← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 198

Sashe 52

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallon mamaki da kuma yaushe yarinyar nan ta haukace yake mata? Me take nufi? Sameera ce ma take kira haka babu sakayawa? Saida ya d'an ja baya sosai ya k'are mata kallo yace "Ke! Yaushe aka haifeki?"

Sai kuwa Harira ta sake juya ido ba tace komai ba, dan haka yace "To ki koma ki tambaya dan kisan shekarunki da nawa ba d'aya bane, ki shiga hankalinki tun wuri, dan ruwa ba sa'an kwando bane, idan kuma baki ji ba, u wil regret it, that's my last warning."

Juyawa yayi a sukwane ya shige part d'in ya barta nan, tab'e baki tayi ta juya tace "Can ka k'arata da turancinka, ni inda zaka dinga min magana ma da turancin da zanfi jin dad'i."

Raihan na kwance d'aki sun gama waya da mahaifiyarta, har zata kwanta dai kuma saita turawa Abdul sak'o tana tambayar ya hannunshi? Ko ba komai yaji dad'in tambayar dan hakan na nuna ta damu dashi ne, amsa mata yayi da sauk'i, Allah ya k'ara afuwa shine abinda ta fad'a ta aje wayar ta kwanta abinta.

*Washe gari* da sassafe duk yaran sun shirya suna kan dinning suna jiran isowar Dadynsu, Abbas kuma na shiryawa ya fito falonshi da niyyar fita, yanzu ma wa zai gani sai Harira wacce tunda Sameera tace mata duk aikin da zatayi b sai ya kaita ga shiga sashin Abbas ba take jin haushi, wato a lokacin da suna matsayin ma'aikata ai ita ce ma ke kula da sashin shi, kenan ita ma tana tsoron a k'wace mata miji kamar yanda ta k'wace ma Salma, dan haka yau saida ta gama kimtsa yaran da ba zasu iya shirya kansu ba ta shiga falon nashi da k'ofar ke bud'e ta falon Sameera, babu wani abu da d'akin ke buk'ata amma haka ta zage tana goge goge tana karkad'a jikinta sosai cikin doguwar rigar wani tattausan less bayan ta cab'a ado.

Saida Abbas ya rintse idonshi dan yanda k'ugunta ke rausayawa abin tayar da hankali ne, gashi har shatin mazaunin pant d'inta yana hange daga inda yake, haushi da takaici ne suka sashi daka mata tsawa yace "Ke!"

Harira da tuni tasan da fitowarshi shiru kawai tayi a tsora ce ta juyo juyo tana saki wata k'ara duk da muryar ba siririya bace da zatayi dad'in sauraro, ba kwalliyar fuskarta ce ta sake shiga madubin idonshi ba sai k'irjinta da rigar ta matseshi sosai yayi sama kamar zasu fito, tabbas mata bala'i ne, dan k'arfin da yaji lokacin daya mata tsawar nan tana juyowa sai yaji ya rasa kuzarin, wani bala'in sanyi ne yaji hannunshi sun mishi ya kasa d'aga su, da k'yar ya iya tattaro jarumtarshi yace "Lafiya? Meya kawo ki part d'ina?"

Sunkuyawa tayi tace "Ina kwana? Kayi hak'uri yallab'ai, na zo gyara..." Bai bari ta k'arasa ba yace "Kije bana so, kuma daga yau kar na sake ganinki sashi na."

Sunkuyawa tayi alamar to kafin ta nufo shi, hakan yasa ya bud'e ido yana kallonta ya ga me zatayi, kan k'aramin teburin ne ta aje k'aramar wayarta da man goge madubi, duk'awa tayi zata d'auka ta d'ago kai taga ko yana kallonta, ganin ya kawar da kanshi yasa tace "Yallab'ai na kawo maka abincin ka nan ne?"

Kallonta yayi zaiyi magana kuma sai yayi shiru saboda abinda ya gani, haka dai ta k'arasa kwarkwasarta ta fita ta barshi, tsaki yayi a ranshi yana fad'in "Dole ma ta kori yarinyar nan wallahi, ba zan iya ba haka kawai."

Falon Sameera ya shiga kai tsaye d'akin ta ya nufa da niyyar sauke mata bala'in da yarinyar can ke son d'ora masa, amma abun takaici saida ya kai daf da d'akin ya tuna rigimammiyar bata gari, a ranshi yace "Bata kira ni ba, nima kuma ban kirata ba, hmmm."

Juyawa yayi yana fad'in Allah ya sota da rahamar da sai ya tara mata uwar gajiya, daf da d'akin da Ma'arufa take ya tsaya saboda tuna akwai bak'uwa a gidan, tunani yake ko tana nan? Ko kuma tana wajen cin abinci? K'wank'wasa k'ofar yayi hakan yasa Ma'arufa dake shirin saka kaya tace "Ina zuwa."

A hankali ta lallab'o ta lek'o ta hudar dake jikin k'ofar kamar yanda sauran k'ofofin suke, saida ta dafe k'irji ta zaro ido ta fara tunanin abinyi, gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta yanke mata yasa ta wangale k'ofar d'akin tana fad'in "Lil sis ke..."

