← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 198

Sashe 188

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ta saki daga nan zaune dan ta fahimci ina zancen ina ya nufa, har ya gama cin abinci suna ta hira dasu Husseina da Hajia, bayin Allah dariya har rik'e ciki sukeyi, sun daddage sai biye mishi suke yi kam, idan ya fad'i wani abu ita kanta Hamna da Ummy sai sun murmusa ko har ma su dara, amma duk da haka bata kalleshi ba bare ta mishi magana. Saida dare yayi sosai kowa yayi haramar nufa inda zai kwantar da hak'ark'arinshi, ta mik'e ta nufi d'akinta na yan mata wanda Nazifa ce a ciki yanzu da Huda shima ya bi bayanta, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace "Ya dai kake biyata malam?"

Wani kallo ya mata yace "Ke kike bina ko ni ke binki?"

Girgiza kai kawai tayi ta wuce, ko da suka shiga suka same su kwance kan gado d'aya Huda har ta fara bacci, wucewa yayi ya kwanta kan gadon Hamna, kallonshi tayi da mamaki cikin rad'a tace "Meye haka malam? Baka ga yara ne?"

Rintse ido yayi yace "Ban gansu ba."

Juyawa tayi ta kallesu sai taga Nazifa ta mik'e zata fita, da sauri tace "Ke dawo kwanta wajenki, ina zakije ke da nan ne wajen baccinki, bak'on daya mana haure shine zai fita."

Ko da ta fad'a ta shige ban d'aki da kayan baccinta a hannu, da murmushi ya bita ya kalli Nazifada ta dawo ko ta koma ta kwanta, bata jima ba ta fito ta aje kayan data canza kan kujera, kan gadon da suke kwance taje ta shige tsakiyarsu tana fad'in "Ku matsa min nima."

Bud'a ido Huda tayi ta kalleta ta hangi gadonta, saida gabanta ya fad'i ganin tonton d'in ta kan gadon a dakinsu, juya baya tayi ta yanda take kallon k'ofar shigowa ta matsa mata, wajen k'afafunsu ta maido kanta ta d'ora matashi ta kwanta, ta lik'e ido taji muryarshi tsaye a kanta yace "Ku matsa min nima."

A tsorace suka tashi zaune tare ban da Hamna data san halin kayanta, kallonshi sukayi ya kuwa tsaya kusan kanta rik'e da pillow shi ma, Nazifa ce tayi saurin wuntsilawa ta sauka daga gadon ta nufi hanyar fita, da sauri Huda ta tashi ita ma ta bi bayanta suka fice Nazifa na fad'in "Yau mun shiga uku, to su kna d'akinsu wai?"

Cikin turo baki Huda tace "Muje d'akin Hajia kawai mu kwanta."

Ko da taga sun fita ta mik'e ita ma da niyyar bin bayansu, da k'arfi yayi tsalle ya fad'a kanta hakan ya tilasta mata fad'awa kan gadon da k'arfi, da k'arfi tace "Aouch."

Kafin ta bud'a ido taji yayi kwance kanta gaba d'ayanshi ya kuma sakar mata nauyinshi, yanda ya tausheta yasa ta kasa yin numfashi mai kyau, bud'a ido tayi ta kalleshi tace "D'aga ni."

Girgiza kai yayi yace "Zaki koma d'akinmu?"

Girgiza kai ita ma tayi tace "A'a, har sai na yarda babu komai tsakaninka da Amie."

Da k'arfi yace "Babu komai kankana, taya kike tsammanin zanyi iskanci a waje bayan ina da ke? Sannan na rasa da wanda zanyi iskancin ma sai k'awar ki? Na yarda ni mahaukaci ne kuma ba mutumin kirki ba, amma bana neman mata Hamna kuma bana shan ko da sigari bare k'waya."

K'afeshi tayi da ido tana kallo, kallon tausayi da jin k'ai da rahama, wa yace shi mahaukaci ne? Dan tana fad'a masa haka ai kawai tana fad'a ne, me yasa zai yarda shi mahaukaci ne kuma ba mutumin kirki ba? Bata ji dad'in abinda ya fad'a ba, a hankali cikin fitar da wahalallen numfashi tace "Wa yace kai ba mutumin kirki bane?"

