Sashe 110
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Gauuuu* ya d'auketa da wani bahagon mari, k'ara ta saki tare da sakin kayan hannunta ta durk'ushe, da sauri Zeituna ma ta durk'usa ta dafata, d'ago kai tayi ta kalleshi da nufin fad'a mishi wannan fa ita ba komai bane a wurinta, amma sai taji ya d'ora da "In kika bari na sake ganin wannan guntulallar k'afar taki a gidan nan wallahi sai kin gane kurenki, na kuma mareki kije ki turo ubanki kowaye shi, a shirye nake dana tsaya da kowa a gaban alk'ali indai akan uwata ne."
Saida ya zuba hannun dama a aljihu ya fara takawa ya nufi falon Hajia, kamar an kirashi sai kuma ya tsaya ya sake dawowa ya sunkuya kusan fuskokinsu yace "Ke kalleni nan."
D'agowa Jumare tayi ta kalleshi da jajayen idonta, saida ya mata alama yace "Kin fara hak'oran hankali ne?"
Duk da tana jin hausa amma yanzu saiya gindayar da ita, kallon Zeituna tayi da alamar tambayar me yake nufi? A harshen fulatanci Zeituna ta mata magana, hakan yasa ta kalleshi cikin muryar kuka tace "Eh sun fito min."
Murmushi ya mata yace "To nan gaba idan kika sake mata rashin kunya Allah su zan zubar miki, kin gane."
Tsaye yayi yana kallonta yace "Ya sunanki?"
Cikin kumburo baki da tsantsar fulatanci a bakinta tace "Jumare."
Yatsina fuska yayi yace "Jumare kuma? Juma'a aka haife ki? To me yasa ba'a saka miki Jumma ba?"
D'an zaro ido tayi ta kalleshi, Jumma? Uwa ta fa kenan? A tunaninta yasan sunan mahaifiyarta ne shiyasa ya mata wannan shagub'en, ganin kallon da take masa yasa shi kallon Zeituna yace "Uwa ya gajiyarku?"
Bai kuma jira me za tace ba ya sa kai falon Hajia d'aukar magana, Zeituna kuma lallab'a Jumare tayi ta tafi gida, saida ta tafi ne tayi murmushi tana fatan hakan da yayi ya zama silar daidaita tsakaninta da Jumare.
Inda Maryama ta bar Hajia nan ya sameta shima, sai dai akwai mutane a falon wanda wasu ke shirin tafiya wasu kuma sai anjima, daga ciki akwai dangin Ummy, gaba d'aya yayi jam'i yace "Ina gajiyarku?"
Duka d'akin da lafiya lau suka amsa tare da d'orawa da "Ya taku gajiyar?"
K'ala babu wanda yace ma sai zaunawa da yayi kusa da Hajia yana kallonta tana kallonshi ita ma, ganin kallon da suke ma juna yasa Hajia k'ara had'e fuska tace "Da wane rashin mutumcin ka shigo kuma yau? Dan wannan murmushin na ka ya bayyana shegantaka ta kawoka."
Hannunta ya kamo ya sumbata sannan ya kalli idonta yace "Hajia ina godiya, Allah ya saka miki da alkairinsa, Allah ya zundumaki aljanna bayan kinsha ruwan khausara, Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki kamar yanda kika saka rayuwata farin ciki."
Cike da shewa 'yan cikin d'akin suka saka tare da amsa mishi da "Ameen."
Bai kulasu ba sai d'orawa da yayi da" Hajia ni kam babu abinda zan saka miki da shi a gidan duniyar nan, amma duk da haka zan sakawa 'yata ta farko sunanki."
Kallonshi kawai take bata tanka masa ba, matsowa yayi sosai kusa da ita cikin tattausa murya yanda babu mai jinsu yace "Hajia maganar al'adar nan ce na zo k'arasawa, ance a rana irin ta yau namiji yana bayar da rak'umi ne ko kuma wata kyauta mai tsoka, to gaskiya ni na zauna nayi tunani na kasa tunano abinda zaiyi daidai da dank'waleliyar jikar nan taki, shiyasa nace bara na kawo kaina saiki fad'i abinda kike so nayi."
