← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 198

Sashe 131

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ya kalli Salma ya mata alamar ta basu wuri kafin ya gyara tsayuwa yace "Lafiya ba lafiya ba Junaid, wata alfarma na zo nema a wajenka."

_*Anzo wajen, Sani dai d'an Innusa ne yayan Alhaji, wanda yace baya buk'atar taimako ko alfarmar Alhaji Suley, dalilinshi yasa Hajia dagewa ta ga yaranta sun zama masu muk'ami a gwamnatacce, meya faru yau da har aka zo neman alfarma a wajen ahalin Suley?*_

Junaid ne yace "Tonton wace irin alfarma kuma? Ai daka kirani a waya sai naje har gidan ma."

Murmushin jin dad'i yayi yace "A'a ba sai ta kai ga haka ba, dama akan maganar makarantar yer uwarka Salma ne?"

Saida ya kalli inda take tsaye da uniforme d'inta yace "Wani abu ne ya faru?"

Cike da damuwa yace "Kasan dai yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi hali ba, tana tare da k'awaye ne da basa jin magana wanda yasa sukayi rashin kunya wa malaminsu, hakan yasa aka koresu tare da tab'a musu conduite (bansan me zan kirashi da turanci ba), yanzu tsawon sati d'aya kenan muna ta bibiya da bayar da hak'uri dan a gyara ta koma, amma abun ya ci tura wallahi, shine sai jiya malamin yace idan akwai wani babba ko malamin da muka sani mu mishi magana, shiyasa na tuntub'e ka dan kasa baki dan Allah ta koma."

Ajiyar zuciya ya sauke, zai so ya taimaka musu sai dai kuma yaji Hajia tace duk wanda d'aya daga cikin iyalin Innusa ya neme shi taimako ya fara fad'a mata kafin yayi, bai nuna masa komai ba sai cewa da yayi ba komai zaiji da matsalar, godiya ya masa suka koma suka tafi, shi ma aji ya koma da tunanin yanda zaiyi, shin ya fara fad'a mata ne ko kuma kawai yayi? Da wannan tunanin ya kammala ya dawo gida, da rana tsaka ya tarar da tashin hankalin da baiyi tsammani ba.

Yaran gidan na wasa tare da Huda wacce ita kanta bata cika sakewa ba idan tana cikin yaran, Hajia na fitowa ta gansu sai kawai ta musu tsawa tace "Kai, maza ku wuce ciki, karna sake ganinku da yarinyar nan dan matsatinku da nata ba d'aya bane, kuji ni ko."

Kai suka d'aga mata alamar eh suka shiga ciki, wannan magana data fad'a a kunnen Maryama wacce ita ma ta fito kiran Huda dan bata so tana shiga cikinsu, tana jin haka ta matso tace "Da me suka fita Hajia? Kina babba kike fad'in maganar nan a gaban yara, ina ce dai nan daga jikokinki sai jikokin Hajiarsu Jibril, ko ita ma jikokinta basa da damar yin wasa a gidan nan ne?"

Su Zeinabu dake zaune suna gyara kayan da zasuyi girkin dare dashi ne suka kalleta, Husseina ma dake gefensu tana b'are musu tafarnuwa ce ta kalleta, Hajia ce tace "Suna da dama, amma dai banda wannan 'yar taki."

Wani kallo ta mata tace "Saboda me? Saboda ita ba jikarta bace? Na ga ita ma daga tsatsonta ta fito, dan haka ki barta ta wala a gidan ubanta." Ta k'arashe cikin d'aga murya.

Mik'ewa Husseina tayi ta matso kusanta da mamaki tana kallonta tace "Me kike nufi Maryama? Tsatsona daga ina?"

Cikin d'aga murya tace "Eh tsatsonki, ki tambayi Jibril zai fad'a miki yanda akayi haka ta faru."

Kallon Hajia tayi tace "Ba kina ganin karuwa ce ni ba, to d'an gidan nan ne ya mayar dani karuwa, shi ya bani lasisin zama abinda na zama, dan haka shima yana da kamashon duk abinda na aikata, nima da fari 'ya ce kamar kowa, Jibril ne ya tirsasni har na samu yar da ban haifeta a gidan aure ba."

