← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 126

Sashe 113

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita waje yace "Allah ya isa na munafukai yar 2k na ya tafi ni ban ci abinci ba, kuma bala'i yinwa nake ji wlh, gashi 500 ya ragemin a aljihuna, wayyo Allah rayuwar tiktok bakiyi ba nazo nayi video mai kyau ina cin lafiyayyen abinci, yanzu gashi na kare ni ba ga video ba, ban kuma ci abinci ba ba kuɗi ba ga kuma yinwa, kai kwata kwata rayuwar karya dai baiyi ba, dole na tuba na koma ga Allah, in godewa Allah da arzikin da yamin, daga yau a gidan ubana zan rinƙa video sai dai followas na su zaje ni ko su daina following nawa ina dalili in wuni ina fama da buga katako duk ƙusa tayi ta fasa mana hannun da kyar muke samu da wuya mu haɗa kujera, oga ya sallame mu naje na karar da kuɗin a yawon restaurant da hotel dan yin video fake life" kamar zararre haka ya tsaya yayi ta suruntan sa a bakin gate ɗin restaurant ɗin, har ya gaji ya kama kan sa ya wuce yana jan tsaki.

A ɓangaren Ibraheem kuwa ba karamin daɗin yaji ba karɓan musu kuɗin da Jehan tayi wajen mutumin nan, sai dai kuma ta wani ɓangaren yana tsorace karfa da gaske mutumin nan zai iya sawa a rufe musu restaurant ɗin su, dan ɗan Adam ba abun renawa bane ta iya yiwu wa yana da hanyar da zai iya yin hakan.

Sai tunai Ibraheem yake bai ankara ba sai yaga Jehan ta nufi hanyar fita daga restaurant É—in, cikin sauri yace "Ke ina zakije?" Ko kallon in da yake ba tayi ba bare ya sa ran zata amsa masa ta wuce abun ta ta fice daga restaurant É—in, baki sake Ibraheem ya bita da kallo yana tunanin yadda zai yi da ita.

Jehan kenan mai abun ban mamaki ita da kan ta ta tsarawa kan ta lokacin zuwa aiki da lokacin tashi kamar restaurant É—in nata ne ko na daddyn ta.

Tana fita ta tari abun hawa ta hau zuwa anguwar su, dan tace sai taje gidan su taci uban Alhajin nan sannan ta dawo asibiti ta duba jikin mum, ba karamin haushin taji ba abun da Alhajin nan yayiwa Hanan ji take kamar idan ta ganshi ta shaƙe ɗan banza sai ya mutu, yau ta ɗaura niyar duk wanda ya dakatar da ita wajen ciwa wannan Alhajin mutunci tofa bazata ɗaga masa kafa ba, sai ta haɗe da shi duk taci uban su.

Tun daga nesa take hango jama'a sun É—an taru a kofar gidan su Sadiq wato gidan su na yanzu

Tsabar sauri irin nata gani take mai mashin ɗin baya sauri dan haka sai tace ya sauke ta a wajen ta karisa da kafar ta zata fi sauri, yana sauke ta ta miƙa masa 500 bata tsaya ta karɓi chanji ba ta wuce, yana ce mata ga canjin ki amma ina bata ji ba, hankalin ta yayi wajen jama'ar nan dan tana zaton su Sadiq ke rikici da Alhajin.

Ai kuwa zaton ta gaskiya ne hakan ne, Sadiq ne yake rikici da Alhajin da kuma baban sa, ga Hanan zaune saman dakali kofar gid tana kuka, jama'a suna ta bawa baban Sadiq hakuri, sai zuba ruwan bala'i baban Sadiq É—in yake wai bai isa ya yiwa Æ´aÆ´an sa magana ba, wannan mijin Hanan ne ya bashi auren ta zai É—auke ta suje duba kaya a shopping Sadiq yace zai hana wlh ba zata saku ba, haka baban Sadiq ke ta surfa uban bala'i, shi kuma Sadiq ya kasa faÉ—in abun da Alhajin ke nufi da Hanan dan ya rufa wa kanwar sa asiri baya son kowa yasan abun da Alhajin ya mata jiya da daddare.

Shikuwa Alhajin babu kunya ba tsoron Allah ya tsaya ya kafe ya tsare zai tafi da Hanan suje sayayyar kayan auren su, a yadda yake faÉ—awa jama'a kenan

Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞

💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)

*GargarÉ—i*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 38-39

Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa, cike da damuwa da tashin hankali ya É—ago kai ya fara bata labarin abun da yake faru, baban sa ya tara musu jama'a wai basa jin maganar sa mijin Hanan zai fita da ita suje sayayya shi Sadiq É—in ya hana, É—agowa Jehan tayi ta kalli Alhajin.

