← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 198

Sashe 169

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Hannu ya d'aga kamar zai mareta yana fad'in "Dallah can malama, ni da nake so kiyi tashin hankali ki hana ni ko da shan iska."_

_Da k'arfi ta cakume shi ta kamkame jikinshi tana fad'in "Yi hak'uri yah Ammar, karka dake ni dan Allah, zanyi kishinka wallahi."_

_Dariya ya mata ya rumgumeta sosai a jikinshi, cikin muryar shagwab'a tace "Yah Ammar zani kishinka sosai, amma ba zan yarda na tayar maka da hankali ba saboda kishi, ni dai kawai so nake ka min alk'awarin ko da ka sake aure ba zaka wulak'anta ni ba."_

_Cikin laushin murya yace "Me yasa kike tunanin zan wulak'anta ki Amna?"_

_"Saboda ba ni ce zab'inka ba, kawai Hajia ce ta had'a mu."_

_Rumgume ta ya sake yi yace "Karki damu duniyata, ina sonki har zuciyata ba zan wulak'anta ki ba."_

Bud'a ido yayi ya tashi zaune duk k'ok'arinshi na son tare kanshi saida ya kasa ya fashe da kuka, wallahi a lokacin da za'a bashi zab'in rayuwa ko mutuwa daya bita shima su rayu acan, bansan taya zaiyi rayuwa bane yanzu babu ita, ita ke saukar dashi k'asa idan yayi samada k'arfin tsiya, an kai an kawo lokacin da Amna ko fita zaiyi waje saita gargad'e shi ya kiyaye abinda zai sa ranshi b'acewa, baiwar Allahn nan ta zab'i ya daketa ko da zai ji mata ciwo akan ya fita ranshi a b'ace yaja rigima, duk da ta kare shi ta kare mutumcin shi, to yanzu wa zai mishi wannan gatan? Wa zai bashi wannan kulawar? Ya rasa kenan har *abada*.

_*Allah ya jik'an duka mamatanmu ya gafarta musu, Allah ka kai rahama k'abarin iyayenmu mata har da ma mazan, mutuwa irin ta Amna Allah ka basu ladar shahada, Allah ka kyautata namu k'arshen.*_

*A gurguje*

Sanyi sosai kamar agogon da batirinsa ya k'are haka al'amarin ya zama a wajen Ammar da Hamna, shiru da zuba ido shi yafi yawa a cikin rayuwarsu ta yanzu, idon Hamna har sunyi fari fat tsabar yawan kuka da rashin saka kwalli, in dai har yaran zasu kewaye ta saita zubar da hawaye ta kuma aika mata da addu'a, kular da take basu kamar daga cikinta suka fito, a dalilinsu ta aje zuwa salon, tace bata da abinda ya kaisu bare ya kai daidai da su, idan ta tashi tun asuba tayi sallah, haka zata musu wanka ta shirya su cikin kayan makaranta, da kanta ta ke kaisu a motarta kuma taje ta d'aukosu, abinda suke son ci shi zata girka musu da kanta, idan na siyowa ne ta siyo musu da kud'inta, a tak'aice dai ta zama uwar yaran wacce ta haife su. *Ahmad* dama tanti Hadiza aka yanke shawara aka barwa ta tafi dashi, amma duk sati biyu sai Hamna ta tafi da yaran sun gano shi, wani lokacin har kwana suke a can kafin su dawo.

Girmanta ya k'aru a idonshi da kuma soyayyarta, yanda take d'awainiya da duka yaran yana birge shi sosai, ko Shureim bata da lokacinshi kamar su, hankalinshi kwance yake akan yaran, ko kud'in makarantarsu shi dai bata tambayarshi sai in anyi katarin ya ga takaradar a aljihun rigar Ameer sannan yaje ya kai da kanshi, sai dare idan ya dawo suke zuwa inda yake su sha hirarsu shi dasu su mishi kwaramniya, inda kowane giftawa nasu yana tuna mahaifiyarsu ne, hak'urinta akan yaran ya wuce misali, duk yaanda yaro zaiyi k'ololuwar rashin ji bakinta dashi sai dai tace "Wallahi zaneka zanyi."

