← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 198

Sashe 195

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta shiga motar babu wanda ya kula wani har suka kai gida, ta riga shi fita ta nufi hanyar shiga cikin jiki a sanyaye, taji sanda ya rufe motar amma bata juyowa ba, sai ji kawai tayi ya fizgeta zuwa cikin gidan da sauri kamar zata kifa k'asa, saida ya tsaya zai bud'e k'ofar da makullanshi ta samu ta durk'usa kan gwiwoyinta ta rik'e k'afarshi tana fad'in "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri, ni wallahi raina bai b'ace ba."

Uwar d'aki ya shiga da ita ya shiga bata horo kan abinda ta masa, horon bala'i wanda ta wani fannin gwara duka dashi, ya gama gigitata tare da galabaitar da ita, zuwa ne na k'eta da bak'in ciki yake mata, saida ya gaji dan gaban kanshi kuma ya koma kimtsata da rarrashi wai tayi shiru ta yafe masa.

Haka Ummy tayi ta kiranta tana ina sai shi ya fad'a mata ai tana gida, a hassale Ummy tace "Uban me take gidan to bayan nan ana nemanta?"

Cikin rarrashi yace "Kiyi hak'uri Ummy zata dawo anjima."

Cikin fad'a tace "To me taje yi a gidan ne wai?"

Cikin nutsuwa yace "Ummy ibada ta zo, kuma ni da kaina na kawota."

Kashe wayar tayi ba tare data k'ara jan zancen ba, kallon Hamna yayi dake kusanshi ta zuba masa ido yace "Lafiyar kallona?"

Da sauri tayi k'asa da idonta, k'ura mata ido yayi shima yace "Kina lafiya?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Bana jin dad'i k'asa, ka mayar dani gida ina so na ga Ummy."

Kamar daga sama kawai taji ya bud'e mata k'afafu ya zura hannu yana fad'in "Bari na duba ki watak'ila k'ari kikayi."

Rintse ido tayi tana jin zafi duk inda ya tab'a, saida taji ya ciro hannunshi ta bud'a ido, gani tayi ya kafeta da ido yana kallo, jawo kanta yayi cikin kunne ya rad'a mata "Kin fiye zak'i da d'and'ano ne, uwa uba ga ruwa."

Kamar yau ne haka ta fara faruwa kawai sai taji kunya ma ta rufe ta, sunkuyar da kai tayi hakan yasa ya sumbaci goshinta yana fad'in "Kankana ta uwar ruwa, a ci gaba da shan kankana ba d'aga k'afa, ni ma ba zan gaji da kawota ba, haka kuma ba zan gaji da tsotsar ruwana ba."

Mik'ewa yayi ya shiga d'akin daya ware na magunguna, ba jimawa ya fito sai ji tayi ya kwantar da ita yana gyara zare da allura, da sauri ta tashi tana fad'in "Me za kayi kuma?"

Hararanta ya shiga yi sama da k'asa yana fad'in "D'inki zan miki, kin k'aru Hajiata."

Girgiza kai ta shiga yi tana fad'in "A'a wallahi bana so, ni ka bari Ummy na zata min, bana so gaskiya."

Sake kwantar da ita yayi yana fad'in "Ni kuma ga mahaukaci kullum sai mu tsaya Ummy ce zata dinga d'inke b'arnar da d'anta ya aikata ko? Ai ko ban iya d'inkin ba kinsan na koye shi dan na dinga gyara kayana da kaina, bare kuma na iya har tiyatar zuciya na iya."

Tana kuka tana k'ari tana ihu tana bata so tana rirrik'e shi haka ya mata d'inki uku, saida aka gama ta yunk'ura da k'yar ta tashi zaune wai sai gani tayi yana share hawaye (D'an iska rairai ne😂), da mamaki tace "Lafiya kake kuka kai kuma?"

Kawai fad'awa yayi kan k'afafunta har da jan majina yana fad'in "Wallahi tausaya miki nake, akwai zafi d'inkin nan, sai naji kamar a zuciyata nake soka allurar da zaren."

