← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 198

Sashe 72

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak yaji tunaninshi ya tsaya kanshi ya kulle, sunan da zuciyarshi ta ambata ne yayi barazanar tafiya da numfashinshi, da k'yar ya iya had'a sunan Sss... al..m...a, k'ara waro ido yayi yace "Kenan Ma'arufa ce? Na shiga uku ni Abbas mena aikata haka?"

Ya d'an jima a wannan halin yana tunanin da sam babu mafita, yana cikin haka yaji wani sak'on ya shigo wayarshi, da sauri ya duba dan a tsorace yake, yana dubawa kuma me zai gani? Sabuwar lamba ce ta turo mishi hotunan Raihan tsirara, zunbur ya tashi tsaye ya rufe ido ya dafe kanshi yana so ya samu kowace irin addu'a a baki amma ya kasa, a karo na biyu sake sakin wayarshi yayi ya fad'i kan lallausan carpet d'in, voice not d'in da aka turo ne yayi saurin d'auka ya bud'e, tattausar muryar Saleem ce yace "Shin da kake nan zaune gida ka tura 'yarka can kasan me take aikatawa ne? To wannan ma sanfuri ne, nan gaba zan turo maka da video yanda nake mu'amulantar ta."

Cikin matsanancin sauri ya nemi lambar Raihan, tana d'auka daga can b'angaren cikin muryar dake son yin kuka yace "Kiyi gaggawa ki shirya kije airport, ki hau duk jirgin da kika samu ki dawo gida *Raihan*."

Tabbas Raihan ta tsorata dan kuwa bata tab'a jin ya kama sunanta ba, cikin sauri kamar yanda yace ta tattaro kayanta ta nufi airport d'in, tayi sa'ar samun jirgin da zai tashi zuwa Abuja, dan haka ta hau aka juyo da ita babu shiri.

Suna gama yawa ya sake yin zaune yana matsa k'irjin shi da yaji ya mishi bala'in zafi, tunanin abinyi yake nema har saida yaji lambar nan ta sake turo mishi da sak'o kamar haka _"Kayi gaggawar aurar da ita, idan ba haka ba zan kafa mata tarihi kuma mummuna, idan bakayi abinda nace ba wannan hotunan zasuje inda baka tsammani ne, domin kuwa zan d'ora su a kafafen yanar gizo ta yanda kowa zaiga tsiraicin 'yarka, a haka ma zata rasa mijin da kuka zab'a mata."_

Had'a kanshi yayi da gwiwa ba tare daya shirya amsar da zai bawa mai turo sak'on ba, shi dai kawai yasan alhaki ne ya fara biyarshi tun yanzu, dama ance idan kayi da 'yar wani za ayi da taka kaima, a hakan kuma yana ganin ko da ace Raihan bata tab'a sanin d'a namiji ba to angama dashi tunda har akaga tsiraicinta, kai shi sam bai ma yarda da babu abinda ya faru ba, tayaya namiji zai samu hotonta haka babu kaya a jiki inhar ba wani abu ne ya shiga tsakaninsu ba? Yana tsaka da wannan tunanin wani sak'on ya sake shigowa cewa _"Tunda baka da lokaci na zanyi abinda ya dace, da fari zan fara tura hotan a wayar mahaifiyarta, daga nan kuma zan sake shi duniya ta gani, ni ba kud'i nake nema a wurinka ba, ka aurar da 'yarka kawai ga wanda ka zab'a mata."_

Sai lokacin ya kira lambar Saleem na d'auka ya canza murya Abbas kuma yace "Bansan ko waye kai ba, amma dai nasan baka nufi na da alkairi, dan Allah karka saki hotunan nan domin kar mutumcin 'yata ya zube, nasan gabarka ba zata wuce dani ba dan haka ka d'auki fansarka a kaina, dan Allah karta shafi iyalina."