Saida ya k'ank'ance idonshi yace "Ke mana, haka kike kallona ai."

A hankali ta d'aga hannunta ta shiga shafa fuskarshi a hankali tana kallonshi, cikin taushin murya sosai tace "Kai mutumin kirki ne Abban yarana, duk gidan nan muna alfahari da kai, dalilinka ne abubuwa dayawa suka canza, ka daina wa kanka wannan kallon, kaji? Ka daina bana so."

Yanda ta k'arashe maganar da matuk'ar shagwab'a da kashe murya yasa shi jin zuciyarshi ta k'ara narkewa, murmushi ya saki yace "Amma duk da haka ai baku sona."

Idonshi ta kalla tace "Waya fad'a maka, muna sonka yah Ammar, muna k'aunarka dukanmu."

D'aya hannun tasa ta tallabo fuskarshi suna kallon juna sosai tace "Ammar *ina sonka*, d'azu nayi niyyar fad'a maka haka, amma wannan Amien..."

Ture shi tayi daga jikinta ta tashi zaune tana kallonshi, shi ma kallonta yake yana jin kamar ya fasa ihu yau Hamna ce tace tana son shi? Yana kallonta ta tashi tsaye tana fad'in "Saina fara cin uwar yarinyar nan kafin hankali na zai kwanta, sai naji abinda ya had'ata da mijina."

Tasowa yayi yana k'arewa fuskarta kallo yana fad'in "Hamna ni kike kira mijinki? Wuuuuu duniya dad'i, Hamna yau nine kike so? Kishi na kike?"

Da sauri ya d'auki wayarta dake kan kujera ya bud'e ya shiga danne danne, tana kallonshi ita dai sai ji tayi ya saka wak'ar *Umar m Shareed* mai taken *soyayya akwai dad'i*, aje wayar yayi sai kuwa ya shiga kwasar rawa ba kunya ba tsoron Allah, da fari da mamaki ta fara kallon yanda yake rawar, amma sai abun ya fara bata dariya, zaune tayi bakin gadon tana kallonshi, tsakaninshi da Allah yake rawar kamar ya ga *Adam A. zango* a gari, bata ankara ba taji ya jawota yana juyata a dole ita ma tayi rawar.

Tun tana tirjewa tana so ya rabu da ita har wata wak'ar ta shigo wacce ta iya taka rawarta fiye da zaton mai karatu, (in baku manta ba tun a farkon littafin ita d'in gwanar rawa ce da iya shoki😂), biye masa tayi suka shiga rawa har da dariya kamar mahaukata.

Ummy da tasan sai sun tsula tsiya tunda taga ya shiga d'akin, kuma a gaban idonta su Nazifa suka fito, ta jima tana k'wank'wasa k'ofar amma basu ji ba, kuma gashi tana jin dariyarsu da sautin kid'a, dan haka kawai ta tura k'ofar ta shiga idonta rufe dan kaucewa mummunan gani, a hankali ta bud'a ido ta hange su sun cake sai kwasar rawa, rik'e baki tayi tace "Inna lilliahi wa'inna ilaihi raju'un."

Da sauri suka tsaya suna kallonta, ko da ya ga Ummy ce ya matso yana fad'in "Ummy albishirinki?"

Ta d'auka zai ce Hamna ce ke da ciki, sai kawai ta kalleta tace "Hamna wace lalacewar ce kuma wannan? Rawa a daren nan?"

Laushi tayi kamar ba ita ba tana k'yabta ido, jinjina kai Ummy tayi tace "To maza d'auki kayanku ku koma b'angarenku kafin ku tara mana aljanu, tunda abun ya zama iskanci, nan kike ta kumbura ke hushi kike ashe d'aurin duniya ne."

Langab'e kai tayi tace "Allah Ummy da gaske ne, yanzu ma da zan ga Amie saina tattaka ta."

Kallonta Ammar yayi yace "Wai ke ba zaki fita harkar yarinyar nan bane?"

