← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 126

Sashe 78

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu ko tsoro a idon Rufee ta fara masa bayani a kan abun da ya kawo ta "Baba daman na zone ne yau ma a kan wacan Aafia" da muryan mara daɗin ji kamar an tada injin niƙa baban yace "Me kuma ya faru? Bata baki kuɗin ne?" Girgiza kai Rufee tayi tana faɗin "A'a tana bani kuɗi ina so ne yanzu a juyamin tunanin ta tadawo sai abun da nace mata shi zatayi dan gaskiya tana kawo min cikas a lamurana, akoi wani Alhajin da yace zai bani 10 millon idan har na kawo masa ita amma ba yadda ban yi da ita ba taki yarda ta masa magana ma bare kuma har ta bishi ta biya masa bukatar sa, ni kuma na samu abun da nake so" shekewa da dariya baba yayi kafin yace "Karki damu kin san aiki na ai yanzu dai ki zube kuɗin ni kuma zan dawo miki da Aafia cikin tafin hannun ki" washe baki Rufee tayi kafin tace "Yauwa baba kuɗi kam yanzu ma kuwa zan zube maka su dan jiya 100k Aafia ta bani" washe baki shima baban yayi, buɗe jaka Rufee tayi ta ciro masa kuɗi ta ajiye masa a gaban sa, tana ajiye kuɗin baban ya ɓace da shi da kuɗin, dariya tayi ta miƙe ta sauƙo kasa daga saman dutsen ta nufi hanyar da tabi tazo sai dariya take tana jin daɗi tana faɗin "Aafia kenan idan kin san wata ai baki san wata ba haka kawai zaki hana manya masu kuɗi su bani kuɗi ga dama na samu amma kina neman hana ni, shegiya gaki da farinjini kamar me, ko wani Alhaji sai yace sai ke yake so, ke kuma kina wulakan tasu to Wlh baki isa ba sai na mai daki tantiriyar yar duniya ki bi maza a guje sannan ki bi kayan maye a guje, kafin na shigo gidan uban ki a matsayin mata kin riga da kin bi duniya kin lalace" kamar wata zararriya haka ta kutsa cikin grasses nan ta wuce sai surutu take ita kaɗai.

*KADUNA*

Kwance saman gadon majinyata Jelly take jikin ta na sanye da kayan majinyata, an mata É—in ki a kan ta duk in da taji ciwo an É—inke mata an sanya mata bandeji, a takaice dai ta samu kulawa sosai sai dai bata motsi, har yanzu tana sume, ita kuma Hajiyar da ta bugeta tana zaune a gefen ta ta buga uban tagumi da alama ta shiga damuwa sosai da sosai, dan sai haÉ—a zufa ma take duk da Ac dake É—akin hospital É—in.

*KATSINA*

Tun jiya sai yau su Jehan suka samu likita ya zo ya duba mum, nan ya gaya musu tashin hankali da yafi karfin tunanin gwaggo, dan da farko ma likitan yaki yarda ya faɗa musu yace su turo masa namiji, sai da gwaggo ta kafe tace basu da kowa dan haka ya faɗa musu kawai, shine ya kira gwaggo office na sa nan yake faɗa mata abun da kan ta ya kasa ɗauka, mum na ɗauke da wani babban ciwo a zuciyar ta wadda dole a mata aiki cikin gaggawa idan ba haka ba zata iya mutuwa, duk ba shine damuwar ba, babban damuwar a nan shi ne dole waje za'a fitar da ita dan wannan asibitin basu da kayan aikin da zasu mata aikin, wannan kwararrun doctors ake buƙata, har wani duhu duhu gwaggo take gani a idon ta, ita damuwar ta ɗaya shine samun lafiyar mum kuɗin ba damuwa bane dan mum tana da manya manyan gwala-gwalai da idan a ka haɗa a ka sayar a kalla zasu kai 10 millon so kuɗi bai dame taɓa, lafiyar mum shi ne a gaban ta.

Da sauri ta fito daga office ɗin dr Jehan na tambayar ta amma ina bata bi ta kam kowa ba ta nufi hanyar fita hospital ɗin dan taje gida, har ta kai bakin gate ɗin hospital ɗin sai kuma ta juyo tayiwa Sadiq da yazo tun safe dan duba jikin mum, alama da hannu gwaggo ta masa a kan yazo su tafi dan bata san hanya ba, a tare Sadiq da Jehan suka miƙe sukabi gwaggo, idon Jehan ya kunbura sosai saboda kukan da ta sha duk ta sauya kamar ba ita ba.

Tare suka wuce gida da mai a daidaita sahu, suna shigowa gida kai tsaye É—akin mum gwaggo ta nufa dan ta É—auko gwala-gwalan mum suje su sayar su san yadda zasu yi su fitar da mum kasar waje a mata aiki da wuri.