D'ago kanshi tayi tace "A kaina ne dama kake kukan?"

Turo baki yayi yace "Ina sonki sosai Hamna, duk abinda zan miki da zai cutar dake ba nayi shi dagangan bane, b'acin rai ne ke saka ni, ki yafe min kinji."

Jawo kanshi tayi ta manna a tsakiyar mamanta tana shafa kanshi tana fad'in "Kayi hak'uri ai nice mai laifi ni ce bana jin maganarka, kuma duk horon da kake min ina jin dad'i dan hakan yana nuna min ka isa dani ne, sannan ina d'aukarshi a matsayin horo na yaya da k'anwarsa, dan haka ka daina zubar min da hawayenka na cancanci wannan hukuncin, ko ba komai kaga gobe zan kiyaye fito da b'acin rai a fili yayin da ka saka ni aiki."

D'ago ido yayi ya kalleta cike da k'aunarta yace "Yunwa nake ji fa."

Hannu tasa a rigarta tana fito da nononta tana fad'in "To dama me ye anfanin nonon da har yanzu yake min zuba? Saboda kai dama nake ta ajiyarshi."

*Iko sai Rabba*, k'ato ya daddage a k'afafun yarinyar sai tsotsar nono yake, rayuwa kenan ta musu dad'i, komawar da bata yi ba kenan wajen bikin nan sai dare, a lokacin da suka je har an zo d'aukar amarya, ko da ya sauketa yace "Ki kula min da kanki Hamna."

Kallonshi tayi tace "Kaima ka kula da kanka, amma ana zaka jirani har mu dawo sai mu koma gida ko?"

Saida ya kalli gabanshi yace "A'a, daga nan majalisa zan tafi, akwai wad'anda na gayyata d'aurin aure kuma ban gansu ba, to zan je ne na shukawa kowa rashin mutumci, sannan su biyani katin d'aurin aurena dana basu, tunda 'ya'yan k'ananan mutane ne su."

Kafin tayi magana ya ja mota ya wuce, da kallo ta bi motar tana mamakin abinda zaije yayi, bata ankara taji an daketa a baya da sauri ta juyo ta ga Sayyada, hararanta tayi tana fad'in "To dad'i miji sai yanzu kika dawo?"

Murmushi ta mata tace "Kin fad'i daidai, mijina miji ne da zan iya kiranshi namiji gaban zaratan maza."

Dariya tayi tace "Ba sai kin fad'a ba ai, kowa ya ganshi zai gane hakan, shi yasa ma nake nan har yanzu banyi aure ba shi nake jira yayi ta biyu dani."

Wata harara ta galla mata tace "Sayyada rufawa kanki asiri wallahi, mijin nawa? Ai kuwa sai dai ki mutu babu aure."

Dariya tayi tace "Au ba'a aure ke ya aure ki?"

Kallonta tayi sosai tace "K'addararsa ce ni babu yanda zaiyi, ke baki ga yer uwata ba ma aka raba shi da ita saboda ni."

Yanda Sayyada taga duk tayi ne yasa ta daddab'a kafad'arta tana fad'in "Sai hak'uri Hamna, ki ci gaba da mata addu'a."

Saida ta goge k'walla tace "Allah ya jik'anta da rahama."

"Ameen ya Allah." Ta fad'a kafin ta d'ora da "Haka naji mutane na fad'a, ashe kema kin fahimci haka."

A nutse ta kalleta tace "Sayyada kullum na kalli Ameera sai na ga fuskar yar uwata a fuskarta, kuma kullum na ga haka saina tuna rayuwata da ita, haka zalika ina tuna cewa tsananin rabon haihuwar dake tsakani na da yah Ammar ne ya amshi rayuwarta."

Jinjina kai tayi tace "Hakane, kinsan shi rabo ba'a rantsewa akan shi, da wani yayi k'ok'arin shiga tsakaninku to sai dai ya mutu."

