Sashe 128
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushin ko dai bata da hankali ya mata yace "Mari ban miki musu ba cewa ina kallon Huda kamar 'yar dana haifa, amma ba hakan zaisa ki ce nine uban ta ba."
Ita ma murmushin ta masa tace "Karka damu Junaid, da sannu zaka san waye ubanta indai har kakar can taka tana sarar kiranta shegiya."
Bai kula da abinda ta fad'a ba kawai ya bar gidan, *da yamma* kuma Jibril ke samun labarin abinda ya faru wajen Husseina, hankalinshi ya tashi sosai, dan haka daya shiga b'angarensu saiya fara wucewa b'angaren ta, Huda dake zaune k'ofar shiga tana wasa yace ta kira mishi ita, bayan ta fito ne rai b'ace yace "Maryamaashe baki da hankali? Akan me zaki musu rashin kunya saboda kawai kina ganin kina da wani sirri a hannunki, to dan Allah in kin cika babbar karuwa kije ki fad'a, ki fad'a sai me? Huda 'yata ce kuma na yarda zan karb'eta, amma kisan wani d'aya shine nima gado nayi, kinsan ko a wurin wa?"
Wani kallo take binshi da shi kamar bata fahimtar abinda yake fad'a, murmushi yayi yace "A gurin kakana mana, ko kuma nace kakanmu ni dake wato malam Rabi'u."
Saida ya had'e fuska ya nuna ta yace "Idan kika bar min Huda anan to ki sani Labaran ma zai koma wajen nashi uban, tunda abun babu mutumci."
Sama da k'asa ya bita da harara ya nufi hanyar b'angarenshi yana fad'in "Yar iska kai duk ki d'aga hankalin mutane, to kaina farau shiga gonar da bata hallata gareka ba."
Da kallo ta bishi, malam Rabi'u, kuma Labaran? Yana nufin malam ne ya haifi mahaifinshi? Kai ia ba zai yiwu ba? Malam daya tsani zina, dalilin da yasa kenan bata nemi taimakonshi ba sanda tayi ciki, dan tasan zai iya kasheta ma da duka, sai yanzu a nuna mata babban mutum kuma uba ace d'anshi ne, to ta yaya? Da wannan tunanin ta koma ciki ba tare data gamsu da abinda ya fad'a ba.
Yamma lik'is Amna ta shigo b'angaren Hajia, kai tsaye wajen Husseina ta nufa, har d'aki ta sameta tace "Hajia dan Allah ba kiyi ajiyar yakuwa ba?"
Dariya ta mata tace "Uwar kwad'ayi, akwai amma busassa ce tana madafa."
"Yawwa, ina zuwa." Ta fad'a tana nufa madafa, tana zuwa ta samu Zeituna suna aiki, ko da ta fad'a mata abinda ta zo yi tace "A'a koma duniyar Ammar, ki bari zan d'ora miki ita a wuta."
Saida ta rumgumeta ciki da shagwab'a tace "Nagode uwarmu, Allah ya barki ke da ubanmu."
Da murmushi kawai ta bita ta fita, tana fita ta d'ora mata, kafin ta tafasa ta gyara kayan had'inta, Amna kuma jin an fara kiran sallah yasa tayi alwala a d'akin Husseina tayi sallah, tana idarwa ta cire hijabi ta mik'e da niyyar zuwa ta gyara, sai ga Zeituna ta shigo da wata roba mai kyau ta mik'a mata tace "To aci lafiya duniyar Ammar."
Dariya tayi tace "Kai aunty Zeituna kin dai rik'e wannan sunan ke ma."
"Kamar yanda kike rik'e sunan uwata ba." Ta fad'a da dariya, bud'a robar tayi tace "Lahh! Aunty Zeituna yanzu gyara min kikayi?"
"Mun gama aiki ne da madafar za'a rufe sai kawai na k'arasa miki." Tana fad'a ta juya tana fad'in "Na tafi nayi sallah nima."
"Nagode aunty Zeituna."
Murmushi kawai tayi ta fita, ta zauna ta d'iba ta kai bakinta, wani masifar dad'i taji kamar zata tsinka harshenta ko yawu zasu dalolo mata, hannu tasa zata k'ara kaiwa Ammar ya shigo da sallama d'akin Husseina, Husseina data sallame ce ta amsa tare da Amna, yana k'arasa shigowa ta bud'e mishi hannu d'aya alamar ya rumgumeta, sunkuyowa yayi ya rumgumeta tare da manna mata suma a baki yana kallon kwanon hannunta, Husseina ya kalla yace "Hajajju anwuni lafiya?"
"Lafiya lau, har an sauko?" Ta fad'a da raha, bai iya amsa mata ba sai Amna da yace ma "Menene kike ci da yasa kika baro can?"
Shagwab'e fuska tayi tace "Duniyata yakuwa?"
Zaro ido yayi yace "Ya me?"
Baki sake ta sake cewa "Yakuwa."
Da k'arfi yasa hannu ya fizge robar yace "Ubaki ma, Allah baki cinta sai kace wata mayya, kina da k'aramin cikin ne zaki ci wannan abun."
Cikin kuka ta tara mishi hannu tace "Dan Allah yah Ammar taimaka ka ban kar yawuna su k'are."
"Sun jima basu k'afe ba, Allah ba zan baki ba."
Kallon Husseina tayi tace "Dan Allah Hajia ki ce ya bani, ina so na ci."
Da sauri ya fito da waya daga aljihu kawai ya d'ora a kunne ya juya zai fita yana fad'in "Hello, Hello, kai bana jinka."
