← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 126

Sashe 52

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama yayi gefen gadon yana faÉ—in "My Jelly har yanzu baki gaji da buga game É—in bane?" A sukwane ta É—ago kai da alama bata san da shigowar sa ba, ture system É—in tayi gefe guda ta rarrafo ta faÉ—a jikin sa tana dariya, shafa kan ta yayi cike da so da kaunar ta, yana kokarin yin magana wayar sa ta fara kara

Cikin sa ya ciro wayar daga aljihu sa, dum dum gaban sa ya bada dukan uku uku ganin sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, Baban Muneer cike da damuwa ya ɗauki kiran tare da kwantar da Jelly saman gadon ya miƙe ya nufi waje

Murya na rawa yace "Hello" dogon tsaki baban Muneer yaja kafin yace "Naji duk abun da ya faru wai gomnati sun yi rejected na later da ka tura ko? To ai ba damuwa in sun san wata basu san wata ba, ka buɗe kunnen ka da kyau ka saurare abun da zan faɗa maka, ina son duk wani abun da zaku saya na aiki, ka raba kuɗin biyu ka bani rabi, ma'ana idan zaku saya abun 10k sai ku sayi local na 5k sai ka turomin ragowar 5k ɗin a Account na, na san duk wani abun da zaku saya a wajen aikin nan kuɗin original gwamnati suka baku, to kai kuma da fake ko in ce local zaka musu amfani da shi, sai ka rinƙa turomin sauran kuɗin, kai engineer ne nima engineer ne nasan komai so baka isa ka cuceni ba kana jina ko?" da kyar daddy ya iya buɗe baki yace "Dan Allah Baban Muneer kayi hakuri wan nan abun da kake son nayi zalunci da ha inci ne kuma zan zubar da nutunci na da kuma darajar company ni nane, kowa yasan ni mutumin kirki ne dan girman Allah karka sa na zama maha inci karka zubar min da mutunci" ya kai karshen maganar hawaye na bin kuncin sa, bushewa da dariyar shakiyanci baban Muneer yayi

sai da yayi dariyar mai isar sa san nan ya tsagaita, cike da iya shege ya fara magana "Yanzu maik har wani mutunci ne da kai? Ko ka manta abun da ka aika tane? Kai fa mazina ci ne number É—aya ko shima ka manta ne? To in ka manta na tuna maka, wlh ko kayi abun da nace maka ko kuma ka tsinci video ka a media" yana kai karshen maganar ya katse kiran, dafe kai daddy yayi yana mai dana sanin zuwan sa duniya, wan nan masifa da me tayi kama, yanzu da hankalin sa da ilimin sa na addini zai cuci mutane, sun yarda da shi su bashi aiki a kan ya sayi kaya masu quality amma dan zalunci baban Muneer zai sanya shi cin amana zai sanya shi sayan fake kaya, why baban Muneer, sosai daddy ya shiga damuwa da tashin hankali mai tsanani, a wajen zaune saman sofa barcin wahala ya É—auke sa, dan kwana biyu kenan baya samun barci tunani da damuwa sun hana sa rintsawa, ita ma Jelly barcin ne ya yi awon gaba da ita rungume da system a hannu tana latsawa.

________________________________

*ABUJA*

Kwance Rimsha take saman sofa 3 seater a palon su na kasa, ta kurawa wayar ta wan nan dara daran sleeping eyes É—in nata tayi shiru tana kallon hoton GAR sanye da face mask a face nashi, shi kullun cikin face mask yake ba wanda zai ce ga kalar face na shi na asali, ko a gida bai cika cire face mask na shin ba, duk wanda zai baka hoton sa to cikin face mask za ka ga face nashi

Kamar wadda a ka muntsina ta miƙe da sauri ta haye sama, jim kaɗan ta dawo hannun ta riƙe da cardboard paper da kayan design irin su color da pencil da dai sauran su

Saman sofa table ta É—aura ta karawa wayar ta hasken sa ta kurawa hoton GAR ido, tana kallo tana zanawa, ta dage yau sai ta cire face mask É—in nan nasa da design nata dan taga asalin face na shi

A wan nan halin gwaggo ta fito ta same ta, zama tayi gefen ta tana faɗin "Rimsha anya ba zamu dakatar da ke daga kallon wan nan Christan ba kuwa? Ɗago dara daran kyawawan sleeping eyes nata tayi ta kalli gwaggo da kyau kafin tace "Gwaggo me ya muku kuma?" Girgiza kai gwaggo tayi tana faɗin "A'a Rimsha abun ne naga ya fara yawa kar abun yazo ya zame miki matsala kin san kwakwalwan yaro da riƙe abu" shiru Rimsha tayi ta ci-gaba da zana GAR ɗin ta, kamar daga sama sukaji murya daddy yana faɗin "Nima nayi wan nan tunani, kaunar da Siha ke wa wan nan mutumin yayi yawa kar yazamo mata wani matsalar dan haka dole a dai na kunna shi a gidan nan daga yau na dakatar" a razane Rimsha ta ɗago dara daran sleeping eyes nata ta kalli daddy, yayin da shi ma ita yake kallo, a hankali tayi kasa da kan ta kamar zata yi kuka, ta ci-gaba da zanen ta

wucewa daddy yayi ya nufi waje yana faɗin "Aunty Aisha zan je meeting na yan takara shugaban kasa na zaɓe mai zuwa" da fara'a gwaggo tace "Allah ta bada Sa'a" Amin ya amsa da shi san nan ya fice