Dai lokacin tayi murmushin zaka raina kanka tace "Komai idan na fad'a za kayi?"
Cike da tabbatarwa yace "A shirye nake Hajiata."
Ita ma saida ta sassauta murya tace "Jan rak'umi zaka kawo lafiyayye, saika had'o da kud'i million d'aya, sannan ka siya mata sark'a da d'an kunnai na zinariya, idan kayi haka ma ya wadatar."
Tana fad'a ta d'an kawar da kanta alamar zaka gane kurenka, shi kuma murmushi ya mata yana shafa sumar kanshi, kafin yayi magana Allah ya kawo lieutenant d'akin, mik'ewa yayi da sauri ya tarbeshi yana fad'in "Yawwa Abba barka, kud'i nake so ka bani."
😂😂😂
Saida ya harareshi kafin ya mayar da hankalinshi kan mutanen d'akin suka gaisa sosai, daf da Hajia ya zo ya duk'a ya gaisheta, yana mik'ewa ya juya ashe Ammar na daf dashi a baya sai kuwa suka had'e, tsabar k'arfi yasa lieutenant yin baya yana neman fad'uwa, da azama Ammar ya tallaboshi baya, kallon jua sukayi ya sakar masa murmushi, d'aga shi yayi lieutenant kuma cikin fad'a yace "Meye haka wai? Yanzu dana fad'i kaji dad'i kenan?"
"Amma ai baka fad'i ba, Abba ina tare da kai fa, haka ba zai faru ba sai in k'asa ce tarufe min idona."
Cikin fad'a yace "To yanzu uban me kake so da kake biyata a baya kamar wutsiya?"
Saida yasa hannaye aljihu kamar wani k'aramin yaro yace "Kud'i zaka bani?"
Da mamaki yace "Kud'i kuma? Gashi kuma ban iya tuna ranar daka bani ajiyar kud'i ba."
Turo baki yayi irin shagwab'a yace "Abba ba fa ajiya na baka ba, kai ne kawai zaka bani kyauta."
Hanya ya kata zai fita yace "To bana da."
Bin bayanshi yayi yana fad'in "Ni dai ka bani kawai, idan ban tambayeka ba wa zan tambaya? Kai kad'ai ne fa ubana a garin nan, kuma duk hidimar nan da akayi sisinka ban nema ba."
Juyowa yayi yace "Amma uban wa ya biya maka sadaki?"
"To ai kai ka biya na kowa da kowa, kaga kenan ba zanyi lissafi da wannan ba."
Har saida ya kai bakin mota zai shiga ya rik'e murfin mota yace "Allah saika bani, in kuma kace ba zaka bayar ba zan je wajen abokaina nace su bani bashi, kaga ku za ama dariya ace d'a kuma jika ga ahalin Gaga amma ya rasa million biyu."
Ba tare daya ankara ba lieutenant ya kai mishi bugu a k'eya yana fad'in "Dan ubanka yi sauri kaje, daga nan saika biya gidan redio da telebijin duk ka fad'a musu ni Hassan na k'i baka million biyu."
Juyawa yayi yace "Shikenan zaku gani kam."
Kallonshi lieutenant yayi, irin tafiyar nan ce idan yayi hushi, hakan kuma zai iya sawa yayi komai, iska ya furzar ya d'aga murya yace "Me za kayi dasu?"
Juyowa yayi yana dariya har ya k'araso kusanshi yace "...
*Yan nigeria Allah ya saka muku da alkairi.*
09/09/2020 à 17:58 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*BADAK'ALA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
👨👩👧👦 _*AHALI NA*_👨👩👧👦
🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_37_
Juyowa yayi har ya k'araso kusanshi yace "Alawa zan siyo?"
Jin abinda ya fad'a yasa lieutenant yi mishi kallon baka da hankali ko me? tsaki yayi yace "Zan tsaya nan sauraren wannan shirmen naka ne?"
