← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 126

Sashe 119

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayanai ne na duk wani abubuwan har kallan su James, bayanai ne na daga in da suke sayo makamai har in da suke sayarwa, duk wani sheɗanci da suke yana cikin wannan memory, ga kuma hotonan manya manyan jiga jigan yan ta'addan na duniya, wasu ma ba wanda ya taɓa ganin hoton su, sai sunan su na ta'addanci kawai aka sani, sunyi kaurin suna wajen ta'addancin amma James yana da hotonan su duka, kasan cewar shi Micheal ba wani karatu ya tsaya yayi ba, sai bai gane komai da ke rubuce a wajen ba, kawai kallon rubutun yake, sai dai ya shiga folder nan ya fita ya shiga wannan amma ba wani abu da ya fahimtar, ga bayanan da gomnati da kuma Romeo suke nema ruwa a jallo Michael ya same su a ɓagas amma ba abun da ya fahimtar, kallon shirme ma yakewa bayanai dan rashin karatu, ba abun da ya iya karantawa aciki.

Da yaga sai gayyan rubutu ne a wajen sai ya cire memory card É—in, kamar zai sanya É—ayan memory ma ya gani, sai ya fasa ya kwashe su ya mai dasu cikin watch É—in yana faÉ—in "Bari lion ya dawo na bashi na tambaye shi ko dai nashi ne shiya ajiye a wajen" da wannan tunanin ya mai da laptop É—in saman drawer ya kwata yana kallon sama, kamar mai tunani.

Abun da Michael bai sani ba shine É—ayan memory card É—in videos ne makare a ciki na yadda suke shirya ta'addancin su har yadda James ke canza fiska ya shiga cikin yan ta'addan yayiwa kan sa video yana cikin É—ayan memory da Michael É—in ya fasa sawa cikin laptop É—in

A ɓangaren su Romeo kuwa, shima ta kofar sirrin yabi ba tare da ya bari wani soja ya lura da fitar sa ba, dan bai son kowa yasan meke faruwa, idan ma wani abu James ke aikatawa to bai son kowa ya sani sai shi kaɗai, dan in wani yasan James na aika ta ba dai'dai ba maganar ba zata tsaya iya nan ba shiyasa yayi fitar sirri shima ko mota bai ɗauka ba.

Sai sauri James yake Romeo na biye da shi a baya ba tare da ya sani ba, dan akoi tazara mai É—an nisa a tsakanin su, saboda James ya riga Romeo fitowa.

Sai da James ya fita daga anguwar su gaba É—aya sannan ya nemi motar haya ya hau, shima Romeo karo na farko daya fara hawa motar haya, kaÉ—an kaÉ—an yacewa mai motar hayan nasa ya tafi a hankali kar James ya gansu.

Suna cikin tafiya ne wata babban mota irin mai kwantena a bayan nan, irin na É—aukan kaya tazo a guje saura kaÉ—an tabi ba kan motar su Romeo, kasan cewar hanyar akoi fitullun kan hanya masu bala'i haske, sun haske ko ina hakan ya bawa Romeo damar ganin motar da kyau, kasa kasa yace da driver motar hayan ya dakatar da mota, dan bai yarda da wancan motar da ta wuce su ba dan yadda take wannan uban gudu alamar rashin gaskiya ne, gashi kuma yana son bin bayan James, amma yafi son bin wancan motar saboda yasan ko ba komai dole James zai dawo gida kuma in ya dawo dole ya faÉ—a masa in da yaje, ita kuma motar idan ya barta ta tafi ba lallai ya sake ganin taba, dan haka sai yace da driver motar hayan daya juya subi wancan motar.

Ba musu driver ya juya duk da bai san waye ya É—auko a cikin taxi É—in nasa ba, sosai wancan motar ke tsala gudu a kan hanya duk da girman ta, hakan yasa Romeo ya kara zargin motar sosai da sosai.

Dai dai wani check point na kan hanya wasu yan sanda dake tsayawa a wajen suka dakatar da motar, shima Romeo dakatar da mai taxi ɗin sa yayi ya fito yace wa mai taxi ɗin "I'm coming" ya nufi wajen motar can, dai dai lokacin driver motar ya bawa ɗan sandan cin hanci, ba tare da yan sandan sun binciki motar ba sukace motar ta wuce dan sun karɓi cin hanci.

Driver ya koma cikin motar yana kokarin tada motar Romeo bai yi wata wata ba ya fisgo driver motar yayi wurgi da shi waje, cikin sauri sauran dake cikin gaban motar suka fito, su biyu ne, da ka gansu kaga rikakkun yan daba, ga jikin sunan duk tabon shatin yan kan wuka,

Saboda jacket da ya sa ya kuma saka hular a hansa ga face mask da glass a fiskar sa gashi dare ne hakan yasa har yan sandan dake wajen basu gane shi ba.

A guje wayan nan yan daba biyun sukayi kan sa da nufin dukan sa, duk kan su duka É—ai'É—ai ya musu suka zube kasa kamar wasu kayan wanki

Abun ku da rashin gaskiya irin na duniyar yanzu, sai yan sandan dake wajen suka ciro bindigu suka saita Romeo da shi wai ya É—aga hannu sama ko su harbesa a kan me zai daki wayan nan mutane, saboda sun basu cin hanci yasa suke wannan hargagin, hakan da yan sandan sukawa Romeo yasa ya kara zargin su ya kara sawa a ransa kenan kullun motar tana wuce suna bata hanya kenan.

