← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 198

Sashe 160

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Husseina yayi yace "Bansan asalin meye tsakaninki da Hajia ba, amma yanda ke ma kike nuna baki damu da al'amuran 'ya'yanta ba abun babu dad'i, sanin kanki ne Alhaji baya nuna banbanci tsakanin wanda suke nashi da wanda suke na yan uwanshi, amma a gaban idonshi duk wani al'amari daya kamata kiyi magana saiki zuba ido kina kallo, saboda a ganinki ai ahalin Hajia ne ke kuma ba kya son shiga sabgarta, amma ya ci ace kina yi ko dan d'an uwanki."

Sauran mutanen ya kalla yace "Yau da kuka ga yarinyar nan akan titi cikin shigar da bata dace ba, kowa na da iko da hujjar da zai iya mata d'an banza duka, kuma babu abinda zai faru duk inda za aje, ku dubeku kuma da kuke gida d'aya, kuna sane da duk rashin mutumcin da take amma kuna kallo, ba komai ya kawo hakan ba sai dukanku kowa yana ji cewa ba ciki d'aya suka fito da ita ba."

Yayi maganar ne yana nuna su Amar da hannu, d'orawa yayi da "Dukanku nan babu wanda baya zarewa k'anninsa ido wanda suka fito ciki d'aya, amma wanda suke yan uwan juna kuma duk abinda yayi sai ka kalleshi da ido ko ka nuna baiyi laifi ba."

Juyawa yayi ga lieutenant da Ummy yace "Tanti Hadiza data baku amanar yaran nan ta baku ne da tunanin zaku tarbiyancesu kamar yanda ita ma zatayi, bakuyi laifi ba da kuka nuna musu soyayya har baku ganin laifinsu, amma kun kasa gane abinda ke daidai dasu da wanda ba daidai bane, kunfi kowa sanin tanti mace tsayayya da jajircewa kan abu, mace ce ita da bata yarda da raini ko shashanci ba, domin kuwa a rashin son wannan abubuwan ne ma yasa yau bata gidan nan, saboda ta k'i yarda a mulketa da ranta da lafiyarta, me kuke tsammanin zata ji idan taji an fasa auren 'yarta? Musamman ma taji dalilin fasa auren."

Hajia ya kalla yana murmushi yace "Hajia, Hajia, Hajia, nasan nan da zan bawa kowa dama ya fad'i dalilinsa na yin shiru, to kowa zai ce ne ke ce baki bayar da damar shiga hurumin iyalinki ba, suna da gaskiya ta wani b'angaren, amma ni dai a gani na ba hujja bace da zata sa kowa ya k'yale kuma yana ganin ba daidai ba, Hajia bansan me ye a kanki ba, amma ni dai kina birgeni, saboda jajircewarki da tsananinki kan iyalinki ya taka muhimmiyar rawa wajen hana faruwar wasu abubuwan, daga sanda kikayi shiru kuma sai komai ya fara lalacewa, matsalar d'aya ita ce ba kya jan iyalinki a jiki ta yanda zasu saba dake, idan akwai sabo tsakaninki dasu zasu iya fad'a miki komai daya shafesu babu tsoro, amma tsoron nufo ki ma Hajia yana gigita wasu, wasu duk maganar da zasuyi sai sun anbaci sunanki da cewa kar a ja musu matsala, misali Ummy na."

Ya fad'a nunata da hannu ya d'ora da cewa "Ita ce surukarki ta farko a gidan nan kuma matar babban d'an ki, a k'alla yanzu tana da shekara talatin da shida a gidan nan, amma wannan shekarun basu sa ta samu kusanci dake ba, har yau har yanzu bata iya kallon cikin idonki ta fad'a miki abinda ya dace da ita ko ya'yanta, uwa ta kan sadaukar da komai nata akan yaranta, amma banda Ummynmu, a jimawarta gidan nan ta kai matsayin da zata iya zartar da hukunci kuma ya yanku, amma har yanzu zuciyarta rawa take idan tana tare dake, jikinta b'ari yake idan tana magana dake, hakan ne yasa ta b'oye miki al'amari mai girman gaske wanda ya kamata ace kin sanshi, da kin nuna ita 'yarki ce data fad'a miki ko da ba zaki ji dad'i ba."

Dukansu ya kalla yace "Rayuwar nan bata da anfani idan ba zaka anfani d'an uwanka ba, ya kamata mu san yanzu mun rasa dattawan da suka rage mana, dukanmu yanzu anan mu ne muka rage ma junanmu, mu rik'e zumuncinmu kar muyi wasa dashi, mu kula junanmu kamar yanda zamu kula wanda muka fito ciki d'aya dasu, idan haka ta kasance wallahi ba *Ammar* marar kunya da rashin tarbiya d'aya za'a samu ba, za'a samu wasu Ammar d'in ma, sannan marasa jin magana ire iren yarinyar can..."

Ya fad'a yana nuna Hamna dake tsaye inda take yace "Indan har Ammar baiyi magana ba Amar zaiyi, idan Junaid baiyi ba Jibril zai tsawatar, idan Jamil baiyi ba akwai Abdul Rashid, in basu min magana ba akwai *Nura* akwai akwai akwai...etc, dole yara zasu gyara su kimtsu, dan in baka had'u da wane akan hanyarka ba zaka had'u da waninshi."

A shek'e ya kalli kowa yace "Yanzu ma nasan akwai wanda zasu ce na tarasu ina musu rashin kunya da fitsara, to ku gafarce ni duk wanda na b'ata masa rai, kuma nayi mamakin zuwanku haka da gaggawa, watak'ila kun d'auka wata dukiyar ce aka sake ganowa da Alhaji ya bari, shine kowa ya zo d'aukar nashi kason, ba'a d'auka ni na kira taron ba."

