← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 198

Sashe 130

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta d'aga alamar eh, cikin fitar da kowace kalma take fad'a mata "Kiyi hak'uri ki koma d'akinki ki zauna, na miki alk'awarin zan sake dawowa ba da jimawa ba, wannan kukan yasa dama tun farko ban zo ba, amma idan kikayi shiru yanzu to zan sake dawowa kuma na taho miki da abinda kika fi so, zuwa lokacin nasan Hamna ta dawo kinga ita ma na ganta."

Turo baki tayi tana d'aga kafad'a da fad'in "Um um, um im, ban yarda ba ni gaskiya, kuma Hamna ma wa yasan ranar dawowarta."

"Au ba zaki hak'ura ba kenan?" Cikin turo baki tace "Na k'iya."

"Shikenan to nasan maganinki." Ta fad'a tana kallon inda Ammar ke tsaye, cikin d'aure fuska tace "Yarona zo ka min maganinta tunda bata jin rarrashi."

Takowa ya fara yi da k'arfi yana fad'in "Ai kuwa tanti bari kiga yanda zanyi da 'yar banza." Takalmanshi ya ciro yana shirin wurga mata da gudu ta koma d'aki tana rusa kuka, dariya suka saka mata inda tanti tace "Ai maganinki kenan, da kin kwantar da hankalinki da munyi sallama cikin farin ciki."

Suna nufa k'ofa Ammar yace "Tanti karki damu, insha Allahu zan kawo miki ita tayi sati d'aya, dan yanzu ta fara kumburo min baki kenan har illa masha allahu indai ba ganinki ta sake yi ba."

Dariya tayi tace "Auta ce ku barta tayi rigimarta, amma zaka iya barinta tayi sati d'aya ko?"

Kallonta yayi sai yaga ita ma kallonshi take kallo mai nuna na fa sanka ba zaka iya ba, sunkuyar da kai kawai yayi yana murmushin jin dad'in yanda ta san shi sosai tare da fatan ina ma mahaifiyarshi ce ta mishi wannan fahimtar, fita sukayi inda ya kaita gidansu dan ta gaisa da yan uwanta.

Kamar yanda ya fad'a kam ya cika alk'awari, ba tare daya fad'a mata ba kawai yace ta shirya, sai kawai ganin tayi sun d'auki hanyar garin, tunda ta ga haka ta fara murna tana jin dad'i sosai, da suka je saida ya wuni kafin ya juyo ya barota, murna a gurin Amna ba magana yau zata kwana tare da ummanta, ba ita kad'ai ba ita kanta tanti tayi farin ciki sosai, da dare da sukayi waya da Hamna ta fad'a mata gata nan ita kanta sai taji kamar tayi hira, anan take tambayarta me yasa yanzu ta b'oye lambarta in aka kirata sai dai ya nuna numéro unkwnon sannan me yasa bata Whastup? Haka kawai shine abinda ta fad'a mata, a wajensu Hamna ma da Ummy komai yana tafiyar musu daidai, sai dai basa cikin kwanciyar hankali, kullum Hamna tana fad'a ma Ummy idan fa asiri ya tonu tana jin tsoron abinda zai faru, ita ma kuma ta sani akwai gagarumar matsala, amma a ganinta lokaci ya k'ure musu.

Tanti Hadiza ta ga abinda yafi k'arfinta, bata san yaushe kuma a wane lokaci Amna ta zama marar kunya ba, dan tunda ta zo idan yau bai zo ba gobe zai zo, a gabanta saita rumgume shi ko ta sumbace shi, idan suka shiga d'akinta duk da babu abinda ke shiga tsakaninsu, amma irin yanda yake jin dariyarsu da maganganu k'asa k'asa abin nasa kanta girma, idan kuma dare yayi suna waya wani abun idan ta fad'a saita kalleta da mamaki, shiyasa yanzu daya shigo gidan ita kuma saita shiga mak'ota ko kuma ta shige d'akin mijinta ita ma, a haka ta kammala sati d'ayan nan suka koma gida.

Lieutenant ya fara mata k'orafi kan rashin dawowarta kan lokacin data fad'a mishi, amma sai take fad'a mishi basu gama bane ya k'ara hak'uri, har saida Hajia ta fara fad'a wanda Ummy tace kamar wak'a take jin fad'an nata, tunda dai har ta riga data tafi to anyi mai wuyar, a haka har lokaci ya k'ara kwararawa.

*Bayan Wata Biyar*

*France*: tunda ta shiga watan ta dama aka basu lokacin da za'a kawota kafin ta fara nak'uda, dan haka k'arfe *11: 54* suka shiga da ita d'akin haihuwa, Ummy bata san tana kuka ba saida wata banasariya ta dafa ta tace mata ta dinga mata addu'a zata haihu lafiya, tunaninta a lokacin shine idan fa aka samu matsala ya zatayi? Alwala ta d'auro ta shiga fad'awa Allah kukanta, bata matsa daga kan sallayar ba misalin *12:38* aka sanar da ita haihuwar Hamna lafiya, yaron bai dameta ba sai mahaifiyar da take tambayar ya take? Lafiya lau ita ma aka fad'a mata, saida tayi sujadar godiya ga ubangiji kafin ta shiga ganinta, murmushin daya sub'uce mata ne yasa Hamna dake kwance kallonta tace "Ummy lafiya?"

Dake tsaye inda take kusan gadon jaririn ta sake dariya taja hancin yaron tace "Ya rantse saiya zo duniya, gashi dai ya zo yanzu kuma *BADAK'ALAR* zata fara musamman mahaukacin ubansa yasan dashi."

