← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 198

Sashe 2

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da k'arfi ya juyo ya k'ura mata ido, zuciyarshi ce ke bugawa da k'arfi yana ji kamar ya mata bugun mutuwa, saidai kuma abinda baiyi da k'uruciya ba shiyasa ba zai iya yi yanzu ba, haka ma baya so yayi magana ta hanyar bankad'o sirrin da yake ta rik'o a ranshi tsawon wannan shekarun, murmushi ya mata yace "Hum! Tabbas ba k'arya kika fad'a ba, ki sani nata karuwancin ne ya fito fili, na wasu kuma bai fito ba watak'ila talala ubangiji ya musu su gama gurza rashin mutumcinsu."

Yana fad'a ya sa kai ya fita dan fad'an su ba k'arewa yake ba, shiru tayi tare da tunanin me yake nufi da abinda ya fad'a, ta jima a haka tana wannan tunanin kafin ta d'auki gabjejiyar wayarta ta dannawa Amar kira, dan daga kallon kayan dake jikinta da yanayin shigarta da kwalliyar fuskarta zaka san tsohuwar wayayya ce ta gidan gaba, yana d'auka cikin sanyin murya tace "Jikalle kana ina? Ka fita?"

Cikin gatsali yace "Me kike so kuma yanzu? Ni bana gida."

Murmushi tayi har saida yaji sautinsa tace "Jikalle kuma guduna kake yanzu? Me ya sa kake haka?"

Cike da k'aguwa yace "Kinga Hajia, ni na fad'a miki bana gida, sai anjima."

Kashe wayar yayi ita kuma ta aje gefe tana kallon wayar tace "Allah yasa ba wajen wata shed'aniya kaje ba, amma idan ma da wani abu zan gano koma menene."

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Jibril ma yana fita bai jima ba ya dawo gida, fitowa yayi daga motarshi mai shegen kyau da tsada, cikin falon ya tunkara ya bi ta inda zai sadashi da d'akin baccin kakarshi, saman bene ya kalla inda hayaniyar yara ke tashi sunata wasa da guje guje, yana kusa da kaiwa ya tsaya cak saboda tuna wani abu daya riga ya zamar masa jiki, a hankali ya rintse idonshi yana kallon fuskar a hoton k'wak'walwarshi tare da tuna wasu maganganu da suke gigita tunaninshi, duk da idonshi rufe suke amma saida hawaye suke zubo mishi saboda tuna wasu maganganu na k'arshe da macen take cewa " *Idan fa ciki ya shiga jikina sakamakon hakan? Ya kake so nayi? Wai kai baka da imani ne?*"

Da sauri ya bud'a ido ya goge hawayenshi ya d'aga kai ya kalli sama yace "Allah ka kareta a duk inda take, Allah kasa bata samu ciki ba a dalilin wauta da mahaukaciyar sha'awata ta k'uruciya."

K'asa yayi da kanshi tare da fad'i a zuciyarshi "Ameen." Cikin sanyin jiki ya k'arasa k'ofar d'akin yayi sallama, amsa sallamar akayi daga cikin d'akin kuma harda muryar mahaifiyarshi, shiga yayi ya samu wuri ya zauna kusa da kakarshi yana fad'in "Mama sanunku, hira kuke ke da yar tsohuwa?"

Dukanshi Husseina tayi tace "Ubanka ne tsohon, ni matsa can ka bani wuri."

K'ara lafewa yayi a jikinta yace "Ina zan matsa ni da na zo miki da muhimmiyar magana."

Mahaifiyarshi mai sunan *Soueba* ce tace "A k'alla ka d'auki sama da wata d'aya kana fad'a min zamuyi magana amma ka kasa nutsuwa ka fad'a min."

Sosa kanshi yayi yace "Mama yau dai zan fad'a muku tunda na samu k'arfin gwiwa daga abinda Junaid yayi yau."

Zaro ido tayi tace "Kai duba ka kiyaye ni wallahi, kai ma rashin kunyar zakawa mutane? To babu ruwa na ni dai, Mama ku zama shaidata."