Kallonshi yayi tace "To Abba gashi na fad'a maka."
Da k'arfi yace "Uwarka! Alawar uban me zaka siya ta million biyu? Ammar ka kiyaye ni fa."
Kwalar rigarshi ya kama yana wasa dashi sannan yace "Zan fara tarawa jikokinka alawa ne."
Girgiza kai kawai yayi cike da damuwa ya fito da k'aramin makulli a aljihunshi ya mik'a mishi yace "Ka samu mahaifiyarka."
Karb'a yayi ya juya ba tare da yace komai ba, yana shiga falon Hajia ta kalleshi tace "K'aryar banza kawai, kud'in ma da za kayi birgar dasu baka da saika karb'a wajen ubanka."
Murmushi ya mata yace "Magana sahihiya, kinji fa kema ubana kika ce, to idan bai min ba wa zai wa? Nine fa sanyin idanuyarshi na farko."
Kai ta d'aga mishi alamar kai tafi can tare da fad'in "Kai dallah can, shalele shine sanyin idaniyar kowa a gidan nan."
Kallon can ta matse muku ke da shalelen ya mata ya nufi d'akin Ummy, tana shirin fitowa suka had'e a k'ofar d'akin, mik'a mata makullin yayi yace "Inji Abba ki bani million biyu."
Fizgar makullin tayi ta koma d'akin inda ya bi bayanta, juyowa tayi tace "Fice min a d'aki ka jira ni k'ofa."
D'aga kafad'a yayi ya juyo ya tsaya k'ofar d'akin, tana d'auko mishi ta same shi da waya a kunnenshi yana amsawa, abinda taji yace kawai shine "Zan turo a duba ta, ni ina cikin cin amarci ne ba zan fara fita ba gaskiya."
Ta gefen ido ta harareshi ta mik'a mishi kud'in, karb'a yayi yana kashe wayar tare da makullin, kallonta yayi irin ba wasan nan yace "Akwai majiyaciya a asibiti dake buk'atar kulawar d'aya daga cikinmu, Ummy kije ki duba ta."
"Saboda me?" Ta fad'a a hassale, kallonta yayi yace "Saboda ni jiya aka d'aura min aure, ina hutu."
Ganin tayi shiru bata da abun fad'a yasa shi wucewa yana fad'in "Duk kwanakin da kikayi ma ba kya zuwa da izinin wa?"
Da kallo ta bishi a ranta tana fad'in "Ya zanyi ma wannan yasan ina da cikin? Zai iya sakani gaba yana min dariya, a k'arshe ma yace na tsufa da haihuwa."
Iska ta furzar tace "Allah gamu gareka."
Yana daf da isa wajen Hajia Hamna ta shigo falon da alama daga waje take, riga da wando ne jikinta irin kayan nan na indiya, sai dai tsagar dake da rigar gefe da gefe har saman k'ugun ta, kallabin dake kalar wandon k'arami ne wanda ke saman rabin kanta, k'ura mata ido yayi yana kallo, har ta fice bata kula da tsiyarshi ba, juyawa yayi ya bita da kallo, shi kam ya fara gajiya da wannan yanayin da yake tsintar kanshi a ciki a duk sanda ya ganta, al'amarin girmama yake ba raguwa ba, har zuciyarshi canza salon bugawa take idan suka had'u. Hankalinshi yafi tafiya ga shigar data fita da ita, akan me Hamna bata jin magana? Me yasa ba zata taimaka mishi ba ta dinga rufe jikinta? Me yasa bata son kwanciyar hankalinshi ne? Hasalima bata damu da damuwarshi ba? *Ba zan lamunta ba gaskiya*, yana fad'in haka ya daka mata tsawa yace "Ke."
Hamna data fara taka makala ko juyowa ba tayi ba, da k'arfi ya sake cewa "Kankana ke."
Hajia dake zaune tana kallonshi ne tace "Wai kai ba zaka daina kiranta kankanar nan ba?"