Bai É—aga hannun sa ba sai ya juyo yana kallon yan sandan, sun dage zasu harbe sa idan bai É—aga hannu ba, a hankali ya É—ago kafar sa ya fara tinkarar su, sai kokarin harbin sa suke amma bindigar taki harbi saboda tsorata da sukayi jikin su nata kerma sun kasa danna kunamar bindigar da kyau, É—aya daga cikin sune ya kira wayar over over akan a karo musu yan sanda ga É—an ta'adda sun kama yana kokarin yi musu illah.

Wannan danganta Romeo da ɗan ta'adda da sukayi hakan ya ɓata masa rai a fusace ya kwace bindugun hannun su, ya musu dukan tsiya, wadda ya sasu sumewa a wajen, da farko bai yi niyar dukan su ba, a matsayin su na jami'an tsaron yaso ya sa a cire musu kakin sune ma'ana a kore su daga aiki sannan a basu hukunci dan sune ɓata garin tun da su suke karɓan cin hanci su bar masu laifi su gudu, amma danganta shi da ɗan ta'adda da sukayi yasa ransa ya ɓaci ya musu dukan kawo wuka duk ya fashe musu fuska, shi kuwa driver taxi daya kawo Romeo tuni ya juya kan motar sa ya gudu, yaga Romeo na dukan yan daban nan kar ya shafesa dan shima bai san wa ya ɗauko a taxi ɗin nasa ba, shima cewa yake ko dai ɗan ta'adda ya ɗauko ne.

Daman yan sanda uku ne a wajen lilis Romeo ya musu da duka, sannan ya É—auki bindigar É—aya daga cikin su yana kokarin har bin kwaÉ—on da aka rufe kwantenan bayan motar dan yaga me suka É—auko suke wannan gudu haka

bai kai ga harbin kwantenan ba sai yaji diran motoncin yan sanda, wanda wancan É—an sandan ya kira office nasu a kan a turo yan sanda ga É—an ta'adda sun kama.

Zubawa motoncin yan sandan ido yayi ta cikin black glass nasa yana kallon su, motoci uku ne, suna iso wajen sukayi parking suka diro kasa suka kewaye sa da bindigun su, suna faÉ—in "you are under arrest keep this gun and raise up your hand" ka ajiye bindigar nan ka É—aga hannun ka sama"

shiru ya musu kamar bai ji me suka ce ba, abun ma haushi ya bashi, hannu yasa a aljihun sa, a sukwane yan sandan suka ja baya a tunanin su boom ko wani makamin zai ciro, haushi ma yaji kamar ya harbe yan sandan duka su mut dan a cewar sa basu da ammafa suna yan sanda suna da wannan tsoro haka, daga sa hannu a aljihun sa sun ja baya

Wayar sa ya ciro suna ta ce masa ya ajiye wayar nan amma kamar ba da shi suke ba, latsa wayar nasa yayi na É—an lokaci kafin ya mai da aljihun sa ya juya ya saita kwaÉ—on dake jikin kwantenan zai harba kenan É—aya daga cikin yan sandan ya harbe bindigar hannun sa, bindigar ta faÉ—i kasa shi kuma bullet É—in ta É—an kuskure hannun sa, a fusace ya juyo yana kallon wanda yayi harbin

Kwata kwata baya jin duka mutane yau kuma baya jin yin kisa, amma suna kure sa,
tsawa yan sandan suka daga masa wai ya zube a kan gwiwowin sa, ran sa ya fara ɓaci yanzu, yana kokarin takawa ya tinkare su dan ya musu dukan mutuwa kenan sai wajen gaba ɗaya ya karaɗe da jiniyan jiga jigan motoncin sojoji masu numfashi kai daga jin jiniyar ma kasan ba sojojin wasa ne ke tunkarar wajen ba, dakata wa yayi dan shi ya kirasu a kan suzo su tafi da gaba ɗaya yan sandan nan, dan yana da aiki a kan James sosai so baya son ransa ya ɓaci yau, yana son cikin nitsuwa idan James ya dawo suyi magana shiyasa ya kira sojojin.

A ɓangaren yan sandan kuwa sai murna suke wai an turo musu sojoji kila manyan su sun samu labarin babban ɗan ta'adda ne suka kama shiyasa suka haɗa musu da sojoji, sai dai abun da ya ɗaure musu kai, wannan jiniyar na motar jiga jigan sojojin kasan ne, kenan manya manyan sojoji kamar wayan nan zasu iya kawo wa kananan yan sanda kamar su ɗauki, abun ya basu mamaki amma dai sun zuba ido suna jiran suga me ke shirin faruwa.

Jibga jibgan motoncin masu numfashi shabiyu ne suka iso wajen, wasu jibga jibgan sojojin masu jini a jika, fararen American tas da su, gasu da kirar karfi sun samu horo mai kyau, fuskokin nan nasu kamar hadari babu wasa a É—aure take tamau ba su san menene dariya ba, ganin wayan nan sojojin kawai ya isa ya sa rundunar mutane zuciyar su ya buga su mutu saboda tsoro.
Chapter 119 · 0% Book details