← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 198

Sashe 176

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai Ummy Abbana mijinki na shekaru barkatai, yau dan kin masa wani d'an laifi shine yana kallonki kika fice a gidan nan bai tsayar dake ba, Ummy ba wannan yafi damuna ba kamar yanda wai saida Hajia ta lallab'a sa tace ya dawo dake, wai Ummy kinga kuwa yanda take rok'onshi, humm ai ni abun ya mugun b'ata min rai wallahi, ji nake ina ma ace nine wallahi...hmmm shikenan dai Ummy sai anjima, zuciyata ma zafi take zan je nasha magani."

Ko da ya gama fad'a ya kashe kiran, Ummy da tunda ya fara magana take dariya ta riga data hango manufarshi, murmushi tayi tana kallon wayar tace "Ja'irin yaro nasan me kake nufi, zanyi yanda kake so dan nima raina ya b'ace."

Shima ko da suka gama wayar wanka ya shiga ya fito ya shirya cikin farar shadda, fita yayi hankali kwance yana istigfari da hailala a bakinshi har ya isa mak'abarta, a gaban k'abarin yake durk'ushe, kallon k'abarin yake inda abubuwa da dama ne ke zuwa mishi a kanshi, na farko akwai wa'azantarwa a game da lamarin mutuwa, sannan rayuwarshi da ita tarihi ya kafu wanda babu abinda zai iya goge shi, addu'a ya shiga kwaranya mata kamar saukar ruwan sama, ya d'auki tsawon lokaci kafin ya shiga gabatar da addu'a ta duka musulmin dake kwance, tare da addua'r Allah ya kyautata nasu k'arshen yasa mu cika da imani, awa d'aya da rabi ya d'auka a mak'abartar kafin ya juya ya tafi cike da kewar ma'abociya aminci da salamarshi. Gida ya koma ya cire kayan nan ya saka wando iya gwiwa ya kwanta abinshi a falo.

Da safe d'aya daga cikin wanda suke zama tare yaje har gida ganinshi daya fad'a masa abinda ya faru dashi jiya, a k'ofar gida suke tsaye yana jajanta masa, shi dai kunya da takaici basu barshi ya fad'i abinda ya faru ba, saida abokin yayi shirin tafiyarshi sai yace "In tambayeka mana abokina?"

"Uhum! Ina ji." Cewar abokin yana kallonshi, gyara tsayuwa yayi yace "Dan Allah kasan yayan yarinyar nan Hamna?"

Kallonshi yayi yace "Hamna? Wacece hakanan?"

D'an tsaki yayi yace "Yarinyar nan mai salon mana ta kusan fada."

"Oho, na gane, wane daga cikin yayanta? Kasan fa yar gidansu Jibril ce."

"Yayanta ne shi?"

Cikin rashin tabbas yace "Eh to ban sani ba gaskiya, kasan yawa ne da mutanen."

"To kasan Ammar?" Shi ma ya fad'i hakane saboda yaji sunan daga bakin Hamna sanda tace ka k'aleshi Ammar, cikin rashin kulawa yace "Ina jin sunanshi dai a gari."

"To baka san wani wanda ya san shi ba?"

Cikin kallon rashin fahimta yace "Akwai Jibril, d'an uwansa ne, amma me yasa kake nemanshi?"

"Ba ruwanka, kayi k'ok'ari ka samo min da hoton shi kawai."

Yanda yayi maganar zaka san ba lafiya ba dan haka yace "Ka fad'amin mana me ke faruwa?"

"Ba komai, in zaka samo min ka samo min, in kuma ba zaka iya ba ka bani lambar Jibril d'in."

Cikin damuwa yace "Haka kawai shi ba mace ba na zauna ina neman hoton fuskarshi, ba zan iya ba gaskiya, d'auki lambar Jibril d'in kai saika kirashi da kanka."