Jim ta d'anyi saboda haushin Ammar data sake ji, har ga Allah tana b'oyewa ne dan kar Ummy taji ba dad'i, da k'yar ta kalleta tace "Kin fad'awa Abba ne?"

Girgiza kai tayi tace "Hamna ba zan sanar dashi yanzu ba, kema kin sani ina fad'a masa zai biyo jirgi ya taho, ni kuma ina so mu fara tafiya gida na d'an shirya ki da kuma ni saina kira na fad'a musu."

Shiru tayi kawai dan bacci ke son d'aukarta, saida aka k'ara tabbatar da lafiyarta da bebyn sannan aka sallamesu bayan an bata magungunan da zasu taimaka mata, suna zuwa gidan da suke Ummy ta zama mai haihuwar tare da anfani da duk abinda zai kawo mata ruwan nono wanda dama ta tanede shi saboda ranar, sai lokacin ta kira gidan ta sanar dasu, lieutenant yayi murna sosai da kuma fad'an rashin dawowa har haihuwa ta risketa tana nesa dasu, ya fad'a mata zasu zo tare da Hajia dan ba zai yarda ta taho yanzu ba, saita nuna masa ba komai kawai idan sukayi ko sati biyu zata dawo, tunda Zeituna ma gaf take da haihuwa bai kamata ya taho ya barota ba, da haka ya gamsu ya zauna sai hotunan yaro da suka game gidan da familyn cikin d'an lokaci.

*Gaga's house* da dare suna tafiya a hankali a cikin unguwar ya ga duk tayi sanyi sosai ba yanda ya saba ganinta, jawota yayi jikinshi yace "Lafiya? Me kike tunani?"

Saida ta d'ora hannunta kan k'irjinshi tana takawa a hankali tace "Hamna nake tunani, tunda na tashi yau nake tunaninta ina ji kamar wani abu na faruwa da ita, ta canza sosai amma kuma bata son yin doguwar magana da ni, bansan me yake damunta ba."

Shafata yayi yace "Karki damu kinji, watak'ila bata jin dad'in zaman gidan nan ne shiyasa, amma idan kina so saina kaiki ki ganta amma fa bayan kin haihu."

Murmushi tayi tace "Nagode."

Wayarshi tayi k'ara yana dubawa ya ga kiran Amar, yana d'auka Amar tsabar farin ciki da kuma tsokana yace "Kai yaro kana ina? Ka zo gida fa Ummy ta haihu."

Gabanshi kawai yaji ya fad'i ba tare da sanin dalili ba, amma saboda jaraba sai yace "Amar ni ne yaron? Ni ne dai yaro ko? To ka bari na dawo gidan zaka maimaita haka da bakinka."

Amar ne yace "Naji dai, yanzu ka duba WhatsApp d'inka na tura maka hoton bebyn, anan dai gida kowa ya damemu da cewa wai yafi kama da kai, ni kuma a ganina ai dani da kai duk d'aya ne."

Murmushi Ammar yayi yace "Hakane, amma ai na fika manyan ido, na fika dogon hanci, kai kawai gaskiya suka fad'a na fika kyau."

Yana fad'a kuma ya kashe wayar ya shiga WhatsApp, dannawa yayi foton ya fara alamar bud'ewa, fad'uwar da gabansa ya sakeyi yasa shi d'auke idonshi daga kan yaron, a hankali ya sake kallonshi idonshi bud'e kamar ba yaron da aka haifa yau ba, sanye da kayan sanyi masu hula safar k'afa data hannu, hancinshi tubarkallah zungurere. A hankali yake jin abun na shigarshi kamar sihiri, ba zai iya tantancewa ba k'auna ce ko soyayya, amma dai k'anan nashi ya shiga ranshi daga kallo d'aya, murmushi yayi ya jawo Amna yace "Kinga Ummy ta haihu."

Da sauri ta k'ura idonta tana fad'in "Na gani." Tana ganin yaron cikin farin ciki tace "Wow mai kama da jarumi na."

Kallon idonshi tayi tace "Kamar kayi kaki ka tofar wallahi."

Kallonta yayi, haka kawai yaji ya tsargu sai kawai ya share yace "Haka zaki haifo naki kema sak ni."

Ko da suka dawo gida sun samu anata wannan murna, lokacin Zeituna ma ita kawai tasan me take ji ana dai ganinta, saida dare yayi ta fara nak'uda sosai, likitar su Ammar aka kaita da gaggawa, ta jima tana nak'uda ta galabaita sosai, ana kiran sallah asuba ta haifo jaririyarta ita ma mai kama da ita gashi har saman goshinta luf luf, amma ana buk'atar k'ara mata jini dan ta rasa shi, lieutenant ne yace a duba nashi, har an duba za'a d'iba Ammar yace a d'ibi na shi, lieutenant yace "Ai akwai buk'atar a fara dubawa idan yayi daidai."

Murmushi ya masa yace "Ni fa jininka ne, ina da masaniya akan jininka da nawa Abba, amma in baka yarda a dararawa matarka ba sai an duba ni to a duba."

Dariya kawai lieutenant yayi, duk da haka da aka shiga ciki saida yasa aka gwada jinin sannan aka diba aka saka mata, tubarkallah masha Allah, a cikin kwana d'aya an samu k'aruwar yara biyu *Fatima Zahra* da kuma *Shureim*, fatan Allah ya raya.

*Bayan sati biyu*...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_47_

*Bayan sati biyu* yau Junaid ya tafi makaranta yana cikin koyarwa aka ce ana sallama da shi, yana fitowa yayi mamaki sosai ganin *Sani* tare da *Salma* a tare dashi, k'arasawa yayi suka gaisa ita ma ta gaishe shi, da mamaki yace "Tonton lafiya dai ko?"
Chapter 130 · 0% Book details