Rimsha na tsaka da zanen ta bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata a idon ta ba, sai dai kawai taga hawayen a kan cardboard paper É—in suna zuba, cikin sauri ta sanya hannu a firskar ta dan taji da gasken kuka take, jin da gaske hawaye ne yasa tayi saurin gogewa ta ci-gaba da design nata, nan take taji kan ta na sara mata kamar zai fashe, idan ta tuna daddy yace kar a sake kallon GAR sai taji kan ta ya kara sara mata da karfi kamar zai fashe, a haka ta jure ta ci-gaba da zanen yayin da ita kuma Gwaggo ta kafe Tv da idon ta, tana kallon Arewa 24,

Sosai Rimsha ta kawata kyan GAR a ranta kuma haka ta fito da shi fili ta zana a cardboard paper ta, wow gashi daman ta kware a fannin zanen, abun ba'a cewa komai, zanen yayi kyau over ta tsara kyan sa iya son ranta har da sanya masa pink lips, da pink color na zane ta zana shi ya fita kamar ki kirashi ya amsa, nan take murmushi ya kubce mata ta kura masa ido cikin ranta tana kawata kayan sa yafi haka

Babu ko sallama Jehan ta shigo palon ta fito daga wajen motsa jiki, sanye take cikin wando skin tight baki da riga irin na yan kwallo shi ma baki, sai zufa take haÉ—awa da alama ta motsa jiki sosai, ko kallon in da su gwaggo suke ba tayi ba ta wuce zata haura sama, cikin sauri gwaggo tace

"Jehan ke dai ba zaki dai na wan nan abin ba ko? Wai ma da kika dage kike wan nan shirmen waye ya faɗa miki a gidan nan a koi wan da zai kyaleki kiyi aikin ɗan sandan?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Wai ke gwaggo ina ruwan ki da ni? To sai ki hanani yin abun da nake so ɗin mu gani, aikin ɗan sanda nake so ko kuma aikin jarida, kai ni nafi son aikin ɗan sandan ma kuma zanga wanda zai hana ni, Kinga gwaggo wlh ki fita sabgata idan ba haka ba ina fara aiki kece mutun na farko da zan fara sanyawa a cell in ce kina dillancin kwayoyin maye kuma ba wanda ya isa ya fitar da ke dan har kwayar sai na nemo na sanya miki cikin jaka dan a ji daɗin kama ki" waro ido waje gwaggo tayi tana faɗin "Sabon topic yau kuma, tohh a ina kuma kika koyo wan nan sabon topic ɗin kuma yau? A ba shakka dole ne kiyi aikin ɗan sanda, tun yanzu kin iya shirya sharri kiri kiri a'a Allah ya bada Sa'a Allah baki hakuri ni Aishatu jeki yi wanka da yamma ma ki kara motsa jiki abun ki daga nan sai koyan harɓi, daga nan sai kaki dan duk wani muna furci na yan sanda kam kin iya shi ba sai kin koya ba kai tsaye kawai zaki shiga aiki" sai murmushin dole Rimsha ke musu dan gwaggo da Jehan basu rabuwa kuma basu haɗuwa

Tsaki Jehan taja ta nufi sama tana faɗin "Ai na zaci zaki yi wata magana ne da kin ga yadda ake tsiya kuwa" shiru gwaggo tayi dan tasan halin Jehan ba sauki yanzu sai ta sa hawan jinin ta ya tashi, miƙewa Rimsha tayi tana faɗin "Gwaggo let me go and sleep I'm feeling headache" zaro ido waje Gwaggo tayi tare da jawo ta jikin ta tana faɗin "Sorry Allah ya baki lafiya" ta kai karshen maganar tare da manna mata kiss a goshi, kakalo murmushi Rimsha tayi kafin ta miƙe daga jikin gwaggo ta haura sama ta nufi bedroom nasu

Ko da ta shiga bedroom ɗin nasu Jehan na toilet tana wanka, hayewa saman gadon ta tayi ta kwanta ta shige lallausan bargon ta ta rufe jikin ta dukka har kan ta, san nan ta rungumi zanen GAR da tayi ta fara ruwan hawaye kasa kasa tana faɗin "Me yasa daddy zaka hana ni kallon sa?" Sosai take hawaye wani na bin wani, nan take zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ga bala'i ciwon kai mai tsanani, a haka barcin wahala ya ɗauke ta,

koda Jehan ta fito daga toilet, bata ma lura sa Rimsha É—in ba, ta wuce taje ta shirya cikin jallabiya irin na shan iska nan Black colar, ta saki gashi har baya san nan ya haye saman gadon ta, tajawo wayar ta ta shiga latsawa tana murmushi tana addu'ar Allah ya cika mata burin ta na zama yar sanda.

_______________________________

*KADUNA*

03:00 pm

Gaba É—aya su Abbi suna zaune a Palo Irfan ya gama shirye shiryen tafiya Uk on Monday zai wuce, sai murna yake while su Aafia na taya sa, sai hira suke cike da kaunar juna, kowan nan su fuskar sa É—auke da murmushi.
Chapter 52 · 0% Book details