"Bani." Ya fad'a yana bud'a sécurité na wayarshi dan d'aukar lambar, yana juyawa ya tafi shi kuma yayi kiran Jibril, faran faran suka gaisa cikin sakin fuska, saida Jibril yace ban gane ba sannan yace "Eh ba zaka gani ne ba, abokin Ammar ne ni, dan Allah inba damuwa fotonshi nake so ka turo min, shi ya k'i turo min ne dana tambaye shi."

Ko alama Jibril baiyi mamaki ba ko tunanin wani abu daban, abinda ya sani kawai shine watak'ila Ammar zai raina masa hankali da fuskokinsu biyu shi da Amar, dan haka sai yace "Ba damuwa, yana son yi maka iskanci kenan ka rasa gane shi."

Da farin ciki yace "Yawwa nagode sosai."

"Ba komai." Ya fad'a shima sukayi sallama, lambarsa ya shigar a wayarsa kafin ya tura masa hoton Ammar d'in na ranar d'aurin aurensu, ko da yaga hoton ya k'are masa kallo yace "Duk yanda akayi wannan soja ne, dan dukanshi ma bana wasa bane, amma zan rama an dad'e ba'a yi sama aka durmiyo k'asa ba."

*Da yamma* Abba suka shiga garin kai tsaye gidan k'anwar mahaifiyarta *Ardayi* suka wuce dan yasan can zata nufa, matar akwai karamci da sanin takamata, dan kamar yanda a gida suke ganin laifin lieutenant ita kuma laifin Ummy take gani, dan Ummy bata b'oye mata komai ba, yanzu ma da suka zo cewa tayi bata ji dad'i ba daya k'yaleta ta zauna gidan har ta gasu, faran faran suka gaisa ta kuma jadadda mishi hak'uri da kanta tare da cewa yarinta ce😂, lieutenant kanshi saida yayi dariya, ciki ta shiga ta kira Ummy ita kuma ta shiga had'a mata kayanta dan su wuce duk sanda suke so.

Tun kafin ta k'araso inda yake zaune kan kujera ta basar ta had'e fuska irin ba wasan nan, tana zuwa ko zaune ba tayi ba ta tara masa hannu, 😂 (Allah gamu gare ka) d'aga kai yayi ya kalleta da mamaki, mayar da kanshi yayi k'asa bai tanka mata ba, cikin jujjuya baki tace "Kai nake jira."

D'aga kai ya sake yi ya kalleta, ba alamar wasa shi ma yace "Baki iya sallama bane?"

Saida ta turo baki tace "Ina wuni."

"Ba wannan na tambayeki ba ai."

Kallonshi tayi sai kuma ta juya baya ta rik'e k'ugu ta sake mik'a hannunta tace "Ka bani na juya na koma ina da abun yi a ciki."

Kallon nutsuwa ya mata yace "Me zan baki wai? Kin bani ajiya ne?"

Juyowa tayi da mamaki tace "Ban gane me zaka bani ba? Takarda ta mana."

Da sauri ya kalli idonta yace "Kinga Sa'ada ba wasa na zo muyi ba, ki d'auko kayanki ki wuce mu tafi, komai dare ina so mu bar garin nan."

Wani yamutsa fuska tayi tana kallonshi tace "Ai ba haka mukayi da kai ba, ko ka manta?"

Kallonta yayi sai kawai ta ma bashi dariya ganin har wani girgiza take wai ita rashin mutumci take so ayi, mik'ewa yayi ya tsaya gabanta yana k'are mata kallo yace "Jaraba kike so muyi Sa'ada?"

Saida ta rage girman idonta tace "Eh, ai gidanmu ne nan ina da masu tsaya min."

Ba alamar annuri yace "To ni kuma kinga a gidan naku zan kakkarya ki kuma a gode min akan haka, amma bana so a k'ara miki wani dukan bayan wanda zan miki, dan haka in bala'in kike ji muje gida sai ayi."

Matsawa tayi baya tana fad'in "A'a me zai kaini gidanku, ni na zo gidanmu kenan ai da kake gani na nan, da kaga na fita to..."

