← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 126

Sashe 49

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin su Abba sun ƙi yi masa magana ne yasa ya sanya hannun sa yana kokarin cire hannayen su daga kan abincin da idon sa ke gane masa shi suke ci, dan shi ɗanyen nama da kwari da tsutsotsi yaga su Abba na ci, su kuma ganin abinci masu kyau suke a saman table ɗin. Tashin sense

Da karfi Imran ya ja hannun Abba da niyar cirewa daga plate ɗin, kamar daga sama yaji saukan bulala a tsakiyar bayan sa, ihu ya fasa bai san lokacin da yace "bura uban nan kai uban waye ya dake Ni?" Bai gama rufe baƙi ba aka sake shinfiɗa masa wata bulalar a wuyar sa da karfi, razanannen kara ya saki, cikin fitar hayyaci yace "Bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah kulhuwalkahu ahad kulya ayuhal kafirun Alhamdulilahil laji an zala fi hil Quran" tsabar azaban bulalar ne yasa shi furta wayan nan kalamai, da bai san me bakin sa ke faɗe bama, Abba da Hajiya Suna kallon meke faruwa da Imran ɗin har wanda ke zane sa suna kallo amma ba halin magana, shi kuma Imran baya ganin komai sai saukar zabga zabgan bulalu kawai yake ji a jikin sa, sai ihu yake yana sambatu, amma duk gidan ba mai jin sa sai su Abba,

Kewaye palon Imran ya farayi ya rasa gane kofar fita sai ihu yake su kuwa dodannin ba tausayi ba imani haka suka rinƙa shin fiɗa masa wan nan zabga zabgan bulalun nasu mai bala'i zafi a jiki, duk sun fashe masa jiki, duk in da yayi sai saukar bulala zai ji

da kyar ya samu ya gane kofar fita a guje kamar wani zararre yayi waje yana gudu yana ihu ya É—age jallabiya sama, yana wurga dogayen kafofin sa bai san ma in da ya nufa ba, kai tsaye sai toilet É—in baba mai gadi ya shige, ya samu bayan kofa ya tsaya yana mai da numfashi tare da jan majina.

Su kuwa dodannin yana fita suka kyalesa suka koma kan Abba da Hajiya, Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara....✍️

💞TRIPLET'S💞

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*THE BEGINNING*

💞*STAR LADY*💞

EPISODE 16

________________________________

Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara zabga mata bulalun sai ihu take, sauran dodannin kuma suka damko Abba suka kwantar da shi kusa da Hajiya suka hau zabga musu bulalun,

dai dai lokacin Akil ya shigo palon yana sauraron kira'ar sudais a wayar sa ya kure volume, shi ma yinwan dare ta tashe sa, jin kira'ar yasa dodannin ɓacewa ɓat, kamar kuma yadda suka ɓace haka suka ɓace da tunanin su Abba.

Ganin su Abba kwance a tsakiyar palon ne yasa Akil karisowa wajen da sauri yana faɗin "Abba Ammie lafiya kuka kwanta a palo yau kuma?" Shiru sukayi basu amsa masa ba, mamaki ne ya kara kama shi yasa hannu yana taɓa su, yana kiran sunan su.

Hajiya ce ta fara tashi a nitse kafin Abba ma ya tashi, "Abba me yasa kuka kwanta a Palo?" Akil ya jefo musu tambaya, kallon juna sukayi kafin su ɗaga ido suna kallon Palon, da mamaki har suna haɗa baki wajen cewa "Me ya kawo mu palo kuma?" Miƙewa Akil yayi tare da rage volume na kira'ar da yake ji ya nufi table yana faɗin "Kila barci kuka yi a wajen kuna hira" ya kai karshen maganar tare da zama saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin, ya fara bubbuɗe takeaway ɗin dake saman table ɗin, dan ya duba wani abunci ya dace yaci.

Jiki ba kwari su Hajiya suka miƙe suka nufi bedroom nasu ransu cike da mamaki yaushe suka zo palo kuma, da kyar suke jan kafar su, har suka wuce Bedroom na su.

Shi kuwa Akil abincin sa ya fara ci yana yatsine fuska

After some minutes.

Wayar sa ta fara kara, dogon tsaki yaja kafin ya É—auki wayar ya kawo ta sai tin face nashi Abla shine sunan da ya bayyana a kan screen É—in sake jan dogon tsaki yayi kafin ya É—auki kiran ya sata a hand-free ya É—aura saman table É—in.

Daga ɗayan ɓangaren cikin sanyin murya a kayi sallama, rai a ɓace Akil yace "Wai Abla baki ganin time ne da zaki kirani yanzu?" Murya kamar zata yi kuka tace "Kayi hakuri yaya Akil wallahi tun karfe 10 nake kiran yaya Imran yaki ɗaukan waya ta" "To naji me kike so yanzu kuma?" "Kuɗi nake so yaya Akil" guntun tsaki yaja kafin yace "Za'a turo" ya kai karshen maganar tare da katse kiran yana faɗin "Da daren nan zaki kira mutun kice masa wani kuɗi gari ba zai waye bane ku baku da aiki sai takurawa mutun, ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗau wayar sa ya fice daga palon ya koma part na su.

