Sashe 118
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dawowa yayi ya zauna jiki na ci gaba da mishi rawa ya d'an zauna kan turmin dake kwance yana kallon Ammar, saida ya kifa k'waryar nonon nan bakinshi yasha kafin ya sauke ya kalli kawu yace "Abba, Abba na ya fad'a min 'yarka ce na mara d'azu da safe, kuma ya fad'a min ranka ya b'ace sosai har kana cewa ma zaka je ka rama mata, shine na hutar da kai ta hanyar kawo kaina."
Zaro mishi ido yayi yace "Ni? Yaushe akayi haka! Allah yaro inaga dai bai fahimce ni bane, ni kam ina ni ina tab'a jikinka yallab'ai."
Wani kakkausan kallo ya masa yace "Kana nufin Abba na k'arya ya min kenan?"
Da sauri yace "A'a Qur'ani, gaskiya ya fad'a, amma bani na fad'a ba Jumma ce, uwar yarinyar."
😂Jumma na d'aki tana jinsu gatsal tayi daga d'aki ta fito tana fad'in "A'a Baffan Jumare, kaji tsoron Allah fa."
Kallonta Ammar yayi, wani irin juya mata kai yayi alamar ta koma ciki kamar maciji, juyawa tayi ta koma tana kallon kawu Mamu, shi kuma binta yayi da fulatanci kafin ya kalki Ammar wanda shima ke kallonshi, saida ya sake kallon bukkokin sannan yace "Ina yarinyar take ne?"
"Tana ciki, ai bata jin magana ne." Murmushi ya masa yace "Ko zan iya ganinta?"
Da sauri ya mik'e yana fad'in "Ba damuwa, yanzu kuwa."
D'akinsu ya shiga ya sameta kwance, murya k'asa k'asa cikin harshensu yace "Kin jawo mana bala'i, to tasoyana nemanki kema, kuma karki kuskura naga kina juya bakin nan ko a b'oye ne, ki barmu mu rabu dashi lafiya dan naga ba mai hankali bane."
Fitowa sukayi tare inda ya zauna inda yake ita kuma ta durk'usa k'asa tana kallonshi, wannan mutumin ne, hakan yasa ta k'ara shan jinin jikinta, kallonta yayi yana kurb'an nonon shi yana mata murmushi yace "Jumare ya kike?"
A tak'aice ta kalleshi ta kuma yin k'asa da kanta, murmushin gefen labb'a ya mata yace "Jumy."
Da sauri ta kalleshi, Jumy kuma? Murmushi tayi saboda sunan ya mata dad'i ita kam, ganin kallon da take masa da murmushi yasa shi cewa "Sunan ya miki dad'i?"
Murmushi ta sake yi ta rufe bakinta hakan yasa yace " Kina sona Jumare?"
Rufe fuska tayi da hannayenta ta mik'e tsaye ta daka da gudu d'aki, binta yayi da kallo yana murmushin mugunta, dawo da kallonshi yayi kan kawu da shima ke murmushi cike da kunyar yaron, wani murmushin ya sake mishi yace "Idan ta amince ai kaga ni da Abbana duk mun zama surukanka."
D'an kawar da kai kawu yayi irin fa shi har ya fara jin kunyarshi ma a matsayin suruki, yana ganin haka ya tab'e baki ya sake kurb'an nononshi, aje k'waryar yayi ya tashi tsaye yace "Abba ni zan tunda kun yafe min."
_Yaushe suka ce sun yafe?_
Gyara zaman bindigar nan yayi tare da nufa hanyar fita, bin bayanshi kawu yayi suna kaiwa k'ofar gidan yayi daidai da zuwan Jano, Ammar ya sanshi farin sani, yasan ba mutumin kirki bane, mamakin abinda ya kawo shi gidan yake yi, dan haka ko sallama bai yi wa kawu ba yace "Kai kuma fa?"
Kamar yanda ya sanshi haka shi ma ya sanshi dan dukansu matasa ne masu ji da kud'i, babu alamar sakin fuska ya bashi hannu alamar suyi musabaha yana fad'in "K'alau."