Gwaggo na shiga É—akin mum taga ikon Allah nan taga ba komai duk wani abu mai amfani an kwashe har da wayan mum, ba abun da aka barmusu sai kayan sawan su, kamar mahaukaciya haka gwaggo ta fito waje tana ihu, da sauri Jehan da ta tsaya ta jingunu da bango ta taho ta tare gwaggo tana faÉ—in "Gwaggo me ya faru menene?" shima dai Sadiq abun da yake tambaya kenan, me ya faru

kamar karamar yarinya haka gwaggo ke kuka tana faÉ—in "Shikenan nan komai ya kare sun kwashe komai sun kashe mu Jehan babu komai innalillahi wa inna ilaihir shikenan yanzu muna ji muna gani zamu rasa Maryam bayan mum rasa Nawazudden ga Rimsha babu ita ya Allah ka É—auki rayuwa ta kafin ka É—auki na Maryam" tashin hankali kalma É—aya Jehan ta kasa furtawa dan ta rasa ta ina zata fara kuka kawai take, shi ma Sadiq kuka yake musu sosai yana addu'ar Allah ya kawo musu mafita.

Da kyar ya iya saita kukan sa yace "Gwaggo meke faruwa ne? Me mum take bukata yasa kuke neman kuɗi?" Cikin kuka Gwaggo tace "Ya zama dole na faɗa muku dan ina ji a jikina zan riga Maryam mutuwa, to ko na mutu kuyi kokarin wajen ganin kun taimaki Maryam idan kuma Allah yasa itama kwanan ta ya kare to Sadiq ga amanar Jehan ka riƙe ta kamar kanwar ka" nan gwaggo ta basu labarin abun da ke damun mum san nan da kuɗin da suke bukata almost 5 million dan su fita kasar waje ai wa mum aiki, ta kai karshen maganar da kyar saboda kuka da ya ci karfin ta, sosai Sadiq ke hawaye yayin da ita kuwa Jehan hawayen idon ta suka tsaya cak idon ta ya bushe gaba ɗaya taji bata bukatar ci-gaba da kuka kuma dan komai ya kare mata me zata yiwa kuka kuma, komawa tayi duk tsabta irin nata haka yau tayi zaman yan bori a kasa ta jingina kan ta da bayan gwaggo ta ɗaga kai sama kamar mai tunani, while ita kuwa gwaggo sai hawaye take haka shi ma Sadiq.

💞WASHINGTON DC💞

Yana yin garin gwanin ban sha'awa a hankali iska ke kaÉ—awa mai nishaÉ—an tar da zukatan masoya, sanyi Ac ne ya ratsa shi kasan cewar Romeo ya kara gudun Ac dan su tashi daga barcin, ya san cewa dukkan su basa son sanyi idan sanyi yayi musu yawa basa iya barci shi yasa ya kara gudun Ac.

A hankali Michael ya waro brown eyes nashi masu ɗauke da barci, kai tsaye kan kyakkyawar face ɗin Romeo suka sauka, yana zaune a saman bedside drawer jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya cirota daga letar ta saboda tsabtar ta, bai ɗaure kyakkyawan dark black curly hair sa ba ya bar shi ya kwanta masa har baya while wannan guntu na gaban yana nan a gaban goshin sa, soft skin na sa nan sai kyalli take a kwance luf taji hutu, sai wani fitinanniyar kamshin dake tashi a jikin sa, lallausan red lips na san nan idan ka gani kace ya sanya lips balm saboda kyalli da yake kuma yayi red sosai, kyawawan hannun sa na sanye cikin hand gloves masu kyau yana riƙe da allura yana kokarin haɗawa.

Zubawa Michael wayan nan dara daran blue eyes ɗin nasa yayi yana kallon sa, ganin abun dake hannun sa yasa Michael miƙewa zaune yana kwaɓe fuska yana turo ɗan karamin bakin nan nasa,
da ya kalla alluran sa Romeo ke haɗawa, sai yayi sauri ya diro kasa daga saman gadon yana kokarin guduwa, gently Romeo yasa hannu ya riƙo hannun sa, turo baki Michael yayi kafin yace "I want to go and ease my self" lumshe ido Romeo yayi kafin ya buɗe su a kan face ɗin James dake ɗan motsi yana son farkawa "No, do it here" ya furta in a cool voice kara turo baki Michael yayi har ga Allah baya son alluran nan amma duk lokacin da aka ɓata masa rai ko wani abun da badaɗi ya faru sai Romeo ya masa wannan alluran, kamar zai yi kuka ya koma ya zauna yana jin haushi dan dai ba yadda zai yi ne bai isa yace wa Romeo baya so ba, da James ne da ba abun da zai sa shi ya tsaya ya masa.

Shi kuwa Romeo ko a jikin sa ya ya ɗaure hannun ya nemi jijiya ya masa alluran san nan ya miƙe ya nufi dressing room na shi ya bar Michael rike da wajen da a ka masa alluran yana turo ɗan karamin bakin sa kamar biro.

Dai dai lokacin James ya farka saboda sanyin Ac da ya masa yawa, kallo ɗaya yayiwa Michael ya gane me ya faru dama kuma yasan da kwanan zancen alluran, dan haka sai ya miƙe yana tsokanar Michael ya fice daga bedroom ɗin ya nufi palon kasa.

Nan ya isko daddy da Tga suna gardama a kan daddy ya dage sai yaje hospital dan an kirasa a waya yar abokin sa tasha poison tana bukatar taimakon gaggawa, gashi kuma shi daddy Romeo ya hana shi zuwa aiki, yanzu ma ya rikice ne yana tsoron kar yarinyar ta mutu sannan kuma bai san Romeo ya dawo ba, dan fitan Romeo kawai ya gani bai ga dawowan sa ba lokacin yayi barci shi yasa yace zai je wajen aikin.
Chapter 78 · 0% Book details