Cike da izza yace "Ka fad'i gaskiya, amma ka sani ba zan huce ba har sai naga ka tara taron jama'a zasu shaida d'aurin auren 'yarka."

A tak'aice yace "Zanyi, zan d'aura mata aure da safiyar gobe da Abdul, ban buk'atar had'uwa da kai, amma dan Allah ka goge hotunan nan daga wayarka, ba mutumcin 'yata bace harda ni kaina."

Cike da dariyar iskanci ya amsa da "Saina gani idan kayi abinda nace."

Makullin mota ya zara tare da takardar da Ma'arufa ta bashi yayi gaba ya bar gidan, a hanya tunani kawai yake wanene kuma wannan? Shin tarbiyar daya bawa Raihan kenan? Meyasa haka ta fara faruwa dashi? Wayarshi ya d'auka ya duba takardar nan ya turawa Ma'arufa wannan kud'in, bayan kud'in sunje yana ganin tana kiranshi amma ya k'i dagawa harya isa gidan, falon Sameera ya zarce ya sameta zaune ta gama waya da Bashir tana tambayarshi ko yasan abinda ke faruwa, amma yace mata bai sani ba tun jiya ma da rana rabon da su had'u, tana ganinshi ta mik'e da sauri tana fad'in "Abban Ameer sannu da zuwa, lafiya ka fita daga gida cikin sauri haka?"

Saida ya kalli falon da kyau kafin ya kalleta yace "Idan Raihan ta zo kice ta same ni a falo na."

K'ofar da zata sada shi da falonshi ya nufa ita kuma tace "Raihan kuma? Amma ai bata nan, ko ka manta ne?"

K'ala baice mata ba harya shige, ita kam mamaki da damuwa ne suka hanata zama sai kai da kawowa, haka yara suka dawo daga islamiyya suka sameta, kiran Harira tayi ta had'a ta dasu ita kuma ta ci gaba da tunani, tana haka taji sallamar Raihan, tana juyowa ta ganta da jaka ta kinkimo cikin doguwar riga sai d'an siririn d'an kwalin data d'ora, da sauri ta k'araso ta rumgumeta tace "Ammie na, ya kike?"

D'agota tayi daga jikinta fuskarta cike da damuwa tace "Mamana lafiya? Meyake faruwa ne? Ya kika dawo haka kwatsam? Meyasa Dadynki ke nemanki?"

Cikin sanyi tace "Ammie i don't know, nima kawai Dady ya kirani a waya yace nayi gaggawa na zo, i hope komai lafiya?"

Girgiza kai tayi tace "Ba nace ba Mamana, amma kije yana son ganinki a falon shi."

Ba tare da tunani ko damuwar komai ba ta aje jakarta ta nufi k'ofar tana fad'in "Ok Ammie."

Da sallama ta shiga falon, ganinshi zaune ya d'ora gwiwar hannunshi kan k'afafun shi kanshi k'asa ya had'e hannaye, sai kuma k'afafun shi da yake d'an bunbugasu, sallama uku tayi amma bai iya amsa mata ko d'aya ba, tsoro ne ya fara ziyartar ta amma a haka ta k'arasa kusa dashi ta zauna k'asa cikin taushin murya da sanyi tace "Dady?"

D'ago kai yayi ya sauke kanta, gabanta ne yayi muguwar fad'uwa saboda ganin idonshi jawur kamar yayi kuka, mik'ewa yayi ya shiga bed ya dawo hannunshi rik'e da wata sharb'eb'iyar waya data sanya gudun gabanta tsananta, yana zuwa zaune ya sake yi ya kalleta ya d'auki wayar shi ya mik'o mata cikin rawar murya yace "Raihan waya d'aukeki hotonan?"