Hajia data kafeta da ido sai kawai ta tintsire da dariya har da d'an rik'e ciki, kallonta kowa keyi da mamakin abinda take ma dariyar, Husseina kuma k'asa tayi da kanta dan tasan ita take ma dariyar sai Inna lillahi da take maimaitawa, Soueiba taso tashi tsaye amma jikinta taji yana rawa rawa sai kawai ta damk'e kujerar da take zaune tana kalmar shahada, a hankali ta kai idonta kan Huda a lokacin ita ma tana kallonta saboda jin tana kalmar shahada, ido cikin ido suka kalli juna ita da yarinyar, ba za tace tana k'in yarinyar ba, sai dai tunaninta ya akayi Jibril ya musu haka. Hajia dake dariyar nan ce ta kalli Husseina tace "Kin gani, illar karuwanci kenan, ke kinyi gashi kuma har yanzu bai daina bibiyarku ba, kin haifeshi a yawon dandi, yayi k'ok'ari shi ya haifi nashi yaran a aure, amma gashi jikanki ya kawo miki yar dakan kuka."

Cike da shak'iyanci ta sunkuya tace "Ina miki barka da k'ara samun k'aruwa."

Wata dariyar ta kece da ita ta juya zata tafi sai kuma ta kalli Maryama tace "Ni ban ma yara da jikokina irin wannan tarbiyyar ba, in dai har kinga d'an gaba da fatiha a ahalin nan to ki tabbatar daga wani k'ugun ya fito amma ba tsatson Zeeya'atu ba, can ku k'arata da matsalarku."

Tana fad'a ta juya ta bar wurin, Maryama ma ta kama hannun Huda zasu juya ta ga Junaid, kallon kallo akayi inda yake binta da wani kallo mai wuyar fassarawa, girgiza kai yayi yace "Ban tab'a kawo haka ba Maryama, zuciya d'aya nake sonki kuma nake zaune dake, ashe Huda yar d'an uwana ce baki tab'a fad'a min ba? Nagode da abinda kika min, amma a gaskiya aurenki ya fice a raina, sam ba zan iya ci gaba da zama dake ba, kawai kije na sakeki."

Tab'e baki tayi tace "Nima ban nemi takardata a wajenka bane dan karka tambayeni dalili, amma ka sani auren gidanka ya jima da fice min a rai, shiyasa ban bari ma na samu ciki da kai ba bare na haihu, hakan zaisa iyaye su dinga tausata da cewa nayi zaman 'ya' ya, ni kuma bana d'aya daga cikin matan da bak'in cikin namiji zai kashe su."

Tana gama fad'a ta kama hannun Huda suka nufi inda Soueiba ke zaune, tura mata ita tayi gabanta tace "Zan koma gidan iyayena nima, nan kuma gidan ubanta ne ta zauna tare da ku, ruwanku ne ku bata guba ta ci ko ku taushe mata kai da matashi har ta daina numfashi, ni dai na sadata daku na huta da bata amsar cewa zai kaita wajen yan uwanta ita ma."

Juyawa tayi ta koma b'angarenta, cikin sauri da kuka da bata san ko na miye ba ta had'a kayanta ta bar gidan ko Huda bata san fitar ta, Zeinabu da surutu ke ciciyarta kai tsaye b'angaren Jamila ta nufa wacce a lokacin ke jin ciwon baya shiyasa ko gaishesu bata zo ba yau, tana shiga ta same ta zaune k'asan carpet ta mik'e k'afafu, ba tsayawa ko tunanin wani abu kawai daga tsaye tana kallonta tace "Ke Jamila, ashe Jibril d'an iska ne shima shiyasa Hajia ta had'aki da shi, yanzu gashi nan asiri ya tonu wannan yarinyar Huda 'yar shi ce."