Kuma ba.zata zanesu d'in ba, Allah sarki, yau gashi ta barsu zasu tashi da maraicin uwa, shi a ganinshi ma har da uban, dan uwar ita ce tasa ya zama uban, uban ma kamili da zai iya amsa sunan uban a gaban ko waye, to yau bata nan sai su kad'ai.

*Sanda* rayuwar ke tafiya a haka a lokacin kuma Hajia da Ummy da Husseina suka zaunar da Abba suka sanar dashi fa Shureim d'an Ammar ne, tunda yake a rayuwa bai tab'a jin an ci mutumcin shi an muzanta shi an wulak'anta shi irin na yau ba, wannan yafi k'arfin k'arya har da yaudara da cin amana, ta ruguza zumuncin dake tsakaninshi da d'an uwanshi, rainin wayon da rainin hammatar ma yayi yawa, haka a wannan rana ya ci fad'a ya gode Allah, yayi kamar zai dake ta abinda bai tab'a yi ba, a k'arshe kuma ya juya mata baya inda yace Ammar baida laifi sai ita.

*Kwana tashi* yau kimanin wata shida kenan da rasuwar Amna, inda kowa ya darrafe yayi hak'uri ya barwa Allah, yara sun tafi école (school) sun dawo ba ayi, suna d'aki tare da Hamna tana canza musu kaya, cikin farin ciki Ameera tace "Ummy."

"Na'am yar Ummy." Hamna ta amsa dashi, cike da yarinta tace "Yau tunda bamu école zaki kaimu wajen Abban mu?"

Da mamaki ta kalli fuskarta tace "Abbanku kuma? To ba yana gidan ba? Kuma jiya ba kunje wajensa da dare ba?"

Turo baki tayi "Ai Abba ne yace idan bamu karatu zai tafi damu yawo."

Shafa kanta tayi tace "To yanzu ai yana wajen aiki ko baby."

Mak'ale kafad'a tayi tace "To mu dai ki kaimu wajenshi ko ki kira shi ya zo ya d'auke mu."

Kallon fuskar yarinyar tayi sosai, d'an matse bakinta tayi a hankali saboda tunawa da tayi da mahaifiyarta, sauke numfashi tayi ta mata murmushi tace "Shikenan baby Ameera, a gama saka kayan sai mu tafi ko."

Cikin jin dad'i tayi dariya, ita ma murmushi ta sake mata ta k'arasa shiryata, su Ameer ma k'arasa shiryasu tayi cikin shiga mai kyau, a tare suka fita ta nemi izinin Hajia sannan suka fita, tana shiga mota wayarta dake hannun Ameer yana game ta shiga ruri, mik'o mata yayi ta karb'a ta ga Hadiza ce, tana d'auka suka gaisa tace mata "Kina gida ne?"

"Eh Mama, lafiya?"

Daga b'angarenta tace "Lafiya lau, dama ina hanyar zuwa ne zan kawowa su Hajia Ahmad su ganshi, kullum sai sun kira ni sun tambaye shi."

Cikin farin ciki tace "Ummy Ahmad? Yanzu zaku taso ne? Nima ina son ganinshi wallahi."

"Wace tasowa kuma Hamna, yanzu haka fa ina cikin adaidaita har mun shigo layin gidan."

Fitowa tayi daga mota tana fad'in "Lah Mama, kinga kuwa da fita ne zamuyi, ku k'araso to."