Shiru tayi da mamaki na k'arya a fuskarta na ganinshi tsaye, da sauri ya kawar da kanshi gabanshi na dukan uku uku, bai tab'a ganin matar da ba halalinshi ba daga ita sai d'aurin k'irji na towel, yau gashi ya gani da idonshi, kana gani kasan hasken mai ne dan har k'arnin mai take, amma santala santalan cinyoyin masu d'aukar hankali ne, k'arin gashin da tayi wanda ya saje kamar gashinta ya kwanta bayanta, bai sake kallonta ba illa fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un da yake yi."

Ita kuma babu d'ar ko kunya a tare da ita sai sunkuyar da kai da tayi tace "Good morning sir, na yi tunanin lil sis ce, dan tun jiya ita ke kawo min ziyar."

Ba tare daya kalli wajen da take ba yace "Ya k'afar taki? Ki fito ki ci abinci."

Yana fad'a kuma bai tsaya jin me za tace ba ya fice da sauri, farfajiyar gidan ya fita kamar zai shiga motarshi kuma saiya tsaya, tambaya yake wa kansa me yake faruwa dashi haka yau? Sai ganin matan da babu komai tsakaninshi da su yake, Allah ya sani yanzu ya zama mai yawan buk'ata, gashi duk sun saka shi ya d'auki caji kuma maganin warakar bata nan, wayarshi ya fito da ita ya danna mata kira, a daidai lokacin daya kira Sameera kuma tana daf da shiga gidan waziri, tana ganin kiran ta tsaya ta d'auka, muryarshi babu alamar wasa taji yace "Ki bar duk abinda kike ki dawo yau d'in nan."

Take ya kashe wayar dan kar ma ta samu damar yi masa gardama, ita kuma da farko ta d'auka rarrashinta zaiyi yace ta dawo, amma sai taji yace wai ta dawo yau d'in nan, mayar da wayar tayi a jaka ta shiga gidan da sallama, ba mutane a gidan sai matar kawai a tsakar gida, amsawa tayi tare da d'agowa, tana ganinta gabanta ya fad'i dan tasan ba alkairi ya kawota ba, mik'ewa tayi daga zaman da take cikin sanyin jiki tace "Hajia ke ce? Sannu da zuwa, shigo ciki."

K'arasowa Sameera tayi cikin wata shegiyar tafiya, d'an takawa matar tayi tana fad'in "Bari na kawo miki..."

Bata fad'a ba taji Sameera ta jawo hannunta ta dawo da ita baya, kallon juna sukayi inda Sameera tace "Da alama ba sai na fad'a miki wacece ni ba? Rabuwar mu ta jiya ba tayi dad'i ba, a dalilinki mahaifina ya tafi gida da b'acin rai, a sanadiyarki mahaifina ya kasa aiwatar da abinda yayi niyya, a dalilinki jiya na kwana da ciwon kai, a dai dalilinki ne na kwana nesa da yara na ba kuma tare da mahaifinsu ba, shin kina ganin idan ban kawo miki ziyara ba nayi daidai?"

Cikin rashin gaskiya ta kalleta tace "Eh...to. Hajia duk me..ya kawo wannan..maganar kuma?"

Tassssss, saukar mari kawai matar taji, take ta dafe kuncinta ta durk'ushe a wurin kanta k'asa, Sameera kuma nuna ta tayi da yatsa dan matar ba wani finta shekaru tayi ba tace " Ki rubuta ki aje, bana sakin rigima cikin sauk'i, wannan marin tun jiya na so na miki shi, amma mijina bai bani dama ba, idan waziri ya zo kya gaishe min dashi, idan kuma kin shirya d'aukar fansa sai ki sanar dashi ya shirya miki bataliya guda wacce zata d'aukar miki fansar."

Tana gama fad'a ta juya ta fita a gidan hankali kwance, mik'ewa matar tayi tana mamakin k'arfin halin Sameera, amma kuma kamar yanda tace ba shakka zata d'auki fansa ko da ba a kanta bane, tasan shirin da suke da shi a k'asa dole zai gigita duk wani makusancin sarki da ma iyalinshi, dan haka tayi k'wafa ta shiga harkar gabanta ba tare da tunanin fad'awa ko da wazirin ba bare wani, ita kuma tana fita daga nan masarauta ta shiga, a cikin fada aka basu wuri ita da Imran suka tattauna akan maganar aurenshi, ta jima suna hira tana bashi shawarwari kafin ta mishi sallama ta fito, tana dawowa tamasal ta fara had'a nata kayan dana Abbas dan shi ma bai d'auki komai ba, amma kuma sai kawu Bakura ya dinga nemanta da shawara kan bikin Husna, a k'arshe dai saida suka tafi da *Jebu* da kuma Husna ta zab'i kayan da take so kafin suka dawo, sai bayan sallah la'asar ta shirya ta zo airport inda ta samu tunda sukayi waya da Abbas ya turo da jirgin da zai d'auke ta, tana shiga suna kimtsa suka lula sai Abuja kuma.
Chapter 52 · 0% Book details