K'arashe maganar yayi da dariya, magana ta gaskiya akwai wad'anda a lokacin suka ji yaron ya birgesu, dayawa daga ciki abu ne da yake ci musu tuwo a k'warya, amma sai gashi yayi magana ya tab'o kowa. Gogan kam Amna ya kalla ya mik'a mata hannu, Amna da taji soyayyar mijinta ta sake huda zuciyarta cikin murmushi ta mik'o masa hannu ya kamota, saida ya kalli kowa yace "To ku rufe da salatin annabi, Allah yasa mu dace."

Amna ya kalla yace "Duniyata muje ki sauke ni, a sama nake wallahi."

Ta gabanta suka wuce inda kowa ya bisu da kallo, numfashi kawai kake ji na fita a wurin, sun jima zaune haka kafin Hajia ta sunkuyar da kanta tace "Kuyi hak'uri, yayi maganganu da dama a wurin nan, amma duka nice mai laifi saboda ni ce ban bayar da fuskar da za'a shiga shirgin iyalina ba, ba nayi haka bane dan bana so a rab'eni ko zuri'ata ba, kawai dai ina so ne naga tawa zuri'ar ta banbanta data kowa, ina so naga babu mutanen kirki irinsu, amma ban tab'a tunanin hakan zai zama matsala da zai iya kawo rabuwar kai ba, ku gafarceni dan Allah ku yafe min."

Alhaji Mani ne yace "Kamar yanda yaron nan ya fad'a ne Hajia ba laifinki bane ke kad'ai, mgana ta gaskiya mu ma muna da laifi, tunda ko baki so zamu iya magana amma muka yi shiru, amma yanzu dai tunda k'aramin yaro ya d'ora mu a hanya sai a yafi juna a kuma gyara gaba."

Su Hassana da jikinsu yayi sanyi ne yace "Allah ya yafe mana baki d'aya."

"Ameen." Aka amsa dashi duk d'akin sai kuma aka kwashi hira, Zeituna ce ta mik'e tare da su Shafa'atu tace suje to a d'ora girki, tunda an riga da an had'u kafin kowa ya tafi, madafa suka nufa sai mazan da suka fita waje, a wannan taro na wannan rana wanda Ammar ne silarshi har suka d'ora zubin kara wanda musababbinshi had'uwa ce ake son a dinga yi duk wata, ba'a fitar da yan mata ko yaran mata ko tsofaffi ba, duk mai so ne wanda ya ga zai iya duk wata, babu wanda ya yarda aka barshi a baya duk da za'a dinga zuba kud'i, amma a lokacin abun ya shiga zuciyar kowa ba kud'in ne abun dubawa ba sai girman zumuncin da za ayi.

*A dole* ta gyara ba dan tana so ba, 😂(rubdugu) rubdugun da akayi akanta kad'ai yasa ta d'an saya shigarta, hatta su Amie ta daina yarda yanzu su zo gidan nan sai dai su had'u a salon d'inta, amma a haka wata rana Amie na zuwa amma bayan ta sako hijab.

*Bayan wata biyu* Hajia ta tisa k'eyar Hamna da Amna Umaimah dasu Jamila suka tafi hadj, wanda tafiyar Amna ta bawa mutane mamaki sanda aka ji ta tafi da ciki, lafiya sukayi aikinsu suka gama suka dawo lafiya, har yanzu ba wani hijab take fita dashi ba, sai ma uwayen rigunan data kwaso tafiyarsu masu kyau, kusan yanzu su tafi sakawa indai ba gida ka sameta ba ka ganta da riga da siket ko da zani. Yau ma tsaf ta shirya ta tafi wani babban mall dan siyayyar abin buk'atarta, ta shiga tana cikin duba abinda take so kawai suka had'e da Habib.

Kallon da yake mata yana tunanin ya mata magana ko kuma ya k'yaleta, shi fa ko yanzu aka yardar masa zai aure ta, amma ganin irin kallon da take masa yasa shi kallonta kawai shima, wucewa taje yi ta gabanshi sai kuma hanyar ta d'an matse, karkatawa tayi zata wuce ta kalleshi tace "Malam zan wuce."

Mamaki ta bashi ganin yanda ta nuna kamar basu tab'a sanin juna ba, kauce mata yayi a hanya zata wuce yace "Hamna abun ba ko gaisuwa?"

Kallonshi tayi ta wurga masa harara taja tsaki ta wuce, da kallo ya bita duk sai yaji babu dad'i, tana gama abinda ya kawota ta juya ta tafi, a hanyarta ta komawa ta had'u da Alhaji *Sabi'u*, babban shahararren d'an kasuwa, babban mutum ne mai iyali da tunbi😂, sanda suka tsaya bakin madakatar danja a lokacin ya sakar mata na mujiya, ba mutumin kirki bane ko kad'an, indai zaiga mace to fa babu lafiya hankalinsa tashi yake, binta yayi a baya har ta isa gida, gira d'aya ya d'aga sama ya cije leb'e sanda yaga gidan data shiga, lallai ko giyar wake yasha bai isa ya tunkari gidan nan da sunan zai wa yar gidan lalata ba, yana da sani sosai akan mutanen gidan, kama daga gwamnansu Gambo, lieutenant na douanes da kuma colonel na soja, kai ba ma zai yiwu ya fara ba wallahi indai yana son kansa da mutumci, amma kuma ya gani yana so saiya kenan?.

*Bari Fan's badak'ala su fad'a maka yanda zakayi? Ni ma idan kuka min comment saina baku wata page muji me zaiyi*.

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*
Chapter 160 · 0% Book details