Kara zaro ido tayi tana kallon sa tabbas tasan wannan fuskar amma ai na ta mance, shiru tayi tana tunanin ai na ta san wannan fuskar

Ganin ta zubawa Alhajin ido tana kallon sa tayi shiru ne yasa Sadiq yace "Jehan lafiya" dago da kallon ta kan Sadiq É—in tayi tana girgiza kai alamar babu komai, shesshekar kukan hakan yasa ta juyo ta kalle ta

A takaice tace "Hanan tashi ki shiga gida" ƙin tashi Hanan tayi dan tana tsoron baban ta, Jehan ta fahinci abun da Hanan ɗin ke nufi, dan haka sai ta dawo da kallon ta kan baban Sadiq wadda yayi shiru saboda zuwan Jehan, yana tsoron aljanun Jehan na dare shiyasa yayi shiru

"Kace mata ta shiga gida" Jehan ta faÉ—a tana kallon baban Sadiq É—in, ba musu baban Sadiq yace "Tashi ki shiga cikin gida Hanan" da gudu Hanan ta tashi ta shige cikin gida, dan dama kamar a kan kaya take zaune.

"Baba ya zaka ce ta shiga gida ban gane ba" cewar Alhajin, shiru Jehan tayi tana kallon su tana son taga ya zasu kare

Cikin girmamawa baban Sadiq yace "Kayi hakuri Alhajin wani lokaci zaku je yanzu dai ka kyale ta" da sauri Alhajin yace "A'a baba ni yau nake son muje, yau nayi niyya" satar kallon Jehan baban Sadiq yayi kafin yace "Dan Allah kayi hakuri Alhaji" girgiza kai Alhajin yayi yana faÉ—in "Ina ba zai yiwa ba gaskiya kawai ta fito mu tafi" sai hakuri baban Sadiq ke bashi amma Alhajin nan ya murje ido yace sam bai yarda ba dole Hanan ta fito su tafi.

Da dai Alhajin yaga da gaske baban Sadiq ba zai kira Hanan tazo su tafi ba, sai ya fara masifa yana faɗin baban Sadiq ya karɓe masa kuɗin sa akan ya bashi Auren Hanan, to wlh ba zai yarda ba dole yau Hanan ta fito su tafi,

Yadda zaka gane da wata manufa a ran sa game da Hanan É—in shiyasa ya dage a kan tazo su tafi.

"Hanan ba zata fito ba kuma daga yau ma karka sake zuwa wajen Hanan idan ba haka ba duk abun da muka maka kai ka ja ma kan ka" cewar DPO wato Jehan, tayi maganar cikin kwanciyar hankali, kallon tsab Alhajin ya mata kafin yace "Idan Hanan ba zata zo ba ke zaki zo kenan? Dan naga kin fi Hanan ɗin hankali zaki fita iya zaɓen kayan sai mu tafi dake kawai a bar hanan ɗin" karo na farko da Jehan ta saki murmushi a rayuwar ta na yanzu, dan ita ko lokacin da suke tare da daddy ba ta murmushi bare dariya haka face nata yake a ɗaure tamau.

Matsowa ta ɗan yi gaba kaɗan kasa kasa tace "Anya zaka iya fita da Jehan kuwa?" Tayi maganar tana murmushi, shiru Alhajin ya ɗan yi kafin yace "Amma ke kin san me kika faɗa kuwa" kashe masa ido ɗaya tayi kafin tace "Eh niko na san me nake faɗe cewa nayi mu tafi, idan zaka iya fita da ni, Jehan a shirye take" Tashin sense, shiru Alhajin yayi Jehan ta jefa sa cikin tunani, "anya wannan yarinya lafiyar ta kuwa, kai ina ga bata san me na shirya a tafiyar bane shiyasa amma bari na gwada ɗaukan ta muje in gani, idan bata san me na shirya ba, na samu ɓagas daman tafi Hanan komai da komai zan more tsuntsu daga sama gasashen" duk Wannan zancen a zuciyar sa yake sakawa.

Yana cikin zancen zucin nasa ne muryan Jehan ta katse shi da cewa "Ko dai ka manta baka kama hotel ɗin bane? Au sorry na manta fa ashe gidan ka zamu je ba hotel ba, amma ina son sani wani abu ɗaya kafin mu tafi, a gidan naka babu kowa ko, ma'ana iyayen ka ba a nan suke ba ko? Dan ban cika son hayani ya ba" tashin hankali, wani irin dukan uku uku gaban Alhajin nan yayi, tunani ya kara shiga "Anya wannan yarinyar mutunce kuwa? Ita da kan ta ta kawo kan ta, to gaskiya ba lafiya take ba, kila tana da wani ciwon dai, dan mace mai lafiya kuma cikakkiyar mace kamar wannan ba zata miƙa kan ta haka ba, gata da ka ganta kaga cikakkiyar mace mai addini to meke shirin faruwa ne"

Su Sadiq dai yau suna ganin ikon Allah

Ganin yayi shiru yasa Jehan ta kara matsowa kusa da shi, kasa kasa tace "Farooq Salahuddeen Abubakar, right?" Zaro ido waje yayi yana kallon ta da mamaki ai ina ta san shi
Chapter 113 · 0% Book details