka su da mota."

Yanda ya rik'e wuyan nata yasa ta cewa "Zan fad'a maka to, sake ni dan Allah."

Sakinta yayi inda ta sake kallon matasan, a hankali ta kalleshi tace "Waccen ne mai jan riga."

Kallonshi yayi da kyau, murmushi ya saki ya kalleta tare da jawo kanta ya sumbaci bakinta yace "Ni ma ina sonki."

Ture shi tayi tana fad'in "Ni bana son ka."

Dariya yayi yace "Baki isa ba yarinya, ko kina so ko baki so dole ki soni, inba haka ba duk zamu mutu tare."

Saida suka siyi ice cream d'in ya mayar da ita gida ya aje, sanda ta sauka kallonshi tayi tace "Kai ba zaka shigi bane?"

"Kije akwai inda zanje." Ya fad'a yana wucewa a hankali, da kallo ta bishi kafin ta shiga sam bata tunanin me zaiyi.

Inda suka bari ya koma ya tsaya, cikin sa'a yana zuwa kuma saurayin ya hau moto zai bar wurin shi da wani, bin bayansu ya shiga yi hankali kwance har ya aje wanda ya d'auko a wani shago yayi gaba, ya shiga layin gidansu kenan yayi gaggawar shiga gabanshi, tsaya yayi da sauri yana kallon motar, bud'ewa yayi ya fito da k'arfi cikin tako mai ban tsoro ya nufi kanshi, shi kam gabanshi ne ya shiga fad'uwa dan yasan akwai matsala, wanda yasa aka daka ne ya dawo d'aukar fansa, gashi shi kad'ai a wurin kuma ko ihu yayi ba za'a iya jinshi a gidansu ba, jiki na rawa ya shiga k'ok'arin sauka daga kan moton.

Bai bari ya gama sauka ba, bai bashi damar sauka ba ko da kare kanshi ne yayi, da iya k'arfin da yake da shi ya gabza mishi wani k'ulli a baki, rikicaaaa sukayi shi da moton duk suka fad'i b'angaren hagu, moton ne ya taushe k'afarshi hakan yasa shi kiciniyar jawo k'afar, k'afa yasa ya take moton yasa hannu ya jawo madubin moton da k'arfi, yana cire shi ya gaud'a mishi a fuska a take jini ya sake gabce mishi, shak'o wuyanshi yayi ya kalli idonshi yace "Wai kai ga sakarai, a madadin ka fuskance ni ka rama dukanka, sai ka zagaya ka turawa d'an uwana yara suka dake shi."

Sauda ya gaura masa mari yace "Shine har da sawa suka karya mishi hannu."

Hannu ya d'aga zai sake marinshi yayi saurin tara hannu yana fad'in "Yi hak'uri, yi hak'uri dan Allah, bansan d'an uwanka bane."

A hankali yace "To ka sani daga yau, ni dashi tare muka fito duniya, sannan ina jiranka ka sake aiko min yara yanzu."

Dungurar dashi yayi ya juya ya koma mota, saida ya bad'a mishi k'ura ya bar wurin hankali kwance, yanzu kad'ai yaji sakayau daya ramawa d'an uwanshi, shi fa bai son abinda zai tab'a mishi Amar, waccen lokacin ma yayi shiru ne dan baisan mutumin ba.

Shi ma saida aka d'aukeshi daga nan akayi asibiti, sai dai al'amarin yayi k'amari sosai, mahaifinshi ranshi ya b'ace sosai ya kuma ce ba zai yarda ba, sai sunyi k'arar shi tunda dai akwai mahukunta a gari, da yake shima d'an dangi ne kuma akwai masu abun hannu sai fa kowa ya goyi da bayan haka, dan haka suka jiran gari ya waye yaji sammaci.
Chapter 189 · 0% Book details