Hannu tasa ta karb'a danta gani, da sauri ta dafe k'irji ta d'aga kai ta kalleshi sai taji wata kunyarshi ta rufe ta, sake kallon hoton tayi ta k'ura musu ido, ita ce ke wanka kuma ba'a ban d'akin gidan nan ba na basraba, to kenan waya d'auke ta? Waya bibiyeta haka? Tana cikin kallon taji tsawa daga Abbas tare da kashe ta da mari yana fad'in "Nace waya d'auke ki wannan hoton? Gaban wani d'an iskan kika tub'e?"

Sakin wayar tayi ta dafe kunci hawaye wani na bin wani ta kalleshi a firgice, d'an siririn hannunta ya fizgo ta matso daf dashi cikin k'arajinmurya yace "Ba dake nake magana ba Raihan? Ke yanzu har ni zaki zubarwa da mutumci? Ina ganinki luf-luf yanzu nan ke har kinsan namiji? Raihan meyasa baki fad'a mana kina son aure ba? Amma shine zaki fita waje kina iskanci har ana d'aukar ki ana turo min da hotunan."

Tsaye ya mik'e ya fara zabga mata bulalar nan baji ba k'akk'autawa, Raihan da zafi ya ratsata ta ko ina kuka take tana fad'in "Wallahi Dady ban san waya d'auki hoton nan, ka yarda dani ban tab'a iskanci ba a rayuwata, dan Allah Dady kayi hak'uri karka kashe ni."

Sameera da taji kukan Raihan da gudu ta shigo falon, ta taho a sukwane zata tunkarosu ya d'ago ya d'aga mata hannu da cewa "Wallahi kika k'araso nan dake zan had'a."

Tsayawa tayi tana kallo ya sake cin gaba da dukanta yana fad'in saita fad'a mishi ubanwa ya koya mata iskanci, da gudu Sameera ta sake fita sai part d'in su Ammie, ta sameta tana shirin kabbara sallah azahar, ai tana fad'a mata suka rankayo tare suka shigo, da k'yar Ammie ta dakatar dashi kafin ya tsaya cikin b'acin rai ya kallesu yace "Ko ku shirya ko karku shirya gobe zan aurar da ita kafin ta ja min abin kunya."

Bed d'in shi ya shiga Sameera tayi kan Raihan dake kwance tana kuka, kamata tayi cike da tausayi tana kallon jikinta da duk ya canza ya fita hayyacinshi, tashinta tayi suka tafi d'akin ta ta kwantar da ita, zage mata zuf d'in rigarta tayi ta cire mata ya rage sai bras d'in ta da pant kawai, kallonta Sameera tayi da kyau tace "Raihan ki fad'a min gaskiya, shin kin watsar da tarbiyyar da muka baki ne?"

Zaune tayi ta janyo blanket d'in kan gadon ta rufe jikinta tana kuka tace "Wallahi ban zubar ba, Ammie bansan ya akayi hoton tsiraici na ya fito ba, Ammie ki yarda dani dan Allah."

Sunkuyar da kai tayi tace "Ba zan iya yarda dake ba Raihan, domin kuwa yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba."

Ammie dake tsaye ne cike da jimami tace "Ki had'a mata ruwa tayi wanka."

Mik'ewa Sameera tayi inda Ammie ta kalli Raihan da duk jikinta ya sauya tace "Kinsan da gobe yace zai d'aura aurenki da Abdul?"

Da sauri ta kalleta kamar zatayi magana sai kuma tasa kuka tace "Ammie ba damuwa na amince, ni kuma zan tabbatarwa da iyayena a budurwa naje gidan mijina."

♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Tun daren jiya Ma'aruf daya fad'awa Meena aikinsu ya kammala ta dinga saka mishi wani tunani tana nuna mishi dukiyar nan fa kamata yayi ace tashi ce shi kad'ai, farko baisa abun akai ba dan ba zai iya cutar da yar uwarsa akan dukiya ba, amma da dare suna zaune d'aki shi da Ma'arufa ya kalleta yace "...

👏👏👏
22/06/2020 à 17:26 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💞 _Kyautarku ce_💕
Chapter 72 · 0% Book details