Kamar ta k'ara sara mata guduma a tsakar baya, sai kawai tayi wani zullo kamar an fizgota tare da dafe baya ta kwamtsa salati ido rufe ruf, hannu ta fara yarfawa tana fad'in "Inna lillahi wa'innailaihi raju'un, la'ilaha illalah, Mama bayana, wayyo Allahana Mama, bayana Mama zan mutu, wayyo Mama..."

A rikice ta fita ta nemo taimako, Soueiba ce tayi k'arfin halin kiran Jibril ya zo a matuk'ar gigice, ganin halin data shiga jikinta sai rawa yake yasa shi lailayarta a hannu ya nufi mota da ita, a baya suka biyoshi da kayan haihuwarta aka nufi likita, Ammar na asibiti a lokacin aka kawota, ko da aka shiga da ita aka ga jininta ya hau ga kuma borin gishiri ta yanda ba zata iya haihuwa da kanta ba yasa docteur d'in cewa kawai a mata aiki, Jibril na kuka yace Ammar dan Allah yasa a dubata ta haihu ba sai an fasata ba, kwantar mishi da hankali yayi tare da umartarshi yasa hannu, yana saka hannu docteur d'in ya shiga d'akin tiyata (tun kafin a bud'a mère et enfants), cikin hukuncin ubangiji saiga santalelen yaro an fito mata dashi sak ubanshi, amma fa uta saida akayi da k'yar aka ceto ta kafin aka shiga bata kulawa, d'akin sama aka kaita tare da hana kowa shiga dan ta huta, a lokacin Jibril da Soueiba suna k'asa ne ta kalleshi da yanayin ka ban mamaki tace "Jibril ashe yaudararmu kake yi, ban tab'a tunanin haka daga gareka ba wallahi, sai ga yarinyar 'yar shekara bakwai wai a matsayin 'yarka."

Jim yayi kanshi k'asa cike da kunya, ya jima haka kafin yace "Kiyi hak'uri Mama, tsautsayi ne da shar..."

Da sauri tace "Sharrin shaid'an ko? Nasan abinda zaka fad'a kenan, wai duk uban daya tsula tsiyarshi a k'arshe sai yace maka sharrin shaid'an, kai yanzu kasan kammaninshi ne?"

Jin yayi shiru yasa tace "Shikenan, yanzu ai ba fad'a zamu maka ba tunda na banza ne, kawai saimu rumgumi k'addarar a yanda ta zo mana."

Cike da son nad'e tabarmar kunyarshi yace "Ko akwai abinda ake buk'ata yanzu?"

Cikin sanyi tace "Akwai mana." Zana mishi tayi duk abinda buk'ata ya tafi zuciyarshi a cunkushe babu dad'i, saida ya kawo komai da ake buk'ata har lokacin Jamila na d'akin hutu ita kad'ai ya juya ya koma, bai zame ko ina ba sai gidan malam Rabi'u, fitowa yayi a soron gidan suka zauna kan tabarma, cikin mutumci suka gaisa kafin Jibril yace "Malam nine mahaifin Huda, maganar gaskiya sanda abinda ya faru har ya faru bansan yer uwata bace, saida nasan waye kakana saina tabbatar da cewa ashe *dara ce ta ci gida*."

Kallonshi yayi da mamaki, Huda yar shi ce dama? Nunfasawa yayi yace "Ikon Allah, 'yarka ce dama? To ya zaayi sai hak'uri ai komai ya wuce, nima waccen d'in daya faru ina mai hak'uri ku yafe min, wallahi daga abinda ya faru yanzu nayi nadama."

Kallonshi kawai yayi bai tanka ba, malam d'in ne yace "Mahaifinka har yanzu bai zo ya ganni ba, nasan shima hushi yake dani kamar Husseina."

Kallonshi yayi yace "Hajia kam tana hushi da kai, amma Abba zai iya zuwa idan kana buk'atar hakan."

Kallonshi yayi yace "Idan ka min haka zan ji dad'i sosai."

Jinjina kai yayi yace "Ba komai zai zo."
Chapter 131 · 0% Book details