Zaburo mishi tayi tace "Eh d'in ba zan fita ba, sai naji dalilin da yasa ta kula ka."

Kallon fahimta ya mata yace "Ki tabbatar zaki b'arar min da ita?"

Cike da tabbaci tace "Allah kuwa zan iya."

Kallonta yayi da kyau yace "Gobe da safe ki shirya idan zan fita na kaiki gidansu, zan so ganin yanda zaki d'auketa ki nunawa sama ta bakwai kafin ki dirota k'asa, dan ni abun farin cikina ne ace matata na fad'a akai na, kinji ko?"

Cikin murna tace "Da gaske?"

Ba alamar wasa yace "Ina fad'an abinda ba zan iya bane?"

Da farin ciki tace "A'a."

"Dan haka ki shirya zan kaiki." Ko da ya fad'a ya juya zai fita, ita har ga Allah ta ma manta wai yaji tayi, kallon Ummy tayi tace "Saida safe Ummy."

Rik'o hannunta tayi ta dawo da ita baya tana fad'in "Zo nan."

Kallon juna suka shiga yi Ummy tace "Hamna ina yace zai kaini? Gidansu Amie fa naji yace."

A hankali tace "Eh Ummy."

Da mamaki Ummy tace "Anya kuwa Hamna kina so mu zauna lafiya dake? Ke fad'a min me kike so ku zama yanzu?"

Shagwab'e fuska tayi tace "To naji Ummy ba zamu je ba."

Tab'e baki tayi tace "To yanzu binshi ne zakiyi?"

Da sauri ta juya ta nufi kan gadon tana fad'in "A'a Ummy, bacci zanyi."

Nufa kanta Ummy tayi tana neman abun bugu tana fad'in "Hamna zan ci ubanki a gidan nan, tashi wuce ki bi mijinki, na gaji da masufarku wallahi karku kashe ni da raina."

Da gudu ta arta ta fito daga d'akin, ko sauka bai gama ba daga matakala tayi tsalle da niyyar haye bayanshi, shi kuma da baisan da zuwanta ji kawai yayi yayi sungululu ya tafi ta kai suuuu.😂😂😂😂😂

*Tsakaninku ne*

Bashi daya rigata ba har ita san da kai tayi duk suka wuntsile a wurin, saida suka gama durkuwa k'asa suka fara kallon kansu dan ganin salon fad'uwar, Ammar😂 da yaji kamar wuyanshi ya karye kallonta yayi, tana zaune kan matakalar ta rik'e k'afa da hannu tana kukan shagwab'a, wani huci ya shiga saukewa da tunanin me ma zai mata ne shi kam, shin ya d'auke ya jujjuyata sannan ya dasata a k'asa, ko kuma ya sake hawan benen da ita sai ya sakota ta fad'o, ko kuma...

*Uwar Lalla ranar da aka kawoni gidana haka na kusa tahowa ta kai na karya wuya😂 amma tuni angona ya cab'oni aradu ta baya, kai bene baiyi ba.*

Ummy dake tsinkayensu ta sama tana jiran taga me zai faru, tashi yayi a hassale yana fad'in "Ke dan ubanki ni kika wuntsilo? Hamna ni kikawa wannan wurgowar? Ashe k'arfin tsiya ne dake kamar bagwariya, ai kuwa yau zaki c..."

Da sauri Hamna data kasa tashi saboda k'afarta ta bud'e hannayenta ta jawoshi da k'arfi har yana neman fad'awa kanta, bai gusar da fuskarshi daga kanta ba yana mata kallon mamaki yaga ta k'amk'ame shi tana fad'in "K'afata! Wayyo Allah k'afata, yah Ammar ka taimaka min dan Allah."

Kallon fuskarta yayi kawai yaji a ranshi ta gama dashi, kallon k'afar yayi wacce ke rufe da dogon wando, sake kallonta yayi yace "Ciwo take miki?"

"Eh." Ta fad'a tana rushewa da kukan shak'iyanci, d'aga kai yayi ya kalli Ummy sannan ya kalleta yace "Bari Ummy ta taho saita kaiki d'akinki, ni dai ba zan d'auke ki ba."
Chapter 188 · 0% Book details