← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 126

Sashe 99

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kasa bacci sai tunani yake, kamar yadda yaga rana haka yaga dare, sai kusan karfe 6 na safe sannan ya samu bacci wahala ta É—auke sa.

A fannin shima Romeo bai yi baccin ba, ya kwanta yana ta tunanin yadda aikin zai kasan ce, sai yiwa yaran sa fatan nasara yake, duk da yana da kwarin gwiwa a kan su, Yasan sun samu horo, bai taɓa turasu aiki basu yi nasara ba, sai dai babban damuwar sa ɗaya ba tare da Tga zasu tafi ba, kasan cewar Tga na kwance a gadon masu jinya, daddy na dubasa, wajen da kwarin nan suka harbesa ya kumbura sosai, abun dai sai addu'a dan kuwa ko wando baya iya sawa, yana kwance yana baje yana shan iska, gashi yaki tsayawa a wani duba shi ma saboda raɗaɗin azaba, duk wannan Romeo bai sani ba, bai san cewa Tga yaki tsayawa a bashi kulawar da ya dace ba, da tuni yaje da kan sa ya danne sa ya bashi kulawa da kan sa, sai dai bai sani ba, kuma duk suna tsoron faɗa masa shi yasa, shi kuma bai cika shiga harkan yan gidan ba kullun yana ɗaki, in dai ba kai ka nemo sa ba, to shi baya neman kowa, ɗan gara Triplets na sa da kuma daddy, idan ya wuni bai ji motsin su ba yana kiran su a waya yaji lafiya.

Haka dai shi ma ya kwana ido biyu ba bacci, yana ta tunanin yadda tafiyan yaran nasa zai kasan ce ba Tga ,wannan ne dalilin da yasa jiya da daddare ya kira James dan ya duba masa jikin Tga ɗin sai kuma ya mance da me yasa ma ya kira James ɗin, shiyasa ya miƙe ya bar james zaune a wajen.

Asuba ta gari

Wannan kenan bari mu leƙo su Jelly mu dawo muga cakwakiyar familyn William jacop.

💞NIGERIA💞

JELLY

Yanzu ta É—an fara sakewa da gidan tana iya zama ita kaÉ—ai, inma a bedroom ko a palo, sai dai fa har yanzu bata wanka da kan ta kuma bata cin abinci da kan ta, sai dai Hajiya ta mata wanna dukka.

Yauma kamar kullun tana zaune a palo ita kaɗai tayi shiru tana kallon Tv ana labarai, duk da ba gane abun da ake faɗe take ba, ta zuba musu ido kamar ta san me ake cewa, yayin da news ɗin ke magana a kan ɓatar ta, dan daddyn ta ya shiga damuwa over, shiyasa har gidan Tv a ka kai zancen, ana cab da sanya hoton daddyn ta, wannan tantiriyar budurwan ta shigo palon babu ko sallama, hakan yasa hankalin Jelly ya kau daga kan Tv ta koma kallon yarinyar, while a Tv kuma an sako hoton ta dana daddyn ta

zubawa attachment ɗin kan yarinyar ido Jelly tayi tana mamaki, ganin babu kowa a palon yasa yarinyar tace da Jelly "Ke zonan" turo baki Jelly tayin kafin ta make kafaɗa tace "A'a ni ba zam zo ba" shiru yarinyar ta ɗan yi tana tunanin yadda zata yi da Jelly ta fara bin ta ɗaki, can wata dabara ta faɗo mata, hannu tasa cikin Jakarta ta fito da chewing gum da take yawan ci, ta miƙawa Jelly, ba musu Jelly ta miƙe ta karisa wajen ta, ta sanya hannu ta karɓa chewing gum ɗin tana dariya, dariya irin na yan duniya yarinyar tayi kafin tace "Yauwa ki saki jikin ki dani ko? Ni auntyn kice, daga yau in nace kiyi abu, ki rinƙa yi zan saya miki sweet kala kala kinyi?" Tayi maganar tana shafa kan Jelly zuwa wuyar ta, Gyaɗa mata kai kawai Jelly tayi tana faman tura chewing gum a baki, murmushi shakiyanci yarikyar tayi kafin ta ɗan duƙo da kan ta, dai dai saitin goshin Jelly kasan cewar ta fi Jelly tsawo, ta mannawa Jelly kiss a goshi tana shafa wuyar ta, ta wuce part nasu, wucewa itama Jelly tayi ta koma cikin bedroom na Hajiya.

Hajiya na kwance Jelly ta faÉ—o mata É—akin babu ko sallama, Hajiya bata damu ba dan ta É—auki hakan a matsayin dan Jelly bata da lafiya ne, bata san Jellyn daddy ba already haka take daman.

Hayewa saman gadon Hajiya tayi ta fara gaya mata yadda suka yi da wancan yarinyar, zubur Hajiya ta miƙe zaune tana kallon ta dan tasan halin afnan sarai, ta santa yar lesbian ce dan kuwa har ita kan ta Hajiya sai da afnan tayi mata tayin lesbian a baya, Hajiya batayi kasa a gwiwa ba taci mata mutunci fes shi ne yasa yanzu Afnan bata mata magana a gidan.

Miƙewa tsaye Hajiya tayi, ta diro kasa daga saman gadon rai a matukar ɓace ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin su Afnan, da sauri Jelly ta sauko kasa ita ma tabi bayan Hajiya.