Murmushi Husseina tayi tace "To ki barshi ya fad'a mana muji me yake tafe da shi, fad'i ina jinka."

Kallonsu yayi dukansu yana murmushi kafin yace "Ni fa dama ina so na fad'a muku ne nima na samu matar aure."

Dogon tsaki Soueba tayi tace "Aikin banza, dama wannan maganar ce zaka fad'a."

Husseina ma dariya tayi tace "Wannan wacece haka zata kwashe min wannan rigimamman mijin?"

Nan ma k'asa yayi da kai cikin kunya ya kalli kakarshi ya jawo kanta yace "Zo na fad'a miki a kunne."

Cikin kunne ya rad'a mata ita kuma ta bud'e baki tace "Iyeee, to kai ai duk gida ne, ah gaskiya nayi farin ciki da jin hakan."

Soueba ta kalla tace "Kinji fa ke, tuwo na mai na za ayi, dan yace dai *Amna* (kamar k'anwa take gareshi saboda mahaifinta da mahaifinshi yayan wa ne da k'anwa, ma'ana ita jikar alhaji ce daya haifi ubanta, shi kuma jikan Husseina ne wacce suke ciki d'aya da alhajin) yake so."

Tashi yayi ya fita wai shi kunya yake ji, ita kanta Soueba taji dad'i daya kasance Amna ce yake so ba 'yar uwar haihuwarta ba *Hamna*, duk da ciki d'aya suka rayu kuma uwa d'aya ta haifesu, amma Hamna idonta a tsaye suke ga wayewa da kuma k'awaye masu ido bud'e, mahaifiyarsu *Hadiza* bata gidan yanzu shiyasa ba wani saka musu ido ake ba sosai, har ma gwara Ammar da basa shiri da ita shine ke ci mata uwa idan tayi ba daidai ba, dan akwaita da shegen yawo kullum ita ce a tafiye gidan sabuwar k'awa, musamman da mahaifinsu ya siya musu moto, ga yawan biki na k'awaye da sauran shagulgula, dan kowane wata akwai wacce zatayi bikin k'arin shekara ko kuma murnar samun wata jarabawa a makaranta, Hamna bata saka kayan kati sai atamfa, amma wani d'inkin da zaka gani a jikinta na atamfa har gwara riga yar kantin, domin kuwa bata saka kaya inba ji tayi sun kama jikinta ba sosai, bata saka zane sai siket ko doguwar riga, haka Hamna bata fita wajen biki ko wani shagali ba tare da tayi k'arin gashi na kanti ba, ko tayi kitso ko ta saka shi hakanan, indai ba sallah take ba ko zata tafi islamiyya to baka ganinta da hijab duk inda take ko zataje, yanzu haka sun shiga ajin lycée shekara biyu data wuce, rawar kanta da rashin kunyarta yasa basa shiri ko kad'an da Ammar, tana da rashin kunya da fitsara da mayar da martani, shi kuma baya d'auka hakan yasa yake mata dukan mutuwa inya samu dama, dan in mahaifiyarsu ko mahaifinsu na nan basa bari su ke d'aure mata gindi, domin kuwa a hannunsu suka tashi tun suna k'anana sosai, hatta filin sada zumunta na ahalin *Gaga* da aka bud'e akafar sadarwa ta WhatsApp Ammar fita yayi saboda Hamna kawai, saboda ko hira ake muryarta ce tafi ta kowa fitowa, ga tsokanar mutane wanda ya girmeta da wanda ta girma, ga yawon turo hotuna na sallama daban na barka da rana daban na barka da dare daban, shiyasa ranshi ya b'ace ya fita saboda haushinta yake ji sosai, duk abubuwan nan da Hamna ta had'a sab'aninsu ne ke ga Amna, dan ita ko magana ma bata cika son yi ba, ba tada kwarmniya ko kad'an, dan inma Hamna ta tsokaneta sai dai tayi banza da ita, to fa da wannan ne yasa ko murmushin Ammar baka gani a gidan, ga haushin hana shi aikin da yake so, ga takaicin rashin kunyar da Hamna ke mishi in tana cikin mutane.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Junaid na barin nan wajen masoyiyarshi ya nufa inda yasan zai iya ganinta, tun daga wajen masallacin ustaz Sani d'an jatau yake baza ido amma shiru harya k'arasa bakin *pacific*, wani lungu ya shiga da motar dan yasan suna zama nan ita da k'awar ta, amma rashin sa'a bai samu ganin ko d'aya daga ciki ba, kiran wayar k'awarta yayi dan Maryama bata d'aukan kiranshi tana ganin kamar yana takura mata, a lokacin sun fito daga cikin d'akinsu tana rufewa da d'an kwad'o kiran ya shigo, k'awar mai sunan *Iklima* ce ta kalleta tace "Mutuminki ne fa Mari, me zan ce mishi idan na d'auka?"