Bai bashi hannun ba sai kallon kawu da yayi yace "Ka san shi ne?"
Jano d'auke idonshi yayi daga kansu yana kallon titi yana murmushi, yasan bala'i ne yake nema dashi kawai, shi kuma bai shirya wujijjiga kanshi ba bare ya biye mishi, kawu kuma da baya so Ammar yasan abinda ke faruwa da k'arfi ya kama hannun Jano suka koma gefe yana waiwayen Ammar dake binsu da tuhumammen kallo, yana kallo kawu ya fito da kudin da lieutenant ya bashi ya damk'awa Jano yana fad'in "Gashi malam, na biyaka dan Allah ka shafa min lafiya yanzu, karka sake zuwa gidan nan."
Wani kallo ya mishi yana yatsina fuska yace "Ko saboda waccen ne ka hana min 'yar taka? To ka sani waccen babu abinda zaiyi da ita wallahi, kawai zai yaudareta ne sannan ya mayar maka da ita sunan da zaka gagara kiranta dashi."
Wani kallon kai kauce kawu ya mishi yace "Kai dallah, ana babbakar giwa wa yake jiyo k'aurin zomo, ai 'yata tafi k'arfin dukanku wallahi, sai dai uban waccen d'in."
Wata dariya Jano yasa yana fad'in "Babban arne kenan."
Ammar dake cike da shakku matsowa yayi wurinsu ya kalli kawu rai a b'ace yace "Me yake faruwa ne tsakaninka da shi? Kasan waye wannan kuwa? Ba mutumin kirki bane."
Wani kallo Jano ya mishi yace "Ammar, ka sanni na sanka, karka shiga sabgata mana tunda bansa da kai ba, kayi abinda ya kawoka nayi abinda ya kawo ni."
Daf dashi ya matsa yana fad'in "Ba zanyi sabgar tawa ba Jano kayi abinda za kayi, kai ka sanni wallahi ba zan lamunci iskancin nan daga gareka ba."
K'asa da sama ya kalleshi yace "Bana jin rigima, kai kuma kullum a cikinta kake kamar wanda aka haifa ana dabbatuwa, dan haka banda lok..."
Bai yarda ya k'arasa fad'a ba ya kai mishi bugu a baki, baya baya yayi ya kaiwa motarshi karo ya dafeta yana kuma dafe da bakinshi, idonshi jawur sukayi har da k'wallar wahala, da sauri kawu ya shiga tsakani yana bawa Ammar baki ya rabu dashi, cikin jin bala'i da masifa yake nuna kanshi yana fad'in "Ni d'in? Ni ne aka haifa kamar ana dambe? To bani ne ba sai dai in kaine ubanka ya haifa yana dambe."
Tasowa Jano yayi yana tofar da yawun bakinshi da yake jin sunyi gishiri alamar jini yace "Ni ka wa haka Ammar? Ni? Tak'amarka akwai iko da masu saka kakia gidanku? To wallahi sai kayi nadamar dukan nan daka min, in kuma bansa kayi dana sanin haihuwarka ba to kace ba d'an halak bane ni."
Cikin d'aga sauti ya fara fad'in "Yeeee, kai ba d'an halak bane, da gani ma ai ana ganewa, banza mata-maza kawai, ashe k'aramin d'an jagaliya ne kai, to kaji da kyau Jano, ba boka babu malam babu d'an bori, kuma a haka zan ci uwarka, ruwan randa kawai zansha na ma iskancin da baka tsammani, idan har kuka gagara kai da matsafan naka to ka nemi lambata a wurin wanda ya sani, ka zab'i rana da lokacin da zamu had'u da kai a bayan gari saika sa min hannu, watak'ila ka iya huce haushinka ta hanyar rama dukanka."
Juyawa yayi ya kama murfin motarshi ya bud'a zai shiga, tsaya yayi ya kalleshi da kyau ya d'aga mishi yatsarshi ta tsakiya wacce tafi tsawo tana kallon sama, sannan yayi alama da yatsunshi cewa sai sun had'u shiga yayi ya tayar ya wuce. Suna had'a ido kawu ya sunkuyar da kanshi yana murmushin mugunta, a ranshi yana fad'in "Ashe kowa da wanda ya raina."