Tsaf ya fice dan kar Husseina ma tayi magana, dariya ta mata tace "Kin gani ko, dan haka ki hak'ura kawai."
Girgiza kai tayi tace "Je ne peux pas wallay, bari na same shi."
Dariya ta mata tace "To kije, kinga idan da rabon kisha mari sai ki dawo kina kuka."
Tsayawa tayi daga d'aukar hijabin tace "Kuma fa hakane? Ba zai dakeni ba Hajia ai yanzu ya daina."
Saka hijabin tayi ta fita da sauri ta nufi b'angarensu, tana zuwa ta same shi zaune sai k'ara kallon yakuwar yake yana b'ata fuska, yana jin shigowarta ya d'aga kai ya sauke mata idonshi da suka bayar da yanayin k'araso na ci ubanki, cak ta tsaya tana kallonshi da tsoro tana d'an cukuikuye hijabinta, hannu ya tara mata tare da nuna mata cinyarshi yace "...
*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*BADAK'ALA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
👨👩👧👦 _*AHALI NA*_👨👩👧👦
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.N.A]* ☆🖊️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_46_
"Zo zauna nan."
Saida ta k'ara yin kalar shagwab'a sosai kafin ta fara takowa a hankali tana nufoshi, k'ank'ance idonshi yayi yana mamakin k'arfin halinta, tasan fa idan ta zo me zai mata, tasan saiya mintsineta ko ya mata wata muguntar, amma duk da haka ta taho kuma a madadin ta koma ko ta nemi wajen b'uya, baisan lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba, tabbas k'arfin hali da jarumtarta sun birge shi, ta nuna mishi zata iya hak'uri da shi duk abinda zai mata, kafin ta k'araso sai kawai ya ji babu buk'atar ya mata abinda yayi niyyar yi. Cike da tsoron nan ta zauna akan cinyarshi ta rufe fuskarta ko da ya kan iya kawo mata mari ko ja mata hanci ya matse shi, a hankali ya janye hannayenta yace "Kalleni mana, tsoro kike ji?"
Girgiza kai tayi ba tare data bud'e ba, yana kallonta shima yace "To in dai hakane kalleni."
Bud'ewa tayi ta kalli fuskarshi amma ba cikin idonshi ba, aje robar hannunshi yayi kan k'aramin teburin yana kallonta yace "Fad'a min duniyata me kike so?"
Robar hannunta ta nuna mishi tare da turo leb'enta na k'asa gaba na sama kuma ta shigar da shi ciki sosai, kallon robar yayi sannan ya kalleta yace "Amna bana son irin wannan ciye ciyen fa, da zogale ce ma tafi anfani a jiki, ki bari gobe da safe na miki alk'awarin zan samo miki zogale kinji."
Yanda tayi da fuskarta yasa shi sumbatar kumatunta dan tayi fayau da ita tayi kyau sosai, shafa kumatun yayi yace "Kiyi hak'uri kinji, ai kin yafe min ko?"
Cikin shagwab'a wai ita ga auta ta kama hannunshi dake kan fuskarta tasa babbar yatsarshi baki tana tsutsa, murmushi yayi yana d'an girgiza kai yace "Autar Tanti kenan, rigamar dai ta motsa ko? To fad'a min me zan miki da zaisa ki hak'ura."
Cike da sangarta tace "Ni kawai ka ban na ci wannan, shi nake so na ci, kuma ai ba laifina bane na beby ne."
Cikin muryar dake isar mata da sak'on kiyi hankali fa yace "Amnaaa." Da sauri tace "To kawai ka siyo min kankana."
Rugugugu! Sautin da gabanshi ya bayar kenan sanda ta ambacin sunan kankana, nisa dashi da tayi da kuma samun Amna sunyi tasiri sosai wajen mantar dashi ita, amma kuma bai kamata ace ya manta da ita ko dan abinda ya aikata mata, to amma ya zaiyi? Dole ya manta da ita tunda dai babu komai tsakaninsu, ciki ne dama yake zargin tana da kuma da akwai ciki da yanzu ya bayyana kowa yaji, dan baya tunanin Ummy zata iya yin abinda tayi yanzun, jin ta sake saka hannunshi a baki tana tsutsa yasa shi dawowa hayyacinshi, murmushin yak'e ya mata yace "To bari nayi wanka sai mu tafi tare."
D'agata yayi daga jikinshi ya nufi hanyar d'akin kwananshi, tsayawa yayi ya juyo yace "Amma ke da baki shan kankana?"
"Haka kawai nake sonta yanzu." D'akin ya nufa yana fad'in "Kinyi waya da kankanar asalin?"
Cikin d'aga murya tace "Eh, tana lafiya."
Bayan isha'i suka fita, haka kawai suka dinga yawo suna zaga gari, sun jima sosai kafin ya mata siyayyar kayan ciye ciye suka dawo gida, tana fitowa daga cikin mota ta d'an matse cikinta tace "Wash."
Kallonta yayi sanda yake fitowa yace " Ya dai?"
Duk da abune da take wayan ji amma hakan baisa ta iya fad'a masa ba sai kawai tace "Ba komai, cikina ne ya d'an juya."
Tsaye yayi har ta zagayo wurinshi ya kama hannunta yace "Ki kula fa Amna, karki ja min asara ki sani sabon aiki."
Dariya kawai tayi suka nufi b'angarensu, saida ya tabbatar ta nutsu harta kwanta sannan ya zo ya ga Abba suka tattauna kafin daga bisani sukayi sallama.