K'ofar gidan ta fita inda yaran suka bita, ko da adaidaita ta aje ta yaran sukayi caa a kanta, tana kawo musu kayan motsa baki shiyasa ta gama siye zuk'atansu (yaron kenan), Hamna karb'ar Ahmad tayi tana ta sumbatar yaron tana kallonshi, masha Allah ya mulmuje sosai fuskarshi ta fito sak ta mahaifinshi, an shirya shi cikin riga da jeans na yara masu kyau ga takalmi gwanin sha'awa, kallon Mama tayi ta marairaice tace "Mama, yanzu haka wajen Abbansu ne suka matsa na kaisu, dan Allah ki barmu mu tafi dashi, nasan zaiji dad'i idan ya ganshi shima."

Zaro ido tayi tace "Hamna kina lafiya, daga zuwanmu ko ciki ban shiga dashi ba ki ce zaki tafi dashi?"

Cikin muryar rarrashi tace "Mama, wallahi ba jimawa zanyi ba, ina kaisu zan juyo na dawo, zai fita dasu ne kinga idan ya ga Ahmad ni sai na dawo tare dashi, dan Allah Mama."

Cike da gamsuwa ta kalleta cikin kashedi tace "To Hamna kamar yanda kika ce dan Allah karki jima, nasan zan sha k'orafi wajen Hajia da Sa'ada, amma zan yi yak'i indai akan wannan d'an gudaliyar ne."

Da farin ciki tace "Wallahi ba zan jima ba, mun gode Mama."

Tare suka shigo ita ta shiga mota tare da yaran, zaunar dashi tayi kan kujerar gaba tare da Ameera ta manna musu d'amarar jikin kujerar sannan suka bar gidan.

Ya gama ganin majinyatanshi yana zaune da wasu takardu yana dubawa aka k'wank'wasa k'ofar, yaran basu jira izini ba Abba ya tura duk suka shiga, saida suka gama shiga ya taso da farin cikin ganin yaran ya duk'a duk suka rumgume shi, cikin murna yace "Waya kawo ku ne?"

Kafin su bashi amsa ta zuro k'afarta d'auke da Ahmad, cikin sanyayar muryar tace "Assalama alaika."

D'ago kai yayi ya sauke tanfatsa tanfatsan idonshi akanta, tsayar dasu yayi ko su suka tsaya da kansu sani sai Allah, amma ta mugun tafiya dashi da imaninshi baki d'aya, mik'ewa yayi a hankali ba tare daya d'auke idon ba, saida ya gyara murya sannan yace "...

*Alhamdulillah* _Wallahi yau na gaji_
04/11/2020 à 14:38 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_65_

"Ke ma haka." Shine abinda ya fad'a yana k'are mata kallo, da sauri ya tako ya zo ya karb'i Ahmad a hannunta, rumgume shi yayi a jikinshi yana satar kallonta, da d'an mamaki yace "Mama ta zo kenan? Amma ya bata sanar dani ba? Kuma daga ina kuke?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Daga gida, sun ce na kawo su ne kace musu zaku fita."

Girgiza kai yayi yace "Halan Amna ce?"

Sak'e tayi ko da taji ya ambaci sunan, ita ta ma rasa dalilin da yasa shi sanya ma yarinyar sunanta, ba tace komai ba sai shi da yace "Ita ce bata da mantuwa ko kad'an."

Ita dai idonta na kan yaran dake ta k'iriniyarsu, shi ma damar sake kallonta ya samu, tayi kyau sosai cikin doguwar rigar atamfarta mai kalar maroon da ratsin orange da bak'i, mayafin d'an babba ne ta rufe duka k'afad'unta da shi, babu jaka ko waya a hannunta kamar yanda babu powder bare kwalli a idonta. Kallon idonta yayi yace "Zauna ko."

Ba tare data kae shi ba tace "Zan koma gida ne yanzu, Mama na jira na."

"Yau zasu koma ne?"

"Eh." Ta fad'a kanta a k'asa, d'aga gira yayi yace "To ki jira ni kad'an sai mu tafi tare, nima yanzu gidan zan tafi."
Chapter 169 · 0% Book details