Shiru tayi tana k'yabta ido dan bakinta yake kallo kamar jiran yaji me zata fad'a yake, saida ya kawar da kanshi yace "Ki d'auko jakarki mu tafi, in kuma ba zaki tafi ba ki gaya min."

Saida ta juya d'an k'aramin bakinta mai d'an tsayi kafin tace "Eh."

Da kyau ya kalleta yace "Eh me?"

Saida taja baya sosai ta saita k'afafunta k'ofar shiga cikin d'akin Ardayi sannan tace "Ba zan tafi ba."

Da sauri ta k'arasa shigewa ciki tana ma kanta dariya, da kallo ya bita yace "Eh lallai yarinta ce kamar yanda Hajia suka fad'a."

Fita yayi ya samu dreba suka k'arasa wani masauki mai kyau a garin suka yada zango anan, dan ya lura wannan bikon mai tsada ne na gaske, watak'ila saiya salwantar da wasu zinariya kafin ta yarda su koma, tunda dai ba zai yarda yayi tafiyar banza ba, uwa uba kuma umarnin gwamnatinshi ce dole a cika ko ba'a so.

Saida akayi sallah magrib yayi wanka yana kwance ya d'auki wayarshi ya tura mata gajeran sak'o kamar haka "Uwar Ammar ce quoi t'on problème? Qu'est ce que tu veux?"

Sanda ta samu sak'on murmushi ta saki ta mayar masa da harufa hud'u tace "Rien."

Shi ma maido mata yayi da "In dai hakane to ki yarda mu koma gobe."

Maido masa tayi da "Indai hakane saika yarda zaka hau rak'umi a garinmu."

Zaro ido yayi yana k'ara nanata karantawa, maida mata yayi da "Amma ai na hau lokacin aurenmu, me zaisa yanzu na hau da girma na haka kawai."

Cikin basarwa tace "Shikenan sai ka koma inda ka fito kai kad'ai."

Ba alamar wasa a amon muryarshi yace "Kinsan Allah, wallahi tare dake zan koma, bari ganin fa ina lallab'a ki sa'a ce kika ci."

Wata dariya tayi kafin ta maido da " *Sa'ada, Sa'adatu sa'ar mata, ko bakiyi kyau ba kinyi sa'a*, ka daina fad'in sa'a a gabana sunanta gare ni."

Iko sai Rabba, da mamakin wannan sabon canjin dan shi dai bai santa da shi ba yace "Nima fa har yanzu ban huce kan abinda kikayi ba, dan kin samu na zo shine sai kin waina ni."

Kafin ta maido ya kirata a wayar dan ya tabbatar mata ta shirya gobe zasu koma, ko da ta d'auka tace "An zo wurin, ai dama an fad'a min ba da son ranka ka zo ba saboda ba so na kake ba dama, shiyasa nake so kawai ka bani takardata tunda banda mahimmanci a wurinka."

Cike da mamaki yace "Sa'ada ni? Ni ne kike fad'awa haka?"

"To ai gaskiya ce." Ta fad'a tana juya baki kamar a gabansa, cike da kokonto yace "Anya kuwa Sa'a baki yi waya da babban d'anki ba? Dan naga irin fitinarsa ke kike min yau d'in nan."

Kai tsaye tace "D'ana ba fitananne bane gaskiya kawai yake fad'a."

"Shikenan." Ya fad'a yana d'orawa da "Yanzu fad'a min abu d'aya, zaki shirya ko kuma ba zaki shirya ba, dan ba zan zauna ina lallab'aki ba sai kace wasu yara masu shirin aure."

Cikin muryar shagwab'a da kuka tace "Eh mana kace haka, idan kana tare dani sai ka nuna min mun girma mun tsufa muna da yara da jikoki, amma idan ka shiga d'aya d'akin saika d'anyance ka zama yaro kana kinibibi..."

Duk da ta kai k'arshen kalmar amma saida ta rufe baki, rarraba ido ta shiga yi tana saurarenshi yana fad'in "Ade nine kinibabben? Ba damuwa karki je d'in ki ci gaba da zama anan."
Chapter 176 · 0% Book details