A palon part na su Afnan Hajiya ta tsaya, ta fara kwalawa Afnan kira, da sauri mahaifiyar Afnan da yaya ta da ita kan ta Afnan ɗin suka fito suna tambayar ko lafiya Hajiya ta shigo tana ihu hakan, rai a matukar ɓace Hajiya tace "Ke Afnan wlh summa wlh ki fita harkan baby, babu ruwan ki da ita, na rantse miki da Allah idan kikayi gigin taɓa hannun yarinyar nan zan nuna miki yadda ake bariki, karkiga kina yin duk abun da kikaga dama a gidan nan muna zuba kiki ido, wlh ba wai kinfi karfi na bane, dan dai kawai bani da lokacin kine, amma a kan baby ina da lokacin ki daga nan har illah masha Allah, ke in takaice miki zance wlh zan iya komai a kan baby" kallon sama da kasa Afnan tayiwa Hajiya zatayi magana mahaifiyar ta ta rigata da cewa "Ke Hajiya Turai bafa tsoron ki muke ji ba zaki zo ki wani tayar mana da hankali a kan wancan shegiya tsintaciyar magen, daman ina cike dake a kan yarinyar, dan Alhaji yazo jiya yana wani ce mana kin kawo yarinya dan Allah kar yan gidan nan su takura mata, to yarinyar yar kanwar uwar ki ce? Ko ma yar kanwar uwar ki ce idan bata mana ba sai munci uban ta a gidan nan bare kuma naji Alhaji yace wai tsintar ta kikayi, to wlh tsintaciyar mage bata isa ta zo tace zata takurawa yan gida ta hana su jin daɗi ba kinji na faɗa miƙi, Afnan kuma koma me tayiwa yarinyar dedene, Afnan ki ci uban ta dan ba gidan uban ta bane, na uban kine" ita maman Afnan a tunanin ta rigima ake dan Afnan ta daki Jelly bata san kan magana ba

Aliyu yayan Afnan ne yace "Ummi kiyi hakuri kije, dan Allah komai ta wuce haka kinji?" Ita kuwa Hajiya jin abun da maman Afnan tace yasa tayi tunanin kenan da sanin maman Afnan, Afnan ke yin lesbian? Ta tambayi kan ta tambayar da babu amsa, amma a zahirin gaskiya maman Afnan bata san Afnan na wanna aika aikan ba, shikan shi yayan nata bai sani ba, su suna tunanin duk wannan masifar da Hajiya keyi tanayi ne dan Afnan ta daki Jelly, basu san dawar garin ba, shi yasa maman Afnan ta zage dantse dan tarewa yarta faÉ—a, shi kuma yaya Afnan kasan cewar baya son hayani sai yayi ta basu hakuri.

Da kyar ya samu Hajiya ta hakura ta wuce ta koma part nata, tana shiga palon ta ta samu Jelly zaune tana kallon Tv, da Jelly ta fito ne zata bi Hajiya, sai taga ana nuna cartoon a Tv sai ta zauna kallo.

Hannun ta Hajiya ta ja suka bar palon zuwa nasu part ɗin. A palon part nasu Hajiya ta zauna ta zaunar da Jelly gefen ta, cikin nitsuwa tace "Baby daga yau karki sake fita babban palo bana so, kiyi zaman ki a nan, ga Tv nan zan rinƙa kunna miki, kuma idan wani ya sake cewa ki zo a gidan nan karki yarda ki je, ba ruwan ki da kowa karki sake yiwa kowa magana daga ni sai Abbo sai yaya Nawid, mu kaɗai zaki rinƙa yiwa magana, kuma mu kaɗai ne idan munce kiyi abu zaki yi kin ji ko?" Kai Jelly ta gyaɗawa Hajiya alamar taji.

Cab lalai Hajiya kin kashe maciji baki sare kai ba, dake da Abbo da Nawid ne kawai zaku mata magana tayi abun hmmm, muje zuwa.

Wunin ranar dai Jelly bata sake leƙa babban palon ba tun safe da abun ya faru, a nan tayi zaman ta har dare, idan ta gaji da zama ta kwanta, idan ta gaji da kwanciya ta shiga bedroom ɗin Hajiya su ɗan yi hira, Hajiya na koya mata karatu, amma fa ba abun da take gane wa.

Da daddare suna cin abinci ne Nawid ke sanar da Ummi zai yi tafiya zuwa Katsina next week, kasan cewar Hajiya Turai ya ce ga sarkin matsina, Nawid jikane ka sarkin, hakan yasa yake yawan kaiwa kakan nin sa ziyara

Da fara'a Hajiya ta amsa masa da to dan tana son daman zumuncin ta da yan uwan ta maza da Æ´aÆ´an su ya kara karfi sosai yafi haka,

Yanzu Nawid na daina hantarar Jelly dan ya fahimci haka take, kuma abun ya haɗu mata da ciwo, shi yasa baya damuwa idan tana wani shagwaɓar nata, yanzu in tace masa yaya yana amsawa har ya biye mata, dan Hajiya ta masa kanwar dole, kuma haka ya karɓa ba yadda zai yi, wani lokaci ma idan Jelly ta tayar da ballin ba zata ci abinci da hannun ta ba, shi yake bata a baki da kan sa, ko Abbo.

Bayan sun kammala cin abin ne kowa ya miƙe ya nufi bedroom nasa, ita kuma Hajiya ta riƙo hannun Jelly suka tafi bedroom nata, dan sun saba sai Jelly tayi barci Ummi ke mai data bedroom nata, dan bata yarda tayi barci ita ka ɗai, wani lokaci kuma a bedroom ɗin nata suke zuwa su kwanta har sai tayi barci, sai su salallaɓa su fice su koma nasu bedroom ɗin.

Yau Hajiya ta gaji sosai, suna kwanciya ba jimawa barci ya É—auke ta, saura Abbo da Jelly, daman Jelly na ta gefen Hajiya, ma'ana Hajiya ce a tsakiyar su.
Chapter 99 · 0% Book details