Tsaki yayi ya juya a fusace shima ya bar wurin, Ammar ma daga nan asibiti ya sake komawa, wannan kayan ya cire dan baya so kowa na gida yasan shi dasu ya mayar da nashi kafin ya sake komawa gida.
Jano na barin nan ya so ya zarce ofishin yan sanda, ba wai dan ya dake shi sai dan ganinshi da kakin soja da yasan ba soja bane kuma yake sawa, yasan inhar doka ce ya taka ta hanyar sa kayan dole hukunci zai hau kanshi, amma saiya bari har safiya tayi sai yayi k'ararshi. Ammar kuma na ko da yaje gida kai tsaye wajen amaryarshi ya nufa, tana zaune kan kujera tana kallo ya same ta, tsaye yayi ya bud'e mata hannayenshi alamar ta rumgume shi, bata fahimce shi ba sai cewa da tayi "Sannu da zuwa yah Ammar."
Mik'ewa tayi ta nufe shi tana k'ara fad'ad'a murmushinta, tana zuwa ta tsaya bata matsa kusa dashi ba, saida ya mata kallon zan ci... kafin ya fizgota da k'arfi ta fad'a jikinshi, saida zaman d'an kwalinta ya canza inda tayi fiki'fiki da idonta, matseta yayi sosai yana sauke numfashi, d'agata yayi daga jikinshi ya kalleta yace "Daga yau kika ga na shigo haka zaki min, kuma ko gaban waye ban yarda ki nuna jin kunya ba, haka nake so kuma dole kiyi."
Yana fad'a ya wuce ya barta tsaye, juyawa tayi da baki bud'e ta bishi da kallo, d'aga ido tayi sama tace "Allah gani gare ka, ka shirya min bawan nan naka."
Zaune ta koma tayi tana ci gaba da kallo, amma duk in taji motsi daga d'akinshi sai gabanta ya fad'i, ana haka dai har ya fito sanye da farin wando iya gwiwa mai aljihu da farar singlet d'in data kama shi sosai, yana zuwa ya zauna kamar zai fad'a mata yana fad'in "Kiyi hak'uri ba zan iya yi miki kwalliya ba, yunwa nake ji kuma na gaji, amma ki sani ni makwoyin sunnar annabi ne."
Dariya tayi ta mik'e tsaye ta nufi teburin abinci, da kallo ya bi manyan kayan dake birge shi tare da ayyana luguden da zasu sha yau a hannunshi, cije leb'en k'asa yayi yana lumshe ido, yana kallo ta d'auko kwanukan abinci ta juyo tana takowa, nan ma ido ya k'ura mata yana kallon komai na hallitarta, bai sani ba ko dan komai nasu iri d'aya ne da kankana, ko kuma dan suna da k'ira da hallita irin yanda yake son mace, dan shi dai yafi son mace mai cika hannu yar dumul dumul, ko gajera ce yana sonta a haka bare kuma su dake da tsayi, sannan ga kyawun fuska masha Allah, haka kuma Amna tafi kyau akan kankanarshi, kawai dai haske kankana tafi waccen, shi dai kawai yasan komai nasu yana birgeshi, tana zuwa ta sunkuya ta aje kayan ta durk'usa ta fara zuba mishi, kallon fuskarta yake yace "Amna yanzu ma abincin kika dafa?"
Ba tare data d'ago ba tace "Yah Ammar idan ban dafa ba to me zaka ci?"
Yatsina fuska yayi yace "Da gaskiyarki kuma, dan kinga banyi tunanin siyo abinci ba."
D'an murmushi kawai tayi tare da kallonshi tace "Na aje maka anan ne?"
Kai kawai ya d'aga mata, gyara wurin tayi sannan ta aje mishi ta zaune yanda suke fuskantar juna, kallonshi ta sake yi tace "Bismillah."