Kama hannunta tayi tana fad'in "Muje ciki na samu zagina a wurin Ummy tun yanzu, yau nasan har uwata sai Ummy ta ci."

Cike da raha tace "Ai ko ni zan kama mata, kina matar uban d'aurin aure ace anyi biki babu ke."

Bushewa sukayi da dariya inda Hamna tace "Kinsan kuwa mutumin naki ya tafi majalisarsu wai zaiwa duk wanda bai zo d'aurin auren ba rashin mutunci, sannan su biyashi katin d'aurin auren daya raba musu."

Girgiza tayi tana dariya tace "Yer uwa wannan mijin naki ki dinga tofa masa lahaula kowace safiya, sannan ki dinga binshi da ayatul kursiyu dan bai rasa shafar mutanen b'oye."

Hararanta tayi tace "Sayyada bana son iskanci fa, mijin nawa?"

Cikin dariya tace "Ai ni labarinku ma zaki ban wallahi ina da marubuciyar da zata rubuta min shi."

Dafe k'irji tayi tace "Ni? Rufa min asiri, idan ya gani babbaka ni zaiyi da raina."

"Ba wani nan, ni zanje har gidan na same shi sai ya yarda ko baya so."

Dariya tayi tace "Gaki gashi ne ai kar tasan kar."

*Ammar* na zuwa duk ya tashi hankalin bayin Allah, kububuwa ya dinga musu ai duk sai ya ci ubansu tunda basu je d'aurin auren fari daya fara ba, sannan su tattara mishi katinshi su bashi inba haka ba zasu ga tsiya, su uku ne a wurin da basu je ba su dai hak'uri suke bashi amma da yake sauran da suka je suna zuga shi saiya dinga botsarewa, fad'i yake ai basu da mutumci ne shiyasa suka mishi haka, kenan ko auren Amreerarsa ya tashi haka zasu mishi? K'arshe dai yace a bashi katinshi kad'ai zai hak'ura, biyu daga ciki har motarsu suka duba basu ga katin ba suka ce bari suje gida su d'auko.

Rigarsu ya rik'e yace "Yo ni saida naje gida na d'auko muku? Anan na baku nima anan zaku ban kayana."

D'aya ne yace "To ai shine zamu d'auko maka a gidan ko."

"Ban yarda ba, a bani yanzu kawai hankali ya kwanta, ko a biyani da kud'i."

Wani daga zaune dake ta musu dariya ne yace "Eh su biyaka da kud'i, kati fa yanzu tsada yake, kuma irin wanda kayi ma na manyan mutane ne mai tsadar gaske, ya kai jaka goma fa wannan."

Kallonsu yayi yace "To kunji dai da kunnenku, dan haka a fiddo a bani kud'i na yanzu."

D'aya da abun ya dame ni ya fiddo jaka gomar ya mik'a mishi yana fad'in "Allah ya rabaka da wannan jaraba Ammar, wallahi ni daga matata ta farko har ta biyu babu wacce ta tab'a titseni irin haka akan abu, yo ni naga jaraba da zafi zafinta."

Saida ya soka jaka gomar aljihu yace "Yo suma sakarkaru ne matan basu san yanda zasu amshi kud'i a hannunka bane."

Haka dukansu suka biyashi kud'in katinsu kafin ya rabu dasu, mik'ewa yayi yana fad'in "Sai anjimanku to."

D'aya daga ciki ne yace "Allah raka taki gona."

Saida ya kwaso shoki ya yarfa mishi yace "Na dai ji, sai dai haushi wallahi."

Suna kallo ya tayar da mota yayi gaba, wajen wani mai soya doya da kw'wai da kaji ya tsaya, ya mik'a mishi abu amma kuma bai amshi komai ba ya wuce, saida suka ga ya bar wajen inda wani ya tintsire da dariya yace "Ammar jaraba, Ammar bala'i, Hamna na hak'uri da bawan Allahn nan."
Chapter 195 · 0% Book details