Masha Allah, tabbas Maryama mai kyau ce ta gidan gaba, ga ta doguwa sosai da d'an kumari, gashi fatarta jawur da ita duk da tana shafa mai amma kasan ita ma akwai asalin farinta, akan luma-luma kumatunta kuma wasu tsage ne suka k'awata fuskar har guda bibbiyu, a take tace "Kawai ki fad'a masa bama tare dake, kar ma ki fad'a masa na fita."

Zata d'auka kiran ya tsinke kuma sai baiyi gaggawar maidowa ba, hanyar gidansu ya nufo wanda ke bayan masallacin daya bari a farko, yana sake kira kuma Iklima ta d'auka tace "Barka da dare."

"Barka Hajia Iklima, ya kike?" Cikin sakin fuska ta amsa da "Lafiya lau, ya yau?"

Saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Yau da dama, ina mutuniyar take? Nasan kema kinsan bata d'aukar kirana."

Kallon Maryama tayi suna kan hanyar fitowa daga gida, kewayen wata mata Maryama ta lek'a ta same su zaune a d'an filin wurin suna kallon telbijin, matar ce ta kallesu tace "Mari fita zakiyi ne?"

"Eh maman *Husna*, ina *Huda* take ne?"

Da sauri wata yarinya da ba zata wuce shekaru biyar zuwa shida ba ta mik'e tsaye ta tunkarota, tana suwa ta rik'e hannunta tace "Mamma, yau ma fita zakiyi?"

Da murmushi ta shafa fuskarta tace "Fita zanyi Huda, amma yau ba zan jima ba zan dawo kinji."

Marairaicewa tayi ta k'ara matse hannunta tace "Mamma kullum haka kike cewa ba zaki jima ba, me ya sa ba zakiyi zamanki a gida ba?"

Ba annuri a fuskarta tace "Saboda saina fita muke samu mu ci abinci." Hannu tasa a jakarta ta fito da dala ashirin (ba zasu gaza naira ashirin ba), bata tayi tace "Gashi kije Aminu ki siyo madara kisha, idan kinji bacci kije lungunmu ki kwanta nayi shinfid'a."

Juyawa tayi zata fita taji ta rik'e hannunta, tana juyowa yarinyar tace "Mamma meyasa ke saida dare kike nemo mana abinci? Ki dinga zuwa da rana mana tunda baki komai a wannan lokacin."

A hankali ta zage hannunta daga na yarinyar ta sake juyawa, kamar saukar ruwan sama ta tsinci muryar Huda na cewa "Mamma kenan da gaske ke 'yar iska ce?"

Tsayawa tayi amma bata iya juyowa ba saboda hawayen da take, Iklima na ganin haka ta fice ta barta, da sauri ta taka ta barta nan ta fita, amma saboda wayo da kuma k'uruciya sai yarinyar ta fito da gudu har k'ofar gida tana kuka cikin d'aga murya tace "Ashe dama ban da uba, ni shegiya ce, to ni dai bana son neman abincin naki hakanan, daga yau ba zan sake cin abincinki ba idan kin kawo, kije kawai karma ki..."
Chapter 2 · 0% Book details