Sashe 198
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"To me yasa ba zaka hukunta ni ta wata hanyar ba sai wannan? Kana so ka lalata ni ne?"
Saida ya jawota jikinshi yace "Babu abinda zai faru, kayana mallakina da ni kad'ai ke da hurumin shigarsu, nasan yanda zan ci gaba da tafiyar dake."
A daren bayan ya fita Sayyada ta zo tare da masu cake d'in da aka bawa suyi, shi kad'ai ma abun birgewa ne kamar kayi ta kallo, ga kyaututtuka daya mata na bazata da gigita tunani, tayi farin ciki sosai tare da mishi godiya.
*Rayuwa dama haka*, duk son kwalliya da k'walisar Hajia tsufa ya kasa barinta ta ci gaba, inda yanzu ta fara rud'ewa wani abun idan tayi sai an kalli juna, ita da Husseina zamu iya kiransu da tsofi masu taurin rai, dan har yanzu suna nan a cikin gidan ana ta damawa dasu ana kuma fama dasu, yanzu Ummy ce kawai mai fad'a a ji a gidan a cikin mata dai, komai sai ace Ummy Ummy, sai dai kuma yanzu gidan babu hayaniya kamar da, dan tunda Ammar ya tashi kowa ya k'wallafa rai yana so ya tashi, a hankali duk sukayi nesa dasu sai dai su kawo musu ziyara.
Har yanzu Amar na fama da Umaimah wacce ta kasa fahimtar inda duniya tasa gaba, sai dai farin cikinshi d'aya Farisa, babban sake da tayi shine barin Farisa ta fahimci irin zaman da suke, daga sanda ta gane saita d'auri niyyar faranta masa, kuma akan haka take yanzu, in dai ba larura ta yau da kullum ba bata yarda ya sameta da k'azanta ba ko da ba ranar aikinta bane, kullum cikin gyaran gidanta da jikinta take, shima kuma yanzu yayi wuri ya aje Umaimah idan ta fara bala'i saiya bar mata wurin, haka ya zage damtse kamar yaro shima yana ta kwasar soyayyarshi da ita, baya jin nauyi ko k'yashin yi mata abu ko million nawa yake, haka zaman nasu ke tafiya farin ciki a hannun dama bak'in ciki a hannu hagu.
Su Junaid ma da Salma da kuma Jibril da Jamila da Zeinab da Jamil duk dai rayuwa ce irin ta yau da kullum, yau farin ciki gobe bak'in ciki sai dai farin cikin shi yafi yawa, sab'ani ne da dama dole a same shi tsakanin mutane bare kuma ma'aurata.
B'angaren Amarya Huda ma tana farin cikin zamanta, kullum suka d'an samu sab'ani ko k'arami ne sai yace karta fad'awa tonton Ammar, dan ya samu labarinshi shi har ga Allah tsoronshi yake, da haka Huda ke tak'ama tana murza rayuwarta ita ma. Matsalar mahaifiyarta dai ce ke d'an mata cikas wani lokacin, duk da har yanzu a dangin mijinta babu wanda ya kalleta yace yar karuwa, amma tana jin kunyar kasancewarta yar Mari dan babu shiriya a gabanta, ta zo gidanta sau d'aya amma saida ta fito fili ta fad'a mata ta dinga canza shiga indai har zata zo gidanta, irin bala'in data gani a ranar kamar zata cinyeta d'anya, ita dai bata biye mata ba tayi ta gama sannan tace ta bata kud'in mota, ko da ta bata ta tafiyarta ko sallamar arzik'i basuyi ba.
Gambo duk da baya kan muk'aminshi amma har yanzu ana damawa dasu a siyaya, Hajia tace ya dawo amma ya kasa dawowa saboda ya saba zaman can, saidai ya zo yayi kwanaki har satittika ma sannan ya koma, Aissata ma na nan banda buga mulkinta babu abinda take yi, shiyasa aka ce *wata shari'ar sai a lahira*.
A k'arshe dai ta samu mijin aure bayan ta kwashe shekara *talatin* cir a duniya, kasancewarta mai k'aramin jiki yasa ba zaka ga shekarun a jikinta ba sai a fuska, Sayyada kenan (my besty na), Hamna sun shiga hidima sosai ba kama hannun yaro inda ta d'auki nauyin gyaran amarya da kanta.
Yau ake kamun amarya, kuma ta rok'i Ammar ya kaita yace babu inda zata je da tsohon ciki, saida ya fita ya bar gidan ganin a gidansu Hajia ne sunfi kusa da plaza kawai ta shirya tare da Ameera ta tuk'a motar Ummy suka tafi.
Bata tab'a tsammanin yasan mijin da zata aura ba dan bai tab'a fad'a mata ba, bata kula da motarsa ba a filin wurin saida ta shiga can ciki, hangoshi tayi cikin abokansu suna ta hira, rik'e Ameera tayi a hankali ta shiga juyawa da nufin su koma, saida ta sauka kan matakala ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, kallon Ameera tayi tace "Beby Allah ya taimakemu bai ganmu, yau da cire mana wando ta kai."
Dariya Ameera tayi tace "Ummy mu tafi to, ni ke nake tsoro ma yaje gida yayi ta miki masifa."
Dariya tayi ta kama hannunta suka sauka, saida ta kama murfin k'ofa zata bud'e ta shiga taji message ya shigo wayarta, ko da ta bud'a message ne kamar haka.
_"Mrs Ammar Gaga, tun kafin ki shigo numfashina ya canza salon bugawarsa, hakan ya tabbatar min kina kusantowa gareni, taya kike tunanin na barki sakaka da har zaki iya min satar hanya, kuje gida sai na zo zamu had'u, ki kula da kanki."_
Lahaula, shikenan ta *faru* ta *k'are*, kallon Ameera tayi tace "Baby ya ganmu fa."
Zaro ido tayi tace "Lah Ummy mun shiga uku, yau zamu sha bulala a gida."
*_Washhhhhh Allah, na tsaya iya nan, dramarsu kullum aukuwa take, kunsan waye Ammar nasan kunsan me zai faru idan ya koma, baya barin ta kwana kamar yanda baya mantuwa da yafiya, baya bawa mak'iyinsa baya sai dai ya tareshi duk a rugumtsuma, see u Ammar, yan matanka na nan lodi lodi birjik suna jiran amsar amincewa buk'atar aurensu daga bakinka, ni ban tab'a jarumi mai farin jini irinka ba ma, ga kuma santaleliyar k'anwa daka samu uwar yarinyata wacce ke shirye da take bayanka bata son b'acin ranka, ni kuma uwar d'akinka duk muna bada gaisuwa shugaba. Auntynmu Hamna gaisuwa gareki ta musamman, masoyanki na nan tare dake, Allah k'ara had'a kanku tare da baki hak'uri da juriya na zama da yayan uwar jaririyata, kishiyoyinki ma suna gaisheki tare da rok'on alfarmar ki barsu su shigo suma su samu nasu rabon d'inkin.🏃♀️🏃♀️🏃♀️*😂
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Yan uwa mun kawo k'arshen BADAK'ALA, sai mun had'e a SALAHADEEN da SARAH*