_____________________________

*WASHINGTON DC*

Motar Micheal na gaba motar James na bin sa a baya, har suka kai babban titin da zata sada su da unguwar su, wayar James ta fara kara, a hankali yayi parking na motar sa a gefen titi dan hakan yana daga cikin dokan Romeo ya hana su ɗaukan waya suna tuƙi.

Sai da ya kashe motar san nan ya É—auki wayar tare da picking call É—in ya manna wayar a kunnen sa, Jim kaÉ—an ya cire wayar daga kunnen sa, sauri sauri ya tayar da motar tare da juya kan motar da wata mahaukaciyar gudu ya figi motar ya bar layin ya sauka daga titin ya canza hanya, yayin da shi kuma Michael ya É—auki shinfiÉ—aÉ—iyar titin gida.

Kai tsaye unguwar *Adams alley* ya wuce, ka ta faren unguwa ne mai cike da dogayen gine gine, na alfarma masu kayatarwa, kai tsaye wajen wani katon guest house ya nufa, tun bai kariso ba suka wangale masa gate É—in gidan kamar daman sun san da zuwan sa, da gudun gaske ya kutsa hancin motar cikin gidan kamar mara gaskiya, yana shiga masu gadin suka mai da gate É—in suka rufe, kai tsaye parking space ya wuce.

Yana kashe motar ya fito ya shige cikin gidan da yar gudun sa.

Still wan nan ogan nasu ne a wajen shi da wasu mutane, da alama wani abun mai muhimmanci suke tattaunawa, wucewa James yayi yaje ya zauna kusa da ogan nasu.

Cikin harshen turanci ogan nasu ya fara magana "Lokacin yayi da zamuyi Oder makamai a China dan kayan aikin mu sun yi kasa, san nan karku manta Jams kai zaka ja ragamar sayo makaman kamar dai yadda muka saba, ina son mu kai hari mumbai mu tura wa gomnatin su gargaÉ—i ta hanyar boom,
sai magana ta gaba, manyan mutane daga sama sun aiko mana da hoton wani matashin soja mai ji da karfin iko, a yanzu shi yake juya gomnati, suka ce mu kawar da shi dan babban barazane a gare su kasan cewar sa a raye, dan yana aiki da gaskiya kuma shi ci-gaba mutane yake so, mu kuma kun san bama son hakan, mun fi so muga talakawa cikin ukubar rayuwa, James na naÉ—a ka a kan wan nan aikin, kai zaka kashe sojan, dan nasan kai kaÉ—ai zaka iya, zan tura maka hoton sa a WhatsApp sai kayi kokarin cika aikin, idan ka gama aikin kashe sojan ne sai ka jagoranci sayo makamai É—in daga nan sai mu fara shirye shiryen meeting a kan cocaine da zamu shigo da su this year, sai muga container nawa ya kamata mu kawo kuma kasashe nawa ya kamata mu sayarwa"

jinjina kai James yayi tare da miƙe wa tsaye yana faɗin "I'm leaving now, saboda ina da meeting da brother na a gida, kuma bana son su fahimci abun da nake suna jirana ne" gyaɗa kai ogan nasu yayi kafin yace "Okey see you next time" sauri sauri James ya fice daga wajen, dan kar Michael yaje gida yayi ta jiran har ya fara tunanin wani abu, motar sa yaje ya shiga ya ja da gudun gaske ya bar wajen.

Yana cikin tafiya wayar sa ta ɗan yi yar kara alamar shigowar sako, sauke hannun sa ɗaya yayi daga kan staring ya ɗauki wayar yayin da ɗayan hannun nasa ke tuƙa motar,

Ganin sakon ogan sune yasa cike da zumuɗi ya buɗe sakon dan yaga menene zai kashe, a sukwane ya taka wata irinyar mahaukaciyar birki wadda tasa sai da ya buga kan sa da jikin staring motar, waro light ash eyes ɗin sa waje yayi yana kallon wayar, a fili cikin tsawa yace "GAR zan kashe kai ina never" lokaci guda yaji kan sa na sara masa kamar zata fashe, jikin sa har tsuma yake saboda ɓacin rai shiru yayi yana tunanin mafita, dan magana ta gaskiya ko wani ya gani zai cutar da GAR sai in da karfin sa ya kare, yau shi za'a cewa ya kashe GAR da kan sa, ina hakan ba zata yiwuba, gashi duk wanda ya shiga wan nan aikin nasu tofa bai isa yace zai fita ba, yana cewa zai fita to fa kashe shi suke har lahira, shi bama fitar bace a gaban sa ya za'ayi ya ceci GAR ya za'ayi ya sauyawa ogan su ra'ayin a kan su rabu da GAR, dan ya san yanayin aikin su, duk wanda a kasa hoton sa a layin wayan da za'a kashe tofa ba makawa sai sun kashe sa, sosai James ya shiga damuwa da fargaban ya za'ayi ya samu mafita.
Chapter 49 · 0% Book details